HUSNA KO HUZNA

Chapter 20

by @mamanyusuf

🅿️️_20




"Kai gaskiya kin hadu baby irin Wannan harka haka , wani luuu tayi da idanunta cike da Jan hankali tace " Allah alhajina , 

  Allah kuwa baby ke zazzafa ce gaskiya wannan karon ba k'aramun kyauta zanwa talatu ba don ta samomin irin kayan da nakeso , wani irin mik'a tayi tareda bank'aro k'irji hade da wani irin Nishi cikin salon ja hankali ,aikuwa tak'ara rud'a Alhaji Badaru (sabon kamun da Talatu tayi masu) aikuwa nan take yak'ara rikicewa nan ya janyota jikinshi sai faman lalubeta yake yana zuba sambatu ,


Alhaji Badaru tsoho ne Dan shekara 66 yanada matan aure biyu da yara goma Sha ukku Mata da maza , Mai kudi ne sosai shahararren Dan kasuwa Yana sana'ar sayar da atamfofi less da shaddodi , rikakken tsohon Dan bariki ne duk inda yaga Mata idonshi na kansu , ganin yanzu yanada yara da jikoki ga sarakkune yasa yarage wasu abubuwan , komai zaiyi yanzu a 'boye yakeyi  basu jima da haduwa da Talatu Bariki ba ita take samo mashi zankada-zankada yan Mata Yana lalata dasu , ba k'aramun kudi yake kashewa mace ba shiyasa lokaci Daya Talatu ta samu makundan kudade a hannunshi hade da manyan atamfofi , lokacin da ta kawo mashi anty Harira , anty Harira kyakykyawa ce sosai don duk yaran Abee ba Wanda bayada kyau sai dai wani yafi wani don dukkansu Abee suke biyowa shiyasa suke farare tas.ga uwa uba kyau,


Sunyi nisa sosai da abunda sukeyi sukaji ringing din wayar Harira , da k'yar ta janye jikinta daga gareshi ganin Mai Kiran nata , Talatu ce , dagawa tayi " Hello Momy , yawwa 'yar momy kin taso ne ? Cikin kasalalliyar murya tace aa Momy yanzu dai zan taso ,


Dafe Kai Talatu tayi tace ke Harira ya mukayi dake na gaya maki karki sake ki biyewa jarabar wannan tsohon don wallahi ko zaku kwana kuna Abu Daya ba gajiya zaiyi ba kawai ki sallameshi ki dawo gida ,kinsan dai halin mahaifiyarki da bin k'wak'wk'wafi , tunda safe take kirana akan ki dawo hakanan tunda dai kin kwanarmun kamar yadda na bukata , 

  Ok Momy ganinan zuwa yanzu , kashe wayar tayi , maimakon ta tashi din inaaa saima Kara janyo Alhaji Badaru da tayi suka k'ara lulawa ,

 Allah ya shirya Mana zuri'a,



___________________



Sati biyu kenan gaba Daya Yaya Mu'azzam yarasa abunda ke damunshi , duk lokacin Daya ke'be shi kadai fuskarta yake gani abun har mamaki da tsoro yake bashi yarinya k'arama yar shekara 10 itace zata hanashi sukuni , ga manyan babys Kamar zasu cinyeshi Amma yakare akan wannan jaririyar tabbas zuciyarshi ta zalunceshi , 

Tun Yana daukar abun Wasa har yafara tsorata don kullum Kara jinta yake azuciyarshi , bacci yanzu gagararshi yakeyi idan har ba yayi tozali da kyakykyawar fuskarta ba sannan ne kawai zai samu salama, 



____________________



Wai Ibarahim lafiyar ka qalau kuwa ? Naga kwana biyu Sam bakada nutsuwa ,miyake damunka ne ? 

    "Hmmm abunda yake damuna Sam bayada dadin ji Mustapha , yanzu wai Kamar Ni da Mata ke ribibi kamar zasuyi hauka yau nine zuciyata ta k'are akan begen yarinya k'arama , wai.........tsabar haushi ma yakasa karasa maganar , 


Kallonshi Mustapha yayi da kyau kamar zaiyi dariya sai Kuma ya kanne don yasan in har yasake yayi mashi dariya bazai yarda ya gaya mashi abunda yake son jin ba,


"Bangane abunda kake nufi ba Mu'azzam kayimun bayani yadda zan gane , 

     Mrtssss "ina wadan nan shed'anun na gidanmu ,

gyad'a Kai Mustapha yayi yace su Hassan kake nufi , ?

