7
_________Cikin mintunan da bai fi sha biyar ba, Abbas da Hajiya Rabi'atu su ka zo gidan Khaleesat tarar da Ibrahim su ka yi zaune a bakin gate ya zabga tagumi, ya na ganin motar gidansu Khaleesat ɗin ta tsaya a ƙofar gidansa ya tashi cikin rawar jiki,duk a tunaninsa ma Yaya Abbas ne kaɗai ya zo, sai da ya ƙarasa jikin motar ya na musu barka da zuwa, ya ga ashe har da Mama, sannu da zuwa ya ke musu, ya na ƙoƙarin durƙusawa a ƙasa ya gaishe da surukar ta sa, "tashi tashi mu shiga ciki"Mama ta faɗa ta na nufar bakin gate ɗin gidan, da sauri Ibrahim ya je ya boɗe ya na ce musu "bismillah" ya matsa baya Mama ce ta fara shiga, sai Abbas sannan Ibrahim ya shiga ya na mai rufe gate ɗin gidan.
"ina kike mara mutunci, za ki fito ko kuwa mu za mu zo?" Mama ta faɗa cikin faɗa Khaleesat da ta gama haɗa kayanta cikin box ta na ta kuka da haɗa karyar da za ta faɗa akan Ibrahim,ta ji muryar Mamansu.Wani irin faɗuwar gaba ce ta dirar mata kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka ta fito ta na hawaye, Ansar kuwa tun ɗazunya tashi jin muryar Mama cikin faɗa ta razana Yaron ya sa kuka, Abbas ne ya ɗauke shi ya na jijjiga shi, Ibrahim kuwa zama kawai ya yi,ya yi shiru, dan shi ma so ya ke yaji wana laifi ya yi wa Matar ta shi, Abbas da ke kusa da Khaleesat ta na shigowa parlour'n ya wanka mata mari, dan ya na da matuƙar zuciya sosai, fashewa ta yi da matsanancin kuka,Mama ta ce "ka yi dai-dai Allah ya yi maka albarka ƙara mata" marin da Ibrahim ya ji shi har cikin ransa sai da ya runtse idanunsa dan zafin da ya ji, Abbas ya ce" haɗiye kukan ko in zane ki anan shashashar banza" daina na wa tayi sai dai hawayen bai dai na zuba ba, Ibrahim da ke ƙasa a zaune kan carpet,ya ce "ayi haƙuri Yaya dan Allah" Mama ta ce "me ya haɗa ku har kike ce masa ya sake ki?" tuni Khaleesat ta fara kame-kame, me za ta ce ta daina sonsa,ko kuwa ba ta so ya ke kusanceta ko kuwa tsanar sa ta yi? "uhm,uhm...Kawai ta ke ce wa ta rasa ta inda za ta fara, tsawa Mama ta daka mata" ba za ki magana ba sai na saɓa miki" Aljanin da ya haɗa wannan masifar ya na kallonsu, sai dariya ya ke ya na jindaɗi zai raba aure, dan son Khaleesat ɗin da kishin ta ya ke shi ya sa bayason ya sadu da ita kuma bil'adama ma ya yi shi ya sa zai raba musu aure ta zama ta shi, shi kaɗai.
Khaleesat ta ce" ni dai dan Allah ku raba auren nan ba na sonsa" sai kuka, wata iriyar mummunar faɗuwa gaban Ibrahim ya yi jin furucin Matarsa Khaleesat, shiru kawai ɗakin ya yi na wasu seconds, Mama ta kalleta ta ga da gaske ƴarta ta ta ke, ta ce "me ya yi miki?" Khaleesat cikin kuka kamar za ta shiɗe ta ce, cutata ya ke yi, ba ya kulanik tsakanina da shi sai hantara da baƙar magama, tunda na dawo daga gida ya sauya min, kuma har bin Matan waje ya ke" hannu kawai Ibrahim ya ɗora a kansa ya na furta kalmar" Innalillahi'wainna'ilaihirraji'un, ni Khaleesat ki ji tsoron Allah ki faɗi gaskiya" daga Yaya Abbas har Mama ba su yarda ba, dan yanda ta ke maganar ma za ka fahimci ba a nutsuwarta ta ke ba, Mama ta ce " ai ruwa ba ya tsami banza, me ki ka yi masa ya faɗa wannan halin?" nan ma Khaleesat ta rasa abinda za ta ce,Aljanin MIJIN DARE da ya ke gudana a jikin Khaleesat ya sa ta kuma ce wa" ni banyi masa komai ba, ko ya sake ni ko na kashe shi" ta faɗa ta na zaro wa Iyayen nata idanunta waɗanda su ka juye su ka yi jajir. Take Ibrahim ya fahimci ba ta haiyacinta, Yaya Abbas ya kuma ɗauke ta da mari zai ƙara mata Ibrahim yai riƙe shi ya ce " dan Allah ka daina dukanta haka Yaya, za mu sasanta kan mu insha Allahu ku yi haƙuri Mama, laifi na ne zan gyara" tausayinsa ne ya kama Mama ta ce" wallahi Abban Ansar nasan ƙarya ta ke yi, akwai masu zugata a gefe kuma kai ta za suyi su baro, dan Allah ka yi haƙuri, ba ni ruwa a cup, da sauri ya nufi kitchen ya ɗauko bottle na ruwa da cup ya dawo, zubawa ya yi ya miƙawa Mama ta karɓa ta fara addu'a ao ruwan Yaya Abbas sai harara Khaleesat ya ke ji yake ina ma an bar shi ya farfasa mata jikinta, Allah ya ba ta Miji mutumin kirki ta na jifansa da munanan maganganu, da shi ne sakinta zai yi dan Ubanta. "karɓi ki yi bismillah ki sha" Mama ta fa ɗa da tsawa,hannu na rawa Khaleesat ta karɓa ta sha, ta na sha kuwa zuciyarta ta yi sanyi, ta ke ta dawo hankalinta ta kallesu sai ta sun kuyar da kai ƙasa, ta na share hawaye Ansar da ke kuka ƙasa-ƙasa Ibrahim na jijjigashi Mama ta ce "karɓe shi" a hankali ta tashih ta ƙarɓi Ansar ta zauna ta na jijjiga shi, ganin ba zai shiru ba ta sa masa nono ta na kallon ƙasa,kunyar abin da ta yi take ji, Mama ta ce" Abban Ansar me ta ke maka?" Ibrahim ya yi shiru, Yaya Abbas ya ce"ka faɗa mana kar ka cutar da kanka" Ibrahim ya ce" ba ta girki, ba ta min magana mai daɗi, duk wata kyautatawa ta daina yi min, amma zamu gyara" tausayinsa ne ya kama Mama ta san tunda ya faɗa, to kuwa hakan ne sosai ta yi wa Khaleesat faɗa, ta kuma bawa Ibrahim haƙuri sannan ta ɗora musu da nasiha, su ka tashi za su tafi har bakin gate Ibrahim ya rako su, ya na ta godiya su ka hau mota su ka koma gida.
