JANNAH

23

by @mommuhseen

*_💔JANNAH💔_*

_{A TRUE LIFE STORY}_


*E.W.F*


By

Mrs Bb

mom muhseen


wattpad name

Humaira3461



🅿️.......23



Kaya na canza sai tuttura baki nake kamar yana ganina na saka turare sannan na dauko wata hijab din shigen kalar kayan jikina yau harda jikka na dauka, inajin araina inama ace gidanmu zai kaini rabona dasu wata cikin na shidda kenan, ina kewarsu kuma suduka ba wanda yake tunanin yazo inda nake,


Ina fitowa compound din na hangoshi shida Aneesa tsaye jikin motar kamar zata shige jikinsa, da karfin gaske kirjina ya buga yadda kuka san na juya na koma ince ban zuwa, hango yah usy danai yasa ban koma d'in ba daina kallon su nai na bada duka hankalina kanshi,ganin zai yanke hanya yasa na d'aga murya nakirashi.


"Yah usy kaji"


Duk wanda ke area saiyaji muryata nasan kuma sunjini, nai kamar ban gansu ba na taka har gabansa ina murmushi hanuwansa duka cikin aljihu yake kallona, kamar marar lafiya yace "Ya akai yine?"


Na b'ata rai ina cewa, "wai menai maka ne? Kwana biyu kenan kanata fushi nayi ma laifine?"


Kallon da yake mun na kasa fassarashi ya lumshe idonsa ya bud'e yana cigaba da kallona kafin cikin sanyin murya yace, "inason na kaurace makine?"


Zaro idona nayi nace, "ni kuma? Danai maka mekenan?"


Yar hararata yayi yajuya indasu Yah Asaad suke yace, "gashi can yana kallonki kin tsaya kina mun magana"


D'an murgud'a baki nai nace, "to saime? Wai meyasa kake haka aibani nai maka ba ko"


"Amman dalilin wa akai mun? Kije yana jiranki"


Kamarna rusa ihu "nafasa ba zanje ba.......na juya zan tafi kuma har raina dagasken tafiyata zan nakoma ciki, saurin rik'o hijabina yayi baiko motsa daga inda yake ba, juyowa nai ina kallinsa shima ni yake kallo yace "inhar bakya tsoron yaganmu tare yau da daddare bayan isha'i kizo muyi karatu"


Jinjina kai nayi nace, "zanzo, a ina zan sameka"


Da hannunsa yanuna mun,"guiden, ai yayiko?"


Rausayar dakaina nayi kurin sannan yai mun murmushi ya shige ciki ya barni nan, kafafuna naji na kasa d'agasu daga wajen duk da inajin yadaina kallona yanzu, tambayar kaina nake inje ko kawai na koma ciki abuna, watau da Aneesar ma zamuje inda zamu d'in? To indai da itane na fasa bazanje ba duk tsoron fad'ansa da nake na danne na nufi inda motar take, a tun zure nake na bud'e bayan kenan na ganta zaune gefensa ta d'ofa kanta jikin shoulder d'insa, ai saidai naji na maida kofar da karfi sannan na wuce fuuuuu nai cikin gida, dakina nai burki na cire hijabin nai wurgi dashi na zauna bakin gado jagwab, huci kurin nake fiddawa duk kokarin na kauda abunda nagani na kasa, na fad'a kan gadon na dora filo bisa kaina ina cikin wannan halin kawai akafara knocking kofata, bansan ko waye ba amman bazan b'ud'e ba ko Abba ne kuwa a yadda nakejin wani irin abu ga kirjina da mak'oshina, ko kadan ba abar bugun k'ofar ba zuwacan kuma saiga kira a wayata filon na dauka na ringa bugunta dashi kamar ita tai mun laifin, muryar Babaah uwani naji tana mun magana.


