OMAR KO FAROOQ?

70-71

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



70_71



"Imaan tayi shiru, omar yace so saina yanke wannan kazamin kunnen naki sannan zaki daina abinda kike, imaan tace nima mummy CE ta aiko ni, omar yyi kwafa sannan ya cillo mata rigar ta, oya saka ki barmin falo. Da sauri imaan ta karba ta sanyi hijab sai rawar sanyi take, "tana zuwa falo shima be dade ba ya shigo, mummy tace ya kaita skul. Ba ason ransa ba ya kaita. Koda suka shiga mota ba me cewa kowa komai. "Sanda suka je bakin skul din sannan ya ajiyeta ba kamar farooq ba d saiya kaita har ciki. "Juyawa yyi ya tafi abinsa batre d yace komai ba. "Ko da rana ma, umarnin mummy ya dawo dashi skul din, saidai shi office ya wuce da ita. 'Lkcn da suka shiga hospital din kowa kallon su yake, dan sunsan waye omar Sam baya shiga sabgar mutane. "Daidai inda umman imaan ta rasu sukabi ta wajen, take mutuwar mamanta ta dawo mata sabuwa fal. "Take imaan ta hade girar sama data kasa wani irin tsanar omr ta dawo mata sabuwa falll, har suka shiga office din omar be lura d yanayin ta ba. "Waje y nuna mata ta zauna. "Sai alkcn y kalleta yaga ta hade rai, tabe baki yyi yasan be wuce dan ya yaki maida ta gida bane. A ransa kuwa yace kyayi kya gama. "Haka yaci gaba da lura d marasa lpy, "fuskar imaan kuwa a murtuke kamar an aiko mata d sakon mutuwa, "karshe ma fashewa d kuka tayi, omar yanajin haka y waigo yana me kallon ta d mamaki. "Saidai kuma ya tabe baki kawai bece mata komai ba. "Aikawa yyi a kawo mata abinci, a zaton shi ko yunwa ta fara ji. "Koda aka kawo mata abincin ma ko kallon sa batayi ba. "Saima kara tsanar shi da takeji a xuciyar ta, "omar cikin tsawa yace malama kina cikamin kunne, idan kuka zakimin ki ficemin a office, imaan najin haka ta tashi, tayi hanyar fita. "Omar ya kalleta da mamaki saidai bece uffab ba dan yasan ba inda ta sani a hospital din.

"Imaan kuwa tana fita 6angaren farooq ta nufa. "Tana bude kofar ta fada kanshi d sauri tana kuka, farooq dake zaune hankali tashe yake kallon ta yace lpy imaan waya kawoki nan? Mwtssss akayi tsaki a gefen su, wata budurwa dake zaune a wajen tayi, imaan tayi saurin dagowa tana kallon ta, farooq ma kallonta yake da mamaki, katse shirun tayi da fadin, ashedai mgnr mutane gsky ce, yau na gani da idanuna haba farooq akan wannan yarinyar dama tuntuni kakemin wulakanci? No wonder idan na kiraraka baka dagawa sai kayi niyya, mutane dayawa sun sanar dani har office kana zuwa d ita shiyasa naxo yau domin na tabbatar wa kaina. Kasani duk son d nake maka bazan iya hada kishiya da 'yar ficiciyar yarinyar nan ba... Tana kaiwa nan ta fici cike d kunan rai. "Imaan ta kalli farooq taga ransa a bace, a sanyaye tace ya farooq wannan din wacece? Farooq kuwa ransa ne yake ta tafasa ya rasa wacce irin kasa muke ciki ta Nigeria fisabilillahi dan yana xuwa d imaan office dinsa shine suke soyayya? Mwtss yaja tsaki, "imaan ta sauka kan tainyar sa tana shirin fita, farooq ya riqo hannun ta yace, INA zaki? Imaan kanta a kasa tace naga kaman ranka a bace ne shiyasa zan tafi, farooq ya kwakwulo murmushi yace no ai bakece kika 6atamin ba. "Imaan tace toh yah farooq wannan din wacece? Farooq yace suhailat, imaan ta zaro ido tace wacce kuke waya? Farooq ya gyada kai. "Imaan tace Amman ji fah yanda take ta fada harda nunani d yatsa. "Farooq yace shareta. "Imaan tayi shiru can tace toh ya farooq d gske ta fasa auren ka? Farooq yace eh, Amman ai kinsan bazan rasa wasu ba. "Imaan tace ehmana, toh yanzu wa zaka aura? Farooq yace ikon god yarinyar nan ko 'Yar jarida zaki zama? Imaan tayi murmushi tace aa yace toh tambayoyin ya isa haka. "Imaan tace toh bari nayi maka ta qarshe, farooq yace inajin ki, "imaan tace toh tunda suhailat ta fasa aurenka ai ni saika aureni mu cusa mata takaici koh.?




Nuceey luv😘