CIWON SO

10

by @khadeejacandy


ABIEY POV. 


Dawowa yayi falon ya zauna, Anty Amarya ta tsare shi da ido irin kallon nan na babban da ya tsare yaro da bayan jin magana, and ba zai iya daga ido ya kalleta ba, sai shafa kansa yake. Cikin abun da be fi minti talatin ba da yan dakiku Ammy ta iso gidan, yanayin yadda ta turo kofar falon ta shigo ya isa ya karantar da su a fusace take. 


“Abu dai kamar wasa sai gashi kin zo”


Anty Amarya ta fada tana dan murmushi domin ta san Ammy ba kanwar lasa bace, sai dai wani lokacin ta kan dauke ido akan abun da ya shafi Masarautar ko Mai Martaba. 


“Au ba zan zo ba, sai na zuba ido a saka min da a gaba? So kike su sake samun wata hanyar ta bata masa suna? Ko su lalata masa rayuwa?”


“Ammy da dai kin yi hakuri kin saurara na wani lokaci bana tunanin Mai Martaba zai yi haka saboda ya musgunawa Abiey...”


“Aa Hajiya Zuwaira ni ba irinki bace da zan sakewa kishiyoyi dama suna yadda suke so, ba zan bari a raina min da ba, ni na haifi abina ni an san wahala da zafin abuna, babu abun da muke nema gurin Mai Martaba kin sani, ko yau Mai Martaba ya fadi ya mutu zan iya ciyarda iyalansa har kashen rayuwarsu, bana bukatar komai daga gurinsa balle kuma abokan zamanki, dan haka bana tsoron kowa a cikinsu, ke dai da kika ga zaki iya zama a raina ki, a raina yayanki sai ki yi ta tsoronsu”


Anty Amarya ta yi murmushi. 


“Ba tsoro ba ne, mahakurci mawadaci wata rana sai labari, su ma da suke ganin sune da gida ba a haka za a dauwama ba”


“Toh ki zauna nan kina tsoronsu, shiga ki sanar masa ina son magana da shi”


Anty Amarya ta yi murmushi mai sauti ta nufi kofar da zata sadata da bangaren Mai Martaba, Abiey dai kansa na kasa be daga kai ya kalli Ammy ba, kuma be saka bakinsa ba. Ammy na tsaye har Anty Amarya ta fito ta yi masa iso suka sake shiga gurin a tare. Har turakar Mai Martaba Anty Amarya ta shiga da Ammy saboda Mai Martaba ya bata umarnin haka. Ammy na shigowa dakin Anty Amarya ta juya ta fice, sai Mai Martaba ya dago kansa a hankali ya kalli Ammy dake sanye da buba ta farin lace da farin mayafi jakarta rataye a hannu. 


“Na ji ance ka saka wa dana masu tsoro saboda me?”


Ta aika masa tambayar kai tsaye abun da ba a taba masa ba, kuma babu wanda yake masa haka ya zauna lafiya sai tsohuwar matarsa uwar dansa. 


“Tambayarka na ke, ko wadacan isassun matan na ka ne suka kawo shawara? To Dana be so”


Uffan Mai Martaba be ce mata ba, sai kallonta yake da duban mai wuyar fassara, domin babu alamun fushi ko bacin rai a tare da shi, kallo ne irin na wanda ido suka yi marmarin gani da kuma burgewa. 


“Dana ba mashaye ba ne, balle ka ce maye yake, ba manemin mata ba ne balle ka ce zai lalata maka sunan zuri'a, to ba shi dogarawa na meye? Daurin zane na baya ga walle? Kai da ka gama kwance masa zane a kasuwa sai kuma ka dawo gida ka ce zaka daura masa? Ai duniya ta gama sani kuma ka riga ka nunawa kowa Aliyu ba shi da uba...”


“Abiey ba shege ba ne...”


Mai Martaba ya fada a tsanake yana taron numfashinta tun gabanin ta karasa furucinta.