"Murjanatu kina jina kuwa? Bud'e mun kofar mana inata kwankwasawa"


Ban kawo ita bace na dauka shine ya biyoni yana buga mun, saurin budewa nai na shige toilet na kunna famfo ina saita muryata nace, "babah gani nan bayi lafiya kuwa?"


"Inkin fito na dawo to"


Ajiyar zuciya nayi na wanke fuskata na bud'e na fito...........cak na tsaya bakin k'ofar ganin sa tsaye rungume da hannuwa yana kallona, cikin wani speed na juya na maido k'ofar zan datse hannu d'aya ya sanya da karfi ya bud'eta, duk kokarin dannewar da nake abanza dole na saki kirjina dagawa kawai yake, daga bakin 'kofar ya tsaya yana mun magana.


”ki fito nan ko kuma in shigo”


Zai aika shiyasa na fito d'in amman ko saud'aya ban dube shi ba, hijabina ya dauko yana mik'o mun ”saka ki wuce muje”


Idona tab da kwalla nace, "Aa kaje nidai, amman bazan iya zuwa ba aiki zamuyi da babaah uwan...........ki saka kafin na sab'a miki anan wujen!”


Afirgice na na durkushe na saka kuka ina cewa, ” ni bazan bika ba, ai dai aiki zanyi ko kuma in banyi ba momy fad'a zatai mun”


Jiyai har juwa na daukar sa saboda tsananin b'acin rai, watau babu ma wanda ya raina kasa wayau irin wannan yarinyar, duk yadda kukanta ke dukan sa yake sashi sassarfa mazewa yai cikin tsananin kishi da masifa yace, ”kinsan zakiyi aikin da fari meya fiddoki? Usman ne yace karkije ko? Dake nake magana nace usman yace karkije ko??”


Naga rigimar data fi karfina rikicewa nai ina shashshekar kukan hawaye kaca kaca da fuskata, ina haki ina cewa ”ba ruwan sa, ni baice mun komi akan ka ba,nice nace na fasa idan na biku zuciyata bugawa zatai"


Kanshi har jijiya saida ta fito yadda ya nufoni na dauka daukeni da mari zai, don ya fusata sosai cikin wata kalar murya yake cewa ”taki zuciyar kad'ai kika sani, kanki kawai kika sani jannah! Watau ni tawa kota buga ba damuwarki bace shiyasa kikeyin dukkan abunda zaisa na mutu ku huta ko!!!”


Ya fad'a da karfin gaske saida na toshe kunnuwana, Aneesa ce da hindu suka fad'o dakin saboda jin tsawar da yake daka mun, da jajayen idanun sa ya kallesu cikin dakakkar murya yace, ”ku fice anan”

Fittt kamar walkiya suka fita, kerma kurin nakeyi sosai kamar an sakani freezer na kasa fahimtar maganganunsa, wadanda suka dakar mun yar zuciyata da bata da wani k'wari akanshi, muryarsa ta dishe sosai ya sake cewa cikin k'uluwa,


”karkiyi fatan na sake ganinki dashi, Jannah kiyi addua karna sake ganinki dashi komi zai iya faruwa, ki tashi ki saka hijab d'inki ki wuce muje"


Sosai nake kuka jikina har jijjiga yake, tabbas na tsorata da yana yinsa amman bazan iya had'iye maganata ba, saidai ya kasheni jefa nai da hijabin ina haki ina cigaba da kukan, magana nake muryar bata fita sosai.


