OMAR KO FAROOQ?

88-89

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓




88_89




"Imaan CE durkushe gaban mummy, a dakinta sai wa'azi take mata na zamantakewar aure, "mummy tace yi nayi, bari na bari imaan shine ribar aure, banban abun kuma shine hakuri, duk yanda masoya suka kai da soyayyar su, har sukayi aure toh INA tabbatar miki abinda zai biyo bayan zaman nasu shine hakuri., dukda na sanki ba baya bace wajen kwalliya da tsabta, toh inaso ki kara zage damtsen ki domin ita mace 'Yar kwalliya CE,... Wa'azi sosai mummy tayi mata, imaan kuwa ba abinda take sai kuka. "Mummy tashi tayi ta kaita falo, alkcn daddy ya fito shima, mummy ta danna kiran omar be Dade ba shima sai gashi, a wannan wajen daddy shi yaja musu kunne sosai a karshe yyi musu fatan Alkhairi, imaan dai kuka take kamar an bude famfo a idon ta, "mummy CE ta rike hannun ta lkcn har omar ya fice a falo, "yana cikin mota mummy ta iso da imaan wajen sa. "Da kyar mummy ta iya cire imaan jikin ta dan wani irin kuka da takeyi kamar anyi mata mutuwa Sam batason rabuwa da mummy. "Haka ta ajiyeta gaban mota, mummy ta leko tana kallon omar daya juya kansa gefe ransa sai tafasa yake dan jin kukan imaan da yake tamkar qara masa guguwar tsanar tane, "mummy ta kira sunan sa, da murmushin yake ya juyo yana kallon mummy, na'am ya amsa, mummy tace ga fateema nan na damka maka amanar ta, Ka kulamin da yarinya ta karka soma cutar da ita. "Omar yace insha Allah mummy zan kiyaye, ohk batun skul, ka dunga kiyaye lkcn tafiyar ta da kuma dawowar ta, omar ya gyada kai alamar ya amsa. "Mummy ta shafi kumatun imaan dake kuka sannan tabar wajen. "Tana barin wajen omar ya fisgi motar a guje Wanda har yasa imaan ta dago tana kallon sa a razane, ganin fuskar sa tayi a murtuke kamar an aiko masa da sakon mutuwa, sunkuyar da kanta tayi a sanyaye a zuciyar tace ni daman nasan za'a Rina Allah kadai yasan irin zaman da zasuyi, take kuma ta kece da wani irin kuka, da sauri omar ya daka mata tsawa yace ya isheki kukan kuma haka, be qarasa bama imaan tayi saurin kama bakin ta wani mugun tsoron sa ya dirar mata lkci guda.


"Gudu yake tamkar zai tashi sama, har ya iso unguwar su, yana zuwa gate, aka bude masa dake ya samo me gadi tun jiya. "Gate man sai daga hannu yake yana yalla6ai sannu da zuwa, inaa ai omar ko kallon sa beyi ba, wani wawan parking yyi, bayan ya tsaya sai yyi shiru, imaan dai kanta a qasa batasan ma a'ina suke ba. "Omar cikin daga murya yace jirana kike na fitar dake ko me? Imaan najin haka tayi saurin bode motar batare da ta kalleshi ba. "Tana fita omar ya sake fisgar motar a guje, kadan ya rage ya buge imaan dam ma ta matsa da sauri, baki galala ta tsaya kallon sa hanyar waje ya nufa, har ya fice a.gidan gaba1 bata daina kallon sa ba. "Wasu zafafan hawaye ne suka sake zubo mata, yana nufin anan zanyi ta tsayuwa kome? Wai wannan wanne irin aure ne? Imaan ta tambayi kanta. "Jikin wata fulawa ta matsa sannan ta samu wani waje tayi zaman agun, tana zaman jiran tsammani.






Nuceey luv😘