HUSNA KO HUZNA

Chapter 21

by @mamanyusuf

🅿️ -21




Aguje ta Danno hancin motar ta, awajan wani makeken get ta tsaya wawan birki ta ja sanna ta danna hon Kamar zata tashi wajan, aguje Mai gadi yazo jiki na rawa ya bude Mata k'ofa Yana budewa aguje ya matsa gefe don yasan halinta tsaf zata iya bi takanshi ta wuce Kuma ba abunda za'ayi , 


Ko parking din takasa tsayawa tayi da kyau haka ta fito ta nufi cikin gidan afusace ,


Hajiya Shema'u ce zaune a cikin wani k'ayataccen falo Wanda ya amsa sunashi karatun jarida takeyi kamar daga sama taji anbanko k'ofar falon anshigo , tun kamun ta d'ago da kanta ta saki wani murmushi don tasan wannan aikin Laila ne da alama yau wani ya janyo Mata rigimar Laila, 


Ko kallon Momcy Kamar yadda take kiranta ,Bata Yi ba tayi hanyar da zata sadata da part din ta , da sauri Momcy ta mik'e tsaye lokacin da tayi arba da kan Laila k'wal ba gashi afusace tace "aa shalele ubanwa ya cire maki gashin ne ? 

Cak Laila ta tsaya kamun tace bakowa Momcy ,

   Aa Laila nasan haka kawai bazaki cire ba tunda ko anan gidan kullum Yana kanki bare Kuma waje wanna ai cin zarafine don wallahi koni Dana haifeki banason ganinki a haka Kamar wata inyamura bare............ Momcy ta Kira sunan uwar cikin tsawa kamun ta fashe da kuka aguje ta haura sama, nan tabar Momcy na sallalami ganin yadda ta 'ballowa kanta ruwa , da sauri itama ta Mara Mata baya don ta lallasheta ,


___________________



Baki ta turo cike da jin haushi tace haba haba Yaya Mu'azzam k'awata ce fa kuma yanzu saboda Allah shikenan an kunyatani Taya zata..........ke Ni kika tsaya kina k'arewa magana , k'awarki din banza waye baisan rashin tarbiya irin na wannan yarinyar ba yarinyar da tayi k'aurin suna a garin nan Babu iskancin da batayi itace har Zaki zo Mana gida da ita to wallahi yazama na k'arshe kar nasake ganin ki da ita shashasha kawai , 

........wallahi k'arya ne kabar ganin komai zakayi ana kyaleka to wannan karon kam wallahi kasha karya daga yau ba ruwanka da yarana ehee akanmi zaka dameta Ina ruwanka da k'awancesnu to banason harkar bakin ciki ehe Laila Kuma ba wajanka take zuwa ba don haka kashafa Mata lafiya ,cewar Ammi cike da jin haushin abunda Yaya Mu'azzam yayiwa Laila gashi yau ko Dan alherin da take Mata kamun ta tafi yasa tayi asara,

   kallon Ammi yayi ranshi a 'bace don ya tsani ayi mashi fada agaban yara , cike da 'bacin Rai yace "wallahi duk Randa tak'ara kawo Mana wannan ballagazar daga ita har yarinyar sai na karya masu k'afa in Kuma tana ganin wasane ta gwada tagani daga haka ya juya cike da Izza ya bar falon ,


Aikuwa nan Ammi tace dawa Allah ya had'ani nan ta tayita faman fada da tsine-tsine sai fada take kamar zataci babu , yaran kuwa Babu Wanda ya kulata sai harkan gabansu suke sai Aliyu ne ma yake kallonta cike da takaici Yana mamakin irin Wannan k'in gaskiyan , Ina laifin Yayansu kullum burinshi su zama tsintsiya madaurinki Daya , a kullum yana kokari wajan bawa yaran tarbiya Amma iyayen na kallon abun amatsayin takura da 'yan ubanci Wanda Sam ba haka bane yanzu.gashinan daga Harira har Saudat sun lalata rayuwarsu a banza don duk yanada masaniyar abubuwan da suke aikatawa a boye yayi shirune kawai don yasan inhar yafad'i wannn maganar to karshenta shine abun bazaiwa kyau ba tunda Sam ba fahimta a tsakanin iyayen nasu , yanzu gashi akan kishin su na banza suna nema su tarwatsa rayuwar yaransu ,yanzu saboda Allah wace irin uwace zataso 'yar ta tayi k'awance da irinsu Laila yarinyar da iyayenta suka rike Mata kan maciji tana Wasa da bindi , tsaki yayi a ranshi Wanda baisan cewa a fili yayi ba sai jin yayi Ammi na cewa ," Ni kake yiwa tsaki Aliyu saboda wannnan yaron da ba kaunarku yake ba to wallahi Bari kaji in gayamaka zanyi mummuna Sa'ba maka akan haka tunda Kai bakasan ciyon kanka ba in Kai Mai kishin kanka ne yarinyar nan saboda Kai take zuwa gidan nan Amma shine za'a disgata a gabanka kana kallo baka dauki wani mataki ba ,

   😨"Akaina fa kikace Ammi , wata irin dariya yayi kamun yace lallai Ammi wato harda ke za'a hada baki a cuceni Allah na tuba Ni ko Mata sun Kare mizanyi da wannan yarinyar ya karasa maganar da dariya don shi zancan ma dariya ya bashi ,