”bazan daina magana dashi ba saika gaya mun dalili, akan me zaka rabani dashi bacin kai kana can da wata, abunda kuke yi nibana yinsa ba abunda ke tsakanina da yah usy..........fizgar da naji yai min yasa ban idasa ba idonsa kamar jini zai fito, rik'on da yai mun jinake kamar an saka igiya an daureni saboda azabar zafi, idonsa kamar zai fad'o k'asa har wasu ruwa ke taruwa acikinsu, yadda naji kirjinsa na bugawa kadai ya isa yagigita ni sakina yayi yana layi kamar zai kifa yai hanyar kofar fita, baijuyo ba ya sake cewa ”ina mota inajiranki”


Zaman yan bori nayi cikin d'akin ina kuka kamar Allah ya aikoni, kakar bazan je ba ssboda yadda nai banza da maganar dayai mun, ban san meyasa nakejin zafinsa sosai ba idan na tuna yadda na Ganshi da Aneesa da safe da kuma yanzu, kamar ana hura mun wuta haka nakeji a zuciyata naje na wanko fuskar sosai sannan nazo na dauki hijab d'in na fita, a kofa muka had'u da hindu tace "Jannah meyafaru? Duk hankalina ya tashi wallahi, dukan ki yayi?"


Girgiza kai nayi ina cewa "idan na dawo munyi maganar Hindu,kice ma babaah uwani naje indawo don Allah"


Cikin rashin jin dadi tace, "Ai yama sanar da ita, kije kawai ba komi amman don Allah jannah kibar kukan"


Share kwallar nayi nace a sanyaye "to hindu nagode sai nadawo"


Ban bita falo ba nabi ta can baya saboda kauce ma idon momy, inda motar take dazun yanzun ma tana nan,kofar baya bud'e take na isa wajen motar na shiga ina kilewa can jikin k'ofar na jingina kaina jikin kofar yatsuna kurin nake tsifa kamar zan cizgesu, haka mannir yaja motar muka fita mu uku babu aneesa bana son ko kadan na tuna abunda ya faru cikin yan mintuna da suka wuce, har tsikar jikina tashi take idan ina tuna rikicin, tunda muka dauki hanya kamar baya cikin motar lamo yai cikin kujerar ga wayarsa anata faman kira kamar bayaji, kuma nasan sarai idonsa biyu, nidai ko tari banyi ba wata babbar plazer naga mun tsaya kamar bazai fita ba haka ya fito ya shiga, tafiyar ma kamar zai fad'i.


Mun dauki minty talatin muna jiransa sai gashi ya fito ma'aikata wajen dauke da manyan ledoji sai kuma wasu matasa daketa daukar hoto dashi, murmushin karfin hali nake gani akan fuskar sa badan yana so yakeyi ba, har aka gama saka kayan aBut bai taho ba zuwan can wasu yan mata suna ganinsa suka hau washe baki, suma saida sukai hotunan dashi sannan ya taho.


Ayanzu na gane cewar ba Aneesa kad'ai na tsani ta rab'esa ba ko wacce mace inajin kamar nai aman zuciyata, rufe idona nayi inajin yadda har yanzu take buga man.


Shigowarsa yasa naja ajiyar zuciya can kasa a duk sadda yake gefena numfashina kansa yana mun wahalar shak'a, wani yana yi ne da nikadai nake jin yadda nakeji, tafiya muka cigaba dayi kamar kurame har shidda ta kusa na yamma, wata unguwa muka shigo inata kallon wurin kamar nagane sa ban ida tantancewa ba naga mun tsaya akofar gidanmu, wannan shine bazata yau nice nazo gida? Wayyo dad'i karka kasheni dan danan fuskata ta washe da murmushi da farin ciki duk da ga alamun kuka nan, still har sannan kishingid'e yake idonsa rufe kamar yana bacci, naji yamun magana da muryarsa data zama so cool,


"Zan dawo bayan sallar isha'i mutafi, ga kaya nan kice kekika kawo musu"


Wani abu ya sokeni na kasa fitar, godiya nake so nai mashi bakina yayi nauyi, saboda nasan na zuba rashin kunyata d'azun sai naji nauyinsa ya kamani, inajin ban kyauta ba duk da kuwa shima yana da laifinsa, uffan bai sake ce mun ba kuma yasan zaman danai magana nake son yi masa amman ya shareni, dole na bud'e na fita zuwa lokacin duk kayan da ya siya a shago dazun mannir ya gama shida dasu cikin gidanmu, siyayyace mai tarin yawan gaske har zuciyata nadamar abunda nayi ta kamani, meya shiga kaina danai masa haka?