    Wane irin su Hassan wadan nan Hatsabiban da suka kusa karya maka k'afa Mana yaran Baffanmu , 

Oh Aljanun gidanku zaka ce , yayi maganar Yana dariya tunawa da abunda suka mashi Wanda saura Kiris ya gurde kafarshi , 


Nan Yaya Mu'azzam ya kwashe dik abunda yakeji akan Huzna ya gayawa Mustapha ,


Tun Mustapha na dariya k'asak'asa har yakasa danne dariyarshi nan yafad'i k'asa yarinka babbaka dariya Kamar zaiyi hauka , Saida yayi Mai isarshi sannan ya dubi Mu'azzam da tun dazu ya kafeshi da ido Yana aikamashi da wata irin harara kamar idonshi zasu fado kasa ,

yace "Kai gaskiya na tayaka murna abokina , irin Wannan kamu haka gaskiya kayi kwashi wallahi, yak'ara tuntsurewa da dariya ,


Bason iskanci kaji ko taya zan gayamaka matsalata don Neman mafita sai ka rinka mun dariya tsabar ka rainamun wayo, yayi maganar ranshi a 'bace , 

Ganin yadda ranshi ya 'bacine yasa Mustapha tsagaitawa da dariyar Saida ya daidaita kanshi sannan ya dubeshi serious yace "look abokina wannan fa ba wata matsala bace hasalima Ni Banga abun damuwa ba a nan ,

Ni shawarar da zan baka itace kawai ka yarda da abunda zuciyarka ke umurtarka dashi saboda yarinyar zata hada duk wani abunda ake buk'ata ga 'ya mace kaima kasan da haka don wallahi nan gaba sai kayi mamakin yaran nan , abunda zakayi kawai shine mi zai Hana ka janyo yarinyar a jikinka sosai yadda zaku shak'u da juna ta yadda nan gaba bazaka Sha wata wahalar amincewarta ba ,


Hmm Mustapha sai kace bakasan halin yaran nan ba , ai Dana Fara sakewa dasu Kuma ai sai su rainani dama ga yanda suke sai a hankali don yanzu ma bawani tsorona suke ba sai nayi masu Jan ido , 


To Kai ka sani tsaya kallon ruwa kwad'o yamaka k'afa wallahi ina tabbatar maka da cewa nan gaba ba k'ananan babys za'ayi ba sai kayi mamakin yadda samarin Abuja zasu bude wuta a gidanku akan wadan nan yan biyun wallahi Kai nifa da za'abani dayar ma da inaso wallahi don nasan zan kece raini nan gaba ,


Nifa da zakabi ta tawa ko da kamun ka wuce Canada wajan karatu ka daure ka samu su Abee kamasu bayanin cewa kanason Huzna zaka aureta na tabbata da zasuyi murna da farinciki sosai ,kaga bakada wata matsala don duk yadda zasuyi bazasu taba Bari wani ya tunkareta da maganar so ba tunda gaka kaga zakayi karatunka lafiya batare da wata fargaba ba shawarace Amma , don gaskiya in nine haka zanyi , da gabar kaje karatun kamun ka dawo wani yayi wuf da ita wallahi ,


Kuma kaga dama can burinka bazakayi aureba sai kanada 35yrs kaga kamun lokacin ita Kuma tanada 18yrs lafiya qalau zasu wanketa subaka ,ya karashe maganar da sigar tsokana,



Shiru Mu'azzam yayi yana tunanin maganganun abokinshi Kuma amininshi tabbas gaskiya ya fada mashi to Amma tayaya zai iya fuskantar iyayenshi da wannan maganar ai sai suyi mashi kallon mahaukaci duba da kankantar ita yarinyar haka dai sukayi ta tattaunawa akan maganar yayinda Mustapha ke faman zugashi akan kar ya yarda wannan damar ta su'buce mashi , 




____________________



Zaune suke a babban falon gidan kowane da abunda yakeyi, Jamil na gefe Yana duba wasu takardu yayinda anty Harira da Nasma ke zaune a dayan gefen suna kallo duk da anty Harira Rabin hankalinta Naga wayarta sai chart din banza takeyi da samarinta , 

Gefe Daya Kuma can wajan dining Yaya Aliyu ne zaune Yana wani aiki a computer dinshi , Wanda gaba Daya ya mayar da hankalinshi akan abunda yakeyi , sai dayan gefen Kuma daga bangaren dama anty safiya ce da wata k'awarta yar makarantarsu Mai suna Laila sun had'e Kai sai k'us-k'us sukeyi , 


Laila itace babbar k'awar Safiya class dinsu Daya , iyayenta masu kudi ne sosai Kuma ita kad'ai ce mace a gidansu shiyasa iyayenta ke matukar kaunarta suke sagartata da yimata duk abunda takeso , Sam kudi ba matsalarta bane don ko motar da take Hawa abun kallo ce shiyasa Safiya ke manne da ita kamar cingum , don Allah yayi safiya da shegen kwad'ayin tsiya , 


Laila Sam batada tarbiya sanna ta tsani talaka sosai.bawani shahararren kyaune da ita ba Amma akwai daukar wanka kullum zaka ganta Kamar d'iyar arna saboda yanayin shigarta Kamar wata k'abila , 

Yau ma sanye take da wani damammen wando baki sai yar 'bingilar riga da in tayi kwakwkwaran motsi zakaga cibiyarta sai wani uban gashin kanti da ta Sanya har gadon bayanta sai wani siririn gyale data yane kanta dashi , yayinda ta saki jelar gashin tana yawo a bayanta ,


