86-87
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
86_87
"Imaan CE ta shigo gidan a gajiye sai kwala sallama take ta dawo daga skul, dake kwana 2 mummy ke kaita skul, lkcn tashi kuma farooq ya kawo ta kafin ya wuce nasa gidan tunda basu koma aiki ba sakamakon hutun amarci da suka dauka. "Dakin mummy ta wuce tayi sallama, tana shiga ta tarad d mummy tana salla, "ajiye skul bag dinta tayi sannan ta fada toilet, wanka tayi, sannan ta fito, "lkcn mummy harta idar da sallah, imaan tace mummy sannu da gida, mummy tayi murmushi tace ya skul. Imaan tace uhum sai du'a'i, can kuma tadan 6ata fuska. "Mummy tace mekuma ya faru? Imaan tace mummy kinga fah kullum naje skul, sai a dinga nunani anacewa wai ga amaryar DR omar. "Mummy tace ke share su, imaan tayi narai2 da ido tace dan Allah mummy wai dgske ne? Mummy tayi shiru itama ta gaji da 6oyewa imaan batun auren ta, "can tace eh ba qarya bace, a rikice imaan tace whattttt??? Mummy ta girgiza kai alamar confirm, "imaan ta durqushe a wajen tana rusa kuka kamar wacce akayi mata rasuwa, "mummy tashi tayi ta isa gareta duk ta rikice da kukan imaan, lallashin ta tafara yi, Amman kamar ana angiza kukan imaan. "Mummy ta rasa abin yi, imaan kuwa bata daina kukan ba, mummy tace kinga imaan bakyason omar din ne? Idan bakyaso sai a raba auren karki cuci kanki ki sanar min, dan banaso naci amanar ki, cakk kukan imaan ya tsaya tayi shiru tana tunanin maganganun mummy, idan akwai abinda zata sakawa mummy tasata farinciki shine ta amince da auren yaranta, rashin amincewar kuwa kamar tayi mata butulci ne, "karki takurawa kanki wajen amincewar abinda bakyaso ke dasu farooq duk daya na dauke Ku cewar mummy, imaan ta dago kanta tana goge hawayen ta tace aa mummy ba nufi na ba kenan, duk abinda kika zabamin wallahi INA maraba dashi Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, da farinciki mummy ta rumgume imaan tana fadin ameen 'yata na gode na gode Allah yyi miki albarka, Imaan ta kwakwulo murmushi tace ameen, mummy tace toh Amman meya saki kuka dazu? Imaan tayi shiru dalilan kukan ta ai sunada yawa barkatai, abinda yafi daga mata hankali be wuce wai da omar aka daura mata aure ba, mutumin data fara tsana a rayuwar ta kenan, kuma itama tana da tabbacin ba wacce ya tsana kamar ita toh taya zaman su zai kasance da wannan hadin gambizar?....mummy ta katse mata tunani da fadin kinyi shiru. "Imaan tayi murmushi sannan ta sunkuyar da kanta kasa dan wasu hawayen ne ke Neman zubowa kan kumatun ta, a hankali tace sbd ya farooq, mummy tace farooq kuma? Imaan ta gyada kai, mummy tace meya miki? Imaan ta sanarwa mummy alkawarin auren ta da farooq yace zaiyi. "Mummy tayi shiru a zuciyar tace itama kanta taso hakan Amman data ga baice komai ba shiyasa taja bakinta tayi shiru, a fili kuwa ta furta tace don't worry, shi daman haka Allah yake ikon sa, kana naka ne shima yana nasa, Amman idan akabi nasa sai aga daidai. Imaan ta gyada kai cike da gamsuwa. "Mummy tashi tayi tabar dakin, imaan kuwa na ganin ta fita ta kifa kanta a jikin gado tana rera kuka yyinda zuciyar ta take ci gaba da tafasa, d wannan kukan bacci ya kwashe ta, kasancewar ba sallah take ba. "Sai da mummy ta shigo dakin sannan ta gyara mata kwanciyar ta.
*******
Tun daga wannan ranar mummy take gyara diyar ta, omar kuwa ko kadan bayason ma ya hadu da imaan, haka zalika itama bata kaunar su hada hanya duk mummy na lura dasu saidai kawai ta basar taci gaba da bawa imaan abubuwan daya kamata, tsumi na musamman mummy tasa aka kawo wa imaan, imaan kuwa sai sha take abunta dan taji shi da zaqi, hadin kankana kuwa ba'ace komai, imaan bata ta6a kawo komai a ranta ba dan haka take shansu hankali kwance. "Imaan tayi bulbul abinta sai qara kyau take tamkar ba itace jaririyar da omar yake ambata ba.
****""
Yau data kasance Friday sati biyu da auren omar da imaan kenan, yau kuma mummy take son damkawa omar Matar shi a hannun sa.
Nuceey luv😘