OMAR KO FAROOQ?

82-83

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓




82_83




Zanyi amfani da wannan dama wajen bawa masoyana hakuri bisa jina da kukayi kwana biyu banyi posting ba, ba komai yaja ba sai lectures da mukeyi sosai ga exam da muke shirin yi, abin dai sai du'a'i, Amman dai insha Allahu yanxu komai normal. Ku kasance tare da mai kaunarku a koda yaushe _*Nuceey*_ _*luv*_.


**************



"A rikice yace nima shi nake nema mummy, mummy tayi kwafa sannan ta juya batare da tace masa komai ba.shima farooq sake ficewa yyi a gidan dan Neman inda Omar ya shiga.


***

Tunda ya fito a taron yake ta falfala Gudu kamar zai tashi sama idon nan nasa sun qanqance sakamakon 6acin rai da yake ciki zuciyar nan kuwa sai tafasa take tamkar ruwan da aka Dora kan gas. "Ikon Allah ne kawai ya kawo omar gidan shi, Wanda daddy ya Gina masa idan yyi aure saiya tare aciki, dake gidan babu gateman dolen sa ya sauko a motar, sannan ya bude gate, unguwar shiru kamar ba mutane saidai daka ga ginin gidajen wajen zaka tabbatar wa kanka ba qananan mutane ne suke rayuwa aciki ba. "Bayan yyi parking motar sa sai ya wuce falon sa direct, abunda yyi matukar bashi mamaki shine bai wuce ganin yanda aka gyara main falon ba, dake gidan me hawa biyu ne, yanda aka sa colours din komai red& ash shiya tabbatar masa da lalle wannan auren fa dgske ake masa, saidai ba laifi ya yaba da tsarin colours din, qarshe kuma ya ta6e baki ya haura sama da sauri, dakin shi ya wuce batare dya duba dayan dakin dake wajen ba, "yana shiga ya cire duk kayan jikin sa sannan ya fada toilet ya sakar ma kansa ruwan sanyi, kusan 15mins ya dauka sannan ya fito, kamar dai tsarin dakinsa na gida, saidai wannan yafi kyau sosai, ran nan nasa saikace ana qara masa fetir a ciki sai tafasa yake, farin idon nan ya koma red, "duk yanda yyi ya mance sunan yarinyar da aka daura masa aure abin ya faskara,tunawa da sunan ta kuwa shike qara tunzura 6acin ransa, a fili yace kai anya daddy yasan waya aura masa? _Fateema_ fah? Mtwss gaskya an gama dashi wallahi, an cuceni toh ma me zaiyi da wannan tatsitsiyar yarinyar? Dayaga dai tunanin sa zai sake birkitashi yasa ya mike kan gado rai a 6ace da wannan tunanin bacci yyi gaba dashi.



"Farooq duk inda yasan omar zai shiga yaje Amman babu labari, kwata2 be kawo gidan omar a ransa ba. "Haka ya koma gida, mummy kam ranta yyi mugun 6aci bata ta6a zaton omar zai watsa mata qasa a ido ba gaban dubban jama'a, Amman koda ta shiga cikin mutane sai tayi kokarin 6oye fushin ta.

"Koda farooq ya dawo, mummy yaja gefe zuwa side dinsa sannan ya sanar mata shifa began omar ba, cikin 6acin rai mummy tace toh shi yaro ne? Yaje duk inda zaije karka qara Neman sa, tana kaiwa nan ta tashi da nufin tafiya, farooq yyi qasa da murya sannan ya shiga lallashin mummy dan ya lura tana cike da 6acin rai sosai, "dakyar ya iya calming nata, sannan tabar side dinsa, a zuciyar ta tace dadin yara dayawa kenan idan wani ya bakantaa maka sai wani ya faranta maka. "Haka biki ya watse batare da omar ba, 'yan gulma sunyi abunsu har sun gama, amarya ameera ta tare gidan angon ta farooq, "koda akace za'a dau amaryar omar, mummy hanawa tayi tace a kyaleta a wajen ta. "Amarya _Imaan_ kuwa hankalin ta kwance batasan wainar da ake toyawa ba, dukda basa shiri da omar Amman kwana biyun da bata ganshi ba ta danyi kewar sa, farooq ta tmby, farooq yace yyi wata 'Yar tafiya ne, imaan ta tabe baki tace shine ko salllama babu, farooq ya kalleta da mamaki tunda yasan bata shiri da omar ai ba yanda za'ayi ta damu, kasa shiru yyi yace a'a kodai kin fara son bro dina? Ya fada yana murmushi, imaan tace cabdin Allah ya sauwake me zanyi da tsoho, farooq ya zaro ido yace Ashe nima kallon tshoho kikemin, imaan tayi dariya, tace lah ya farooq Allah banda kai, farooq yace toh yanzu akace ki auri omar zaki auresa? Imaan ta zaro ido tace dan Allah ya farooq ka rufamin asiri ko maza sun qare bazan auresa ba. "A razane yace what? Imaan tace umhu ai kaima kasan Kaine mijina, farooq ya girgiza kai yana tunanin hadin gambizar da su mummy sukayi, *OMAR* bayaso *FATEEMA* Tace tsoho, _daddy_ da _mummy_ kuma sun ```hada```.






Nuceey luv😘