“To miye ya rage? Tun na haife shi ka taba saka hannu ka dauke shi? Ko ka taba tambayar lafiyarsa, da na bar gidanka ka taba aikawa a dubo lafiyarsa? Ko ka taba taba siyen tufafin naira biyar ka aika masa? Sai yanzu? Ka ce zaka juya shi yadda kake so? Saboda ka auro Matar kwarai ta dawo tana neman cilasta muku alaka kai da shi? Aa ba zan yarda ba babu wanda ta haifa min Aliyu a cikin matanka dan haka babu wanda zata bada shawarar yadda zai yi rayuwa, ni ce uwar ďana ni ce ubansa”


“Har gobe.... Baki da... Uban diyan da ya fini...”


Mai Martaba ya fada a rarrabe irin ta masu isa da Martaba da basa furta magana mai tsawo a jere, yana kallon cikin idon Ammy cike da jin zafin furincin da shi kansa ya san ba karya ta fada ba. Sai ta girgiza masa kai. 


“Ni uban yayana ya mutu, bayan shi kuma ban san wani uban yaya ba, domin Aliyu a gurina shege ne ba shi da uba”


Take Mai Martaba ya mike tsaye ya nuna ta da yatsa cikin bacin rai. 


“Bakinki kar ya sake furta sunan Abiey idan ba zaki iya kiransa da lakaninsa ba, karki sake kiran sunan Mahaifina”


Ammy ta gyara tsayuwarta irin na daman jiranka nake, domin da ganganci take nanata sunan bayan kuma ta san Abiey ya ci sunan tsohon Sarki ne. 


“Kai yake sunan mahaifinka, ni kuma sunan ďana ne”


Tana furta haka ta juya ta fice daga dakin fuuu kamar an turata. Bacin marar misaltuwa ya taru a zuciyar Mai Martaba tun da yake a rayuwarsa baya jin an taba masa cin mutunci irin na yau da Ammy ta yi masa ba tare da tsoron komai ba, babu abun da ya tsana a duniya kamar a ambaci sunan mahaifinsa, komai zaka aikata a duniyar nan idan ka ci sunan mahaifinsa zai daga maka kafa kuma zai girmamaka, yana daya daga cikin dalilin daya saka ya hana ko wace mace a cikin matansa sakawa danta ko yarta sunan iyayensa sai Abiey da shi ya rada masa sunan da kansa, a wani lokacin can kamin duniyar soyayyarsu ta ma'aurata ta rikide zuwa kiyayyah. Mai Martaba irin mutanen nan da basa wasa da sunan iyayen balle abun da ya shafe su. 

 A fusace Ammy ta iso falon, sai ta samu Abiey zaune shi kadai yana latsa waya. 


“Tashi muje”


Ya dago ya kalleta. 


“Cewa yayi na bar masa gidansa?”


“Na ce maka dai ka taso muje”


“I just want to know so that na bar masa gidan har abada”


Furucinsa na karshe ya saka Ammy zubar da makamanta ta matso kusa da danta da ya mike tsaye fuskarsa na nuna ransa a bace yake ta soma masa magana cikin sanyayayiyar murya. 


“Aliyu ba a fushi da iyaye, no matter what Mai Martaba zai maka mahaifinka ne ko kaƙi ko ka so, and ba zaka tana iya shiga aljanna ba idan babu yardar ďaya daga cikinmu, ya alla ni ko shi, matukar kana son ka yi albarka dole na ka bi mahaifinka, so ka saka wannan a zuciyarka ba zaka taba fushi da mahaifinka ba zaka tana rabuwa da shi ba har sai idan mai rabawa ce ta raba, but for now he need some space ka san bana son abun da zai bata maka rai Autana? Zo mu je”


