25
by @mommuhseen
*_💔JANNAH💔_*
_{A TRUE LIFE STORY}_
*E.W.F*
By
Mrs Bb
mom muhseen
wattpad name
Humaira3461
*END OF BOOK ONE*
🅿️.......25
Gaba d'ayan su suna zaune reception acikin wani private hospital da aka kawo Jannah, Asaad ne d'urk'ushe k'asa ya had'e kai da guiwa ba abunda ke tsiyaya a idonsa sai ruwan hawaye, zuciyarsa kuwa karma atona don hayak'i take saboda wutar dake ci acikinta, usman yana daga can baya shima ya had'e kanshi da guiwar Hindu har yanzu kuka take saboda ta girgiza da abunda akaima Jannah, kadan kadan tace "Allah ka tona asirin ko waye, Allah karka barshi ka saka ma wannan baiwar Allah"
Abba ne gefen Asaad hakuri kurin yake bashi yana bashi baki, don ya jima da sanin cewar yana Son yarinyar tunda shi ba yaro bane, momy da aneesa suna zaune waje guda sai khalid dayaja tunga wayarsa kurin yake dannawa hankalinsa kwance.
Kusan awa guda kenan da suka kawota asibitin, kamar gawa haka suka daukota, saida akai rikicin gaske kafin aka ansheta saboda sunce case din rapping babban case ne saida d'an sanda suke duba mutum, Abba hankalinsa tashi yayi don in akace a sanyo yan sanda sunan sa ne zai lalace, siyasar sa kuma ta tab'u shiyasa yai duk yadda zaiyi aka ansheta, a ransa kuwa soyake ta farfad'o duk wanda yai wannan abun inhar acikin gidan yake babushi babu koma waye, yagaji da wannan masifar tayima yan aiki fyade acikin gidansa shekara hudu ana fama da abu guda to yagaji hakan, wannan karon dole ai bincike agano ko waye...........likitan da suka shiga da Jannah ce ta fito dayake macece fuskarta a kuntace kafin ma tai magana Abba da Asaad sun mik'e sunbi bayanta zuwa office, yadda kukasan tafasashen ruwa haka jikin Asaad ke kerma yana jijjiga, saida ta gama rubutu cikin file din Jannah sannan ta dago tana cewa, "Alhaji anzalinci yarinyar nan, wannan case d'in bai kamata abarshi haka ba, ka kuwa san irin raunin data samu? Anan asibitin gaskiya ban tab'a samun wanda akaima zalinci irin wannan yarinyar ba, ansaka karfi sosai wajen yimata fyad'en, don haka zamu kira police yanzu"
Ta fad'a tana fara danna telephone dake bisa table dinta, cikin zafin nama Abba ya dafe wayar cikin tsoro yake mata magiya yana cewa, "doctor ki rufa mun asiri wannan case din na cikin gidana ne,idan yan sanda suka shigo ciki ina cikin damuwa sosai, wallahi da kaina zan dauki tsatstsauran mataki akan koma waye,dole zanyi bincike sosai wannan abun bazai tafi haka ba insha Allahu"
Asaad yana jikin k'ofa ji yake kamar ya kwashe Abba da mari, taya za'ai ya hana a sanar da hukuma wannan abun, kodan ba yarsa bace akaima wa? Tausan kanshi da kanshi yake saboda komi ma zai iya faruwa idan ya bud'e baki yai magana, jayayya akaitayi tsakanin Abba da doctor daker da sidin goshi ta hakura sannan ta soma masu bayani.