Abbas ya ce"Allah Mama kawai iskanci ne dan taga ya na sonta sosai, ta ke gasa shi, wallahi da ni ne sakin ki zanyi ki je gidan naku sai me" Mama ta ce" to sarkin saki, abun da Allah ba ya so ayi shi kake faɗa to ba kai ba ne, shaiɗan ne ya ke wasa da zuciyarta da alama ta na sakaci da addu'a, kasan Manzon Allah (s.a.w) ya faɗa ma na cewar Shaɗanu su na gudana a cikin jikin mutum kamar yarda jini ke gudana ko" Abbas ya jinjijina kansa ya ce "hakane Mama"to shi ne ya zugata ta ke wannan abun, sai dai kawai Allah ya kyauta" da haka su ka isa gida, Dan Abba baya gari ma da yau Khaleesat sai ta gayawa ƴan garinsu.
Aljanin da tunda yaga Mama ta fara addu'a ya gudu daga ɗakin yana mai baƙin cikin zuwansu gidan tare da ɗaukar alwashi akan sai ya raba Khaleesat da Mijinta......
SHAMS da ke zaune a gadon hotel ɗin da ya ke ciki, ya na ta accepted ɗin Architects ɗin da su ka yi apply ta E-mail ɗin sa,ya na duba duk wani qualifications da aka turo, sosai ya ji daɗin ganin irinsa da yawa ƴan arewa da su ka gama karatu
,sai da ba aiki wasu sun jima da graduation ma, date ɗin da za suyi interview ya aika musu sannan ya ta shi ya shiga wanka dan komawa Lagos.
Iftihal da ke kwance cinyar Mami suna hira, ƴan aiki na ta kai kamo a parlour domin haɗa dinner, Iftihal ta ce"Mami ina so zanje gidan Abba in kwana biyu, tunda aunty Feenat ta dawo ban je ba" Mami ta ce"a'a Iftihal kinsan dai Daddy ba zai bar ki ba,ina ma laifin ki ce za ki je ki wuni ki dawo ihum" shiru Iftihal ta yi ta na mai wasa da zobunan da ke hannun Mami. A kwai shaƙuwa da fahimtar juna tsakaninsu dan Iftihal ba ta da ƙawa kamar Mahaifiyarta duk wata damuwa da ta sa me ta babu wanda zai fara sani sai Mami.
"barka da hutawa Hajiya an kammala komai" Lantana mai aiki ta faɗa cikin girmamawa " sannunki da ƙoƙari,Allah ya yi albarka" sosai Lantana ta ke jindaɗin aiki a gidan Mami dan babu tsangwama ko cin mutunci kuma babu takura, Iftihal ta ce" Baba Lantana gobe dan Allah za ki min kitso amma manya za ki min" da fara'a Lantana ta ce" to Auta Allah ya nuna mana goben lafiya" ta fita ta koma sashinsuj na ma'aikata.
D.S P. Muhammad Hashim aboki ne ga Alhaji Alhassan Nuhu mutum ne ɗan bokoh ya na da ƴaƴa huɗu Abulbashar shi ne babba sai Abdulmaleek sai Abdurahman sai autar su Feenat sun taso cikin gata da sangarta, Matarsa ɗaya Doctor Raihana, wacce ta ke aiki a hospital ɓagaren ƙashi wato orthopedic, gida ne na rashin tarbiyya kowa sha'anin shi ya ke, dukkan Yaran sun yi karatu ne a waje Feenat yanzu ta na karatu a Australia ta zo hutu ne a yanzu haka, Feenat ta na masifar son SHAMS wanda bai san ma ta na yi ba, gaba ɗaya halayenta ya koma na turawa, kiss hugs, tsakanin ta da Maza ba komai ba ne idonta ya gama buɗewa, bata kunyar kowa hakama Yayunta kowa sabgar gabansa ya ke, Dr.Raihana ba bu ruwanta da kula da mai su ke yi dan ta yarda da cewa duk wanda ya kai eighteen years to yana da right ɗinsa, dan haka su ke abinda su ke so.
Feenat ta na son Iftihal hakama Iftihal duk da akwai tazara tsakaninsu Iftihal tana seventeen years, Feenat kuwa ta na twenty four years...