Chapter 18
by @mamanyusuf
♠️♠️ *HUSNA KO HUZNA* ♠️♠️
*MALLAKAR*
*Maryam Umar Abdullah (mmn Yusuf)*
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
*____________________________________*
*Littafin na kudi ne 200 maiso ta turo kudinta ta wannan account number 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Account no 1647784887
Account name Access bank
Name Maryam Umar
Ko katin waya ta wannan number 👉🏻***
🅿️_ 18
A firgice suka dawo jiki na rawa Jummai da Umma suka tallabi Saudat suka kama hanya yayinda Talatu tuni ta Isa ga mota ta shige tana jiransu, haka sukaja motar aguje sukabar jejin , yan kan uba🙊
Zaune suke a falo sai faman ajiyar zuciya suke Wanda har wanna lokacin jikinsu bai daina rawa ba , yayinda Saudat take ta aikin kuka don wannan wahalar da Tasha ba k'aramun Kara Mata jin zafin k'afar yayi ba sai Allah ya Isa takewa Jummai da Talatu don duk sune masu zugawar , bayan sun.dawo cikin nutsuwarsu ne sannan suka ci gaba da shawarar abunyi ,
Saudat kuwa tuni ta kudirta Sam bazata Kara yarda su kaita wajan wani boka ba ,
*Washe gari*
Tunda sassafe Abee da Abba sukayi Shirin zuwa wajan malamin , yayinda Mamah Hafsee ta shirya su HUSNA cikin dogayen riguna bak'ak'e masu matukar kyau inda ta yafa masu mayafin rigar , nan take suka rikida suka koma tamkar yaran larabawa sunyi kyau sosai acikin abayar ,
Nan Mamah ta janyo hannunsu ta fito dasu inda su Abee ke jiransu , kallonta Abee yayi yace jeki turomun da Saudat Kuma suyi sauri karsu 'batamun lokaci ,
"To Mamah tace sannan ta juya ta nufi part din Umma ,
Zaune suke acikin falon Umma suna karyawa yayinda Saudat ke gefe sai faman rintse ido takeyi saboda abunda takeji a k'afar ga kafar kullum Kara hayewa take ,
A dak'ile umma ta amsa sallamar Mamah , kamun ta kauda kanta taci gaba da abunda take ,
Yaran kuwa ba Wanda ya gayar da Mamah , Bata damuba don dama tasaba da halin rashin tarbiyarsu, kallon Umma tayi tace "Alhaji yace a fito da Saudat zasuje waja Mai magani Kuma yace kuyi sauri Yana jiranku , daga haka batajira cewarsu ba ta juya tabar part din , wajan Su Abee ta koma tace "suna zuwa , sai kun dawo Allah yasa adace suka amsa da Amin daganan ta juya Takoma part din mama Hafsee don yiwa jariri wanka ,
Nifa wallahi banason zuwa wajan wani Mai maganin nan malamin zaure ne fa miysani karshenta ko anje baza'adace ba tunda aikin mayu ne , Ni yanzu ma mun yanke zamu kaita can Jos akwai wani mashahurin boka da yayi kaurin suna a wannan harkar ,can nakeson muje daga can na shigar da tawa matsakar akan Alhaji don Sam hankalina bazai kwanta ba sai Naga Alhaji ya dawo a tafin hannuna kamar da , .............jin kawai sukayi Saudat ta fashe da kuka tana cewa wallahi Umma nikam ba inda zan Kara binki ,gashinan.saboda magungunan da kuke duramun kullum k'afar Kara hayewa take ba wani sauki , nikam Abee zanbi wallahi bazan bikuba inkuma kin matsamun wallahi to zan gayawa Abee duk abunda ke faruwa ,
"To shegiya ana son a rabaki da wahala kina hauka , inkinbi uban naki shi wannan dan uwan nashi Bari zaiyi amaki maganin da gaske ,bayan yasan cewa yaranshi ne , wawuya kawai to gaki gasu ina nan Zaki dawo ki nemeni , tsaki tayi ta tashi tayi shigewarta daki ,
Da sauri ya nufi wajan dasu Abee suke , har k'asa ya duka ya gaishesu , amsawa sukayi cikin farinciki da kaunar 'Dan nasu mussaman Abba yana alfahari da Mu'azzam sosai ,
Abee yace "Mu'azzam je maza ka fito mana da kanwarka Saudat zamu kaita wajan Mai magani gashi lokaci na tafiya Amma har yanzu Bata fitoba ,
To Abee bara na kirata , amma Abba ai hardani zakuje ko ? Yayi maganar Yana kallon Abba ,
Eh Mana mizai Hana indai kana ra'ayi , ai zuwanka nada muhimmanci sosai , " to yayi Abba ngd bara na kirata muzo,
Ke ubanmi kikeyi a nan anajiranki Amma ke kina nan zaune bamaki da niyar tashi,?