"Ta samu tear in and out, mun kwashe awa wajen yimata d'inki, sannan abun ya bugeta sosai don tunda aka samu ta farfad'o fizge fizge kurin take in ba'a sa'a ba kwalwarta na iya tab'uwa, munyi dukkan abunda zamuyi yanzu haka Allurar bacci mukai mata saboda ta d'an samu natsuwa ko yayane, rashin yin baccin zai iya sawa zuciyarta ta buga zamu rik'eta anan na kwana biyu muga yana yin jikin nata, ga magunguna da ku siyo da allura sai bill din da zakuyi yanzu"
Abba ne ya amsa yana mata godiya suka fito, Asaad zubewa yai bakin kofar yana kerma hawaye na kwarara daga idonsa, "Abba mezance da iyayenta? Wane irin zalincine wannan akai mata,wallahi tallahi ko waye saina kashe shi! Bazan kyalesa ba kuma nasan ko waye zai aikata wannan abun............"Aa Asaad wannan hukunci bakaine zakayi shi ba, kabar komi Hannuna wannan karon dole indauki mataki sosai akan wannan abun, kayi hakuri kar ka yanke hukunci cikin fushi,mu samu ta dawo hayyacinta shine fatan mu sannan duk abunda za'a sai ayi"
Daker ya shawo kanshi suka je suka biya kudin aka sai magungunan suka je suka ba nurse din dake cikin dakin, ta taga yake lek'enta hawaye masu zafi suna zubar mashi ba yadda Abba baiyyi dashi ba yazo suje gida k'iyawa yayi dole aka barshi nan shi kad'ai, daga baya aka turo babaah uwani don ta zauna da ita, a ranar usman shima ya kwanta mugun zazzab'i amai ba kakkautawa ba arziki shima aka kawosa ranga ranga, cikin shida Asaad an rasa wanda abun yafi dukansa saida ya kwana guda aka sallamesa yai muguwar rama kamar yai shekara yana ciwo,don yafi Asaad zabgewa ainun shi firgicewa yai gaba d'aya ma kamar wanda yafita hankalinsa,ko wanka bai karayi ba daga randa abun ya faru abinci sai Abba ya tsaresa sannan zaici kadan, ranar da aka cika kwana biyun na farka daga wannan dogon baccin.
Ahankali nake bud'e idona ina sauke su akan rufin silin din dakin, idanuna kawai nake juyawa ina kokarin gane inda nake Motsin da naji ne yasa na juyar da kaina gefe inda naji motsin, bakina da naji ya bushe yai mun nauyi naji nace, "Babah uwani"
A firgice ta juyo kaina ganin nice yasa ta saki hijabin da take linkewa tayo kaina a guje tana murna ga kuma hawaye nan sun cika idonta,
"Murjanatu kin farka ko? Sannu murja,sannunki ubangiji ya kara miki lafiya"
Kallonta nake kamar wadda tatashi daga hauka bangane metake fad'a ba, na dubi hannuna naga an saka carnula drip nata shiga, na dawo da kallona kanta cikin shakakkar muryata da bata fita sosai nace, "ina ne nan Babaah? Menene ya sameni ake samun ruwa?"
Kuka Babaah ta fashe dashi wiwi kamar karamar yarinya, sosai take kukan ta kasa cewa komi ban san me take ma kukan ba, sai na yunk'ura zan tashi naji na kasa bayana ya rik'e da k'uguna, sannan daga can k'asana naji ya daure ga wani zago zogi da nakeji a wajen, koma wa nayi na kwanta ina rufe idona na fara tunanin meya saman?tun daga safiya zuwa rana da marecen, fadana da yallab'ai,tafiyata dashi zuwa gidanmu, dawowar mu har zuwa fallasa soyayyarmu da mukai rabuwar mu dashi na tafi zuwa cikin gida, tiryan tiryan nake tuna komi naje na dafa indomi na dawo nayi fitsari tare da wankan tsarki,na koma dauko indomin na dawo daki..............jinai zuciyata ta dage ta buga da karfin gaske, saboda abunda ya faru dani bayan kwanciyataa bacci cikin wata irin gigita na fasa wata irin k'araa mai sauti mai firgita duk wanda yajita, Babaah uwani aguje ta fita daga d'akin hannuna nasaka na fincike drip d'in tare da carnula jini ya samu damar fita ba kakkautawa, ihu kurin nake ina kururuwa ina dukan bango hular da aka sanya mun na fice gashina ya watse kuka kawai nake ina dukan bango, Babaah uwani ce suka dawo tare da doctor da Asaad sun tsorata matuka da ganina cikin wannan halin, doctor kasa tab'ani tayi saboda fizge fizgen da nake jinake dama in mutu bana son na bud'e idona inganni ina cikin wannan duniyar, "kaga ka rik'eta saka auduga danne hannunta dake zubar jinin, daman nasan hakan saita faru shiyasa nake zullumin farkawarta"
Inji doctor d'in kwalla ne suke layi a fuskar sa jikinsa na rawa ya iso inda nake, k'amshin turarensa na naji ya sake haukata yana yina saboda shine abunda hancina yaji mun alokacin da ake aikata mun wannan zalincin, wata irin bangaza nai masa ina son dirowa daga gadon, kokowa muke dashi duk karfinsa amman ina neman gagararsa yadda bake kuka nake zubar kwallah shima kwallar yake zubarwa, muryarsa na rawa yake mun magana.
