πŸ§‘β€πŸ¦½πŸ˜­SUN GUJE NI πŸ˜­πŸ§‘β€πŸ¦½

15

by @111922694126240833629

πŸ‘¨πŸ»β€πŸ˜­SUN GUJE NIπŸ˜­πŸ‘¨πŸ»β€πŸ¦½

(SANADIN CUTAR LAKKA)

IT BASED ON TRUE LIFE STORY.


LABARI DA RUBUTAWA:FARIDAT HUSAIN MSHELIA(UMMU-JIDDAH).


*This page goes to my Facebook Fans duk da Mark ya hana ni post Ina son ku fisabilillah😘*


SHAFI NA GOMA SHA BIYAR.


MAHAKURCI MAWADACI.


Yusuf kuwa wanda yafi kowa matsuwa da son fidda shi daga cikin motar saboda tarin gajiya da azabar da ya ke ciki,


ya kalli d'an'uwan na sa dishi-dishi dan shi kadai ya San irin azabar da ya ke ji a cikin jikin sa ya ce"Ina su ke ma'aikatan lafiyan,ku ka zo ku kadai",


"Sun sanar da ba gado Amman Yanzu za mu Kai ka gidan gwaggon mu(kanwar mahaifiyar Yusuf da ke zaune a Dorayi Dan Mahaifiyar su Yusuf bakanuwa ce iyayen ta na nan a dorayi),in ya so sai asan yanda za'ayi"k'anin ya furta hakan cike da dagiya da jarumta ka,


Yusuf kuwa shiru ya yi tamkar wanda ruwa ya cinye shi, ganin nan ma ba su karbe shi ba ya sa ya ji zuciyar shi ta karaya,


"Yanzu haka rayuwar duniya ya juya mi shi baya har ya zamto abin gudu a gurin mutane,ta yaya zai cigaba da rayuwa a haka?


"Tabbas mutuwa zai yi matuk'ar a wannan yanayin zai cigaba da rayuwa tun da nan ne last hope din shi Amman gashi sun ma ki ganin sa balle su tallafa mashi",


Murmushin yake ya yi Wanda ya fi kuka ciwo cike da bak'in ciki yace"Tabbas ubangijin da ya daura min cutar nan shine kadai ya ke da ikon yaye min shi so Akwai Allah! na tabbatar da zai taimake ni bisa ga wannan jarabawan tunda ba Wani zunubin na aikata a gareshi ba balle ace shiyasa na ke k'arban wannan ukubar"shiru ya yi na wasu dakiku kafin ya umurce su su ta da mota su tafi gidan gwaggon na su,


Sun isa lafiya tare da samun kyakykyawan tarba Amman yayin da aka nemi taimakon matasan domin a fito da Yusuf daga mota kuka Yara da manya su ka barke da shi saboda ganin yanda Yusuf ya dawo,


Kusan kowa a gurin Yana tuna yanda Yusuf ke shigowa cikin Kamala yayin da ya kawo mu su ziyara(saboda ya kasance mutum Mai matuk'ar son zumunci)cikin fara'a da haba-haba da jama'a Amman yau sai gashi ranga-ranga aka dakko shi cikin Wani irin yanayi mai tab'a zuciya,da kyar aka samu mata su ka yi shiru bayan mijin gwaggon na su ya daka mu su tsawa"Ku fice min daga nan Dan Allah ku bar mu Muji da Mai jinya"nan ta ke kowa ya shiga taitayin sa sai kukan zuci da yawancin ahalin gurin ke yi,nan da nan aka gyara ma Yusuf gurin kwanciya Wanda ke Jin tamkar a garwashin wuta aka Sanya shi nan da nan aka dinga watsa yayyafa mishi ruwa tare da goge mishi jiki da tawul da ruwa Mai sanyi,Dan ciwon Sam Sam baya son zafi,masu fiffita na yi har aka samu Wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da shi.


Sai a sannan k'anin shi ya samu sukunin yin ramakon sallah, tsabar tashin hankalin da ya ke ciki ko yunwar cikin shi baya ji,


Ya tafi d'akin gwaggon su domin su gaisa su tattauna dangane da wannan matsalar da su ke ciki,shigar shi ke da wuya ya same ta itama duk jiki a sake tana ganin shi ta fashe da kukan da ya ke cin ta acikin zuciyar ta,Sam bai Hana ta ba dan a Wani lokacin kuka ma rahama sai da ya bar ta ta yi Mai isar ta kafin ya fara ba ta hakuri tare da ban baki,tsit ta yi tana sauraron shi nan ta yi mi shi tambayoyi da ya danganci ciwon Yusuf d'in,


Ya yi ma ta bayani akan komai ,gurin mijin ta ta Aike shi ya yi ma ta k'iran sa nan ta sanar da shi halin da a ke ciki ya babbata baki hade da kwantar mata da hankali har ma ya daura da cewar Insha'Allahu za'a samu mafita.