Saidai naga har sun bar kofar gidan, kamar kwai ya fashe mun aciki haka na lallab'a na shiga gidan, da zainab mukaci karo wata kara ta saki tana sakin butar da take alwalla da ita, aguje tazo ta makalkaleni tana murna ihunta ya fiddo innamu, ai tana ganin nice itama kamar ta taka rawa saigani ina kuka na rungume innamu, saboda ba kadan nai kewarsu ba kasa sakinta nayi inata kukan,farin ciki kamar yai mata me tace "haba murja minene na kukan to, muma munyi kewarki sosai agidan nan"


Ina kukan nace, "Amman arasa wanda zai neman yaje inda nake innamu? Kamar kun siyar dani fisabilillahi, ko yayanmu ai yaci ace yaje yaganni tunda suna waya dashi Yah Asaad d'in"


"Yanzu dai kiyi hakuri zamu samu lokaci duk muje muganki da inda kike, tashi muyi sallah tukunna"


Na cire hijabina nace , "ina baba yake zainab"


Tana shimfid'a abun sallah tace, "ai baba yanzu ba zama bakisan kasuwa yake yi ba, yallab'ai ya bud'e masa wani shago a sabon gari, wallahi karkiso kiga dukiya Yaya murja, sannan yazo ya siya mun keken s'ak'a kinga duk unguwar nan ba wanda baisan ina sak'a ba, har daga wani waje zuwa ake siyen kayana, labarin fa da yawa bari nayi sallah"


Bakina kasa rufesa nayi jin wani sabon labarin daga zainab, sai lokacin na lurax da sauye sauyen cikin gidan baki d'aya, anyi tayil ga generator nan harda rizabuwa akai musu, sannan cikin dakin tv ta bango babba ga babbar freezer nan, komi ya sauya sabanin sadda na tafi a cikin wata shidda aka samu wannan cigaban, mezan cewa yallab'ai nikam? Jinake baki yayi kadan wajen yin godiya dame zan saka masa a rayuwata?


Har nayi salla sake sake kurin nake a zuciyata, babu wanda ya kawo cigaba da sauyi a cikin rayuwar mu irinsa, wace irin kauna ce yake mana haka???


Innamu tace, "wannan siyayyar fa murja?"


Na tuna maganarsa kafun ya tafi,

Cikin sanyin jiki nake cewa, "ni na siyo maku innamu ku samun albarka"


Ai kuwa nasha albarka kamar ba zata bari ba da aka zube kayan ni kaina na tsorata ainun, shaddoji kala biyar atamfofi da less biyar biyar, iyayen kayan shafa da mayuka da shampoo burjik, turaruka gasunan na baba daban shida yayanmu saina matan daban, sai takalma da jikka na zainab dana innamu sabida farin ciki innamu harda hawayenta, tace "murja hakika haduwar mu da wannan mutumun alkairice, don Allah kicigaba da yimusu biyayya kina kyautata masu,nasan duk inda kake dole ka samu kalubale murja ki rufe idonki da kunnanki,kiyi abunda ya kaiki karki sab'a masu,shima kuma ki kasance maiyi mashi biyayya don kyautatawar da yake mana baki bazai iya liassafi ba, bayan shago daya bud'e ma babanku kingamu da injin wuta idan an dauke, bamuda matsalar ruwa ga sana'a yabamu nida zainab ni keke napep ya siyamun ake mun haya, duk sati dubun nan goma ake kawo mun, yayanku yana makaranta komi na dawainiyar karatunsa shine ga kudi da yake bashi, sannan ya sakaa zainab ta koma makaranta harda islamiyya, murja meyai saura? Inajin kiris babanku ke jira yace ya bashike,don inhar ba sonki yake ba ai bazai wannan wahalar hidimar damu ba, nikam ina fatan. Ace sonki yake din koda hakan mu biyasa wahalar da yake damu"