"Please Jannah, please stop crying ki natsu bakida lafiya,don Allah ki natsu ki taimaka mun kibar wannan abun, bakida isassar lafiya karki jawo wani abun kuma"
Lallashina yake yayinda hawayensa suketa kwaranya ahankali kuma na fara sakin jikina saboda gajiyar danai, nishi nake ina jan numfashina dake neman daukewa, turarensa ne natsani injisa cikin hancina a duniya yanxu ba abunda nake tsana sama da turaren jikinsa, sannan na tsani inganni raye ban mutu ba, so nake ya sakeni yak'iya saboda gani yake sake buge bugen zanyi, cikin masifa da kufula na fizge ina cewa, "ka saken! Karabu dani nace!!, wayyo Allah na nashiga ukuna innalillahi wa inna ilahir raju'un, hazbunallahu wani imal wakil ya Allah na rok'eka ka dauki rayuwata, don Allah ka dauki rayuwata bazan iya ba Allah ka taimakeni na mutu, na tsani duniyar nan da duk mutanen dake cikinta, wayyo Allah na nabani na lala..............hannunsa ya saka ya rufe mun bakina, duk kokarin kwacewar da nake na kasa, duk wanda ke dakin saida ya zubda kwallarsa kafin kuma Abba ya shigo shima hankalinsa tashe, yadda naketa kuka ina surutu duk da rufen bakina dayai baisaka na fasa maganganun ba, zuwa can kuma naji juwa na daukata numfashina yana daukewa daga haka ban sake sanin inda kaina yake ba.
Silalewa k'asa Asaad yai yana saka kanshi cikin kafafunsa yana kuka kamar wata mace, abun duk wanda yagani duk taurin ranka saiya tab'a maka zuciya shiyasa har Abba saida ya share kwallah, tare suke da Hindu itama ta isa jikin yayanta tana kukan, doctor dince tace "please kuyi hkr na dubata kuje daga waje"
Fitowa sukai daidai isowar usman ganin kowa na kuka hankalinsa yai mugun tashi, ya dauka mutuwa Jannah tayi jikinsa na rawa yake ma hindu magana, "Hindu meyafaru? Jannah tafarka ne? Don Allah karkice mun mutuwa tayi don Allah kice mun tana nan da ranta............saidai yaji Asaad kamar daga sama ya kaimasa wata shak'a yana dakashi ga bango yace, "karya kake Jannah ba zata mutu ba, zata cigaba da rayuwarta insha Allahu"
Usman bai wata wata ba shima ya cakumi wuyan Asaad yana haki yace, "kaine kake karya bani ba, pretending kurin kakeyi waya sani ma ko kaine ka jefata wannan hal.......jikake tas tas tas cikin wata kalar zuciya Asaad ya kwasa mashi marika,yana yin jifa dashi gefe yana huci zuciyarsa kamar ta fito, da gudu Abba ya iso yana salati.
"Menake gani haka Asad? Usman kunyi hauka ne? Yau junan ku kuke fada akan Mace? Innalillahi wa inna ilaihir raju'un"
Daidai zuwan su momy da fareeda da Aneesa, Abba kwalla sun cika idonsa yace, "Abunda baku yi kuna yara ba shine kukeyi da girman ku, mace zata had'aku Asaad? Usman akan kace kake cinkwalar yayanka? Hafsat kina ganin abunda hake faruwa kuwa? Fad'a suke da juna akan Jannah hazbunallahu wani imal wakil"
"Abba bakaji me yake fad'a ba, gabanka fa yake kiran mutuwa zatai? Wallahi ina tantama idan ba usman ne yai wannan abun b...........karya kake munafuki kaine babban wanda za'a zarga adaren ranar ina kaje har karfe shabiyu? Ba kana tare da ita b"............wani kukan kura Asaad yai ya dira saman usman dukan sa kurin yake yana zubda hawaye, yama kasa magana bakin cikine kamar zai kasheshi........Abba kanshi hankalinsa yai mugun tashi yana kokowar rabasu ya kasa momy na gefe tana kyalkyala dariya ita da fareeda, duk abunda suke Hindu na kallon su da taimakon wasu maza Aka samu aka raba Asaad da Usman, don har bakin usman da hancinsa sun fashe kowa huci yake kamar wasu zakaru, Abba ya zama abun tausayi yake magana.
