ZAMANI... riga kowa da irin na shi

02

by @rahmakabir13

ZAMANI...

  *Riga kowa da irin nashi*


Na

Rahma Kabir mrsMG

Wattpad @rahmakabir

Page 2.

Inna tana shiga gidan hajiya ta fara kwada sallama da karfi, maman Abba tana taya ta, cikin sauri Haj. Sa'a ta fito tana amsa sallamar, ganin maman Hibba ce yasa ta washe baki tana cewa.


Ina kwananku.


Ba gaisuwace ta kawo mu ba.

Cewar maman Abba a tsiwace. Haj. Sa'a tace cikin mamaki.

To me yaka kawo ku?

Nazo ne domin naja miki kunne akan Hibba, daga yau ki fita harkarta karki kara shiga lamarinta, kuma itama ba zata kara kawo miki chagy ba dan naja layi a tsakaninku, tana dawowa zata kawo miki kayanki da kika bata ta sauya.

Haba mama daga abin arziki sai ya zama tsiya, ina ce taimakonta nake yi har nake jure sanya mata chagyn wayarta.

Ai babu wani abin arziki a gareki domin mugun halinki nake gudun ki koyawa Hibba, saboda babu wanda bai san cewa zaman kinki kike yi ba, karki bata mata tarbiyya da muka jima muna yi saboda na san halin karuwai kun san duk yadda zaku dauki hankalin mutum, to ahir dinki wlh.

Gwara dai ki gaya mata dan wlh an sa muku ido ne dama da kika bar Hibba tana mu'amala da ita, amma babu abin arziki a wajen wannan matsiyaciyar mai dauke da najasa.

Cewar maman Abba, Haj. Saa ta ce cikin bacin rai.

Sai kuje ku fara jawa 'yarku kunne dan kuwa ba ni ce na jawota dole sai tayi mu'amala dani ba, kuma wlh kin haifi Hibba baki isa ki raba mu ba tunda abin arziki ya hadani da ita ba tsiya ba, sannan in da ace nayi niyyar bata ta da tuni na kwance mata birki wlh, kinyi sa'a ba Hajiya Sa'adatun da ba ce yanzu, da sai na sa kinyi kuka da ido bibbiyu.

Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, to ta Allah ba taki ba, insha Allah sai Allah ya shiga takani na dake, kuma wlh 'yan sanda zasu rabamu in dai baki rabu da Hibba ba, 'yar iskar banza da wofi kilaki wacce ta kulla kawance da shaidan. Maman Abba mu je.

Cewar Inna a fusace, sai suka wuce fuuu kamar guguwa, Hajiya ta rakasu da dariya tare da sakin guda tana rike hanci, sai ta kara kular dasu domin sun zata zasu bata tsoro da masifarsu sai kuma suka ga akasin haka domin ta fisu masifa hadi da rashin kunya, Inna duk abin duniya ya cikata sai kawai ta kuduri aniyar yau sai ta yiwa Hibba iyaka da gidan Hajiyar ko ta hanyar duka ne. Ita kuwa Haj. Sa'a ta shige daki tana mamakin yadda innar Hibba ta iya ci mata mutunci duk iya kokarinta data kyautata musu, wanda tasha bawa Hibba abu ta kai mata sannan ma duk azumi ba karamin siyayya take yi musu ba saboda dawainiyar da Hibba ke mata na aika, har kayan sallah ta bata dinkawa Hibba amma lokaci guda ta yi mata wannan rashin arzikin, hakan yana nufin kenan ta soma daukar zugar 'yan unguwan, domin Hibba tasha sanar da ita irin zagin da ake yi mata, to amma bata jin zata iya rabuwa da Hibba akan wannan dalilin ba tunda har zuciyarta bata nufin ta cutar da ita, hasalima so tari ita ce ke kwabar Hibba akan tana yiwa su inna biyayya, tare da nuna mata muhimmancisu a tare da ita, ta sauke gauron numfashi kana ta cigaba da sanya lallanta da bata gama sawa ba a hannu.

Hibba tana isa bakin titi ta tsaya, minti biyu sai ga mai napep ya tsaya a gabanta yana murmushi tare da cewa.

Yan mata ina zan kaiki.

Hibba ta ya mutse fuska ta kalle shi da kyau, saurayi ne matashi kuma ba laifi ba za a kirashi mummuna ba, sai ta sanar da shi inda zai kaita yace ta shiga kana suka wuce, a hanya mai napep sai kallonta yake ta madubinsa ya dai kasa shuru yace cikin zakuwa.

Amma ke shuwa ce ko?

Eh ta amsa masa a dakile, ya kara da cewa.

Gaskiya ba zan boye miki ba, kinyi kyau sosai. Dan haka zan kaiki har inda zaki kyauta albarkacin wannan wankan naki.

Uhum na gode.

Daga haka bata kara cewa komai ba shima bai ce ba, har sai da ya kaita bakin gate din makarantarsu kafin ya tsaya ta sauka, tana kokarin tafiya yace.

Ga numbern wayata in kin tashi komawa gida ki kirani na maidaki kyauta.