Tunda aka fara wannan badakalar su Husna na gefe suna kallon kowa d'ai d'ai jin abunda Aliyu ke cewane yasa suma suka fara dariya Husna tace Kai Yaya Aliyu wannan ai kama take da maza hhhhhhh wai kaga kanta Allah na dauka ma namiji ne yayi shigar Mata ,aikuwa nan suka Kara fashewa da dariya wanda har Aliyu da Jamil Nasma Saida suka Dara 

   Kai zan faffalamaku Mari wallahi shegu Hatsabiban yara ai duk ku kuka janyo maza kubar nan kamun na tattakaku ,

  Tunzuro baki Huzna tayi tace to Ammi mi muka maki dafa Yaya Aliyu muke magana Kuma haka kawai zai yarda ya aure mai kama da maza bayan ko gashi batada , 

.........kwantar da hankalinki yar kanwata ai bama zan aureta ba Ni sai Mai irin gashin k'anwata Huzna zan aura yayi maganar Yana Jan jelar gashinta Wanda aka tufke Mata da k'aton ribom


Dammm gaban Yaya Mu'azzam ya buga jin abunda Aliyu ke cewa akan Huzna , dawowarshi kenan cikin falon zai dauki abincinshi , cak ya tsaya Yana sauraren Huzna da Aliyu yadda suke ta zuba shirme Yana biye Mata suna kwasar dariya , kasa karasowa yayi ya juya ya koma dakinshi 


Ammi kuwa tuni tabar waja ganin inta biye ta Aliyu sai ya sa amata dariya cikin kishiyoyi gara ta Bari ya sameta zata yi mashi wankin babbar atamfa,


Kwance yake yana tunanin wanna sabon al'amari shi abunda yake bashi tsoro ma baiwuce ace wai akan wannan yar jaririyar yake jin hakan ba  

  To wai kodai aljanun su ne suka sanyaka acikin wannan halin ? Wata zuciyar ta tambayeshi , afili yace Kai inaga fa hakane inba hakaba Ni yaushe ma na Isa wata soyayya , Kuma akan kankanuwar yarinya , gaskiya yakamata na Fara Shirin barin k'asar nan inaga da nabar k'asar ai doli zasu shafamun lafiya , daga haka ya tashi ya nufi sashen Inna don kwana biyu Bata jin dadin jikinta,


__________



Amma wallahi Salim bakada mutunci ,yanzu dama Ashe ba Sona kake ba adalilinka na samu matsala Amma tunda ka kirani na gayama ko sau Daya baka k'ara nemana ba , a tunaninka shikenan na tashi daga aiki ko ? To Allah yayi zan koma taka k'asa ,

    Oh baby ba haka bane wallahi na gaya maki Dad dinmu ne ba lafiya Ni nake jinyarshi kinga ai ba yadda za'ayi na d'aga na tafi wani wajan ko , Amma kiyi hkr hakan bazai sake faruwa ba kinji my sweet baby , yayi maganar Yana kashe Mata ido d'aya ,

   Hmmm salim kenan ai Ni tuni na dawo daga rakkiyarka wallahi in da gaske kake Babu waya ne ? KO ka manta har wayarka nayita Kira Amma baka d'agawa , Ni ba shashasha bace don haka karka Kara nemana 

Nagodema Allah da mayaudarar kalamanka basuyi tasiri akaina ba da tuni ka kaini ka baro ,don haka yanzu saidai abi wani sarkin Ni kaga tafiyata , daga haka ta juya ta yi shigewarta cikin gidan ,

Saudat Saudat don Allah tsaya kiji , 

  Ko waigowa batayi ba haka tana jinshi tayi tafiyarta ,don ta kudirta aranta sai ta wahalar dashi kamun sukoma Kamar da don tanason Salim sosai Sam bazata iya rabuwa dashi ba,


Oh wai mi yake damun wannan yarinyar ne , Ai wallahi k'arya kikeyi Saudat sai na cimma manufata akanki , daga haka yayi k'wafa sanna ya shige motar shi yabar wajan ,



______________


Assalamu alaikum tsohuwa Mai ran k'arfe , amsawa Inna tayi tace to yau antuna damu shekaranjiya har aikawa nemanka nayi Amma kayi biris wai kai kana fushi to yanzu ubanmi kazo kayimun , 

  Hhhhhh to yanzu dai ayi hakuri nazo biko ne , kedin ce Sam bakison ayiwa yaran nan magana bayan Kuma kema kinsan bajin magana suke ba Amma da an ta'basu sai ki hau yiwa mutum masifa , 

   "Eh naji dai ai kuwa bazan Bari ka dakarmun jikokina ba da wadan nan hannayen naka masu kama da katako ka halakamun su ,

Dariya yayi sosai kamun yace Amma tsohuwar nan kin gama Dani wallahi hannuwan nawa ne Kamar katako hhhhh salon ki kashemun kasuwa nakasa samun Mata ,

    A haf yo Kai kanada niyar auren ne tunda iyayen naka sun daure maka gindi har suna maganar turaka wata k'asar karatu , ai Kai kam bansan randa zakayi aure ba ,shiyasa Kanenka Aliyu yafika hankali gashinan har yanaso ya fito da matar aure , ka zauna nan har Kanenka yayi aure ya barka tunda haka kakeso


Dammmm_damm gabanshi yayi wani irin fad'uwa Wanda yarasa dalili , yak'e yayi yace ki kwantar da hankalinki Inna insha Allah kamun nayi wannan tafiyar zan fitar da matar da zan aura kinga ina dawowa sai maganar biki ,


Washe baki Inna tayi cikin matukar farinciki tace Kai Alhamdulillah Allah na gode maka , a ina kasamu matar ne .............✍🏼