OMAR KO FAROOQ?

80-81

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓




80_81





"Tunda suka isa taron ake busa saikace 'yan'yan sarakuna kai duk wanda ya halarci bikin zai tabbatar was kansa lalle wannan auren bana wasa bane, manyan mutane harda shugaban kasar america ya hallaci wannan hamshakin daurin auren, makada da mawaka kam ai sai abinda yyi gaba, dan sun sami sun baje kolin su, "ba'a dau wani lkci ba aka fara sanarwa kamar yadda al'ada ta tanadar a musulunci, kowa ya shaida daurin auren _FAROOQ_ _DA_ _AMARYAR_ _SA_ _A'ISHA_ akan sadaki me inganci, habawa nan aka fara tafi da Sam barka abindai ba'a cewa komai. "Bayan minti biyar dakyar aka yi sanrwa a lasifiqa akan a saurara, "abinka da dubban mutane baka gane abinda ake cewa,

"Sanarwa aka sake yi, bayan haka mutane da shaidu sun shaida an daura auren farooq da a'isha haka mukeson su shaida an daura auren omar da amryar sa.... Arazane omar ya mike da sauri ya matsa kusa da daddy dake suna kusa, ya rike hannun sa cike da tashin hankali, bakinsa na rawa yace dan Allah daddy, kayi hakuri dan Allah karkamin haka daddy, daddy yyi murmushin sa irin na manya, sannan ya kalli me sanarwar yace ci gaba da abinda kke, farooq yana gefe shi kansa ya tausayawa bro dinsa dukda dai basusan dawa daddy zai hada auren ba. "Me sanarwa yabi umarnin dadi, ya cika aikinsa. "A firgice omar yake kallon daddy da matukar mamaki, anya yasan wacce ya aura masa kuwa? "Ba'a iya tantance yawan tashin hankalin da suka bayyana kan fuskar omar, mikewa yyi yabi cikin mutane fuskar nan babu alamar annuri, haka yyi ta keta mutane har yaje inda sukayi parking, toh Allah yaso shi akwai extra key a hannun sa, hakan ya bashi damar tuka motar a guje, "mutanen dake wajen kuwa sai mamaki suke, sundai ga an sanar frooq za'a daurawa aure Amman sai sukaga sa6anin haka, haka taro ya watse, farooq dai yaken dole yakeyi burinsa yaje ya duba inda omar ya tafi, yasan sa da zuciya idan yyi zuciya abun ba kyau, har zai tashi ya bishi daddy yace ya tsaya karya soma binsa. Haka ya hakura, mutane kuwa sai tayasu murna suke, haka taron ya watse.

"Dakyar farooq ya samu ya sulale yabar wajen, shima wata motar ya shiga sannan ya karbi key gun wasu abokansu, ba inda ya nufa sai gida. "Tun abakin gate yyi parking sannan ya wuce side dinsu direct, dakin omar ya nufa ya Ganshi a bude, alamar be ma dawo gidan ba kenan. Zai fito kenan suka hadu da mummy fuskar nan tata a tamke 6acin rai qarara a fuskar ta, abinda ya sake hargitsa tunanin farooq kenan, cikin tsawa tace ina omar din yake?





Nuceey luv😘