ABIN DA YA BAKA TSORO

7️⃣

by @maidambu41

ABIN DA YA BAKA TSORO...🦋

       (Arrow Of Destiny)

بسم الله الرحمن الرحيم

*EWF*

7️⃣


Bata fahimci abinda yake nufi ba, amma kuma tana jin kamar wani babban al'amari ne shi din a tare shi. Dan haka kanta a sunkuye ta damke hannun ta sakamakon rikon da yayiwa hannun ta.

"Kuka kike? Bakin san na tafi ne? Na zauna a tare da ke? Kiyi hakuri kiyi karatu sosai zan dawo Insha Allah, zan dawo kin ji ki nutsu ban da kula maza" Duk da ya jera mata tambayoyin ne lokaci guda tare da manyan jan hankali, dan haka ta d'ago kai tana faɗin.

" Allah ya baka sa'ar tafi"

 Daga haka ta janye hannun ta daga na shi ya tafi cikin gida ta bar shi a durkushe, yana jin kamar zuciyar shi zata buga.


 Wannan shine rabuwar shi da ita, itama kuma ta saka a ranta zata yi karatu Tukuru.


   Sai dai kash ko wata daya ba a rufa ba, ta fara fuskartar matsala daga su Nadrah imma su tafi su bar ta, ko kuma idan suka tsaya su mata duka a cikin motar, wannan yasa mata wani irin rauni a ta fuskar karatun. Baki daya ta zama mara mai da hankali, ga tsangwama da kyara, duk abinda take basu gani dan haka ta fara ja baya da karatun dan kokarin da take da shi ya fara shiririncewa, sai da Rabe yayi da gaske inda ya kai karan Nadrah har cikin gidan Allah ya taimaka ya samu mazan gidan sun zo daga Mali har da Wan uban Nadra din, dalilin da ysa yayi magana shine marin Meriama da tayi a saman idanun ta, karshe sai dawo da Meriama din gida aka yi dan idanun sun yi luhu-luhu, lokacin da suka ga abin da tayi kuma da aka tambaya bata iya musantawa ba, ya ce musu.

"Gaskiya tana cin zarafin Meriama, mun yi kokarin dannewa ne dan Aliyu bama son alakar da ke tsakanin mu na zumunci ya raunanna, don Allah ku mata magana ba a san inda rai da karan kwana yake ba, idan har aka yiwa tubkar hanci itama zata huta"


 "Kayi hakuri don Allah, ka bawa Baaba me kosai hakuri ita da Malam insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba." Inji Alhaji Hamza Mansa. Ya Ciro kudi xai bawa Rabe ya ce mishi.

"A'a ban zo dan a bamu wani abu ba, nazo ne dokaciya ka duba al'amarin dai itama ba haka ta zabawa kan ta ba, ƙaddara ce babu wanda ya fi karfin shi." Daga haka ya rike hannun ta suka fita.


  Bayan fitar su Hajiya Asma'u ta cewa yayan Baban Nadrah.

"Ina ga ku koma da ita wurin iyayen ta, wallahi ba zan iya masifar Nadrah ba, tasan yau da Sayyid yana kasar wallahi sai na lahira tafi ta jin dadi masifar ta ya ishe ni, haka kwanaki suka mata cin mutunci na rasa yadda zan yi kuma dan zalinci ba ita daya ba dukkan su Uku suke wannan abin ku tafi da su ma Nagode"


 "A'a ba zai ayi haka ba, a bar Widad sauran mu tafi da su." Inji Alhaji Musa, kuka suke suna rokon a bar su amma babu wanda ya kula su, har suka koma dakin su. Ganin haka yasa Widad ta yi alkawarin babu ruwan ta da Meriama. Domin a can rayuwar su a takure suke, sannan basu da wani yancin walwala domin daga makaranta sai makaranta, anan kuwa suna fita lokacin da ransu yayi musu . Kuma a nan ne zasu yi karatu kafin ayi musu aure amma a can fa, sai dai suna gama secondary school za a musu aure kowacce ta karasa a dakin mijin ta.


  Dan haka ta rufawa kanta asiri, bata kuma sakawa a ranta zata yiwa Meriama rashin mutunci ba, dama ganin idanun Nadrah ne.


