96-97
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
96_97
Kamar saukar aradu haka tmbyr tazo masa, imaan CE ta kafe shi da ido tana jiran amsar dazai bawa mummy, ga mamakin ta sai gani tayi yyi murmushi yace mummy kingan ta nan kullum sai nayi mata fada akan ta ragewa kanta tunanin exam dinnan, kumafa wani lkcn sai nayi dgske takecin abinci wai idan tana kr2 batason tashi, nima walhy abin na damuna duk ta rame tayi baki tasa tunanin exam a ranta."baki galalaaaa imaan ta saki tana kallon yanda omar ya karkace baki yana zabga uban karya. Mummy ta maida kallon ta ga imaan ga dukkan alamu ta gamsu da bayanan Omar sannan tana yiwa imaan kallon me ciki dan wannan ramar tayi yawa, mummy tace haba imaan be kamata ki zurfafa tunani akan exam dinnan ba kinji, komai saffa2 ake, ki dinga cin abinci kan lkci kodan abinda ke cikin ki... Da sauri imaan ta kalli mummy a zuciyar tace wato kallon me ciki ma takemin? Kallon ta ya koma kan omar shima yyi mamakin abinda mummy tace, saidai suna hada ido da imaan ya saki murmushin mugunta waton ya toshe duk wata hanya da za'ayi zargin sa kenan. "Mummy kam nan taci gaba da jawa imaan kunne, daga nan sukaci gaba da hirar su, kusan karfe 10 omar yace mummy zamu tafi, mummy tace aa I tot kwana zakuyi a nan? Omar yace aa, a hankali imaan tacewa mummy dan Allah kice ni ya barni na kwana anan. "Mummy tace gsky kabarmin imaan ta kwana tunda gobe Sunday babu skul. "Omar ba yanda yaso ba kenan. Gani yake idan yabar imaan zata iya fadawa mummy gsky, dan haka yace shikenan mummy nima anan zan kwana. "Farooq ya mike yana fadin toh mummy nikam na wuce raba wa'annan masoyan za'a sha wuya. "Omar ya harareshi yace bamason sa ido. "Nan yyi musu sallama yabar gidan. "Daddy ma dakinsa ya wuce, "sai 11 mummy tace suje su kwanta. "Da sauri imaan ta shige dakin mummy, omar yana kallon ta batare d yace komai ba ya wuce side dinsa. "Mummy CE ta shiga daki zaton ta ko wani Abu imaan zata dauka saita ganta a kwance kan gado. "Mummy tace ke lpy kika kwanta anan? Imaan tace mummy bacci zanyi. "Mummy tace a'a tashi ki tafi wajen mijin ki banason kauyanci. "Kunyace ta lullube imaan, wai ta tafi wajen ya omar, imaan tace dan Allah mummy ki barni na kwana anan. "Mummy tace kinsan ni dai banason gardama. "Baynda ta iya ta tashi, sannan ta jawo hijab dinta, taso cire kayan bccin dake jikin ta Amman bazata iyaba dan batason yin bcci d dogon riga, dan Allah yyita d son kayan bcci. "Haka tabar side din mummy tana ta kumbure2, "bude kofar falon tayi taga omar a falo. Qarasawa tayi a hankali, sannan ta nemi wata kujerar ta zauna batare d tace masa komai ba. "Omar yace kee mekika zoyi a anan? Imaan tayi banza dashi dan wani irin haushin sa takeji. "Omar yace ba mgn nake maki ba? Imaan tace bcci zanyi. "Omar yaja tsaki sannan yatashi a falon ya koma ciki. "Imaan na zaune falo sanyi ya isheta, gashi bazata iya komawa wajen mummy ta karbi bargo ba, dan haka tayi ta maza ta nufi dakin omar. "Kwance ta ganshi saidai ba bcci yyi ba, sunan shi ta kira, omar yace lpy? Tace am.. Dan Allah ka aramin bargon ka na rufa dashi. "Omar ya dago yana kallon ta sama da kasa sannan yaja uban tsaki yace lalle bakida hankali ko. "Imaan tace dan Allah, omar yace bazan bayar ba. "Imaan najin hakan ta nemi waje ta zauna a dakin, sannan ta kwanta a Capet dake ta gefe a dakin sannan ta nade cikin hijab din dake jikinta, bcci ne ya fara fisgar ta saidai har yanzu bata dainajin sanyin ba. "Omar yana daga gado duk yana kallon ta, ganin bata daina rawar sanyi ba sai kuma ya kira sunan taa, tana jinsa tayi banza dashi. "Omar ya sauko daga gadon sannan yazo inda take kwance, daukar ta yyi ya sanya ta kan gadon. Imaan najin sa, bargon sa ya lulluba mata a jikin ta, sannan ya cire hijab din jikin ta, da sauri imaan ta shige bargon a matsayin juyi tayi tana bcci dan batason yaga jikin ta, omar be kawo komai ba duk zaton shi bcci take, bayan ya aje hijabin ya matsa gefe shima ya fara bacci.
"Cikin dare sanyi ya dami omar, yarasa dame zai lulluba duk yanda yaso yaci gaba da bccin a haka ya kasa, dole ya matsa inda imaan ke bcci, sannan ya jawo bargon ya shige, numfashin imaan ne yake sauka kan hannun sa a hankali haka nan yaji dadin saukar numfashin da haka shima bccin yyi gaba dashi, "sai kusan asuba omar ya farka, abunda ya matukar bashi mamaki shine yanda yaga imaan makale jikinsa sai bccin ta take hankali kwance, da farko yyi niyyar tureta, Amman daya lura cikin bcci tayi hakan sai shima ya rungumo ta tabaya wani irin dumi me dadi yaje a jikin imaan, take wani bccin yyi gaba dashi.
"Basu suka farka ba sai 5:30 imaan CE ta fara tashi, ganin ta jikin omar ba qaramin mamaki tayi ba, motsin tashin ta shiya Tayar d omar, bude ido yyi yana kallonta yace matsamin mana daga taimaka miki ki kwanta sai shigemin jiki? Kunyace ta kama imaan dukda ta kasa yadda ko itan ta rungume shi da gske. Tana nan zaune har omar yayo alwala sannan ya tada salla dan lkcn masallaci ya wuce. "Imaan itama tashi tayi tayo alwala sannan tayi sallar ta, kafin ta idar har omar ya koma kan gado. "Itama tana gamawa ta koma kan gadon saidai ta matsa gefe Sosai, sannan ta rufi da bargo. "Omar daya juya mata baya ya kasa bcci tun dazu, qarshe ya gane dumin imaan yakeson ji, kallon ta yyi yaga tayi nisa a bcci, a zuciyar sa yace wannan wacce irin kasa CE? Daga kwanciya sai bcci? Da wannan tunanin ya matso inda take kwance ya bude bargon a hankali, sannan ya shige ciki.
Nuceey luv😘