Ta karasa tana kai hannunta ta rika hannunsa su nufi kofar fita falon, duk abun da ke faruwa akan idon Anty Amarya dake tsaye upstairs tana kallonsu cike da burgewa, sai dai bata nuna tana ganinsu saboda ta bawa Ammy damar natsar da danta da kuma fada masa gaskiya irin ta uwa ta gari. Ammy na fitowa daga falon Anty Amarya ta kusa cin karo da Mama Lami dake kokarin shigowa falon rike da bandir din kudi a hannunta, da alama wani ya labarta mata cewar an ga shigowar tsohuwar matar sarki a gidan, domin ba kasafai kake ganinta gurin Anty Amarya ba sai irin wannan ta samu, kasancewar kowa da bangarensa kuma da masu yi masa hidima ga kuma yayansu, sai dai idan Ammy ta zo gidan da kanta take zuwa gurinta ta gaisa da ita ko kuma ta fakewa da ta zo gurin Anty, idan ba haka ba ko kusa da part din Anty Amarya bata bi, Anty Amarya dai ce take biye da su kullum kamar yarsu. 


“Aa Maa Shaa Allah, Hajiya Umaima yau a gidan na mu”


“Ni ce, ai kin san idan aka gan ni a gidan nan ďana Aliyu aka taɓo”


“Haba dai Hajiya ai ba a cin gira kusa da ido, ko ba komai an mun ci ki a sakaya sunan Abiey, kuma yan iya magana sun ce ka ki naka duniya ta so shi”


“To ni na so ďana, ki buga tambura ki yi shela ki ce duniya ta ki Aliyu”


Murmushi Mama Lami ta yi tana kallon Abiey da tuni ya kai gurin motarsa domin basa shan inuwa ďaya da Mama Lami duk cikin mata mahaifinsa ya fi tsanarta kara ma Hajiya Kilishi yana daga mata kafa sosai, amman Mama Lami ko Anty Amarya ta cilasta shi gaisheta ji yake kamar tace ya cire ranshi ya bata. Dauke kai ta yi ta tura kofar dakin Anty ta shiga tana dariya, Anty na ganinta ta karasa sauko da take suna gaisawa. 


“Wai ni Umaima tana ba ni mamaki, ka bar gida amman kishi baka bar shi ba? Ko gani take kamar ni na kashe mata aure da Mai Martaba ne? A duk lokacin da zan hadu da ita magana sai wance ta manta?”


Anty Amarya dai bata ce komai ba bayan murmushin da ta yi ta mika hannu ta karbi kudin da Mama Lami take mika mata. 


“Yar ribar da aka samu ce ta watan daya shige Mai Martaba ya bada yace a raba, shi na na dan debo miki ke da su Aisha”


“Toh mun gode Allah ya saka da alheri ya karawa yi ma arziki albarka”


Ta fada bayan ta karbi kudin, Amin ma wuyar fitowa take a bakin Mama Lami idan isar ta tashi haka tasa kai ta fice ba tare da ta amsa addu'ar da Anty ta yi ba. Sai da ta fice sannan Anty ta girgiza kai. 


“Uhmm wasu mata na mulki, wato har an kawo an raba ban sani ba sai da aka debo aka sammana, akwai Allah ba a nan zamu dawwama ba Lami”


Ta fada tana jin wani kololon bakinciki na taso mata, haka suke mata sun maida ita ba kowan kowa ba a gidan, tana cikin gidan sai a yanke hukunci ayi komai bata sani ba, yaya biyu ma da Allah ya bata sai sun ga dama Mai Martaba yake musu abu, kuma abun da duk suka ce haka za'ayi musamman ma Mama Lami, Anty Amarya kam da ita ta banza duk daya a gidan aikinta kawai ranar girkinta ta yi girki ta shiga ta kula da mijinta, amman komai na shi bata sani ba kuma ba a iya yanke hukunci tsakaninsa da shi sai abun da abokan zamanta suka yanke. 




ZAHRA POV. 