Tun lokacin da Laila ta k'yalla idonta akan Yaya Aliyu taji duniya ba Wanda takeso sai shi , wannan dalilin ne yasa ta nacewa Safiya musamman da ta kula safiya nada mugun kwadayi sai akayi dace Ammi ma haka take da son banza wannan yasa take ganin Kamar tasamu Aliyu tagama tunda tagama da uwarshi dakuma kanwarshi 

Yaya Aliyu kuwa baima San tanayi ba ya dai kula tana yawan shige mashi yayinda shikuma ya ke ba babu ajiyarta don ya tsani mace marar kamun Kai, yanzu da suke zaune ma duk rabin hankalinta na kanshi hasalima saboda shi take zaune a falon,



Husna da Huzna ne tareda Hussaina suka shigo falon aguje da nufin zuwa part din Mamah , wani wawan birki Huzna taja lokacin da takawo dab da Laila , k'are Mata kallo tashiga yi yayinda tasanya hannunta ta rike baki irin alamar mamakin nan , 


Husna da Hussaina har.sunyi gaba suma suka juyo suka dawo da baya ganin Huzna ta tsaya ,

K'arasawa Huzna tayi kusa da su Safiya , safiya na ganinta ta Sha mur tace "lafiya 

    Washe baki tayi tace anty safiya wannan k'awarki ce ,? Tayi maganar tana wani washe baki , 

  Tsaki anty safiya tayi tace ina ruwanki da ko wacece kinga maza kibar nan kamun yanzu na makeki ,tayi maganar tana harararta, 


Maimakon ta tafi sai k'ara matsowa tayi tace laaaa anty Ashe anan man akwai masu irin gashin nan Mai yawa irin Wanda muke gani ga TV sannan.........ke Dan Allah ki bar nan kamun zuciya ta d'ibeni na babbalaki wallahi , 

To anty zan tafi Amma don Allah kibari na Dan ta'ba gashin nan naji yadda yake kinji , kamun safiya da Laila wadda ta zaburo a fusace suyi magana tuni Huzna taja jelar gashin iya karfinta , Wanda tayi hakan ne don tanason bakuwar taji zafi kawai duba da irin kallon wulakancin da take masu.amma ga mamakknta sai ganin gashin tayi a hannunta daga ita har su Husna ido suka zaro suna kallon Laila , Laila kuwa jin ancire Mata hullar gashinta yasa batasan sanda ta buga wata irin k'araba saboda gaba Daya wannan hular itace rufin asirinta batada gashi ko kadan kullum kanta kamar anci goruba da wuka yake ko wani namijin yafita tsawon suma wannan yasa kullum take amfani da hullar gashi Wanda mutane ke kallon duk cikin gayune a zahirin gaskiya Kuma ba haka bane donta rufawa kanta asirine don duk yadda kake da Laila kayi karya kace ga yanda gashinta yake,


Aikuwa gaba Daya jama'ar falon suka fashe da dariya harda rik'e ciki bama kamar Yaya Aliyu don haka ya ganta kamar wata horo ko irin yaran yarbawan nan da akema aski , 

Husna da Huzna da Hussain kuwa nan sukayi kwance suka rinka babbaka dariya kamar wasu tababbu sai faman rike ciki suke , ,hakama Harira da Nasma wani abunma don su cusawa Safiya haushi sukeyi nan fa suka shiga nunata suna dariya ,


Wata irin kunya ce ta rufe Laila kamar k'asa ta tsage ta shige haka takeji , yanzu shikenan wannan yarinyar ta kunyata ta agaban Wanda take so da kauna ? 


Aguje Laila da safiya suka bi su Huzna da niyar kamasu su jibgesu ,.aikuwa ganin hakan yasa yaran arcewa.aguje suka nufi kofar fita daga falon , 


Fitowar Huzna tayi daidai da k'arasowar Yaya Mu'azzam da sauri Huzna ta rungumeshi tana haki tace Yaya kaga anty safiya zata dakemu Kuma bamuyi Mata komai ba , d'ago kan da zaiyi sai ganin safiya da Laila yayi aguje sun nufo wajan Amma ganin Mu'azzam yasa sukaja birki suna kallon yaran suna huci,


Lalala mizan gani haka Kuma oh yanzu iskancin naku yakai har 'ya'yan arna kuke kawo Mana gida ! Uban waye ya kawo Mana wanna abar to wallahi ba'a gidan nan ba ,wato kyalenku da akayi shiyasa kuke abunda duk kukaga dama ko .....ke oya zoki fice Kuma karna k'ara ganin k'afarki anan gidan , wata irin kunya da takaicine ya rufe Laila da safiya a zuciye Laila ta nufi parking space ta dauki motar ta aguje ta Bata wuta ta fice daga gidan tafe take tana zubar da hawayen bakin ciki don ba'a ta'ba tozarta ta ba Kamar yau tabbas daga wanna saurayin har wannan yarinyar sai ta wulakanta rayuwarsu wannan alk'awarine ..............✍🏼