 ★

Idan aka ce cigaba na rayuwa toh tabbas Sadi ya samu, domin a cikin abin da bai fi Shekara goma sha biyu ba, siyasar shi ta kara girma da yaɗuwa har garin su na Damagaram, sai dai a duk lokacin da ya zauna yana yawan shiga tashin hankali akan abinda suka aikata, idan abin ya fado mishi yana iya rufe kofar shi ko ya bar kasar baki daya, domin har ga Allah yana cikin wani irin yanayin da bai san iyakar shi ba, abu daya ya sani Lawali duk abinda yake bukata ko yake so shine mishi jagaba.


 A yanzu haka matar shi Alhaji Azumi, Allah ya albarkace su da Yara uku. Yar shi sunan ta Sulaimah bata jin magana. Amma babu yadda ya iya domin duk abin da tayi tana samun goyon bayan Lawali haka kuma me bin ta Quraish, shima sai haka sai Yar karamar yarinya Fahdeelah, ba zai iya manta alkhairin Lawali ba. Domin kusan shine a tare da iyalin shi. Kusan sun fi sabawa da Lawali sama da shi da ya haife su.


   Yau juma'a ya dawo a gajiye, dan haka yana shigowa ya sami Hajiya Azumi a falo ita da Sulaimah. Sai Fahdeelah tana dakin Uwar tana wasa shi kuma Quraish baya gidan.

"Sannu da dawowa Alhaji" ta taso ta amshi jakar shi, yana kallon Sulaimah ko inda yake yake bata kalla ba. Wani irin abu ya ji a ran shi. Kawai sai ya wuce.

Tura baki tayi tana hararan shi, duk da shi ya haife ta, amma bata son ganin shi a rayuwar ta. Domin sun shi Uba ne, amma bata ga abinda yake mata na uban ba. Tsaki tayi tana saka earpies a kunnen ta, tana zaune a wurin Quraish ya shigo sannan ya wuce dakin Maman su, tana zaune taga ha fito dauke da abu a cikin leda.

"Ina zaka da shi?"

"Gidan Ubanki tunda ba naki na dauka ba"

    Tabe baki tayi bata kuma kallon shi ba.

A can dakin Sadi, tunda ya shiga gaba zauna a bakin gado yake cike da damuwa.

"Alhaji ga ruwan wanka na kai maka" d'ago kai yayi sannan ya zuba mata ido, kafin ya juyar da kan shi.

"Me yasa Sulaimah bata son gani na ko min magana?"


  Shiru tayi kafin ta ce mishi.

"Kasan akwai yarinyar a tare da ita har yau bata san ciwon kan ta ba, don haka dole a bata lokaci.". Gyada kai yayi sannan ya mike ya nufi ban daki, ajiyar zuciya ta sauke ta ciro mishi kayan shi kafin ta fita, kitchen ta nufa ta bada umarnin a kawo kayan Abincin shi.


    Tana dawowa falon, ta sami Sulaimah.

"Kin gaida Abbanku kuwa?" Tab'e baki tayi sannan ta ce mata.

"Sau nawa yana mana alkawarin yana fasawa ko wancan lokacin alkawarin zuwa Dubai yayi mana da paris akan me zan wani addabi rayuwata dan ya dawo shi ba watsar da mu yayi ba ya tafi na shi harkan gaban ba" ta fada tana barin falon. Bata wuce shekaru goma sha biyu ba,.amma yadda take abu zaka ɗauka irin wacce ta girman nan ne, duk abinda take fada a kunnen shi yana jin ta amma bai san yadda zai iya tankwara gidan shi ba, dan haka ya watsar da abin da take fada ya zauna ya fara cin abincin.


  Yana gamawa ya tashi ya koma dakin shi sannan ya kira Lawali a wayar telephone. Sun jima suna magana. Can zuwa yamma sai ga Lawali da uban kaya niki niki, ya kawowa Yaran, cikin murna suka tare shi. Sai da ya gama ganawa da yaran kowannen su ya fada mishi abin da yake bukata, sannan ya nufi falon Sadi da yake zaune ya turawa tv idanu.

"Yallabai da fatan dai ba wani abu bane ya taso" lumshe idanu shi yayi sannan ya sauke ajiyar zuciya.

