HUSNA KO HUZNA

Chapter 23

by @mamanyusuf

🅿️ _23




*BAYAN SHEKARU TAKWAS*



Acikin wadan nan shekarun abubuwa da yawa sun faru masu dadi da marasa dadi , 

    Shekara Hudu kenan da akayi auren yaran gidan su ukku Anty Harira Anty Saudat da anty Safiya , bayan faruwar wasu abubu da dama , 


Bayan tafiyar Yaya Mu'azzam , bubuwa da yawa sunci gaba da faruwa a gidan inda Harira tak'ara gogewa sosai aka harkar karuwanci inda takai ta kawo har Bata tsoro ko shakkar wani yasani , lokaci 'Daya ta faso gari saboda yadda Talatu ta kaita wajan malaman tsibbo akayimata aikin samun farinjini tareda rufe bakin duk wani makusancinta saboda gudun kawo masu cikas , haka kuwa akayi Umma da Abee harma da sauran mutanen gidan sunaji suna gani Harira tazo tafi karfinsu Alhazawa kuwa har cikin gidan suke zuwa su dauketa Umma tayi kuka tayi danasanin haduwarta da Talatu yafi cikin kwando babban abun takaici shine Sam takasa tunkarar Talatu da maganar duk yadda taso taje gareta don daukar fansa saitaji ta kasa ga yarta Sam Bata Isa da itaba ,tafijin maganar Talatu akan tata , wannan damuwar ita ta haifarwa da Umma hawan jini yau lafiya gobe ciyo a haka rayuwa taci gaba da tafiya daga Abee har Abba sunkasa tank'wara Harira yayinda Abee yace zai koreta daga gidanshi , shi Sam bazai iya kallon wannan bakincikin ba da k'yar Abba ya shawo kanshi akan ya hakura suci gaba da Yi Mata addu'a Amma korarta bashine mafita ba , 


Ana haka Kuma sai ga Saudat ta tsiri shaye-shaye Wanda saurayinta Salim ya koya Mata dama can rikakken Dan kwaya ne , lokacin da Abee ya fahimci halinda Saudat take ciki ba k'aramun bakinciki yayi ba , Wanda har saida ya kwanta a asibiti don shima tuni jininshi ya hau Abba ne kullum ke tausarshi da nuna mashi muhimmanci yarda da kaddara don tabbas wannan kaddararsu ce in sukayi hakuri komai zai wuce , haka akayita fama da ita har kulleta akeyi Amma hakan baya Hana inta samu hanya ta 'balle taje wajan Salim ,Haka zai cikata da kayan maye sai tayi tatil sannan zata dawo gida ,

  Inda Allah ya taimaketa shine har yanzu takasa yarda da Salim duk yadda yaso ya keta mutuncita hakan ya faskara ,


Umma kuwa duk abun duniya ya taru yayi Mata yawa ga bakincikin Harira gana Saudat ga Kuma damuwar Abee Sam baya kulata , tunda suka gane halinda yaran nan suke ciki gaba Daya ya dauki laifin ya Dora Mata , ya dauke mata wuta Sam baya shiga shirginta sannan ya hana Mata girki acewarshi duk ita ta 'bata mashi tarbiyar yara , 


Ganin abun kullum yakici yaki cinyewa ne yasa Inna ta hura wuta aka lallai lallai sai ayiwa yaran aure tun basu janyo masu abun kunya ba , haka kuwa akayi don Umma ma sosai taji dadin wannan shawara ta Inna , nan aka umurcesu akan su fito da mazan da sukeso , nan take Saudat ta gabatar da Salim , yayinda Anty Harira ta nuna ita batada wani tsayayye , 


Lokacin da Abee yayi buncike akan Salim sai ya samu ashema Babanshi yaron shi ne Alhaji Saminu , Yana sarin Kaya sosai a wajan shi , Babu Bata lokaci Abee ya sameshi har gidanshi akan maganar yaransu , kuma bai boye mashi komai ba akan halin da yaran nasu suke ciki, da yake dama can yasan hakinda Salim ya jefa kanshi sai bai ja ba hasalima murna yayi tunda sunason junasu wata kila auren yazama shine sikar shiriyarsu baki Daya , nan take ya Kira Yayanshi Malam Sa'idu nan suka tsayar da lokacin biki wata biyu , haka suka rabu da Abee cike da farinciki da mutunta juna,


Lokacin da Abee yazo da maganar yadda sukayi da iyayen Salim ba k'aramun farinciki Abba da Inna harma da Umma sukayi ba , nan Inna ta dubi su Abba tace ku gayawa Harira da safiya su fito da samarinsu don suma nan da wata biyun zamu hadesu gabadaya mu aurar ba Kuma abunda zai Hana wannan auren ,inkuma har basuda manema to Ni zan nema masu ,daga haka ta tashi tabar wajan , 