"Idan Kuka sake wannan fadan ban yafe muku ba Asaad da usman, ni zaku kunyata cikin taron mutane? Mace zata had'aku fad'a ban tab'a ganin ranaku masu munin wad'anan ba"
Momy ta tako cikin makirci tace, "kayi hakuri Abba, harda kuruciya kai Asaad ai babba ne bai kamata kabiye ma kanen ka ba, kuma inhar kasan bakai ba miye na tada jijiyar wuya............idanunsa kamar zasu fad'o yace "meeee? Mekika kace? Sake maimaitawa"
Kauda kai tayi tana jan hannun Abba tana cewa, "karka biye su hawan jinin ka ya tashi,idan mun koma gida sai ayi wacce za'ai"
Wani irin duka ya kaima bango jiyake zai iya kashe matarcan kowa ya huta,shi zatai ma munafurci so take ta juye laifin kanshi ga dukkan alamu kuwa, amman Ai Abba ba haukacewa yai ba kuma shima da nashi hankalin,itama Jannah tana cikin hankalinta koma miye gaskiya zatai halinta,yayi imanin Khalid zai iya wannan abun inbashi ba kuma tabbas usman ne,don jikinsa na bashi abun baya wuce su biyunan,.
Suna nan tsai tsaye don zaman ma kasa yi sukai Asaad da usman, momy da fareeda firarsu suke afakaice Hindu kallonsu kurin take gaba d'aya bata yarda dasu ba, zuciyarta tana bata cewar 100% suna da hannu aciki,amman bata da shaida bata da hujja ba zata iya yin wani abu ba.
A daidai nan doctor suka fito ita da wasu nurses ta zare glass d'inta tana kallon Abba da Asaad, tace "Daman na gaya maku dole zata shiga cikin firgice da dimaucewa,wannan halin da take ciki tana iya daukar dogon lokaci tana cikinsa yanzu dai tana bacci zuwa yamma allurar zata saketa ina fatan ace ta samu sassauci ko yayane, kuyi mata addua a ruwa idan tatashi sai tasha,don Allah banda hayaniya bisa kanta kubita ahankali ta dawo hayyacinta koma me kukeso kuji daga gareta"
Usman gumi kurin yake yana jin kamar yaje ya goge mata abunda ke ranta daya jefata cikin wannan halin, juyawa yai ya koma yaje ya had'e kanshi da guiwa kurin.
Godiya Abba yai mata yana dafa kafada Asaad cikin damuwa yace, "zan dawo da yamma din, don Allah ka kwantar da hankalinka kajiko"
Jinjina kanshi yake sannan yace, "zanje wajen baba malam na amso mata rubutu yanzu"
Jinjina masa kai yayi alamun goyon baya, da maganar dayai, (Baba malam kakan su ne daya haifi mahaifiyarsu)
Su momy Abba suka bi akabar usman nan da Babaah uwani, Asaad Mannir ya kira yazo ya daukesa suka wuce Tudun yola daman yana yawan zuwa gaidashi kuma yana aika masa da alkairi, koda ya isa baida shamaki zuwa dakin malam d'in, bayan ya gaisa da tsohuwar gida ya samesa yana rubutu jikin Allo, koda Baba malam ya soma tambayar abunda ya samu Asaad din kuka ya sanya mashi kurin, saboda duk wanda zai ganshi dole zaisan baya cikin natsuwarsa da hankalinsa, saida yasha kukansa sosai sannan yake labarta mashi abunda ke faruwa, shima kanshi Baba malam din ya girgiza sosai hakuri ya bashi yana kuma yi masa nasiha sannan nan take ya hauyin rubutun da kanshi,ya kwashe minty arba'in ina rubutun sannan ya gama yai tofi acikin ruwan bayan ya wanke rubutun, sannan ya daure mashi ga leda yana cewa.