Hawayene ya zubo Mata tace Wallahi Yaya nakasa tashine Kuma Umma batason naje shine tayi shigewarta ta barni , tsaki yayi yace " ina su Harira ne , " suna d'aki ,
'daga murya yayi ya kwada masu Kira , aikuwa sai gasu a 360 don sun San rauran matukar suka 'Bata Masa lokaci, kallonsu yayi fuska a d'aure yace maza ku kamata ku kaita waje ,ke Kuma ki dauko hijab dinki ki biyomu yayi maganar Yana kallon Harira , aikuwa da sauri ta koma daki ta dauko hijab din sallanta ta fito sannan suka kama Saudat suka fita da ita don Yaya Mu'azzam tuni ya fice yakoma wajan su Abba, nan suka Sanyata mota anty Harira ta shiga inda Abee yaja motar suka dau hanya,
Sun isa k'ofar gidan malam sun tarar da layi sosai a wajan , ganin hakan yasa Abee kiranshi a waya , nan suka gaisa ya cewa Abee yabashi minti biyar Yana zuwa , nan suka bude motar suka fito Husna da Huzna kuwa har matsuwa sukayi su Gansu a waje shiyasa su Abee na fita itama suma suka fito nan suka fara kalle-kalle sunabin mutanen dake wajan da kallo ,
Cak suka tsayar da kallonsu akan wata Mata dake rungume da yar ta ,kana kallon yarinyar sai tabaka tsoro yarinyar ta rame sosai kamar skeleton sai k'aton Kai Wanda har idonta ya shige ciki sosai abun gwanin ban tausayi , a hankali-a hankali su HUSNA suka karasa wajan matar suna zuwa suka Sanyata a tsakkiya ba zato ba tsammani sai kawai ji matar tayi Husna ta tsinkawa yarinyar Mari ,kamun tayi magana Huzna ma ta tsinkama yarinyar Mari , wani irin ihu yarinyar tayi cikin wani irin amon sauti Wanda ya tsorota gabadaya mutanen dake wajan , Hakan ne ya janyo hankalin Abee da Abba Babu shiri suka karasa wajan don janye su HUSNA ,
Matar kuwa tuni ta fusata Hannu da daga zata kwadawa Huzna Mari sai kawai taji Huzna ta buga Mata wata irin tsawa tana cewa karki kuskura kiyi wannan ganganci , tana fadin haka tamayar da kallonta ga yarinyar tace " *Kai bakin azzalumi da baka tsoron Allah akan mi kake wahalar da bayin Allah nan to wallahi maza ka fice ka kama gabanka ko yanzu Ni Safara'u na kassara rayuwarka* jin hakan yasa kowa tsayawa Yana kallonsu cike da mamaki da al'ajabi ciki kuwa harda su Abba da wannan matar , Yaya Mu'azzam kuwa baki da hanci ya saki Yana kallon ikon Allah
Kamar da wasa sukaga yarinyar na wani irin lank'wasa kamar maciji kamun kace mi wani bakin hayak'i yafara fita ta kan yarinyar , hayakin yajima yana fita kamun yagam fita gaba Daya. Nan take yarinyar tadunga atishawa saiga kanta Yana sacewa Yana komawa karami kamun kace mi kanta yakoma Norma hakama idanunta, aikuwa nan wajan ya dauki kabbara sai Kiran *Allahu Akbar* suke mahaifiyar yarinyar kuwa sai hawayen farinciki take tana fadin Alhamdulillah , kallonta Huzna tayi cikin wata murya da duk Wanda yaji yasan ba tata bace tace tsohon aljanine yashiga jikinta Amma yanzu yafita kuci gaba da Bata magani dakuma abunda zai Kara Mata lafiya ga jiki wannan ramar zata tafi daga haka suka juya suka koma inda motarsu take ,
Duk abunda yafaru akan idon Malam sambo Wanda suka zo wajanshi tuni ya fito don ansa Kiran Abee sai ya tarar da wannan abun al'ajbin sai murmushi yake don ba k'aramun dadi yajiba ganin an taimaki wannan boyar Allah don akalla tafi shekara ukku tana kawo yarinyarta ana Mata addu'a don aljanin tabbas irin masu wuyar sha'anin nan ne masu tsananin naci da kafiya Amma gashi yanzu tunda ya hadu da daidai shi cikin lokaci kankane yarabu da yar mutane,
