OMAR KO FAROOQ?

78-79

by @nuceeyluv

*OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓



78_79




"Shirye_shirye ake, both gidansu ameera da farooq, farooq har gida ya kawo ameera suka gaisa d mummy, sosai mummy tayi farinciki dan ta lura yarinyar tanada hankali da nutsuwa, imaan kam ta saba da Anty ameera kamar sun dade, har gidan su tana zuwa tayiwa farooq rakiya, dake imaan sun sami Hutu sai bikin yazo mata a daidai, yawo sosai suke zuwa ita da farooq da ameera, itakam burge ta suke yanda suke tafiyar da soyayyar su. "Akwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yauta ta kasance Friday inda dubban jama'a suka taru domin daurin auren farooq, 6angaren omar ma sosai yake taya dan uwansa murna, kowa sai mamakin sa ake shine babba Amman beyi aureba. "Shadda wacce tasha dinku ubansu, na hango taurarin sun fito daga side dinsu, duk yanda kaso ka banbanta omar da farooq, bazaka iyaba sbd tsantsar kyaun da sukayi, dinkin sosai ya amshi jikin su, abunka da basu saba sa babbar Riga ba, sai abin ya zama gwanin sha'awa son kowa kin Wanda ya rasa, cikin takun kasaita suka fito a side dinsu fuskarsu dauke da murmushi, "daidai lkcn imaan ta fito a dakin mummy, kwalliya sosai mummy tasa akayi mata, ba karamin kyawu tayi ba, make up dinnan yahau, ga daurin da akayi mata ya matukar karbar ta, saikace itace amaryar, fitowar kenan isowar su omar da farooq me camera na gefen su, masu kirari nayi, imaan na ganin su tayi sauri da nufin hugging din farooq, saidai ta kasa banbanta su, haka ta qarasa wajensu inda zuciyar ta ya bata, ba zato ba tsammani omar yaji imaan tayi hugging dinsa, dagowa tayi tana dariya tace kagani nayi kyau? Omar shime besan lkcn da yyi dariyar ba ai kamar jiran sa ake sai ganin hasken camera suka gani, dukkansu suka juya da sauri dan ganin Wanda ya daukesu camera man suka gani da farooq da shima yake riqe da waya yana, daukar su pic, juyowar su shiyayi daidai da qara musu pic din, raf-raf-raf aka hau tafi, wasu sai fadi suke ko sune amaren? Dan sun rasa waye farooq din. Hotunan da akayi musu ba qaramin kyau sukayi ba. Omar dai yyi murmushi batare da yace komai ba ya kama hannun imaan da take ta washe baki jin ance sunyi kyau duk azaton ta da farooq akayi mata photo. "Har dakin mummy ya kaita still ta sake cewa ya farooq bakace nayi kyau ba? Omar yyi mata shiru, sannan ya fara tafiya, imaan tayi saurin tashi kamar zatayi kuka tace nayi kyau? Kai ya daga mata da murmushi sannan ya wuce da sauri, imaan a zuciyar ta tace haladai yau axumin mgn kke. "Shikuwa omar yaso ya disga ta da niyyar sa ya tureta, Amman yana tsoron fadan mummy dan a falon ta abin ya faru, shiyasa ya samawa kansa salama bayan haka sosai ransa ya 6aci haddai ma hotunan da akayi musu saikace sune amaren, mwts yaja tsaki, mota guda suka shiga shida farooq dan zuwa daurin aure, abokansu suka hau wata motar, wasu kuma suka hau tasu omar, ma'ana daya yyi driving daya ya zauna a kujera me zaman banza. "Koda suka shiga be tankawa kowa ba sa6anin da dayake murmushi, farooq yana lura dashi saidai shima ya basar yana hira da abokan su. "Wanda yake driving din babban abokin farooq kenan, yace kai Amman fa omar kunyi bala'in kyau d wannan yarinyar fah, omar yanajin sa ya share shi, farooq yace kaifa dan iskane wannan sister mu ce, da sauri yace kai dan Allah? Farooq yace dgske, abokin ya kalli wanda me kujerar me zaman banza yace Yusuf d alama na samu mata a gidan su farooq fah. Sai alkcn omar yaja tsaki yace malam kayi abinda ke gaban ka bawai surutu ba ka wani cika mutane da surutu akan wannan yarinyar, wanda yake driving din yace aa kace rowar sister Ku zakumin, farooq yace ah karka damu idan imaan CE zamu baka, omar ya sake Jan tsaki a karo na biyu, shi haushin sa daya yarasa me suke gani jikin imaan da kowa zaice yana sonta, baya manta lkcn daya kai imaan skul, bayan ya ajiyeta har zai tada mota wani dake cikin mota ya fito da sauri yana masa alamar ya tsaya, "lkcn daya tsaya mutumin ya tmbyeshi imaan ko sister sa CE? Yace eh, bawani 6ata lkci ya fada masa tunda take zuwa Skul din yaji yana sonta kuma da aure, ya yaba da hankalin ta da nutsuwar ta da kuma kokarin ta. "Sosai omar yyita mamakin wannan mutumin, qarshe yace yyi hakuri kr2 zatayi, mutumin yace shi zai jira ko shekara nawa zatayi, cikin tsawar d be shirya yinta ba yace malam anyi mata miji, ai d sauri mutumin ya bashi hakuri ganin yanda ransa ya 6aci sannan yabar wajen., da wannan tunanin kala2 suka isa babban masallaci na Kano inda za'a daura auren farooq da amaryar sa ameera.







Nuceey luv😘