Cikin ikon Allah kuwa a Daren ranar aka samu Wani kwararren likita da ke makwabta ka da shi ya zo ya duba shi,maganan farko ya ce "maganan gaskiya ba bu Wani asibiti da zai karbe ku matuk'ar da medical report din nan za ku je ma su,Babu babban Mai laifi kamar likitan da ya rubuta wannan report din Amman ni shawarar Da zan Baku gobe da sassafe zan ba ku numban wani abokina da ke Asibitin Murtala in Kun je na tabbatar da zai bincike matuk'a tare da gwaje-gwajen duk da ya kamata kuma insha Allahu zai warke ku daina damuwa",


Farinciki sosai su ka yi da samun wannan mafitar aikuwa asubar fari su ka nik'i gari,aka Nemo mota aka sa Yusuf sai asibitin Murtala, taimakon gaggawa aka fara ba shi Dan suna isa a emergency aka ajiye shi,cikin shi da ya kumbura ya yi suntum sanadin yogot din ziza da ya saba sha tun ya na da lafiya,so acikin zafin ciwon Yana yawan ambaton sa Dan haka ake dura mishi kad'an-kad'an,ai kuwa sai ya hana mi shi bahaya tun a asibitin Bauchi da Wani likita ya ga yanda cikin na shi ya suntume ya daddanna aikuwa nan bayan garin ya dinga fita Mai matuk'ar wari to Bai k'ara yi ba,so tun acan aka Hana su bashi madarar yogot d'in sai ruwa kawai Wanda Shima sai lokaci zuwa lokaci,


To anan din ma Hakan ne ya kasance kafin su ka tura su yin gwaje-gwaje,nan aka gano Cutar lakka(spinal cord injury)ce ta samu Yusuf wuyar shi ba karyewa ya yi ba,


Kuma Alhamdulillah lakkar Yusuf ba karye wa ya yi ba sharking ya ke yi Wanda matuk'ar za'abi matakan da likitoci su ka gindaya ma su to Insha'Allah zai warke,



Nan ta ke aka gindayo musu sharuddan da ya kamata su bi tare da rubuta mu su magunguna hade da allurai aka je aka sassayo ya yi mi shi, 


alhamdulillah wannan cigaban da aka samu ya Sanyaya zukatan masoyan Yusuf da ma su jinyar shi Dan haka aka dawo da shi gida cike da kwarin gwiywa,


Suna dawowa suka sanar da iyayen Yusuf wannan kyakykyawan albishir d'in,fad'in irin farinciki da innar Yusuf su ka shiga ita da Yan'uwan sa ma b'ata baki ne kawai sai su ka cigaba da bin shi da kyakykyawan addu'a na samun nagartaccen lafiya.


Bangaren Shugabar marasa Imani kuwa duniya sabuwa ce ta bud'e ma ta saboda Karin samuwar hanyar kudaden shiga aljihun ta saboda yanda abokan Yusuf Yan amanar sa ke kokarin ziyartar ta suna yi ma ta kyauta kudade saboda tausaya ma ta akan rashin miji a tare da ita gashi jinya ta same shi an San Babu matallafi sai Allah,Dan haka su ka alhairai gabas da yamma kudu da Arewa Yana zuwar ma ta ba tare da ta sanar ma innar Yusuf ba saboda kasancewar ta cikakkiyar y'ar mara mutunci,


A wannan lokacin Ra'isat Jin ta ta ke tamkar a Saman gajimare ga kud'i na zuwar mata ga abinci iri-iri sai Wanda ta zaba Dan haka ta murmure ta yi bulbul abin ta,yawo ta fara fita ba tare da tunanin auren da ya ke kan ta ba,ta je in da ta so ta dawo a lokacin da ta ga dama Sam ba ta tab'a kwana da tunanin a Wani hali mijin ta ya ke ciki ba,


Garin yawace-yawacen ta na banza cikin da ake tink'aho da shi ya salwanta ba ta bari kowa ya sani ba saboda iskancin da ta ke yi ma mutane a kan sa Dan haka ta cigaba da yi musu basaja tana k'ara fito da salon rashin mutunci kala-kala.



*Da Babu ance gwara ba dadi Dan haka kuyi manage baki na yi su ka hanani typing yau wallahi nagode masoya*




Ummu-jiddah.