JANNAH

22

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......22



Kallon kiran nai tayi kamar shine a gabana, babu abinda yake dawo mun cikin kaina sai hirar mu da hindu d'azun, tabbas nasan yana da gaskiya aduk maganganun sa to Amma wannan zafin da ya d'auka yayi yawa, miye laifin yah usy fisabilillahi ya bashi amanata ya rik'e baitab'a cutar dani ba, duk da inaji kasan zuciyata cewar Yah usy he is in love for me, Amman banda tabbas d'in hakan tunda bai fito fili ya sanar dani ba, inhar dagasken sona yake miye laifina aibani na sanya shi yasoni ba dazai huce haushin sa akaina, wata zuciyar take ce mun "to in kishin ki yasa duk yake wannan abun fa?"


Girgiza kaina nakeyi hakan bamai yuwuwa bane, yace baida wani buri akaina sai yaga nayi karatu inda yana sona kokari zai yaga yasanar dani,koma yaga ya samu ya mallakeni bazan masa uziri ba shiyasa ma naji na kasa daukar kiran, duk da yadda gabana kuwa yake fad'uwa, inajin kamar banyi daidai ba gatsoron sa daya kamani saboda fad'an daya surfa mun d'azun, cikin yan seconds kamar bashi ba kuma yazo yana lallashina...........murmushi naji inayi saboda abun yaban dariya ni kaina dariyar nake ma kaina yadda na saki baki naita rusa masa kuka kamar wata yar yarinya.............kiran ne ya sake shigowa nasaka wayar gaba ina kallon no din kamar zanga fuskar sa aciki, har cikin raina so nake na d'auka amman bansan meyasa nakeson yaji babu dad'i ba, atakaice saida yai kira biyar inata kallonsu zuciyata bata huta da dokawa ba kawai ina hango rikicin da zamuyi, idanunsa yadda suke juyewa kamar ba nashi ba sunfi komi fizgata, duk da yana cikin mood marar dad'i kyau suke sosai idan suka canza launi, burum naji anshigo saurin tashi nai ina cewa, "haba dai Hindu ba knocking"


"Ashe ma idonki biyu, shine Yah Asaad nata kiranki Jannah baki dauka ba"


Kauda kai nayi nace, "silent takefa niban gani ba..........wayar na gabanki kice mun biki gani ba, kawai dai kice mun wulak'anci zaki masa yace kizo in kuma inkoma ince kince bakizuwa to"


Sai lokacin naji hankalina yai mugun tashi, dirowa nai ina rik'o hannunta kamar zan kuka, "hindu please kice nafara bacci, don Allah karki ce ina gani ban dauka ba"


Hararata tayi tace, "nak'i na fad'a d'in tunda abunda na gaya miki dazun bai shiga kunnan ki ba, har Yah ASAAD yakira Jannah kina kallon kira ba zaki dauka ba? Tabdijam tunda nake da Yah ban tab'a ganin macen da yake bi irinki ba"


Ta juya ta fice ko tsayawa duba sitirara jikina banba na figi hijabin dana dawo da ita nabita a kid'ime, har ta isa sadda naje a bakin k'ofa mukai karo da Yah usy,kallon juna mukai kamar bazai daina kallona ba sadda kai nayi ina ce masa , "Yah usy barka da dar..........wuceni kawai yayi with out said anything, banji dad'i ba saboda ban masa laifin komi ba shiga nayi da sallama duk na rikice, Hindun na iske tsaye shi kuma yana cikin kujera kanshi k'asa, three quarter wando ne fari jikinsa sai sheet mai gajeran hannu coffee brown, duk da bai d'ago ba kayan sun masa kyau sosai, kadan da inda yake na durkusa kan guyawuna Hindu tace ”Yah gata nan”


Banjira yace wani abu ba nahau kare kaina bakina har rawa yake, ba abunda nake gudu irin ya daka mun tsawa irinta d'azun,


"Don Allah Yallab'ai kayi hakuri wayar silent take bacci na fara banji ba, don Allah kayakur..............dagowar dayai yana kallona yasa nakasa idawa tsoro naji yadda naga fuskarsa idonsa sun lumshe sunyi wani iri, zare ido kawai nake Hindun tace "Yah mezan kawo maka"


"Jeki ki kwanta akwai school gobe"


