ABIN DA YA BAKA TSORO

8️⃣

by @maidambu41

8️⃣

PAID BOOK

Har kwanan gobe baya jin yana da wani aboki sama da Lawali, kuma dan uwa na Amana, yardan da yayi kuma ya bashi amanar shi.

  Shi yasa ya rufe babin dangin sa, baki daya yana rayuwar shi cikin farin ciki.

Yana tsaye har Lawali ya bar gidan, sannan ya koma cikin gidan, yana jin Hajiya Azumi tana zagin yar aikin ta.

"Munafika waye zai shiga ɗakina bayan kece kika shiga? Na gaji da dauke dauken da kike min"

Kallon Quraish yayi yaga ko a jikin shi. Sannan ya sauke idanun shi akan Hajiya Azumi.

"Ba ita ta dauki kudin ki ba. Muje na miki magana"

"Zata bar gidan nan dole"

"Ba zata bari ba, domin ni nake biyan su, idan kuma zaki cika min kai da surutu ne kiyi zaman ki" ya wuce abin shi, tana mugun son Sadi. Duk da bata samu wani abu daga gare shi na soyayya ba, sai dai har abada ba zata iya cire Sadi a ranta ba.

Tana shiga dakin ta same shi zaune yana duba ayyukansa, zama tai tana cewa.

"Amma kuma"

"Quraish ne ya dauki kudin ki" da mamaki take kallon shi.

"Duk rashin kaunar da kake nuna mana bai isa ba, sai ka daurawa danka sharri"

"Hmm" ya fada yana kallon takardun da yake gaban shi.

"Akan me zan mishi sharri? Bayan ni na haife shi. Gaskiya na gaya miki ko yana da wani Uban ne bayan Ni?"

Sunkuyar da kai tayi bata ce kome ba.

"Bata dauki kudin ki ba, shi ya dauka dan haka kar na kuma jin wani hayaniya" daga haka ya mike ya nufi ban daki. Ruwa ya tarawa kan shi sannan ya shiga cikin ruwan ya kwanta a ciki ko jallabiyar jikin shi bai cire ba, wani irin kunci yake ji mara iyaka, baki daya ya a tsani kan shi da kome.

 Anya ba hakkin mahaukaciyar nan ba ne ke bibiyar shi? Wani irin damuwa yaji a ran shi, kafin ya ji kwalla ya cika mashi idanu. Bukatar shi ta biya ya shahara. Burin shi ya cika ya daukaka ya zama babban mutum wanda har ana tunanin zaman shi Minista, amma bin takaici ne har yau ya kasa mantawa da Yarinyar ya gaza mantawa da ita. Ya gaza daidaita nutsuwar shi da matar auren shi gani yake kamar bata kai wancan din ba, gani yake kamar bata kama kafar wancan yarinyar ba,.bai tab'a kuskuren da ya dame shi ba, kusan shekaru goma sha biyu amma har yau kome sabo yake a ran shi kome dawowa yake a duniyar shi bai sa nutsuwa bai da kwanciyar hankali.

  Yaran shi da ya haifa basu da maraba da yaran da suke yawo titi da kwaroro. Domin yayi imani da Allah bayan hakkin mahaukaciyar nan babu wani abun da yake damun shi, sai na Mahaukaciyar nan.

Sadi ya manta da hakkin Uwar shi ya manta da cewa itama tana da hakkin akan shi, ya samu duk abinda yake bukata amma ya manta da uwar shi da dangin shi. Ya rike Lawali kamar shi ya haife shi.

   A lokacin da Azumi ta fita hararan me aikin tayi duk da ba Yarinya bace, amma kuma tayi girman da bai dace a ci zarafin ta ba,(kalubale gare ku masu ɗaukar yan aiki ayi hakuri fa ba son ran su suke zuwa aikatau ba, sannan kai ma ba fin su kayi da har Allah ya baka ya hana su don Allah a daina wulakanta su) 

    Kallon Sulaimah tayi tana faɗin.

"Kince zaki gidan su Ummi ba zaki bane?"

"Zan tafi mana, ni ba zan kwashe yaran nan bane ni daya na zan tafi"

"Toh shi kenan ki je, kicewa Hajiya Ina gaishe ta"

"Zata ji" ta nufi dakin ta, ta sauya kayan ta, sannan ya fito tana rungume da wata ƙatuwar Teddy bear pink. Ta fita abin ta yaran ne sun taso babu fada babu tsangwama babu me hana su babu me hana su. Yan gata ne na fitar hankali.

