94-95
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
94_95
Haka ya kasance kullum imaan ke wannan aikin kamar jaka, saidai kam yana kaita skul, Amman bashi yake dawo da ita ba, kuma yyi mata gargadin kada ta sake taje wajen mummy idan ta dawo a skul, baiwar Allah wacce tsoron sa ya gama zama jinin jikin ta haka take bin umarnin sa babu ko kwakkwaran musu.
****
"Imaan duk ta damu taga mummy, gashi bata da waya, ranar bayan ta gama aiki, ta shiga dakin omar da sallamar ta, yana kan gado yana duba system dinsa, imaan ta sunkuya, cikin sanyi murya tace dan Allah ya omar ka kaini wajen mummy, omar yana jinta Amman yyi banza da ita, imaan tace dan Allah fah ya omar, cikin tsawa yace mamarki CE? Daga samun waje saiki wani makale mana ita. Imaan ta sadda kanta qasa, idan da sabo kowa ya sani wannan zafafan hawayen nata suka fara zubowa, kukan ma da biyu take yinsa, na gorin mahaifita da yyi mata da kuma missing din mummy. Cikin muryar kuka tace kayi hakuri ya omar a ganina duk Wanda yyi maka halacci a rayuwa ya maida ka tamkar mutum ba abun a yasar bane domin ya zame maka wani ji6i na rayuwa, Allah daya fini son ummata shi ya dauke ta bawai dan bayaso na bane tana kaiwa nan ta fice a dakin da sauri, tana shiga dakinta ta fada gado tana risgar kuka.
"Tunda imaan tabar dakin kalaman ta suke ta yawo a kwanyar sa, shi kansa yasan be mata adalci ba kusan 2months da auren su kenan bata sa mummy a idon ta ba, can gida ma mummy sai tmbyr ta take sai yyi mata karya yace kr2 take tunda suna exam dake anyi mata jumping tana zana waec., aikin sa yakeson ci gaba Amman ya kasa, wata wawiyar tsuka yaja sannan ya rufe system din, toilet ya fada yyi alwala dake lkcn magrib ya gabato, masallaci ya wuce, bashi ya dawo ba sai bayan isha. "Dakin imaan ya nufa dan kiranta ta fito ya kaita wajen mummy. "A daidai lkcn imaan ta fito daga wanka bayan tayi sallolin ta, towel din dake jikin ta ko Rabin cinya bekai ba, sai wani dan karami dake hannun ta tana goge gashin kanta dashi, batare da knocking ba omar ya bude komar a hankali, idanun omar ba inda suka sauka sai kan santala santalan cinyoyin imaan masu matukar haske, sosai ya tsurawa wajen ido yana yiwa Allah tasbihi, tunda yake a rayuwa be taba ganin mace me kyawun cinya irin imaan ba sosai ya tafi duniyar tunani har lkcn idonsa nakan cinyar ta duk wannan tunanin cikin minti daya yyi shi, imaan kuwa tayi saurin jawo katon hijab dinta tana kare jikin ta, wani uban tsaki yaja sannan yace kiyi sauri ina jiranki a falo zamu wajen mummy, "jin an ambaci mummy batasan lkcn da tayi karar murna ba, cikin kayan ta ta nufa, ta dauko doguwar Riga marar nauyi, da dan karamin hijab ba wata kwalliya tayi ba sannan ta fito a dakin. "Omar yana zama kan kujera hoton cinyoyin imaan ke masa yawo a ido, mwsss yaja tsaki a zuciyar sa yace saikace ban ta6a ganin mata cikin wannan shirin ba? Meye wata imaan?... Imaan CE ta katse masa tunani da fadin ya omar na fito, omar ya dago ya kalleta sai kuma ya tabe baki, ba tare da yace mata komai ba ya nufi hanyar waje.
"Koda sukaje mota imaan gidan gaba ta shiga dan gujewa masifar shi, omar ya kunna mota, imaan kam farimcikin ta ya kasa boyuwa, omar duk yana lura da ita ta gefen ido.
"Kusan tafiyar 30mins tayi musu a gidan mummy, ko gama daidaita parking omar beyi ba imaan tahau kokarin bude kofa burinta kawai ta ganta gaban mummy. "Da sauri omar ya riko hannan ta, saida ya daidaita parking din sannan ya kalleta cikin ido, imaan tayi saurin kauda nata idon. "Omar yace bakida hankali ne ban gama parking ba ki fice a mota? Imaan tayi shiru, omar yace bari kiji kada ki kuskura ki sanar wa mummy abinda nake saki a gida, matukar kika sanar mata sai ranki yyi mummunan baci, bayan haka, idan ta tambayeki dalilin rashin zuwanki kice mata kr2 ne ya saki a gaba dan bakyaso kiyi failing, kinaji na? Imaan ta gyada kai duk ta kosa ya sakar mata hannu ta tafi wajen mummy. "Omar yace gud. Sannan ya sakar mata hannu, kaman jira take tayi saurin bude kofa. "Har zata falfala da gudu omar yace dakata ya fada adan tsawace, dole imaan taja burki. "Cikin takunsa na kasaita ya iso inda take sannan ya rike mata hannu. "Imaan ta kalleshi saidai ta kasa CE komai a zuciyar tace me ya omar yake nufi da hakan? Bata da wani answer haka suka isa bakin falo. "Mummy da daddy har farooq daya zo gidan suna zaune a falo, sai jin knocking sukayi. "Farooq ne ya bude kofar, ganin omar da imaan ba karamin mamaki yyi ba, imaan kuwa tayi kokarin kwace hannun ta takasa saboda rikon da omar yyi mata. "Farooq ya matsa gefe yana fadin welcome sis &bro. "Mummy njin haka ta juyo ganin imaan yasa ta saki murmushn farin ciki, saida suka shiga cikin falon omar ya sake wa imaan hannu. "Dama hakan take jira da sauri ta fada kan mummy cike da murna. "Daddy yana gefe yyi gyaran murya yace wato Mummy kadai akayi missing, imaan tayi saurin juyowa cike da kunya ta shiga gaishe dashi, da murmushi a fuskar sa ya amsa mata. "Itadai mummy sai kallon imaan take yanda ta zuba uban rama da baki. "Itako imaan sai zuba take, farooq dake gefe yace a'a mudai an manta damu. "Imaan ta kalleshi tace ya farooq fushi nake dakai ai. "Farooq ya zaro ido yace Tofah wanne lefi nayi? Imaan tace kaki zuwa inda nake, kaki turomin Anty ameera kamar yanda kace zaka dinga kawota Amman shiru. "Farooq ya rike kunnen sa afuwan matar bro zaki gammu insha Allah. "Imaan tayi murmushi tace Allah yasa. "Haka duk suke hirar su gwanin sha'awa, can mummy ta kasa hakura tace omar anya kana kula da imaan yanda ya kamata?
Nuceey luv😘