Haukane kawai safiya batayi ba lokacin da sakon ya sameta hakama Ammi tashiga damuwa sosa don ita ba irin Wannan auren takeson yiwa yaranta ba tafison ayi bikinsu irin Wanda zai karade garin na Abuja harma da kewaye , to babbar matsalar shine har yanzu Yar tata Bata samu irin mijin da suke da muradi ba , duk samarin dake zuwa wajanta duk yan k'aryane kawai ba ko sisi , ana haka Akayi bikin wata k'awar Safiya din inda sukayi shagali sosai a bikin , alokacin safiya ta hadu da Daya daga cikin abokan ango Mai suna Ishaq , lokaci Daya suka k'ulla soyayya, ba k'aramun farinciki Safiya da mahaifiyarta sukayi ba ganin sun samu irin mijin da sukeso Kuma a lokacin Daya dace don sosai Ishaq ke masu 'barin kudi , Babu wani 'bata lokaci suka Kai maganar Ishaq wajan Abee , sosai Abee yayi farinciki nan ya umurceshi da ya aiko da magabatanshi a tsayar da magana indai a shirye yake , sosai Ishaq yayi murna dajin hakan don Sam bayason aja lokaci ba'ayi auren ba don kar karyarshi ta k'are🙊



Ishaq Sale d'ane ga malam sale da Inna Salamatu , iyayenshi yan kano ne Kuma acan suke zaune shine dai yake aiki a Abuja , Ishaq mugun dan k'arya ne Allah yayishi da shegen son abun duniya ,wannan yasa yasha alwashin Sam bazai auri Yar talakawa ba sai yar masu dashi ko shima zai yagi rabonshi , saurayine hadadde don badai kyau ba sannan kallo Daya zaka mashi ka dauka d'an wani shahararren Mai kudi ne saboda yanayin shigarshi dakuma yanayin jikinshi , ba k'aramun kashewa fatarshi kudi yake ba shiyasa zaka ganshi kullum kamar wani Mai rayuwa a k'asar waje sutura kuwa ba'acewa komai duk acan Dan kudin albashinshi yake karewa , gashi da shegen shishigi kullum yana manne da 'ya'yan masu kudi shiyasa in ka ganshi da wannan motar yau gobe zaka ganshi da wadda ta fita , wannan yasa Wanda baisani.ba Kai tsaye zai mashi kallon wani DON , Wanda hakance ta faru da safiya don a tunaninta tasamu miji Mai kudi na nunwa sa'a 


Ishaq kuwa sai murna da farinciki yake ya komarshi ta kama babban kifi don yasan doli zai yagi rabonshi ganin uban safiya ya Tara Kaya shiyasa shima yakeson anyi auren da wuri tun kamun su ganoshi don yakula Sam bashi takeso ba abun hannunshi takeso,



Wuta sosai Abee ya budewa Anty Harira akan takawo Wanda takeso don aure Sam Babu fashi Amma kullum maganarta Daya ce batada Wanda takeso ganin abun nata iskanci ne yasa ya bayar da ita ga Abokinshi Alhaji Bashir , aikuwa nan ta tubure akan bazata auri Alhaji Bashir ba yayinda Abee yayi biris da ita sai shirye-shiryen auren akeyi , 



A wata safiyar Assabar aka daura auren *Harira Hussain Abubakar* da *Alhaji Bashir sani* *Safiya Hussain Abubakar da Ishaq sale* *Saudat Hussain Abubakar da Salim Saminu*


Anyi shagali sosai Kamar ba gobe kamun a Kai kowace gidanta , yayinda Abee ya mallaka masu motoci na gani na fada duk don dai yasamu su zauna a dakunansu , hakama Salim da Ishaq motoci masu kyau da tsada ya siya masu , aikuwa abun nema ya samu nan suka shiga murna ,



Tunda akaje kai Safiya ido ya Raina fata tuni yan uwan Ammi suka sha jinin jikinsu sai mamakin gidan sukeyi , gidane na haya Mai part part sama da goma sai dai kallo Daya zakama gidan kasan cewa gidan gidan hayane duba da yanayin mutanen gidan , gasunan tsaye wajan fanfon dake haraban gidan sunyi layi reras suna diban ruwa sai gefe Daya wasu yan matane ke fada sai zage-zage suke ba Wanda ya kulasu , yayinda wasu daga cikin mutanen gidan suka rinka binsu da kallo kasancewar da yamma aka tafi Kai Amaren 

Jiki a sanyaye Haka suka rinka bin Dan jagoran Daya kawosu suna tinanin kodai yayi 'batan Kai ne, basu Kara tsinkewa ba Saida sukaga sunshiga part din Amarya , sukaga tsadaddun kayan gadonta da duk wani Abu da yake mallakinta , nan suka Kara tabbatar da lallai gidan ne tunda ga kayanta , ko zama basuyi ba suka Kira Ammi suna kora Mata abunda ya faru, nan take Ammi ta haukace sai faman fada da zage-zage take akan anci amanarta an yaudareta Kuma wallai sai an warwaren auren nan don ba Wanda ya Isa ya kunyatata acikin kishiyoyi , yayinda Amarya safiya tafad'i a wajan ta fashe da wani irin kuka Mai tattare da bakinciki ,da sauri wata Yar uwar Ammi maisuna Mariya ta Sanya Hannu tarufe Mata baki tace ke miye Haka Zaki Tara Mana mutane..........✍🏼