"Insha Allahu Zata samu sassauci daga halin data shiga,ko yayane zata samu natsuwa da dangana sannan bayan kwana biyu ka sake zuwa ka amsar mata wanu rubutun, Allah zai saka mata hakuri dole abun akwai rikitarwa"
Sadda ya dawo anyi la'asar yaje yai salla ya dawo inda yabar usman nan ya iskeshi,ko kallon sa baiba da Babaah uwani kurin yai magana zuwa can mannir ya dawo da take away ya aje gabansa, leda biyu yaba Babaah uwani yace "kici guda dayar idan tatashi sai taci"
Godiya tai masa tana jin tsananin tausayinsa ganin ga usman shima tun sha daya na safe yake nan zaune, tace "ko na bashi nawa idan naje gida sai naci wani aabun"
Nashi ya dauka ya bata yace "ta mik'a mashi"
Inda yake ta isa tana durkusawa tace cikin sanyin rai, "usman tashi kaci abinci kaji ko,sai kayi salla ko azahar bakai ba kana nan tun dazu"
Tabbas yanajin yunwar don haka dole ya ansa yana mata godiya tace, "yayanka ne ya kawo mana"
Yasan kowane yayan take nufi sai baice komi ba,daukar ledar yai yana nufar hanyar waje ko kallinsa Asaad bai ba harya fice, anan wajen Babaah uwani taci abincin sannan take masa nasiha tana kokarin nuna masa yarda da kaddara da kuma hakuri,karya biyewa zuciya itace ke kai mutum ga dana sani karka sake tanka kanenka don Allah"
Lumshe idonsa yai shikad'ai yasan halin da yake ciki, zuciyarsa jiyake kamar ta tsage saboda ciwon da yakeji a cikinta, suna nan zaune nurse ta fito tana cewa,
"Kune masu jinyar Murjanatu?..........ehy mune tafarka ne?"
Cewar Asaad cikin sauri tace, "ehy tatashi kuzo ku bata abinci kitai maka mata tayi wanka da sallah ta canza kayan jikinta"
Jikinsa rawa kurin yake yace, "Babaah ga wannan ta fara shan shi don Allah,bari naje na samo mata kayan sakawar"
Yadda yake b'arin jiki dole ne ya baka tausayi ainun, Babaah uwani tawuce cikin dakin cikin fargaban halin da zata isketa,kaina had'e yake da guiwata ba abunda idona ke tsiyayawar sai hawaye banda karfi ko kadan jikina shiyasa kukan kanshi babu sauti yake fita, ban zaci zan sake bud'e ido na ganni a duniya ba banso ace na farka ba daman sadda zan farka in ganni cikin kabarina,muryar Babaah uwani yasa na dago da kaina kwalla akan fuskarta ta zauna gefena cikin lallashi da ban baki tace, "Murjanatu na kiyi hakuri kinji ko, babu wanda yake tsallake kaddararsa, karkiyi jayayya da Allah ki amshi jarabawarki da hannu biyu ki kuma gode masa, kowa yasan an zalinceki amman ya zamuyi to? *MAI AFKUWA* ta riga ta faru bamu isa mu gyara ba kuka da iface iface bazai kawo miki komi sai tarin kunci da bakin ciki, don girman Allah murjanatu na kiyi hkr, Allah baya bacci haka kuma baya zalinci kuma baya son maiyinsa,ina mai tabbatar miki watan watarana zakiga sakayya kisa aranki cewar duk inda kike Allah zai nuna miki irin hukuncin da zaiyima wanda ya aikata wannan abun, da wanda yabada goyon baya da wanda yasani kowa zai fuskanci kalar abunda ya shuka,kuka dolene kiyi muma masoyanki munyi maki balle ke,don haka bazan hanaki kuka ba amman ina baki hakuri kiyarda da hukuncin Allah,anshi nan kishanye muje na taimaka miki kiyi wanka sannan kiyi sallah ki kai karar duk wanda keda sakaa hannu acikin wannan ta'addancin, Allah yana gaggawar amsar adduar wanda aka zalinta"
Kalaman Babaah uwani sun ratsani sun taimaka mun wajen jin cewar ashe fa inda Allah,firgici da dimuwa yasa nafara fita hayyacina na mance da Allah subhanahu wata Ala,hawaye wani na korar wani labbana rawa suke tare da muryata nakamo hannunta na rik'e fam ina cewa cikin kuka,
"Bab.....Babaah uwa......uwani ji nake dam......dama in mut.....mutu kawai, na tsani Ray......rayuwata meyasa saini haka zata same........sameni? Menai ma wani dazai hukuntani da wannan hukunci, Babaata har.....har rokon.......rokonsa nake na ringa hada shi.......hadashi da Allahn daya haliccesa, ina cew......cewa yaji tsoron Allah karya keta.......keta mun haddina.........Amman baiji ba Babaata! Yasa.....yasanya karfinsa ya keta mun rig.....rigana"
Kukan ya hana na cigaba da magana har bansan shigowar sa ba,tsaye yayi bakin k'ofa rik'e da leda ga hannunsa, ni kuka Babaah uwani kuka shima yana hawayen jikina kar karwa yake ina cigaba da cewa,
"Baiji......bai....baiji tausayina ba haka ya ring........yaringa gana mun azab......zaba, ina zan saka Rayuwata da wannan.........wannan abun? Amman kince mun Allah yana jina ko babaah ta..........."