Bayan sun kwantar min da shi a saman gado suka fice suna masa addu'ar samun sauki, ni kam ban da aikin hawaye babu abun da nake, na kai hannu na taba shi na dauke na tambaye shi me ke masa ciwo amman be amsa min ba, sai runtse ido yake alamar yana jin azabar ciwo. Sai can hankali na ya bani na kira Hajiya na fada mata, jiki na rawa na dauki wayar na kirata ina kuka na fada mata halin da yake ciki sai hankalinta ya tashi kamin karasa maganar ta kashe wayar, sai na kira Mama na fada mata ina ta kuka. Sannan na kashe wayar na dawo kusa da shi na zauna na kama hannunsa na rike sai ya kalleni ya lumshe idon yana matse hannuna da yake dake cikin nasa. 


“Sannu”


Na fadar daker saboda kuka, be amsa min ba, be kuma yi min wata alama ta amsawa ba, be kuma sake bude idonsa ba hakan ya saka hankalina yayi mugun tashi, da sauri na tashi na shiga daki na dauko hijabina na saka na fito da zimmar na shiga makota na samu mai taimaka min mu kai shi asibiti kamin Hajiya ko Mama su iso, sai na yi kicibus da Hajiya da ta nufo kofar gidanmu ina kuma na fito sai na nufeta ina kuka, ita ma kana ganinta ka san karfi hali ne kawai irin na manyan iyayen da basa son nuna kuka a gaban yayansu. 


“Ba kuka ake ba, addu'a ake”


Tana rufe baki na hango Baba tare da Mai Napep suka faka a inda muke tsaye sannan ya fito da saurinsa. 


“Shiga mu fito da shi a kai shi asibiti”


Na juya da gudu kamar ba mai ciki ba na shiga cikin gidan Hajiya ta biyo bayana, da taimakon Baba da Hajiya suka fito da shi waje suka saka shi napep din, makotan da ke kusa da mu suka fito suna fadin


“Subhanallahi Allah ya bashi lafiya”


Ni dai ko kallonsu kasa yi na yi balle na amsa sa Amin, sanin Napep din ba zata dauke mu gaba daya ba yasa na rufe gidan na nufi titi na tari wata napep din na hau na bi bayansu. Kamin mu isa asibitin Mama ta kira tana tambayar muna ina ta zo gida a rufe sai na fada mata cewar muna hanyar asibiti. Kai tsaye mai Napep sin daya dauke su Emergency ya nufa da su ni kuma nawa mai napep din ya sauke ni a ida aka kayade ma masu abun hawa aje passengers, na saka hannu a jaka na dauko kudinsa na mika masa ban ko tsaya karbar canji ba na nufi cikin asibitin da saurina kamar na tashi sama. 

 Ko da na isa har sun karbe shi sun shiga da shi ciki, ni da Hajiya muka zauna a inda muka ga wasu zaune kam kace kwabo har wata nurses ta fito ta fada mana inda zamu je mu karbo file dinsa bayan ta gama tambayar cewar yana da file a asibitin, sannan likitan ya kira Baba yana tambayarsa miya faru kamin mu kawo shi asibitin, Baba ya kira ni ni kuma na fada masa abun da abokan aikinsa suka fada mine, sannan suka tambayi ciwonsa muka fada musu, a take na ga hankalinsu ya tashi. 

Ana kawo file din suka ware masa wani daki dabam suka rubuta mana wasu tests da hoto da zamu je mu yi, ina mika hannu na karba Baba ya karba ya ce na zauna na yi jinyar mijina. 


“No ba a matse mutum mai irin wannan ciwon, ke kanki kina bukatar gwaji a yanzu, duk wanda yake tare da shi yana bukatar a gwada shi, balle ke ma da kike da ciki”


Likitan ya fada, sai na daga ido na kalleshi. 


“Saboda me?”


