6
__________Sai magriba su Umma su ka baro asibitin, Inteesar duk ta yi laushi, haka su ka isa gida Irfan na niyyar zuwa" assalamu'alaikum" Umma ta yi sallama ta na mai riƙe da hannun Inteesar,duk kan Yaran su ka fito suna mai yiwa aunty'n nasu sannu da jiki, ko amsawa ba tayi ba, ta ce"akwai ruwan zafi, zu ba min nayi wanka" Na'ima ta ce " eh akwai" ta na mai zuwa ta ɗau bokitin wanka ta juye ruwan da ke kan garwashin wuta, ta sirka ta ce" Yaya Imran ba zan iya kai mata ba,ka zo ka kaimata bayi" Imran ya ɗauka ya kai mata, Inteesar da ta fi daraja wanka akan komai ta shiga ɗakinta ta fito ta shige bayin, Umma ta rataye gyalenta akan igiya ta ce"ina Malam?"
Salma ta amsa mata da ce wa" bai dawo ba, na je rumfarsa kuma naga ya tashi" Umma ta ce"ayya ina jin ya bi mu asibitin ne, Irfan kira woshi da wayanka mana" Irfan da rabon da ya sa wa wayarsa kati har yai manta ya ce" wallahi babu kati a wayan" ana haka sai ga Baba Ayuba ya yi sallama,sannu da zuwa Baba duk su ka ce masa, Umma ta ce "ka je baka same mu ba ko?" Baba ya ce"a'a ai nasan za ku dawo, na je gidan Yakubu ne, ya jikin nata?" Umma ta ɓata rai ta ce" yanzu sa bo da Allah Malam komawa gidan kayi, mutumin da ba ya taimaka mana da komai,kullum cikin aibata mu yake, kullum cikin gorin rashin samun Mijin ga Inteesar ya ke,kullum cikin yi mana dariya ya ke amma shi ne ka koma,to ni kar ka sanar da mu duk abinda ya yi maka, ka riƙe takaicinka kai kaɗai"tun da ta fara magana Yaran su ka yi shiru kowa zuciyarsa ta na masa soya dan su san Kawu Yakubu baya son a ce su ƴaƴan ƙaninsa ne, haka ma Ƴaƴansa ba sa shiga harkarsu sa bo da talauci abun kunya ne a wajensu ƙanin Mahaifinsu ya na sai da kayan miya a cikin unguwa, Mahaifinsu na buɗe dilolin shadda a kasuwa, hakan ya sa su Irfan ba sa zuwa gidan.
Baba ya ce "dalla kin cika ni da surutu, me kike nufi da komawa nayi, ni da gidam ɗan'uwana dole na je ko kina so ko bakya so, ɗan'uwa na ne babu wanda ya isa ya raba ni da shi, kuma da naje ce miki nayi zancen wannan ƴarta ki mai baƙin jinin tsiya na yi iyee, to ni shawara naje nema akan wani mutum da ya zo min da tayin aikin company shi ne naje inji ra'ayinsa ba komai ba, amma kin taso min kamar za ki cinye ni"
Irfan da sauran Yaran duk su ka bar wajen,ganin shi ma Baba ya hau, Inteesar ce ta fita ta na kallon iyayen nata, in da sabo sun saba da halinsu, ta ce" sannu da zuwa Baba"
"Yauwa ya jikin naki?" Inteesar ta ce da sauƙi, ta shige ɗakinta, da harara ya bita da shi ya ce " Yarinya duk ta gamdame a gida ta zama Uwar mata, amma babu Mijin aure" Umma ta ce " idan siyowa ake a kasuwa mai zai hana ka je ka siyo mata" Baba ya ce" ni dai wannan baƙin jinin wallahi ba a danginmu ya ke ba, sai dai a cikin danginku" abun ya fara ƙure Umma, ta fashe da kuka ta na shigewa ɗaki, su Na'ima da Salma da tun ɗazu suke kuka ganin Umma na yi ya sa duk suka dawo jikinta su na fashewa da sabon kuka.
Irfan da Imran da su ke ji, ina ma su na da hanyar da za su samawa Aunty Khaleesat Mijin aure da sun yi, ko dan Umma ta huta da wannan abu da Baba da ɗan'uwansa su ke musu, sun rasa inda matsalar ta ke, duk da ba ta da mutunci amma su na ƙaunarta, Imran ne ya dafa Irfan, ɗagowa ya yi baisan hawaye ya ke ba, sai da Imran ya fara share masa ya ce" Yaya Irfan insha Allahu sai aunty ta yi aure gidan Miji na gaban misali, kuma insha Allahu za mu yi arziki, a daina wulaƙanta mana iyaye, idan ka yi kuka mu kuma muyi ya ya, ka na ji dai Umma ma kuka ta ke yi, cikin tashin hankali Irfan ya fita da sauri Imran ya bi shi suka nufi ɗakin Umma.
Baba da ke tsakar gida ya na ta mita, dan shi gidan ma ya ishe shi, Allah ya so ya ci abinci gidan Alhaji Yakubu, har da nama da lemo da yanzu shinkafan da Imran ya dafa ma ba zai iya ci ba, dan takaici, "wai kazo gida da abun arziki a ɓata maka rai, Allah wadaran wannan hali"Baba ya faɗa ya na shigewa ɗakinsa.