Waja Abee ya karasa jiki a sanyaye Abba da Abee suka gayar da dattijon sannan yamasu iso zuwa cikin gidan inda yake ganawa da manyan baki, nan suka zauna suka Kara gaisawa kamun Malam ya tambayesu Karin bayani , nan fa Abba ya gyara zama ya kwashe komai ya gayawa Malam , jinjina Kai kawai Malam keyi jin abunda ke faruwa nan Malam ya umurcesu da ashigo da yaran harma da yarinyar da aka rikewa k'afa , aikuwa nan akaje aka shigo dasu
Daga Husna har Huzna zama sukayi irin na sarakuna sannan suka sadda kansu kasa basu Kara kallon kowa ba Saudat kuwa can kusa dasu Abba Takoma don yau ba k'aramun tsorata da al'amarin yaran tayi ba ,
Wani ruwan rubutu Malam ya dauko zai yayyafama su HUSNA da sauri ta dakatar dashi da cewa basai munkai ga haka ba mi kukeso ?
Zama Malam sambo yayi yace abunda mukeson musani shine minene dalilin zamanku acikin jikin wadan nan bayin Allah , ?? Sannan Abu na biyu munaso kubar jikinsu gaba Daya kufita daga rayuwarsu har abada ,
Huzna ce tafara magana cikin wani kalan yare cikin wata siririyar murya da kanaji kasan ta yara ce Amma Kuma ba muryarta bace , Hannu Husna ta d'aga ma Huzna sannan itama cikin yaren tabata amsa Amma itakam muryar babba ce , su Abba kam sunyi zugum suna kallon ikon Allah
Husna maida kallonta ga Malam bayan tagama bawa Huzna amsar maganarta da bamusan abunda sukace ba ,
Sunana Safara'u mahaifina Zulk'ass mahaifiyata Maimunatu mun kasance mabiya addinin musulunci tun Kaka da kakanni mahaifina shine babban bawan Mahaifin Abubakar wato kakansu su Huzna yasance yanayiwa Mahaifin Abubakar Malam isah hidima tsawon shekarru Wanda daga baya Allah yayiwa Malam Isah rasuwa , inda Malam Abubakar ya gadeshi , haka mahaifina ya wanzu Yana yiwa Malam Abubakar hidima Kamar yadda yakema mahaifinshi duk wasu abubuwan da suka shafi jinni mahaifina ke taimaka mashi hakama fannin wasu sirrikan magunguna , kamar yadda mahaifina ke yiwa iyalan Malam Isha hidima haka muma muke masu hidima ko da saninsu ko Babu muna taimakamasu ta bangarori da dama batareda saninsu ba Kuma hakan baisa mun taba zama ajikin kowannensu ba sai akan Husna da Huzna
Na kasance mace Mai tsananin kyau da Babu kamarta a wanna lokacin hakan yasa nayita samun masu Sona daga nahiya daban-daban Wanda cikinsu akwai sarakuna attajirai tareda shahararrun matsafa ,wanna abun ba k'aramun tayar da hankalin iyayena yayi ba don sun sani tabbas akwai rigima sosai agaba
Acikin manema aurena akwai wani Dan sarki Mai suna shamzil , shamzil yakasance da Daya ga iyayenshi hakan yasa suke matukar ji dashi duk abunda yakeso shi suke mashi daga shi har iyayenshi sun kasance suna bautawa Rana ma'ana sudin ba musulmai bane ,
Duk da rashin kasancewar shamzil ba musulmiba hakanan Ni shi naji ya kwantamun arai , nan muka Fara soyayya dashi ,inda lokaci Daya iyayena suka tuburemun akan basu yarda da alakata da shamzil ba Wanda shima hakance ta faru ga nashi iyayen , munshiga tashin hankali ba kadan ba don ba k'aramun sin junanmu muke ba , dayan gefe Kuma makiyan Shamzil Dana mahaifinshi sukayo caaaa akaina duk burinsu suga bayana saboda Susan hakan zai kassara rayuwar Yarima Shamzil Wanda dama burinsu kenan suga bayanshi shida mahaifinshi , Wanda ba akan komai suke ba sai akan mulki,