Hibba tayi farr da ido har cikin ranta taji dadi, dan haka ta mika masa wayarta ya sanya number dinsa ta amsa ta wuce da sauri ko saving bata tsaya yi ba, ta dai yi dailing ta kashe yadda koda anjima zata kirashi, kana shima ya wuce yana jin sonta a ransa duk da zuciyarsa tana kwabarsa akan tafi karfinsa ba lallai ya samu karbuwa ba. Hibba tana shiga gate students suka fara kallonta duk hankalin mutanen wajen suka dawo kanta, duk da akwai wanda shigarsu tayi kyau sosai amma ganin Hibba cikin lafaya ya shanye nasu, saboda shigace data rufe jikinta sannan ma atamfa ce a ciki, sabanin wasu da suka sanya matsastsun kaya duk halittarsu a waje. Yan class dinsu suna hangota suka saka ihu suna kwala mata kira wadanda basu kula da ita ba a lokacin suka maido da hankalinsu gunta, Hibba ta karasa wajensu tana washe baki, suka gaggaisa sai suka soma yin hotuna, wata malamarsu tazo wucewa a gefensu tana ganin Hibba ta saki murmushi tana tsokanarta akan me barci a aji, ta yaba da shigarta kana tace.

Zo muje Staff room na saki aiki.

Hibba bata so haka ba amma ba yadda ta iya dole taje, haka suka wuce malama Hadiza tana gaba ita kuma tana binta a baya har suka isa ciki, Hibba ta gaise da malaman da suke ciki, malama Hadiza ta daura da cewa.

Ga Muhibba nan na daukota ina ganin zata iya karanta speech din tunda Maimuna ba zata samu zuwa ba akan rashin lafiyarta.

Malam Tasi'u ta kalleta sai ya girgiza kai da cewa.

Eh Hibba zata iya dan akwaita da kokari, kuma shigarta masha Allah tayi, sai ki bata takardan tayi bitarshi kafin zuwa anjima.

Malama Hadiza ta amsa da to kafin ta ja hannun Hibba suka fice zuwa wani karamin office, ta zaunar da ita ta bata takardan speech din kafin ta soma gaya mata yadda suke so ta karanta. 

Karfe goma da rabi manyan baki sun gama halarta an shirya komai a kan tsari a cikin farfajiyar makarantar, aka soma gabatar da addu'ar bude taro daga bisani suka daura da gabatar da shirye shiryen da suka tsara akan taron, har lokaci yayi aka kira Hibba ta fito ta fara speech dinta harta gama aka bita da tafi, ba karamin burge mutane tayi ba yadda take karantawa daki daki a natse, bayan an gaba gabatar da komai sai aka fara raba kyautuka ga dalibai wanda suka bada gudunmawa a makarantar, har aka zo kan Hibba da aka bata kyautar tsafta tare da na kyautar wacce shigarta tafi na kowa a wannan taron, Hibba har fidda kwallar farin ciki tayi bata taba zaton zata samu wannan kyautar ba musamma na shigarta na yau, a ganinta akwai da yawa wanda suka yi shigar tsadaddun kaya amma tayi musu fincinkau, ashe komin arhan kayan da mutun ya sanya muddun ya iya shiga zai doke mutane masu tsadaddun kaya, haka aka watse taro kowa cikin farin ciki musammsn hibba da ta samu kyauta akan shigarta wanda ya shiga cikin kundun tarihinta, haka ta kira me napep yazo ya dauketa har kofar gida ya direta ta sauka tana yi masa godiya ya nuna mata ba komai, sannan duk lokacin da zata fita ta kirashi in dai yana kusa zai zo ya kaita, Hibba ba karamin farin ciki tayi ba yau, haka ta wuce gidan Hajiya ta bata labari tare da nuna mata kyautukan data samu ta daura da cewa.

Ashe haka shiga me kyau ke fidda mutum ya yi zarra a cikin taro, to gaskiya zan zo na fara tara taro da sisi na siya lafaya da yawa wanda zan rika sanyawa.

Hibba ai shiga me kyau ba karamin kankaro wa mutum mutunci yake ba, sannan ba shigar lafaya kawai ba hatta in kika yi shigar gyale zai miki kyau, sannan kika iya tsara kwalliya tare da iya hada kaloli wanda suka dace da shigar, sannan ki tanadi jakuna da takalma da dan kunne da sarka awarwaro da bangus, tare da kit din kayan kwalliya to kin gama zama haɗaɗɗiya.

Cewar Hajiyar tana 'yar dariya, Hibba tayi narai narai da ido kamar zata yi kuka tace.

Hmmm hajiya ba kayan ba kudin, duk a ina zan same su? Kin san dai wannan hidima ce ta kashe kudi, ni ba sana'ar fari balle na baki, sai dai in gani a gun wasu ko in zanyi aure na samu na akwati.

Hibba kar ki cire rai tunda kin gama secondary saiki dage ki koyi sana'ar hannu sai kiga kin siyawa kanki komai, dan yanzu wannan zamanin dole sai kin fito da kanki a yan mata sosai saboda ki samu miji na gani na fada.