     Daga nan gidan su, Drive ne ya kaita har gidan su Kawarta, yara ƙanana ne fa amma a take suka sauya kaya, sannan suka nufi gidan su wani abokin su na makaranta, shi ma nan basu tsaya ba, fita suka yi suka bar unguwar baki ɗaya, inda suka nufi wurin party, haka suka yi ta shiga cikin wurin. Babu Wanda yasan da cewa yaran badakalar su suke.

    Tunda suka shiga suka samu yara maza da mata, sai wasa suke Yaron da ya kawo su, ya ja hannun Ummi suka shige Sulaimah tana kallon su, daga bayan ta,.aka tab'a ta juyawa tayi tana kallon shi. Yaro ne amma ya fita a shekaru. Juyawa tayi taki kula shi, bai wuce ba ya tsaya ya kuma tab'a ta. Nan ta ce mishi.

"Meye matsalar ka?"

"Muje mana" ciki suka wuce inda kowa yake ta sha'anin su. Party na wani yaron babban mutum ne aka shirya mishi, dan Birthday party din shi, inda ya gayyaci abokan shi na makaranta suma kuma suka gayyato abokan su na wasu makarantar, idan ka gan su daga kan Sha biyu ne zuwa sha biyar, yara ne da idan ka saka musu hannu a baki ba mamaki ba zasu ciza ba, amma abin mamaki shine yadda suke gudanar da sha'ani kamar sun jima da gogewa, har takai ta kawo suke ana ciro yan yaran nan matan suna nuna irin nasu rashin kunyar. Allah ka shirya mana zuri'a.

 ★

Baki daya idan ka cire tsoron da ta dangafawa ranta, tana da kokari da mugun hakuri, ga zafin nama wurin aiki idan har tana aiki kamar ba yarinya ba. Kallon ta Baaba tayi tana faɗin.

"Yanzu dai sai da kika yi wankin nan a cikin wannan muku-mukun sanyin?"

"Eh mana Baaba idan na bar wankin waye zai min? Ko kullum sai kin tuna min"

"Wannan baki naki ya iya zaro magana" Baaba ta fada tana kallon ta. Ganin ko kadan bata dauko kalar fatar uwar ta ba, abin yake bata mamaki Uwar da Fara ce jar tana wani irin kore kore, amma ita wannan baka ce me sheki, d'ago kai tayi ta same Baaba tana kallon ta.

"Baaba kallona kike?"

"A'a hararanki nake"

Dariya tayi fararren hakoran ta, suka bayyana.

"Allah ko?"

"Ke bana son ja'iranci" Baaba ta fada tana nufar kitchen.

  Haka rayuwar take tafiya a makarantar ta sami sauki domin dai babu Nadrah sai Widad, Jalilah ma tunda aka dakatar da ita Baban ta ya kamata ya mata duka ya kuma yi alkawarin sai ya dakatar da karatun ya aurar da ita da sai ga Meriama har da walwala, gwanin ban sha'awa. Duk da ajin su ba daya da Widad ba, amma suna dan d'asawa sama sama ba kamar sauran yayun ta ba.

   Haka suka shiga aji uku, suka maida hankali sosai,. musamman ita da tun tana aji biyu ake hasashen bata matsayin head girl, saboda kokarinta nutsuwar ta, da rashin son fada da har zuwa lokacin ba a tab'a samun ta da laifi ba. Wannan dalilin yasa baki daya take samun cigaba ta kowani fuska. A hadda kuwa malam da kan shi ya hanata sauka. Yana yawan ce mata a duk lokacin da ta kasance cikin kadaici Alqur'anin da yake yawan maimaita shi, shine zai zame mata abokin tarayya da hira. Amma daga ita har Baaba haushi Malam suke ji. Duk lokacin da za ayi sauka ana sako sunan ta zai tura Rabe ya ce a dakatar da ita, haka yasa baki daya take jin haushin malam. Litattafan da take karatu a wurin shi ta hada wasu, kama daga fiqhu, hadisi, Tauhidi. Baki daya ta hada ita kanta malamar wasu dalibai ne. Amma Malama sai da ya mata gangancin kin sauka.

     Shi yasa ya ce mishi.

"Malam don Allah ka bar ni bayi sauka?"

Dariya yayi sannan ya ce mata.

"Shekarun ki nawa?" Juyawa tayi ta kalli Baaba ta ce mata.

"Baaba don Allah shekaru na nawa?"

"Sha hudu"

"Yawwa malam sha hudu" shiru yayi har da rike habb'ar shi.