Ab'oye nake share kwallar dake zubo mun, nace "innamu bafa sona yake ba kawai dai shidin mai alheri ne, abun hannunsa bai tsole masa ido ba, duk wahalar da yake daku nima cikin yimun yake, bakin rai bakin fama yana kokarin ganin wani bai cutar dani agidan su ba, ina zaune kalau innamu bansan dame zan saka masa ba"


Muryata harta karye saboda raunin da nakeji a zuciyata, kamar na dawo da baya na wanke laifina danai masa,


"Bamu da wani abun da zamu saka masa dashi sai addua, ina fatan watarana yazo da buk'atar aurenki wallahi babuja zan amunce, haka babanku wannan ranar yake burin zuwanta,"


Munsha fira sosai dasu mukaci abinci tare, kowa cikin farin ciki yayanmu ne ban gani ba saboda makaranta hostel yakoma don yafi jin dadin karatun acan, sai isha'i baba ya dawo yadda naga yacanza abun ya mun dad'i kaface kuri baida ita,amman ya samu lafiya jikinsa yai kyau, yanada yan sandunan nan da ake dogarawa dasu.

Shima dai maganar Yah Asaad dince yajeta yimun yana ta fad'ar alkairinsa,yana sake jaddadamun na rik'e amana inyi masu biyayya ba ruwana da abunda ba'a sakani ba, in kauce ma abun wani sanan yace "ina adduar cikin dan lokaci inhar sonki yake yaron nan, yazo ya gaya mun ni kuma nai alk'awarin ko bayan raina yayanku ya aura masa ke, amman baxan gaggawa ba har sai shi yace yana so"


Zuwa yanzu zuciyata tagama yarda da cewar tabbas yana sona d'in, dana zauna na ringa tunano abubuwan da suke faruwa, har kawo yau d'in nan zargina ya tabbata amman ban idasa yarda ba tunda bakinsa bai furta ba, sai na tambayi kaina "shin inya furtan ni ina sonshi kenan???"


Tambayar da tasani cikin wani sabon tunanin, ban samo amsar ba abunda kawai na sani shine ina tsananin kishinsa, idan naganshi da wata zafin da nakeji kamar zai sumar dani, bansan yaushe na fara jin hakan ba amman halin da nake tsintar kaina kenan, sannan idan ina kusa dashi jinake tamkar wurin yaimun kadan, kwarjini yake mun muryar sa har tayar mun da tsikar jikina take, komi ya saka kyau yake ga idona ba abunda ke fizgata irin sassanyen murmushinsa da kallonsa,


"Yaya murja kiketa murmushi bama jina kike ba"


Dafe kai nayi ashe tunanin sa ma danake murmushi nakeyi ban sani ba, dole na bata hankalina tana ta ban labarin makarantar su, da costumer dinta.


Sai wajen karfe goma ya dawo na dauka ma kwana zanyi, saida ya shigo ya gaida su baba da innamu ya aje masu katuwar takaddar nama da kud'i bandir din dari biyu.


Har waje suka rakoni jinake kamar na koma amman ya zanyi dole na tafi, muka shiga bayan mu duka mannir yaja muka dauki hanya, ga garin in dare yayi go slow ake tarawa sosai.


Yanzun ma tunda muka taho uffan baice mun ba, f-cap dinsa ya jawo ya rufe fuskar sa daita,da yake kayan da yazo dasu d'azun basune jikinsa ba alamun yayi wanka kenan, suma din kananu ne bai cika saka manyan kaya ba sai juma'a da litinin, ganin cewar dama ce dazan yi amfani da ita in bashi hakuri saboda in mun isa gida ba lallai ya sake bi takaina ba,bai tab'a yin fushi dani irin wannan ba ada idan muna tareshine yake kokarin ganin nai masa magana yana jana da fira, amman yau kamar muna tare da gunki haka ya nuna.