Duk mai saurarena saiya fashe da kuka, idan kaga yadda nake karkarwa ina zubar da hawaye kamar famfo duk taurin ranka saika matse, rungumeni tayi tana bubbuga bayana tana lallashina.
"Tabbas Allah yana jinki murjanatu kuma zai saka miki nan bada jimawa ba"
Ita tabani rubutun nashanye sannan muka wuce toilet da ita ruwa mai zafi ta had'a mun, tana tambayata zan iya yin wankan kaina kurin na d'aga mata,tace "to ki gasa jikinki kafin kiyi wankan akwai d'inki jikinki kinjiko kibi sannu"
Wankan nake ina zubar da hawaye na mance ma da bayi nake, ina magana ina rokon Allah ya saka mun, "yah Allah banyi wani abuba,banda laifi ban tab'a kusantar zina ba, kana gani ka saka mun da gaggauwa"
Harna gama ina kuka hawaye sun kasa barin idona,kayan daya siyo tamik'o mun na saka sannan nayi alwalla na fito ta shimfid'a mun abun salla na hau na zauna,don bana iya tsayuwa juwazata iyakayar dani.
Sallar nake ruwan hawaye na zuba ban damu ba, haka na cigaba dayi bansan iyakar lokacin dana d'auka ba ahaka na dad'e cikin sujjada ta ina addua ina kuka ina kai kukana wajen lillahi warasuluhu,nasan kuma yanajina yana saurarena saida naji numfashina zai dauke na sallame, abinci ta tusa mun gaba tana bani tana kara kwantar mun da hankali na, har naci na k'oshi duk da ba wani ci nayi ba haka naji ya isheni, naman dake ciki kadan naci tabani ruwa nasha tace, "Asaad mik'o mana magungunan can tasha"
Jikinsa na rawa ya dauko yazo wajenmu ya durk'usa yana bud'e ledar hannunsa har rawa yake, ban gigin kallon fuskarsa ba saboda kukane zai kubce mun, idan na tuna yadda muka rabu cikin farin ciki aranar ban sanin kuka yazo mun, amman abu guda ne yake gigita tunanina idan na dora idona akanshi yanzu, shine turarensa da yake amfani dashi wanda nake masifar so shine naji ajikin mutumin daya hark'e mun ajiya, amman kuma kunnena bazai mance muryar mutumin ba, alokacin da yake ce mun.