"Mai gado dama meramu ta girma haka ne?"

"Eh malam"

"Toh lallai ayi mata aure kawai. Sai ta sauke a dakin mijin ta"

"Wallahi ma fasa, Ni fa aikin asibiti zan yi"

"Aikin asibiti??" Suka tambaye,"eh Baaba, zan yi aikin asibiti ne sabida Mamma, ina son ta samu lafiya ne a daina kirana yar Mahaukaciya. Malam meye ma'anar shegiya mara uba?" Kallon ta Baaba tayi tana faɗin.

"Waye ya fada miki haka?"

"Ai ba yau aka fara gaya min ba, kuma ba yanzu ba. Insha Allah sai na nimawa Mamma maganin ta daina hauka."

Hawaye ne ya zubowa Malam domin bai tab'a kawowa zata tambayi su wannan maganar ba sai yau.

Goge kwalla yayi sannan ya ce mata.

"Tambayar ki tana da amsa amma dukkan mu nan babu me baki ita, idan kin kara hankali zaki fahimci abinda nake nufi, batun aikin asibiti Insha Allah zaki yi kin ji"

Gyada kai tayi tana kallon shi.

"Malam toh yaushe zan yi saukar?"

"Kiyi hakuri nan da shekara biyu zaki yi kin ji kan lokacin Alqur'ani ya zama jinin jikin ki yadda duk ayar da aka dauka zaki kai har karshen shi ji dage kiyi karatu"

"Toh malam nagode " hakurinta da juriyar ta, gwanin ban sha'awa ne, domin kafin tayi kuka zai dauki tsawon lokaci, sai dai tsoron bala'i da take da shi wanda kusan dabi'ar ta ce.

  Haka ta dage karatu ba dare ba rana, musamman haddar Alqur'ani da ya zame mata kamar ruwan ahan ta, domin so take ta cikawa malam burin shi, kuma Alhamdulilillahi domin kwaliya yana biyan kudin sabulu, sosai take karatun shi kan shi malam yasha dauko aya takai karshe . Tunda ya fara gwadata, da kan shi ya fara tunanin tayi saukar yadda zata ji dadin karatun.

  Dake yarinya ce me naci da kulafuci, baki daya bata da lokacin kanta.

    Mafi girman kaddarar da tazo ta gifta lokacin da take tsaka da karatu, shine rasuwar Malam, ranar da ta gama zana jarabawar karshe na kammala aji ukun sakandare. Suka dawo gida. Tun daga nesa ta hango kofar gidan su a cike da al'ummar musulmi, jikin ta ya kama rawa. Har zuwa kofar gidan motar da yake dauko su da Widad ya sauke ta, a hankali ta sauka a motar, ya nufi cikin gidan. Lokacin da Rabe ya fito daga dakin Malam aka kama mishi makara za a saka malam a cikin shi. Wani irin tsoro ne ya kamata, ta damke jakar makarantar ta, tana kallon ikon Allah. A haka suka saka malam a cikin makaran suka kira Baaba. Wacce take kuka sosai. Haka yayi mishi addu'oi. Riko hannun ta Rabe yayi sannan ya ce mata.

"Ki mishi addu'a, ya tafi yana saka miki albarka. Ya roka miki Allah ya albarkaci rayuwar ki, ya roki Allah ya sanya kukan ki ya zame miki dariya har darul Islam, ki mishi addu'a ya tafi yana fatan rayuwar ki tayi kyau sama da ta kowa." Zubewa tayi akan gwiwar ta. Ta shaku da malam sama da yadda ta shaku da tayi da uwar ta, ko Baaba bata san damuwar ta kamar yadda malam ya sani ba, shine abokin hiranta.

Wani irin kuka ne ya kwace mata lokacin da ta bude baki zata mishi addu'a. Kuka take tana kara rike makaran shi. Haka aka dauke shi bata iya mishi addu'a ba, sai da aka kamata aka kaita daki domin bin su take itama. Abin gwanin ban tausayi. Haka Baaba ta rike hannun ta gam.

"Ki mishi addu'a, shi yake bukata."

"Baaba waye zai koya min karatu....

*TOP-NOTCH WRITERS*

 

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*

 _Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_

  _Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_

  _Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_

 

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_

  _Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

   _Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

   

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_

  _Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_

   _hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_

  _Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_

_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_

  _Don Allah fa_

  _Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_

_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_

_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._

_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_

  _Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_

 _Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._

_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350₦

_Guda Biyu_700₦

_Guda Uku_ 1k

_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_

_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_

_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_

**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*

_Welcome ta Top-notch Team_