Baba karatu yake so nayi, ni dai nasan bana cikin yan matan wannan zamani, dan wani abin sai dai na gani a makota tunda su Inna ba su da karfin siya mini irin kayan kwalliyar nan. Allah dai ya rufa mana asiri, bari naje gida zan dawo anjima na samu kalacin dare dan yanzu na dawo cikina a cike, naci abinci a makaranta.

To Allah ya kaimu Hibba sai kin zo din.

Hibba ta amsa da Amin kana ta wuce gida, Hajiya sa'a ko kadan bata nuna mata cewar su Inna sun zo sunyi mata dibar arziki ba da zun, sai ma kara jin kaunar Hibba da tayi tare da ji a ranta zata tsaya mata kai da fata wajen kashe mata kudi, da wayar mata da kai ta zama cikakkiyar budurwan zamani a dama da ita, dan Hibba ba matar kananan mutane ban ce, dole ne ta daurata a layi harta samu wani kusan yayi wuf da ita. Haka ta yi ta sakar zuci wanda take ganin su Inna sunyi kadan su raba su duk da sune suka haifeta. 

Hibba tana shiga gida ta wuce dakin Inna da kyautukanta a hannu, tayi sallama Inna ta amsa, Hibba tace cikin yalwar farin ciki.

Inna sannu da gida, kinga kyautar dana samu yau a makaranta, wlh ba karamin yaba wa shigata aka yi ba.

Ta fada tana washe baki, inna ta dago kai tana kallonta kana ta mike ta ce.

Amma ba dai kyautar wannan kayan jikin naki kika samu ba, sai dai wasu kayan ko?

Hibba tayi tsuru tsuru da ido sai yanzu ta gane tayi subul da baka tunda ta san inna bata san ta sauya kaya ba, sai ta soma sosa keya.

Dama kyautar tsafta na samu.

Inna ta matso kusa da ita ta wanketa da mari ko kafin tayi aune ta rufeta da duka da hannu, ta shiga ɗumarta a baya har sai da ta kaita kasa, sai ta fisgo chagyn waya dake kan tv ta shiga sabga mata, tsoro da mamaki hadi da azabar duka yasa Hibba ta kasa kwakkwarar motsi hawaye ne kawai ke zarya a kuncinta, bata yi yunkurin gudu ba sannan bata yi ihu ba saboda kar hankalin yan gidansu ya dawo kansu, tunda ta tashi da girmanta inna bata taba dukanta ba sai yau, tunanin laifin da tayi mata har da ta cancanci duka ta ke yi, sai da chagyn ya tsinke kafin inna ta daina dukanta, sai ta koma gefen gado ta zauna tana mai da numfashi, Hibba tana durkushe sai kuka take mara sauti, inna ta ce a fusace.

Wannan kadan nayi miki muddun baki rabu da Hajiya sa'a ba, saboda kin raina ni jiya na gama yi miki gargadi akan zuwa gidanta amma sai yau ki ka koma har da aron kayanta kisa ki tafi makaranta dasu, wato ban isa dake ba kenan, to na je na sameta tana gaya min ban isa na rabaku ba, saboda kin gama bada ni a wajenta, to wlh hibba zan tsine miki muddun kika ki bin umarni na.

Hibba ta dago kai a zabure, tana sanya hannunta a kirjinta.

Inna duk wannan hukuncin akan Hajiya sa'a kika yi min shi har kike ikirarin tsine min, fisabilillahi wani hali kika ga na sauya da har na cancanci wannan hukunci, dai dai gwargwado ina yi miki biyayya bana yawo sannan bana wani yin abin alatir, ina kokarin rike mutuncina, duk wannan abin da kike min ba shi ne shiriya ba, addu'a shine abu na farko da zaki yi min sannan ki hada min da nasiha, shine zai sa na yi miki abinda kike so, duka da fada babu abinda zai kara mana sai bacin rai, kuma insha Allah zan daina zuwa gidanta, shikenan ko.

Hibba ta kare da matsar kwalla, inna tace cikin fada.

Kin jero min magana saikace mai hankali, idan kin so karki fasa zuwa gidan ina dai dai da rashin jin maganarki, tashi ki bani waje.

Hibba ta mike ranta nayi mata suya ita dai bata san meyasa Inna ke yi mata haka ba, har yau bata ganin aibin zuwanta gidan hajiya sa'a tunda bata sauya hali ba, tana fitowa taga 'yan gidansu sun yi cirko cirko a tsakar gidan, duk sun fito jin gulmar abinda inna tayi mata, sai ranta ya kara baci, ta kallesu ta watsar ta shige daki, ta san har da zugansu yasa Inna take kokarin rabata da Hajiya.


_______________


Don sauraren littafin ƘAZAMIN TABO a youtube channel ku danna wannan link zai kai ku kai tsaye, ku danna subscribe tare da danna kararrawar sanarwa ayi saurare lafiya. ***


*Idan kuna bukatar a tallatar muku hajar ku a pages ko a daura a status ku tuntubi wannan number ***, zaku samu akan farashi mai sauki.*