90-91
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
90_91
"Tun yamma imaan ke zaune a wajen, sai bayan isha, sannan omar ya dawo, bayan yyi parking ya fito har zai wuce sai yaga imaan kwance ta shimfida dankwalin kanta ta kwanta bcci, "mamaki ne ya isheshi dan zaton sa lkcn daya barta zata shiga ciki da kanta, wata uwar tsuka yaja sannan ya buga qafar ta, a firgice ta tashi sbd tsoro har wani zare ido take har zatayi ihu cin karo da fuskar omar a murtike yasa ta rufe bakin ta, cikin tsawa yace uban me kike anan? "Imaan tayi shiru lkcn data maimaita tmbyr da yyi mata a zuciyar ta, renin hankali ma kenan...katse mata tunanin yyi da fadin ba mgn nake miki ba? Imaan me makon ta bashi amsa tsabar takaici ma sai ta kece da kuka, mwtss yaja tsaki sannan yace oya muje, imaan tayi tsaye ko motsawa taki yi, omar ya samu keyar ta ya hankada ta, dolen ta tafara tafiya tana share hawaye. "Har falo suka isa daga nan ya haura sama ya barta a wajen, kusan 10mins imaan na tsaye ko zama batayi ba, jin shirun yyi yawa yasa tabi bayan sa dan tagaji da tsayuwar, qirjinta na bugawa ta haura sama, daga nan taga daki guda biyu tunanin be wuce wanne omar din ya shiga ba, "kofar dake kusa da ita ta tura a hankali hade da sallama, gani tayi ba kowa saidai da alama yana toilet dan taji qarar ruwa, juyawa tayi ta fita a dakin, duba dayan dakin tayi, tsayawa tayi tana kallon tsaruwar dakin yanda taga gaban mirror cike da kayan kwalliya hakan ya tabbatar mata nata ne, dan haka ta shiga ciki ba wani bata lkci, "toilet ta fada tayi wanka tayo alwala sannan ta fito, bayan ta idar da sallar da ake Binta ta tashi tabi lpyr gado, saidai me? Wata mahaukaciyar yunwa ke damun ta, dan rabon ta abinci tun safe, na rana kuwa kasa ci tayi dan yanda tasha kuka, "juyi take sosai, ganin babu sarki sai mahalicci yasata mikewa dan nemawa kanta abinci, "hijab dinta ta sanya sannan ta fito zuwa qasa, ga mamakin ta taga omar yana zaune kan kujera yana kallo yana shan coffee hankali kwance, "kauda kanta tayi sannan ta wuce kitchen, tunda ta shiga nan ta shagaltu da tsaruwar kitchen din, babu abinda babu a kitchen din, indomie ta dauko ta dafa tare da kwai 5mins ya isheta ta gama komai sannan ta juye a plate, "falo ta fito rike da indomie'n sannan ta nufi wajen fridge, omar na falon yi yayi tamkar besan da mutum a wajen ba, "budewa tayi dan daukar ruwa, ganin lemo a ciki yasa ta dauko, zaunawa tayi kan daya daga jerin kujerin dining table din da shima ya tsaru dan kyau, saida ta gama ci sannan ta maida plate din kitchen bayan ta wanke shi ta fito, yanxu kam garau takejin ta sabanin da datake jinta sai a slow.
"Zata haura sama kenan taji ance ke zonan, ba musu ta juyo dan tasan waye me kiran, gaban sa ta tsugunna tace gani ya omar, omar dake kallo yyi banza da ita, kusan 15mins tana tsugunne a wajen, sannan yace karkiyi zaton dan an makala min ke ki zata zan daukeki a matsayin Matar aure NO, har abada bazan ta6a son kiba imaan, kin shigo rayuwar gidanmu hakan be isheki ba sai da kikayi yanda kikayi aka cusamin ke cikin rayuwata kinyi sanadin rushewar fariciki na duk wani plan dina kin rusa, banda niyyar aure Amman ta sanadin ki an qaqaba min ke, toh bari kiji kada ki zata dan mummy tamin mgn a gida ki dauka nayi na'am d zaman lpyr ki a'a saidan inaso ki gane kin rasa farincikin ki kenan imaan, kisa a ranki kina cikin _rayuwa_ da _mutuwa_ kisa a ranki kinyi bankwana da farinciki na har abada matukar bakije wajen mummy kince ke bakyason auren nan ba, koda yake is too late, kin zabi zaman kunci saidai nace miki welcome to black house. "Imaan banda hawaye babu abinda ke ambaliya a fuskar ta, magana ma kasawa tayi yo me zatace? Ai ita kanta shaida CE omar bazai taba sonta a rayuwa ba kamar yanda baza ta taba sonshi ba toh Wanda yyi silar mutuwar mahaifiyar ta har akwai wani sauran so da zatai masa?... Omar ya katse mata tunanin da take bayan yyi murmushin mugunta yace da kin Adana wannan hawayen naki inaga zuwa nan gaba zasufi maki amfani, tunani kuwa yanzu ma kika fara, so get out of my side ya fada a tsawace. "Jikinta a sanyaye ta mike dakyar ta iya daga kafafun ta sannan ta haura sama hawaye na zarya a kan kumatun ta. "A zuciyar ta tace shin dama haka ya omar yake? Wai wanne irin aure akayi mata? Yanzu me ya omar yake nufi da kalamansa?????
Nuceey luv😘