OMAR KO FAROOQ?

66-67

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓ 



    66_67



"Qarshe imaan rufe idon ta tayi tana sauraron abunda zai biyo baya. "Omar kuwa kunnen ta ya kama auchhh ta furta, da daya hannun y buge mata baki, sannan yace uban waye ya baki izinin shigomin room? Imaan tayi raurau bayan ta bude idon ta dan azaba, tace Mummy CE ta aikoni, omar yace shine ke baki iya sallama ba? Imaan tace Allah nayi kusan 3tyms. "Omar ya jijjiga kai bayan ya sake mata kunne yace daga yau idan bakiji na amsa ba ki koma kice bcci nake, imaan ta zaro ido waje tace ya omar qarya ba kyau...bata qarasa ba ta kama kumatun ta yace nine me karyar? Imaan ta jijjiga kai. Omar yace toh kiyi abinda nace, imaan tace toh duk hawaye ya cika mata ido. "Omar yace matukar naga hawayen nan sun sauka kasa sainayi maganin ki. "Imaan tayi shiru tana maida hawayen ta. "Omar yace toh ficemin a daki, ai be karasa mgnr ba ta bara dakin da sauri har tana tuntube, "tana fita daidai lkcn farooq ya fito a nasa side dan haka ta kece da kuka. "D sauri farooq ya qaraso wajen ta yana tmbr ta meya faru? "Imaan cikin kuka tace yah omar ne ya mintsine ni ya kuma mareni, "farooq ya dauko hanki a aljihun sa sannan ya fara goge mata hawayen yace sorry zan rama miki rabu d shi, oya muje wajen mummy, "suna zuwa shima omar ya shigo dakin. Mummy ta kalli omar tace maza kaita kayi mata shopping, omar ya kalli imaan, sannan y kalli mummy yace akwai abunda nakeyi a daki fah mummy tunda ga farooq sai ya kaita... Mummy ta katse shi d fadin ka sanni sarai banason musu ai naga farooq din ko ka fini ido ne? Omar ya sunkuyar da Kansa sannan yace shikenan mummy, "juyawa yyi d nufin ficewa, imaan kuwa taso ace farooq ne ya kaita dan tafi sakewa d shi. Mummy tace tashi ki bisa ki dauki duk abinda kike buqata imaan tace toh mummy, farooq ta d'agawa hannu, shima y daga mata yana murmushi dan shima yaso ace shi ya kaita., saidai y lura ran mummy yadan 6aci gwara yaja bakinsa yyi shiru.

  "A mota ta tarad d shi, har zata bude kofar baya omar ya daka mata tsawa yace ni driver dinki ne da zaki shige baya? Imaan tayi saurin rufe kofar, sannan ta bude ta gaba, ko daidaita zama batayi ba ya fisgi motar a guje, imaan dai cikin sai kadawa yake tsabar tsoro. "A wani katafaren store sukayi parking, bayan yyi omar yace jeki na baki 10mins kiyi sauri. "Imaan ta kalleshi d sauri tace toh kaxo mu tafi mana. "Omar ya watso mata wani mugun kallo, ai batasan lkcn data fice a motar ba. "Shiga tayi sannan ta fara daukar kayan kwalliya a gurguje d turaruka, saida tayi kusan 15mins a ciki sannan ta fito, kasancewar omar ya shigo ya bada ATM dinsa akan duk abinda ta dauka, a ciri kudin. "Lkcn da imaan ta kusan zuwa jikin motar, mamaki ne yasa ta tsaya cakkk, wata siririyar mata ta gani tare d ya omar, suna gaisawa sai murmushi yake mata abunda bata taba gani ba kenan. "Dan a zaton ta baya kula kowacce mace. "Ta dayan 6angaren tabi ta sanya kayan ciki sannan ta shige mota zaman jiran sa. "Omar kuwa sai alkcn ya lura d zuwan imaan, lekowa yyi yace ke fito, imaan tace na gama ai. Omar yace ki fito nace, imaan ta fito sannan ta zagayo inda yake, wannan matar tace woow omar wannnan sister dinka CE? "Omar yace yes, da murmushi a fuskar ta tace no wonder naga kuna kama kaii ta fika kyauma ta karasa mgnr tana dariya. "Omar kuwa dariyar da yake dazu ta tsaya tsakk ji yyi tamkar ta watsa masa garwashin wuta, kai a duniya ma ba'a ta6a ya6a masa mgn ba irin ta yau taya zata hadashi d imaan? Sannan harda qarin ta fishi kyau??? Kai Amman ta cuceshi wallahi. "Imaan kuwa dadi taji har cikin ranta taji ance ta fishi kyau, take ta dago ido ai tsarab suka hada ido dashi dan haka tayi masa gwalo sanna ta sunkuyar d kanta kasa, ran omar ne ya sake 6aci wannan Matar ta katse shi d fadin yadai Omar? Naji kayi shiru. "Omar yyi murmushin yake yace am.. Muna sauri ne Meenat.sai mun hadu next time. Meenat tace oh sorry, buh kadan bani number ka, so dat mu dinga gaisawa. "Omar yace ohk a gurguje ya bata sannan ya tisa keyar imaan suka bar wajen. "Meenat course mate dinsa ce.a inda sukayi makaranta a america.

  "Koda suka shiga mota ba me cewa kowa ci kanka. "Saida suka isa gida, bayan yyi parking, sannan ya riko kunnen imaan, imaan ta kalleshi a tsorace, omar yace uban wa kikema gwalo dazu? "Imaan tayi shiru. "Omar yace karkiyi zaton abinda tace gsky ne, dan babu inda kika baro a kamannin gwaggwon biri, imaan ta zaro ido. "Omar ya gyada kai yace yes kamar ki sakkk data gwaggwon Biri. 

 "Imaan ta ture hannun ta sannan ta bude kofar da Sauri ta fita tana goge hawaye, a daidai bakin kofa sukaci karo da farooq, farooq yace mekuma ya faru? Imaan ta bare baki ta fara kuka dan takaici ta kasa cewa komai. "A haka ya jata falo. "Mummy ta kalleta d sauri tana tmbyr ta abinda ya faru, imaan kuwa ta sake barke baki, mummy tace yimin mgn mana, imaan cikin muryar kuka ta sanarwa mummy abinda omar yace mata. "Atake mummy tahau salati sai alkcn omar shima ya shigo. "Mummy tace wai omar yaushe ka baci da shirme ne? 





Nuceey luv😘