"Yah tunda ka iso fa bakaci komi ko tea ne naje na had'o maka"


"Banson musu Hindu, kije nace miki ko"


Ta kalleni ta maka mun harara ta fice daga falon, abunda ya tada mun hankali shine jin danai cewar tunda ya sauka yau d'in baici komi ba, innalillahi halan ma kiran da yake mun kenan? Nashiga ukuna nayi haka?jinai kwalla ta cika mun ido zanyi magana kenan ya katseni cikin muryarsa datai sanyi sosai,


"I'm sorry na tadoki ashe bacci kike, kije ki kwanciyarki"


Yana tashi zai shige ciki ban san sadda na ganni gabansa ba, "Aa yallab'ai ai na tashi zan iya yimaka koma me kace, don Allah kayi hakuri"


Idonsa keta lullunshewa gaba d'aya babu kuzari tattarre dashi, idanunsa ya zuba mun kamar zai cinyeni nai saurin sauke idona kasa daga kallon da yake mun, "nace kije ki kwanta ba abunda nake buk'ata"


"Hindu tace bakaci komi ba tunda ka dawo, don Allah kar kayi fushi zanje na dafa maka duk abunda kake so"


Lunshe idonsa yai yana bud'esu kaina taku biyu ya k'ara ya iso daf dani, dole na runtse idona inajan wani irin numfashi cikin yin kasa da murya yace, "kin san a yadda kika shigo nan kuwa?, hakan ya tabbatar mun ba bacci kike ba sadda baketa kiranki"


Idanuna duka na zaro kafin na kalli jikina, riga da wando ne jikina na bacci, wandon iya guiwa yake hajibin kuma bata wuce guiwar ba itama, rud'un dana shiga a sadda hindu tazo yasa ban tsaya dauko dogon hijab din ba, dukan santala santalan kafafuna suna waje wata irin zabura nayi na duk'e k'asa na cusa kaina cikin kafafun, na lullub'e kafafun da hijabin inajin kamar na ringa marin kaina saboda takaici, duk yadda yakejin kanshi dole saida ya sake siririn murmushi durk'usawa yayi gabana yana cigaba da murmushin yace,

"Aikin gama ya gama ai, gaya mun meyasa kika ki daukar kirana?"


Shiru nai kamar xan rusa ihu yace "saboda ki tada mun hankali ko? Idan na sake kiranki kina gani biki dauka ba a ranar zaki san waye ni, watau Usman ya koya miki rashin kunya ko?"


Azabure na dago ina yin kamar zan kuka, "Wallahi aa yalla.........inkika sake cemun wannan yallab'ai din saina sab'a miki,"


Na sauke kaina ina turo baki nak'i tashi daga inda nake, jinai kawai yace "kike zagina Jannah"


Bakina da idona duk na bud'e ina zare ido nace, "nashiga uku wlh ban zageka ba don Allaah kayakuri"


Wsni irin kallo yake mun yace, "bazan yi hakurin ba,"


Yak'i tashi daga gabana balle na samu damar guduwa, na sadda kaina ina cewa "to ka rama"


"Ai banji mekika ce balle inrama"


"Wallahi fa bance komi ba, taya zan iya zaginka ni koba kaiba bana zagi ma gaba d'aya"


Ajiyar zuciya ya sauke jiyake kamar su kwana haka da ita, saiyaji duk yunwar ta fece shikadai yasan abunda ke fuzgarsa akaanta, "meyasa? Wani matsayine dani ban sani ba"


Sauke kaina nai inajin murmushi na son kubce mun, nace ahankali "yallab.....ohh kaya kuri don Allah, ina nufin kafi karfin na zageka duk laifin da kai mun,"


Wata irin ajiyar zuciya ya sauke ahankali yana cigaba da kallona kafin cikin lallausan lafazi yace, "shiyasa nace meyasa?"


D'an turo baki nai saboda k'osawa, "karki sake turo min baki tau!"


Na saka hannu na rufee bakin, nace "kaya kuri,"


"Injinki meyasa?"