Kwalla ta cika idona ban san meyasa yanzu kuka baya mun wahala ba,kodan hada kari da cewar zuciyata tayi matukar rauni akansa, zoben daya tab'a bani naketa jujjuyawa ina wasa dashi, ina tuna ranar daya saka mun shi ranar da zai tafi yabarni, na tuna saddana kama hannunsa na rik'e yana mun murmushin dake lumar dani, yake cewa


_Kona bar miki shi_


Alokaci guda murmushi da kwalla suke fita a fuskata, ban damu na goge su ba ban dubi inda yake ba nake magana, don nasan ba bacci yake ba duk motsin da zan yana jina,shiyasa ban damu saiya dubeni ba cikin muryata da ta karye ta zama so cool nake cewa ahankali duk da nasan mannir zai iyaji,amman ban damu ba burina ya fahimceni ya kuma daina wannan fushin dani.


”Yah Asaad I'm sorry”


Na fad'a inajin kamar naita masa kuka, na danne kukan shiyasa muryata ta fito like kamar inayin kukan, nasan yajini sarai magana ce bazai mun ba..........


"Bakina yayi kadan wajen yimaka godiya amman duk da hakan dole na gode maka akan dawainiya da kake da ahalina, Allah ya saka da alkairi"


Sai lokacin naji yai magana inba dan ina gefensa ba da kila bazanji ba,saboda yadda muryar tai silent sosai.


"Ba danke nayi ba, ban kuma yi donki gode mun ba"


Hawayena suka silalo tabbas zafina yakeji, ya zanyi naja majina ina saka kallabina ina goge fuskata, duk da wasu na sake zuba nace masa.



"nasan ba danni kayi ba, amman ya zama dole na gode maka koda baka so, nasan na maka laifi don Allah ka yafe mun, bansan mekake tunani akaina ba amman har cikin zuciyata ba ina nufin nai maka rashin kunya ba, Yah Asaad ka fahimceni please! Bana cikin hayya....ya....cina duk nai......nayi abunda nayi.........."


Na karashe ina yar shashsheka kasa kasa don ko karfin yin kukan ma bana dashi, ko tari bai sake yi ba hakan ya sake tun zira kukana na saka fuskata cikin hijabina nayi tayi harna gode Allah, har muka iso gida bace mun ba nima ban sake cewa komi ba, wurin parking mannir ya isa yai parking, saiya fita kurin ya barmu.


Zaman me zanyi to? Kawai nima na bud'e zan fitan kenan naji ya rik'e hannuna sosai, saida na runtse ido saboda damkar da yai masa kamar zai karyani,


"Wayyo Allah na, hannuna zaka balla mun plz"


Na fad'a cikin jin zafin rik'on dayai mun,


"Rufe mun kofar motana"


Dole na jawo murfin na rufe na zauna inda nake, yana nan yadda yake tsawon lokaci baice komi ba, da kamar nai magana na fasa saida ya mulmule yace,


"Maimata abunda kika fad'a dazun"


Bai saki hannuna ba amman ya sassauta rikon da yaimun, gabana bugawa kawai yake sosai sai motsa baki nake na kasa cewa komi, saida ya sake cewa "kin zama kurma ne?"


Bansan manayi maganar cikin shagwab'a ba, "to Aidai kaji me na fad'a ko?kuma saina sake maimaitawa"


Ajiyar zuciya yayi yana yin kasa da murya, "kidaina mun shagwab'a please"


Yadda yayi maganar saida tsikar jikina tatashi,kunya ta kamani wallahi ban san nayi ba,


"hum inajinki maimaita mun"


Runtse idona nai sannan nace "nasan na maka laifi don Allah ka yafe mun, bansan mekake tunani akaina ba amman har cikin zuciyata ba ina nufin nai maka rashin kunya ba, Yah Asaad ka fahimceni please!"