Su Irfan na shiga su ka ga Umma da su Salma su na ta kuka a jikinta, Irfan ya aro dauriya ya zauna kusa da Umma ya ce" ku ku tashi, me ye abun kuka anan, kun sa Umma cikin damuwa haka aka ce ana yiwa Uwa a makaranta" su Na'ima su ka ce "a'a" Irfan ya ce " to ku da zaku sata dariya ku faɗa mata Allah ya na ce wa "bismillahirarahim Innama'al'usriyusrah, duk kan tsanani ya na tare da sauƙi,kuma sai ku sa ta a damuwa" ta ke Umma ta saki murmushi dan Irfan akwai hikima, ta ce "ba su suka sa ni kuka ba Irfan, abinda Mahaifinku ya ke baya kyauta mana, da ina da halin samawa Inteesar Miji da na yi, burin ko wacce Uwa ta kauda ƴarta idan ta kai munzalin aure, to ya zanyi da wannan ƙaddarar" Irfan ya ce"jarabawa ce Umma, kinsan Allah ba kowane bawa ya ke jarabawa ba sai mumini,kin san me annabawan Allah sunfi kowa shiga cikin jarabawa, anjarabi annabi Yusuf da kaidin Mata, sai da yayi zaman kurkuku tsawon skekara bakwai, anjarrabi annabi Ayuba da tsananin rashin lafiya tsawon shekara tara, har ta kai ga mutane sun guje shi, anjarrabi annabi Yunus da zama cikin kifi, ga duhun ruwa ga duhun cikin kifi, amma da suka dogara ga Allah duk sai Allah ya kawo musu mafita, annabinmu ma Muhammad(s.a.w) sai da aka jarrabe shi, da cutarwa ta kafurai, tsananin ya kai da sai da ya bar Mahaifarsa,an karya masa haƙori,an ce masa majnun, an jefe shi, to Umma mu su waye da ba za a jarrabe mu ba indai mun yi imani da Allah?" sosai Umma ta sami nutsuwa ta gamsu da zancen Irfan, ta dinga sa musu albarka, sai da Irfan ya ga sun ware sannan hankalinsa ya kwanta ya bar ɗakin.
Inteesar kuwa ko a jikinta, gyara kanta tayi ta fito ta ɗauki abincinta ta koma ɗaki, jin ƴan gidan su na ɗakin Umma ta taɓe baki ta na ce wa" ba su da aiki sai uban surutu"ta shige nata ɗakin, ba bissimillah ta fara cin abincinta, ta gama ta wanke hannu da baki ta kwanta ta janyo wayarta da tun safe bata ɗauka ba,ta ga kiran ƙawarta Nazifa, da tun ɗazu ta kira dan ta dubata tunda Na'ima ta faɗa mata, shi ne bata ɗauka ba sai ta haƙura tasan halin Yayartasu da miskilanci.
Bin kiran ta yi, Nazifa da ke kusa da Mijinta Dr.Zayyad da ƴaƴanta uku, Ahmad da Muhamud da Amina su na zaune su na kallo a tashar arewa 24 ta ji kiran Yayartasu ɗauka ta yi da sallama ta ce "aunty Inteesar ya jikin naki?" daga can Inteesar ta ce" wana shegen ne ya faɗa miki ba ni da lafiya" ta shi Nazifa ta yi ta na mai barin wajen dan kar Dacta ya ji, ta ce"kai aunty ba kya so na sani ko, to gobe ina nan zuwa gidan insha Allah" Inteesar ta ce" to sai kin zo" ta kashe wayarta ta ci gaba da kwanciyarta ta rufda ciki sanin ba sallah za ta yi ba, ya sa ta ji daɗi a ranta daman a dole ta ke yinta batasan me ya sa ba ta son sallah ba, bacci ne ya ɗauketa ta na sauraron waƙar Shakeera.
MIJIN DARE ne ya bayya na, ya na mai fashewa da dariya ya na yiwa kansa kirari, da gayya ya motsa mata mararta, a gigice Inteesar ta farka da matsanancin ciwo........
A fusace Abban Ansar ya bi Khaleesat ɗakin, "ke dan wulaƙanci ni za ki mayar mahaukaci, ina miki magana ki na tafiya"
Khaleesat da take jiran ƙiris ta miƙe ta na riƙe ƙugu ta kalle shi sama da ƙasa ta ce" anyi ɗin ka yi duk abin da za ka yi" hannu ya ɗaga zai shara mata mari, ko me ya tuna sai ya sauke hannu ya na huci, ganin ya fasa ya sa Khaleesat fara kuka " wallahi sai ka sake ni,ni nagaji da auren nan ba na son ganinka" Abban Ansar ya cika da mamaki Khaleesat, ina soyayyar da suke wa junansu, ina tarbiyyarta ina iliminta, ko shekara biyu ba su yi da aure ba, ta bijiro masa da sababbin abubuwa kala-kala duk haƙurinsa nema ta ke ta ƙure shi, ɗakin ya bari ya na ɗaukar wayarsa dan kiran Yayanta ya gaji da halinta.
Shanye ɓacin ransa ya yi, ya na jin Abbas Yayan Khaleesat ya ɗauka su ka gaisa sannan Ibrahim ya ce " daman Khaleesata ce ta ke ta ce wa sai na saketa bansan me nayi mata, ta na ta haɗa kayanta" Abbas da ya ke zaune kusa da Mamansu Rabi ya ce"ita Khaleesat ɗin ce ta ke ce wa ka sake ta?" Ibrahim ya ce "eh yanzu ma gidan na kulle na bar mata" Abbas ya ce gamu nan zuwa dan Allah Abban Ansar ka yi haƙuri" godiya ya yi masa ya na mai dafe kansa a ƙofar gidan gaba ɗaya duniyar ta yi masa zafi ya na bala'in son Matarsa........
*Zinariya ce✍🏻*