"Ka zama wani sashe daga gareni, zan iya kiranka dangina inajinka kamar yayanmu"


Jiyai kamar ana shawagi dashi, ya sake sassauta murya yace "danginki kad'ai Jannah, matsayin yayanku kad'ai Jannah? I need more"


Bansan sadda na dago idanuna ina kallonsa ba, saboda furucinsa kasa jure kallon nashi nayi, na sadda kaina nace "nima kaina bansan iyakar adadin matsayin ka ba, ka dauka kana gaba da kowa"


Wannan maganar tayi tsananin tasiri akansa huci ya furzar yana shafa sumarsa, nai saurin cewa "dare yayi Yallab.......wayyo na mance wallahi"


Girgiza kai yayi kurin don yasan ba iya daina cewa xatai ba, "don Allah ji had'a mun oat nasha yunwa nakeji jann kamar zan mutu"


Idona na zaro "ba zaka mutu ba oat tayi kadan Yah, bari na had'o maka da indomi"


Ban jira cewarsa ba naruga nafice daga bangaren nashi, saida na saka doguwar riga na wucena dora mashi wani irin farin ciki nakejin kaina aciki, ban san meyasa ba amman ji nake bana cikin wani bacin rai, cikin kan kanun lokaci na gama naje na kai mashi lokacin har shabiyin dare tayi, tsareni yai wai bazan tafi ba saiya gama dukz spoon din dazai sai mun had'a ido, jinake kamar ina narkewa anan wurin daker yabarni na tafi.


********


"Yanzu ne lokacin da ya kamata muyi dukkan abunda zamuyi, shiyasa nace maku kudakata tukunna, komi daki daki ake binsa ba karamin abu ke sanya Abban ku yinma Asaad fad'a ba, banajin yadda yake kaunar sa yanajin sauran yaran azuciyarsa haka, rabin kadarar Abba sunan Asaad ne akai, ko duba cewar shima yana da tarin dukiya kamar ta kasheshi baiyyi ba, shiyasa a wannan karon nakeso na rabasu har abadan, ba Asaad ba haka ba usman ba kai bana jin ko hindu zan cigaba da zama da ita acikin gidan nan, Abban ku kissa da kisisina bata sanya shi kuka bata hana shi nayi hakan banga riba ba, wancen karon na had'a da malamai na kori *ZUHRA DA HISHAM* a wannan karon malamai ba zasu ci kud'ina ba duk da naga nasara, na tuba daga wannan hanyar makirci kad'ai ya isa Asaad da usman Jannah ce kaddarar su don haka ku saurara kuji yadda abun zai kasance...........momy don Allah komj zai faru kifara barina na lashe yarinyar nan, wallahi kullun sai nayi mafarkinta duk sadda idona ya ganta marata har daurewa take"


"Amman dai yah khalid baka da hankali momyn kake fad'a ma wannan maganar? Kayi asara.......zanci ubanki inkika sake mun magana ina ruwanki dani ne ehy,taya ina ganin abunda raina yabiya zaki nemi hanani"


Ya katse fareeda da fad'ar haka yana huci, fareeda tun isha'i tazo gida bata yadda wani ya ganta ba ta b'oye dakin momy, sai lokacin da kowa ya kwanta sannan tafito.


"Ku refan baki dalla can,zaku saurareni ko kuwa fad'a zaku cigaba dayi?"


Hakuri suka bata sannan suka maida hankalin su kanta wajen sauraren abunda take shirya masu...........


********


Asuba nayi naji wayata na motsi kasan filo, kamar na rushe da kuka saboda baccin bai isan ba, jiya sai kusan daya baccin ya saceni idona rufe na saka ga kunne ina cewa cikin muryar bacci,


"Uhmm inaji"


Bashiri ya lumshe idanun sa daker yace, "ki tashi kiyi sallah karki makara"


Saida naji muryar sa sannan na bud'e idona cikin bacci-bacci nace, "Sallah kuma?"


