84-85
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
84_85
"Haka omar yake rayuwar sa cikin wannan gida shi kadai, saikace maye, farooq kuwa yana gidan shi anacin amarci dukda yana cikin tunanin dan uwansa, kamar daga sama ya tuna da gidan omar, ai ko minti daya be qara ba yabar gidan shi, direct gidan omar ya nufa, "a tura kofar gate din yyi ga mamakin sa yajita a bude, hakan ya tabbatar masa da akwai mutum a ciki, yana shiga kuwa yaga motar omar aciki, hamadala yyi, sannan ya kutsa kanshi cikin falon, sallama yyi yaji shiru, dan haka ya haura sama, dakin omar ya gwada budewa yaji ta budu, dan haka ya tura, bayan yyi sallama, nan ma shiru, mamaki ne ya kasheshi ganin omar sai baccin sa yake hankali kwance, saidai da mutum ya lura zai tabbatar wa kansa ya danyi rama. "Matsawa yyi yadan bubbuga kafar sa, omar dake bcci yaji ana bugun sa a razane ya tashi yana kallon farooq da mamaki, "farooq ma mamakin yake dukda yadan daure fuska, atake baccin omar ya washe sannan yace malam lpy? Farooq ya nemi bakin gadon ya zauna, sannan ya kalli omar yace haba bro abinda kayiwa su mummy kayi adalci kenan? Yanzu kusan 4days baka je inda suke ba just bcoz sunyi maka gata? Haba bro. "Omar ya tabe baki yace kaga malam gidana kazo ba dandalin wa'azi ba idan shi kkeson yi kaje ka masallaci ko inda akeyi kayi inaga zakafi samun lada. "Da mamaki farooq yace bro ni kke fadawa haka? Akan an baka imaan? "Cikin tsawa yace ni nace inason ta? Cewa nayi a auramin ita? Bana sonta, bana qaunar ta har abada baxan ta6a sonta ba. "Farooq yace bekai ga haka ba ai, abinda nake jiye maka shine ranar da zakayi nadaman wannan kalaman da kake furtawa.. Omar yace ya isheka haka farooq tun muna shaida juna ka daina min mgnr jaririyar, farooq ya cije baki cike da takaici yasan hakane ai da tun farko ya sanarwa mummy zai auri imaan da duk hakan bata kasance ba, a fili yyi murmushi sannan ya fara mgn a nutse, yace sorry bro, Amman inaso ka gane fushin iyaye kan 'ya'yan su ba karamar masifa yake jawowa ba, duk abinda iyaye zasuyi wa yaransu bazasu taba yin abinda zai cutar da su ba, abinda iyaye sukayi mana bazamu ta6a biyansu ba biyayya itace tamu duk abinda sukace muyi zamuyi matukar be kauce addini ba, koda bama son Abu yakamata mu tausasa zuciyar mu muyi na'am da za6in su sai kaga qarshe mune dacin moriyar abun, INA rokon kayi kr2n ta nutsu kaje ka bawa su mummy hakuri dan Allah. "Omar yyi shiru shi kansa yasan be kyautawa su mummy ba, Amman harga Allah beji zai iya aminta da imaan a matsayin Matar sa ba. "Tabe baki yyi sannan yace sai nayi tunani. "Farooq yyi murmushi sannan yace ohk no prob, ahankali abinka da tsakanin twins, ba wani bata lkci farooq yyi ta Jan omar da hira har saida ya tabbatar ya ware daga bacin ransa sannan yabar gidan zuciyar sa wasai.
"Tunda yabar gidan omar yake ta tunani qarshe dai ya yanke shawarar komawa gida dan bawa mummy hakuri. "Cikin shirin sa ya fito na T shirt da wando, kwalliyar tayi matukar amsar jikin sa, yyi kyau sosai. "Motar sa ya shiga sannan ya kama hanyar gida, a hankali yake tuki harya isa gidansu. "Ya Dade cikin mota sai yanxu ma yakejin tsoron haduwar sa da mummy, dole dai ya fito a motar qirjinsa na bugawa dafdaf yasan mummy idan ta fara masa fada sai ikon god, gefe guda kuma tsanar imaan tana masa yawo a kwanya.
"Ahankali ya tura kofar falon hade d sallama, jin shiru ya tabbatar masa d ba kowa a falon. Qarasawa falon yyi Da nufin sake yin wata sallamar tarrrr idanun sa suka sauka kan wani photo dayayi bala'in yi masa kyau dake maqale jikin bango, idan bazai manta ba wannan shine hoton da akayi masa shida imaan lkcn data rungume shi, sosai ya shagaltu da kallon hoton, dan ba qaramin kyau sukayi ba. Mwtsssss yaji anja tsaki, juyawar da zaiyi yaga mummy ce data fito a dakin ta, da sauri ya sunkuyar da kansa, mummy kam juyawa tayi dan komawa dakin ta. "Ganin haka yabi bayanta da sauri, har dakin ya bita batare da tace masa komai ba tayi zaman ta tana duba wata jarida. "Mummy, omar ya kira sunan ta, mummy tayi banza dashi, kusan sau uku ya kira Amman ta share shi. "Omar yace dan Allah mummy kuyi hakuri akan abinda nayi muku sharrin zuciyane ya debe ni har na aikata abinda nayi, tsaki mummy ta sake ja cikin kunan rai tace ka tashi kabar min daki inada abinyi, omar ya rike kafar ta yace mummy dan Allah kiyi hakuri bazan sake ba insha Allah. "Mummy tace ka bani mamaki omar, ko a mafarki ban zaci akwai ranar da zamuyi maka kyautar Abu kayi watsi dashi ba, bama a iya gaban mu ba aa a gaban duniya ka nunawa duniya iyayen ka basu isa da kai ba, omar ya sadda kansa qasa ko kusa baison bacin ran iyayen sa, da kyar da sidin goshi ya lallaba mummy harta yadda, "qarshe mummy tace naji abunda nakeso kasa aranka shine auren ka d imaan babu saki, a rikice ya kalleta saidai ya kasa cewa komai dan bayason ya qarawa kansa wani lefin dakyar ya iya gyada kansa a matsayin ya yadda, mummy tace duk lkcn daka musgunawa imaan ta sanar min ko na gani da idona sai nayi mummunar sa6a maka, nan qirjinsa ne ya bada darararam, a fili kuwa yace insha Allah mummy zanyi yanda kikace, mummy tace gud, next week zaka dau Matar Ka. Omar yace Allah ya kaimu. Yana fadin haka yabar dakin sannan ya nufi side dinsa. "Mummy kuwa addu'a tayi Allah ya hada kan omar da imaan. Allah kuma ya sanyawa auren Albarka da daurewa har abada, nima dai nace ameen.
Nuceey luv😘