Cikin ikon Allah sai gashi shamzil da iyayenshi sun kar'bi musulunci a dalilina nanfa iyayena suka hau murna sannan bayan wani lokaci akayi bikinmu da Yarima Shamzil ,
Bayan aurenmu anyi ta kawo mana Hari muna tsallakewa kasancewar shamzil ba kanwar lasa bane Kuma a lokacin mahaifinshi ya sauka daga kan mulkin ya dorashi ,
Ana haka Allah yabani ciki , aikuwa nan iyayen shamzil suka umurcemu da kar Wanda muka sanarwa da maganar cikin don tabbas komai zai iya faruwa daga makiyanmu , shamzil ya dauki soayyar duniya ya dorawa wanna ciki nawa wannan yasa ya shawarci iyayenshi akan zai nesantani da wannan nahiyar gaba Daya har na haihu sannan in dawo , don inhar makiyanshi sukasan da cikin nan tofa kota karfin sihiri ne sai sunga bayanshi Wanda dama burinsu shine su kawar da zuri'ar lamriss gaba Daya daga doron k'asa Wanda Kuma tuni sunci wannan alwashin,
Lokacin da Hafsee take dauke da cikin yaran nan Nima a lokacin na dawo wannan nahiyar Wanda har wannan lokacin ban koma ba
Akwai wata Rana cikina ya tsufa sosai ta fito inadan zagayawa muka hadu da Hafsee a lokacin itama cikinta ya girma sosai , Nan muka gaisa kamar munsan juna konace Kamar tasanni don nikam najima da saninta hasalima Ni da kaina na zabi zama acikin gidansu don inyi rainon cikina anan , acikin gidan akwai wata babbar bishiyar gamji anan nake zaune Wanda ba komai yasa na zabi zama acan ba sai kafin da Malam Abubakar yayiwa gidan , indai ba zuri'armu ba ba wani aljani da ya Isa ya shiga gidan da sunan cutar da wani ,
Tun lokacin da muka hadu da Hafsee yarana suka nuna sha'awarsu ga yaran Hafsee ,hakan yasa kullum in Hassan ya fita zan shigo wajan Hafsee musha fira indan har nayi tafiyata to bazata sake tuna Ni ba bare tabawa wani labarina sai Kuma idan na dawo sanna Sam bazata iya tambayata daga inda nake ba haka muka shafe tsawon lokaci muna tare mun shaku sosai da juna , k'wasam rannan na tashi da nakuda kwana biyu ina nakuda kamun na haufo yarana 'yan biyu maza wato *Taufiq da Tahriq*
Bayan sati Daya Hafsee ta haifi *Husna da Huzna* tun baya haihuwarsu ba inda Hafsee ke Kai yaran kamar gindin wannan bishiyar da muke zaune nida yarana , musamman idan suna Mata fitina to zatace zafi sukeji Bari ta masu shimfida anan wajan yafi iska , ganin duk ta kawosu wajan basa sake yin wata fitina yasa takara gasgata tunaninta akan lallai zafine basaso , haka zata barsu a nan taje tayi ta aikinta ,
Mukuma a lokacin ne yarana ke Wasa da yaranta Wanda sannu-sannu sun shak'u sosai da juna don yaran suna ganinmu rass , haka suka rinka rayuwa har kawo yau , Taufiq yafi shiri da Husna Tahriq Kuma da Huzna ,
Taufiq da Tahriq sun kasance yara masu matukar kishi da junasu Sam d'ayansu bayason yaga anyiwa 'Daya Abu shi ba'a mashi ba sannan sun kasance fitinannu na k'arshe a fannin rashin ji da tsokana , Wanda a zahirin gaskiya duk abubuwan dasu Husna keyi basu bane su Tahriq ne duk da suma zama da madaukin kanwa yasa sun iya k'iriniya sosai amma duk abunda zakuga sunyiwa wani to ainahi basu bane su Taufiq ne don Sam basason abunda zaisa a taba *Husna ko Huzna*...............✍🏼