"Abunda nace kenan fa"


Wata ajiyar zuciyar ya sake saki yace, "baki kai karshe ba ai,ba kince baki cikin hayyacinki duk kikayi ba? Meya jawo fita hayyacin???,"


Duburcewa nayi saboda sai yanzu naji nayi hauka amaganata dazun, ina in ina nace "Aa....dama.......daman ba haka zan.....zance ba"


Gyara zamansa yayi duk da d'an duhun dake wurin akwai dan haske kadan dayasa muka had'a ido dashi, saurin daukewa nai saboda kalar kallon da yake mun.


"Kina so mu kwana cikin motar nan?........Aa don Allah wallahi bana so kayakuri"


Cizon lips dinsa yayi yana cewa, "ok kiban amsar tambayar danai miki yanzu nan"


Shashshekar kukan karya na fara ina cewa, "nifa ban sani ba, don Allah kayakuri Yah Asaad............."ya salam! Jannah nace kibar yimun shagwab'a ko"


Tsitt nayi saboda ni nama mance, kuma ban sanin inayi na rasa meke damuna jinake kamar zan zare anan inda nake, cire F-cap din yayi yana cusa hannuwan sa cikin gashin kanshi,ya fesar da huci duk na tsorata cikin karma nace,


"Ka......kayakuri don Allah"


Muryarsa ta shak'e yace, "kiban amsar tambayata, meya kawo fitar hayyacin dazu? Tunda kince bakya cikin hayyacinki"


Jujjuya hannuna nake bansan me zance ba, duk abunda zan fad'a zai fallasani, zai tona mun asiri bacin ban shirya ba bana son ya fahimci cewar ina cikin wani hali akansa,


"Ohh my god, ba zakiyi magana bako?"


Yafad'a yana juyowa yana fuskantata idonsa sun wani juye, kusancin mu yasa kamshinsa kamar zai zautani, na matse jikin k'ofa ina turo baki nace,


"Nidai ka matsa to zan fad'a maka"


"Nak'i na matsa din, inbaki bud'e baki kin mun magana ba wallahi nan zaki dawo"


Ya nuna cinyarsa zaro idanuna nayi ina rufe bakina da hannu, gabana duka kurin yake ina rawar murya na b'oye fuskata cikin abaya nake cewa,


"To ba......bakai bane ba, ni....ni....natsani ganin ku tare, saita ta wani shige maka ko? Da safe ma ba haka ta ringa kama maka han.....hannu ba kuma ko hanata bakai ba, dazun kuma amota akan shoulder dinka fa.......na.....naganta.......sai kuka ya kubce mun,ina tuna yadda naji kamar zan tashi sama don bakin ciki, dunkulewa nai wurin ina kukana kasa kasa............cikin wata voice dinsa mai gigita mace yace, "to kibar kukan please"


Makale kafad'a nayi murmushi ya saki yana sake cusa hannunsa acikin kanshi, jiyake kamar yana shawagi ne asama shikad'ai, kasa-kasa yake cewa "in bakiyi shiru ba nan zan doraki wallahi"


Wani abu na had'iye muk'ut dole na tsayar da kukan, inata jan ajiyar zuciya ga wata irin kunya dake shawagi dani, kamar na b'oye nakeji jinai ya kira sunana............


"Jann"


Lumshe idona nayi na kasa amsawa, ya sake kirana still,


"Jann"


Daker na amsa can kasan makoshi, "uhmm"


Magana ya cigaba dayi cikin natsuwa da tausasawa, "yadda kika fita hayyacinkin nan dazu nima nafita nawa fiye da naki, yadda kike ji dakika ganmu da Aneesa jannah inajin fiye da haka idan na gankis da usman, taya kike tunanin zuciyata zata huta???"









Mom muhseen✍🏻