_"ki taimaka mun kibarni nayi, in banyi ba mutuwa zanyi"_
Nai iyakar nazarina bansan muryar ko waye ba,tabbas muryar yallab'ai ko acikin hauka nake idan najita zan gane, hakan yasa nagane ba shibane to amman waye? Shikadaine wanda nakejin turarensa ajikinsa bantab'a jin wani yayi amfani dashi ba,ajiyar zuciya na sauke sadda yake mik'o mun maganin daya b'allo, sha na ringayi har ya gama ballowar daidai Abba da usman sun shigo kaina k'asa yake kurin bana son kallon ko wane namiji ayanzu don naji na tsani kowane namiji, uffan na kasa cewa Abban wanda yaita jera mun sannu kaina kurin na d'aga, Yah usman yai mun magana yana can rab'e jikin k'ofa muryarsa na kerma yace "Jannah sannu,yajikin naki"
Shima uffan bance masa ba duk mukai tsitt Abban yace bari yaje yaga likitan, kwanciya nai kan cinyar Babaah uwani inajin kamar innamu ce nake kwance bisa cinyarta, likitar sallama ta bada tana cewa na ringa shiga ruwan zafi sau biyu a yini sannan na kula da shan magunguna na,Abba ne yake amsa mata muka taso Babaah uwani ce ke rik'e dani har mota, motar Yah Asaad muka shiga usman sa Abba suka shiga ta Abban tare da drivernsa, mu kuma Yah Asaad d'in ne yaja mu zuwa gida motar shiru kamar mun zama kurame har Allah yasa muka iso gidan lafiya, muna tsayawa wani gigitaccen kuka ya kubce mun saboda dan danan abun ya dawo mun,rikicewa yai shida Babaah uwani hakuri suke ban sunata lallashi, yake cewa "bamu da abun da zamuyi maki ko mu baki daya wuce hakurin nan Jannah,kowa yasan an cuceki don Allah kiyi kibar kukan nan"
Daker na hakuri saida Abba yazo yasaka baki sannan muka taho da Babaah uwani har cikin babban falo, momy Khalid fareeda da Aneesa sai hindu duk suna falon,yadda momy ke nan nan dani yaban mamaki amman na nuna babu komi, zata fara magana kenan Abba yace "not know hafsat,mubarwa gobe kuma"
Yashige ciki yabarmu ciki muma muka shiga ina hawaye nace, "Babaah kije dani dakin ki bazan iya zama acan ba"
"Daman bazan barki ke d'ayaba ai murja,muje dakin nawa"
Inajiyo dariyar fareeda a falon ina mamakin irin tsanar da take mun, bayan ban kashe mata kowa ba ban hana mata komi ba,kwanciya nai kan katifarta ita kuma ta fita don dora sanwar dare.
Abba da Yah Asaad da Hindu ke zaryar zuwa dubani, yah usy kamar yana tsorona daga bakin kofa yake mun sannu sai yajuya Hindu kuwa nan ta tare tana talallashi tana bani hakuri, karshe bacci ya daukeni.
Saida na sake shiga ruwan zafi kafin safiya, da safen ma ta sake had'a mun na shiga nasha magunguna na sai naji na samu sauki sosai da ga rad'ad'in da nakeji.
**********
Gaba d'ayan mu muna falon saboda kiran da Abban yayi muka fito nida Babaah uwani saboda na danji sauk'i, ina iya tafiya da kaina amman a hankali nake takawa har cikin falon, had'a ido mukai da Yah Asaad da ido yai mun sannu na jinjina kai masa kaina kurin,yayin da gabana ke muguwar fad'uwa saida kowa ya gama hallara sannan Abban ya fara yana tambayata cikin wani irin yanayi,
"Jannah zaki iya mana bayanin abunda kika akan abunda ya faru dake"
Jinai kamar ya fama mun inda yake mun ciwo, hawaye suka balle mun cikin kukan na fara gaya masu daga sadda na shigo gida bayan rabuwar mu da Yah Asaad, har zuwa sadda na kwanta kukana ya k'aru sosai momy tace, "kibar wannan kukan na munafurci kicigaba da yimana bayani"
Mamakin maganarta nayi sosai sai ban kulata ba nacigana da cewa, "dakin akwai duhu sosai bazan iya ganin fuskar ko waye ba, sannan ta karfi ya sanya mun bai barni nasamu wata makama ba, abu biyune kawai na rik'e daga mutumin shine kamshin turarensa da kuma maganar dayai mun,ita kuma ban san muryar ba basan kuma kota waye ba"
Na cigaba da share hawayena ina cewa, "alokacin da muke kokowa dashi naji wani k'amshi turare irin na Yah Asaad jikinsa, cikin muryar da bansanta ba yake cewa _ki taimaka mun inyi, in banyi ba mutuwa zanyi_ abunda yace kenan daga nan bazan iya sanin meyafaru ba,nasan dai naita rok'onsa akan ya kyaleni ya rufa mun asiri amman bai sassauta mun ba,abunda zan iya tunawa kenan Abba"
Muryan momy kawai naji tana cewa, "kaji ko Abba? Kaji abunda ta fad'a cewar kamshin turaren Asaad taji, na gaya maka Asaad ne yai wannan abun shiyasa duk yabi ya gigice haka,idan kuma nai masa musu ya furta da bakinsa kafin na bayyana hujjojina"
Idanunsa kadai ka kalla zakaga tashin hankali baro baro, nuna kanshi yake yana sonyin magana ya kasa ya dad'e yana kakalo maganar daker ya iya cewa, "ni.......ni......zakima sharri Hafsat? In rasa wanda zanyi ma Fyad'e sai wacce nake kauna nake burin zamowarta uwar yayana,......tirrrr da halinki Allah ya tsine ma mai karya,Jannah ki gaya ma Abba idan har zan iya aikata miki wannan abun, wallahi tallahi Abba ko giya nasha bazan iya aikata fyad'e ba,balle akan Jannah wadda nakeji kamar numfashin.......................jikake tas tas tas maruka sun sauka akan fuskar Asaad Abbane kuma yasauke masa su,kwallane suke kwarara daga idanun sa yake cewa "ka cuceni Asaad,ka kuma bani mamaki sosai! Ashe duk wannan haukar da kake ashe kasan abunda kayi? Tsakanina dakai Allah ya isa..........wani irin duka naji a zuciyata wace irin magana ce wannan Abba yakeyi? Ni nasan yallab'ai bazai aikata haka ba duk da cewar turarensa ne naji amman hakan bai saka naji cewar shine ba, kuka nake sosai ina rok'on Abba da cewa.