“Ciwonsa ya kai matakin da zai iya shafawa wani”


Na kalli Deen hawaye na sauko min, can cikin kuka na ji Hajiya ta mika hannu ta karbi wayar hannuna tana amsawa Mama dake kirana tare da fada mata inda muke. Yanayin yadda jikin Deen yake ya saka sai a dorashi saman gadon zuwa gwajin da aka rubuta masa da kuma hoton, wannan karon kudin da muka kashe ya fi wacan yawa saboda sun ce wannan babban hoto ne gwajin ma babba ne. Kam kace kwabo mun kashe kusan 100k+ a rana daya na gwaji kawai sai na dan maganin da muka siyo masa. 

Bayan sallah La'asar muna zaune office din likitan ya dubu ni ya ce. 


“Karki ji kunya ko nauyin tambayar da zan miki, kuma karki boye min komai”


Na daga masa kai idanuwa a kumbure saboda kukan da na sha. 


“For how long kika san mijinki yana dauke da wannan cutar”


 Na fada masa, sai ya dora min da wata tambayar. 


“Idan mijinki zai yi mu'alama da ke yana saka condoms? Kuma ya yanayin mu'alamarku yake? Kuna sharing the same room”


“Har abinci tare muke ci, kuma baya amfani da wata kariya”


“Ya taba fada miki cewar likitoci sun ce ya kebe kansa?”


Na girgiza masa kai alamar aa. 


“Seriously kina bukatar a gwada ki, gwaji na gaggawa ba ke kadai ba har iyayensa suna bukatar gwaji”


Gaba daya sai kaina ya kulle taya ciwon anta yake iya shafar wani? A zatona hiv ne kawai yake irin wannan illar! Ban ankaro ba na cinkayo muryarsa yana fadar. 


“Gaskiya idan har kuna son rayuwarsa dole ne, ku samo kudin nan idan ba haka zai iya rasa rayuwarsa, domin ciwon ya kai matakin da baku tsammanin mataki ne da ake kiransa da stage 4, and for now on ba za a sharing komai da shi ba har sai idan ya samu lafiya”


“Amman zai warke likita?”


Na tambaya domin shi ne kawai abun da nake burin ji a yanzu, sai ya kalleni kamar ma nazarin yadda zai furta min amsar da zata fito bakinsa. 


“In Shaa Allah”


Ban ga alamun haka a furucinsa da yanayinsa ba, sai dai hakan be isa ya karya min guiwar nemawa mijina kudin maganin ba. Ba mu bar office din ba sai da ya rubuta min gwaje gwajen da zan je na yi ni da Hajiya, duk yadda uwa zata yi ta karfafawa yarta guiwa Mama ta yi sai dai hakan be hana ni kuka ba, kuma be hanani shiga dakin da Deen yake ba, na ja kujera na zauna. Na yi zaton bachi yake sai ya bude ido ya kalleni kamin ya miko min hannunsa, ba tare da tunanin komai ba na mika masa nawa hannunsa sai ya maida idon ya lumshe, wanda hakan yayi daidai da shigowar Mama. Kallona ta yi kamin ta kalli hannunmu dake tsarke da na juna. 


“Ki bar shi ya samu bachi mana”


Bana son musa mata ko ba komai be kamata na rike hannunsa a gaban idonta ba hakan ya saka na sake shi, sai ta yi alama da na fita da ido, a take na mike tsaye na nufi kofar, ina fitowa ita ma ta fito. 


“Ki tafi ayi miki gwajin, kina jin abun da likita ya fada”


“Babu wani gwajin da za ayi min Mama, idan ma na kamu da ciwon ko ban kamu da shi ba, ba zan nisanci mijina ba”


“Ko baki yi dan kanki ba ai kyayi dan abun da yake cikinki ko?”


Na sauke ajiyar zuciya, ba dan na so ba tafi aka min gwajin a anan ma kudi aka kashe kan kace kwabo dan abun da Hajiya da Baba suka tara ya kusa karewa abu ga talaka.