92-93
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
92_93
"Da wannan tunanin ta shige dakinta, ko d tazo bcci ma gagarar ta yyi tunanin Abinda omar ya fada mata take.
"Da safe ya kasance Saturday, tunda imaan tayi sallar asuba wani wahalallan bacci ya kwashe ta sbd bata samu tayi jiya ba dalilin tunani data sa a ranta, "omar kuwa yana dawowa a masallaci har zai wuce dakinsa sai kuma ya bude dakin imaan, kwance ya ganta tana sheka bcci, "ruwa dake cikin roba a dakin ya dauka ya yayyafa mata, a matukar firgice imaan ta tashi sakamakon jin ruwa a jikin ta da taji, ga wani nauyi da kanta yake mata hade da Sara mata, "cikin tsawa yace ke uban wa ya baki izinin komawa bcci? Imaan tayi zuru tana kallon sa itafa har yanxu mamaki omar yake bata dan bata taba zaton zaiyi rabin abinda yake mata yanzu ba saikace me aljanu?.... Omar ya katse ta da fadin kin zubamin wannan idanun naki masu kama Dana ungulu bazaki amsani bane? Imaan ta sadda kanta kasa wasu zafafan hawaye na Neman zubo mata ita batasan amsar da zata bashi bama. "Omar yace well, tashi ki biyo ni, yana fadar hakan ya juya zuwa falon kasa. "Imaan ma binshi tayi tamkar jela. "Saida ya zauna sannan yace, zaki fita waje akwai tsintsiya a inda ake ajiyewa, kullum zaki dinga share gidan nan sau uku, imaan ta dago kanta da sauri tana kallon sa qirjin ta sai dukan 3,3 yake, omar ya sake daure fuska yace safe, rana, yamma kenan, haka zalika duk wata fulawa dake gidan nan zaki dinga bayin su suma sau uku a rana, falo da dakina ma, suma sau uku har mopping, imaan tun tana daure zuciyar ta qarshe saida ta 6alle da kuka, "cikin kuka tace dan Allah ya omar kayi hakuri wallahi bazan iya dukkkanin abinda ka zayyano ba dan Allah, ko kuma ka sauwa kemin auren dan Allah, omar yyi murmushin mugunta yace a gidan ubanki Zakice bakya aiki? Ai bari kiji baki da Mara da mai aiki a yanzu, sannan ki sani banason wasting time a aiki na, so jeki fara tun yanzu. "Yana kaiwa nan ya tashi ya haura sama, yana shiga daki ya kwanta yabi lafiyar gado.
"Imaan a nan ta durkushe tana kukan bakin ciki, ita gaba1 ma rayuwar ta isheta, "jiki ba kwashi jiki ta fita waje, ga wani irin sanyi da ake busawa kasancewar sanyi asuba dake kadawa, dakyar ta iya fita wajen, wani irin tashin hankali ne ya bayyana kan fuskar ta, ganin yanda fadin gidan yake, gashi kota INA ganyen flowers sun bata wajen, wani hawaye ne dumi suka gangaro kan kumatun ta, "jikin ta na rawar sanyi, ta qarasa inda aka tanadar dan zaman tsintsiya, idan zata iya tunawa tofa rabon ta da shara tun umman ta nada rai, dan a gidan mummy akwai masu aiki, abinci ne kawai sukeyi tare da mummy dan mummy batason me aiki tayi mata abinci ta gwammaci tayi da kanta, bayan wannan saidai taci ta kwanta ko tayi kallo, ko kuma taje farooq ya koya mata kr2, wasu hawayen ne suka sake zubo mata lkcn data tuno da ya farooq dinta shikenan yyi mata nisa. "Hawaye na ambaliya kan kumatun take sharar ta, tun wajen 6 ta fara shara ba ita ta gama ba sai 8. Duk jikin ta yyi laushi ga gajiya, haka ta kwashe sharar ta zuba a dustbin, tana gamawa ta koma kan flower, nan ma dakyar da sidin goshin ta kammala bayin flowers din. Hannun ta kamar ya cire a jikin ta, sai to 9 ta gama da gyaran waje, "tana komawa falo, daidai lkcn omar ya fito cikin shirin sa yadau wanka yyi kyau fuskar nan kam kamar an aiko masa d sakon mutuwa, shi haka omar yake idan tun farko ya nuna bayason Abu to kada a takura sa akai, dan koda yanason abun idan aka takura masa zai tsaneshi, shiyasa tunda aka tilasta masa auren imaan yaji babu halittar daya tsana tamkar ita dan ko kadan baida burin aure a yanzu. "Har zata wuce yace kee, imaan ta juyo tana kallon sa, omar yace a gidan Ku ba'a koya miki yanda ake gaisuwa bane? Imaan ta sadda kanta qasa tace kayi hakuri dan Allah sannan tace good morning, omar ya tabe baki sannan yasa kai ya fice, ita kuma imaan ta fara haurawa sama, har zata bude kofa taji ance kee, a razane ta juya, yace zonan, imaan ta tafi da sauri har tana hada stairs wajen sauka. "Tana zuwa omar ya jawo hijab dinta suka fito waje, suna zuwa wajen omar yace haka ake shara a gidan Ku? Imaan ta juya tana kallon wajen cike da rashin fahimta ta dawo da kallon ta wajen sa duk wannan uban wahalar sharar da tayi miye aibun ta? Omar yace kin kafeni da ido ba tmbyr ki nake ba? Imaan a hankali tace na share komai fa ya omar, omar yaja tsaki yana nuna ganyen flowers guda uku da suka sauka yace wancan kuma ba shara bace kenan? Imaan ta juya tana kallon wajen, tace bayan nabar wajen suka fado, "omar ya girgiza kai yace so ni kike jira na kwashe miki kenan? Imaan tace aa, sannan ta taxi wajen dan kwashe wa, omar kuwa mota ya shige ya fice a gidan.
"Yana barin gidan imaan lkcn itama ta dawo falo, ganin falon tayi tsaftsaf a zuciyar tace toh miye abin gyara anan? Wata Zuciyar tace kawai ki share ai bazai gane ba, hakan kuwa akayi tafiya sama tayi tabar falon. Saidai koda ta haura saman dakin omar ta nufa dan cika umarnin sa.
Nuceey luv😘