"Wallahi tallahi Abba ba shi bane, Yah Asaad bai aikata abunda kake fada b...........zaki rufe mun baki kosaina karyaki ko kuwa,ashe ke munafukace ban sani ba,ashe ba tun yanxu kuka saba shek'e ayarku ba sai yanzu kice mun wai bashi bane, hotunan su waye wadannan? Nace daku suwaye anan ehy?"
Ya fad'a jikinsa na rawa ya jefoni da wayar momy jikina wata irin rawa yake sosai na dauki wayar ina dubawa, wata kara na saki saboda ganin mummunan abunda ke faruwa acikin wayar, gadai Yah Asaad nan bisa ruwan cikina amman duk da haka wata zuciyar tawa bata yarda ba, wata irin bugawa kirjina yakeyi sosai komawa nai kamar wata zararra yaci gaba da cewa,
"Kingani KO baki gani ba,kun dauka duk abunda kuke bamu sani,zuwanki bangarensa cikin dare da abunda kukeyi a waje in kun fita, da duk iskancin da kuke mun sani daman wannan ranar mukejira asiri da asirinku zai tonu, don haka bake babu gidannan munafuka?"
Momy ke maganar tana mun kallon tsana, yah usy ne jikinsa ke kerma ainun yake kallon Yah Asaad bakinsa rawa yake sosai,yace "ashe dai ka tabbata kaine makaryacin, ga dai gaskiya tayi halinta ashe dai dagaske maha'incine ka kawo yarinya don ka lalatata............bugun da Asaad yake masa yasaka kowa ya gigice don kamar Asaad ya haukace yake dukansa yana kuka, daker khalid da Abba suka raba su, tsawar da Abban ya daka masu yasa suka natsu yana layi juwa na daukarsa, muryarsa na rawa yake cewa cikin karyar yayyar murya.
"Bansan haka kake ba, bansan zan fuskanci matsala daku ba, ina maka kallon nagartacce kamilallale, ashe daga bayan fage kai d'in ashararine ban sani ba, ka cuceni Asaad amman bazan maka baki ba inaso dai dakai da kannan ka kubar gidan nan yanzu, nagaji da masifar yayan *ZUHRA* shi wancen dan shaye shaye ne har yana dokar mun mata, kai kuma duk yan aikin gidan nan kakebi kana lalatawa ban sani ba, na tsaneku ku duka bana son sake ganinku a rayuwata, ku dauka bakuda uba kema karna bud'e idona na ganki bakar munafuka ashe ke maha'inciya ceke, karna sauko na sake ganin fuskokin ku........................
*ANAN NA KAWO KARSHEN LITTAFIN JANNAH BOOK ONE, GA DUKKAN MAI SON CIGABAN LABARIN ZAI BIYA DARI UKUNSA KACAL TA WANNAN HANYAR*
3150952555
First bank
Aisha Abubakar
Idan ka turo saika turo mun shaidar biyanka ta wannan lambar ***.
Masu turo katin waya kuma zaku iya turo MTN KO AIRTEL na dari ukun ta hanyar wannan lambar
***.
karki bari abarki a baya domin akwai sauran rina akaba,akwai sauran daru sosai ki hanzarta ki mallaki naki.
Ina godiya ga dukkan masoyana na kusa dana nesa👏🏻
Mom muhseen✍🏻