Murmushi kurin yake yace, "ehy sallah, ko bakiyi"


Tabbas banayi ina period ne amman hauka nake nagaya mashi, sai nace "Aa zanyi yanzu"


"OK tashi yanzu, sai naji shigarki toilet sannan zan kashe"


Doriwo nayi daman kuma fitsari nakeji na bud'e kofar toilet d'in na shiga na kunna famfo ina cewa, "to na shiga fa,"


"Ok by, don't forget me acikin adduar ki"


Kasa- k'asa na amsa masa "uhmmm"


Na kashe na aje wayar nai fitsari nai tsarki sai kawai nace bari nai wankan yanzu, wanka nayi na fito na shirya na canza auduga na saka hijab na fita don fara aikina, sai lokacin muka had'u da babaah uwani taji dad'in dawowata tana ta ban labarin lokacin da bana nan yadda aiki yai mata yawa, "yusra kuma yanzu ta giga Murja,ban sani ba ko daurin gindi ta samu cikin gidan,yanzu kanta tsaye takeyin abu ga wata sabuwar alak'a da suka k'ulla ita da khalid"


Nai mamaki sosai nace "Amman babah uwani khalid bana masa kallon mutumin arziki,meyasa yusra zata ringa biye masa, ni kam tsoron ma had'a ido nake dashi wallahi"


"Taji zata iyane, nidai nayi mata nasiha danaga bataji ba sai na kawo ido na sanya mata, don haka kema ba ruwanki komi kika ga zatayi"


Da haka muka bar maganar naje nafara aikina yanzu anyi timetable din girki, sai muka samu sauki cikin lokaci mukai duk abunda zamuyi muka gama,na wuce don gyara dakin momy,


Da sallama na shiga sai lokacin take sallar asuba wajen karfe bakwai da minty biyar, tirr da wannan d'abia risinawa nai ina gaidata.


"Lafiya lau Jannah antashi kenan, yau zan huta da gyaran dakin nan ai ba kadan naji dadin dawowarki ba"


Murmushi kurin nayi sannan na fara aikin, na dad'e saboda saida na gyara mata wadrope dinta, dazan taho ne ta bani turare mai kamshi naita godiya,


"Laaa kibar gode mun, kema yata ce ai ki saki jikinki dani kinji ko,"


Da haka na fito na isa kitchen na fara shirya table, ina cikin shiryawar Yah Asaad ya fito kamshin sa kad'ai ya sanar dani wanzu warsa, da sauri na d'ago ina kallonsa, shima nidin yake kallo yai mun masifar kyau ainun, kananan kaya yasanya masu kala d'aya rigar ciki kadai ce fara ta saman da wandon sune kala d'aya dark blue, rigar saman bai saka mab'allan ba hakan yasa ana ganin ta cikin, kashi yasha gyara bansan na dad'i ina kallon sa ba saida naji ya d'an buga cokali bisa table sannan na dawo hayyacina, kunya cema ta kamani na juya nabar wajen cikin sauri, sadda na kawo sauran kayan Aneesa ta fito da Yah usy gaidata nayi ta amsa mun a dak'ile nazuba mata nata sannan na isa ga Yah usy ina gaida shi,


"Ina kwana yah usman"


Dan har usy yazo mun nai saurin canza wa, cikin natsuwa ya amsa yana cewa "kina kallon time kuwa?"


Ina zuba masa nashi break d'in nace, "yanzu zanje na idasa shiryawa"


Yah Asaad naje na xuba mawa sannan na wuce ciki don sauran basu fito ba, dana tuna yadda Aneesa ta kama hannun Yah Asaad ta makale sai wani narkewa take tana masa magana k'asa k'asa, wani abu ya tsaya mun ga mak'oshi saboda haushi.


Drivern sa mannir shiya kaimu makaranta nida hindu, sai masifa take mun wai ina wulak'anta mata d'an uwa, abun ma sai ya ringa ban dariya yadda duk tabi ta rikice sai masifa take daker na shawo kanta da lallashi,


Muna tasowa karfe biyu nai wanka na ci abinci sai bacci, saboda gajiya na kwana biyu banyi aiki irin na yau ba, ban tashi ba sai karfe hud'u harda rabi gyara jikina nayi saboda kamar nayi stain, wayata na dauko da naji tana vibrate na saka ga kunne tunda on ready na san ko waye,


"Kishirya yanzu ki sameni compound,"


"Turo baki nayi saboda har yanzu in natuna yadda Aneesa take masa dazun, haushi kamani yake shi kuma ko wani anshewa bai ba can kasa na bashi amsa,


"Aikin yamma fa zanyi"


"Aikin yamma yaci k'aniya Jannah, karki bari na sameki a dakin nan"


Cikin haushi ma na kashe wayar.






Ayi hkr faa da rashin yawan pages👏🏻




Mom muhseen✍🏻