"Jiya Shugaba ya kira ni akan ya tura suna na cikin mutanen nan da za a turawa prieminister. Gashi ina son zuwa Frence." D'ago kai yayi da sauri yana kallon Sadi.

"Toh amma ai ba laifi bane kawai abin da na sani, shi ne yaran nan suna bukatar fita dasu don Allah ka saka su a cikin tafiyar ka"


  "Eh toh ina ga ko zaka raka su ne, daga Frence zan tawo nan Dubai din" shiru yayi yana kallon shi. Domin yaga rashin amincewar shi a fuskar shi.

"Don Allah Lawali ka taimaka min"

"Shi kenan Allah ya kai mu." Daga nan suka shiga tattaunawa akan abin da ya shafi siyasa anan ne zaka ji muryan Sadi kamar me, amma batun iyalin shi baki daya ya rasa su domin bai da lokacin su, babu shakuwa irin ta D'a da uba sai dai a gefe guda yana sauke duk wani abin da ya rataya akan shi.


  Haka suka gama tattaunawa Ya rako Lawali waje, ya haɗa da Quraish, ya mikawa wani katon saurayi abu a leda suna ganin su Alhaji Sadi suka runtuma a guje, juyawa yayi ya kalli Mahaifin su ya bata rai sannan ya sa kai zai wuce.

"Quraish meye hadin ka da wancan mutumin?" Lawali ya tambaye shi.

"Kawu Lawali babu kawai dai ba fito ba shi kyauta ne dan naji yana Bara."

"Kar na kuma ganin shi, kana ji na!"

"Naji" ya fada ya wuce.

"Lawali Nagode sosai yadda ka tsaya min akan iyalina. Wallahi bani da ikon musu koda tsawa ne "


"A'a ba sai kayi musu fada ba, ka gaya min Insha Allah zan musu fada yaro dan lallabe ne idan aka ce za a musu fada da ƙarfi abin ba zai yi dadi ba, kar ka damu da yadda suke rashin shakuwa ne ka samu lokaci ka zauna da su. Zasu fahimce ka domin kowani Yaro yana bukatar kulawa da tattali, kai kuma gaskiya ja rungume aikin ka da siyasanka niman duniya baka da lokacin kowa sai na kan ka,.hatta ita me dakin ka baka da lokacin ta,.kar ka manta rayuwa dole sai ta kula da iyalin ka idan baka kula da su ba, ko mutuwa kai wuyar ta ayi addu'oi bakwai ne sun manta da kai, don Allah ka kula da kyau yaran nan bamu da sama da su."


"Lawali kayi gaskiya insha Allah zan ware lokaci guda na basu domin kaina da kuma su bana jin dadin rashin kusancen mu, amma insha Allah idan na gama abin da nake zan dawo ga iyalina "

"Masha ALLAH, yanzu dai ba shi ba. Kana nufin zaka bar garin Dusso ne zaka koma Nieyme da zama kenan idan aka baka ministan?"

"Insha Allah haka nake fata" inji Alhaji Sadi.

"Muna nan muna tayaka murna , Ubangiji ya baka nasara da sa'a Allah ya tayaka riko "

"Kai Lawali tun ba a bani ba ma ka jira a bani sai ka taya ni murna ko?"

"Nasan Insha Allah zaka samu ne Gara nayi murna ta tun yanzu kafin kayi wuyar gani"


"Allah ya shirya ka, waye ya gaya maka zan manta sa kai har abada ba, kai kafi min yan uwana, domin kai ka zauna da ni bayan na rasa kowa nawa. Don Allah kar ka ci amana na"

*TOP-NOTCH WRITERS*


  

*TALLA! TALLA!! TALLA!!!*


 _Kasancewar bikin kanwata ake ta biyar me suna Zahrah sai kaiwa da komawa nake Hankalina yana kan Babbar kawata Farisah tsaki nayi na wuce can na kuma dawowa na zuba mata ido cikin takaici mahaukaciya ta zare_


  _Malama kin zo biki ne ko kin zo karanta chat kin yi shiru kin b'ata shiru_


  _Wani banzan dariya ta saka min tana d'age min gira_

  

_Hmmm Bestie wai ke ko irin karance-karancen social media baki yi irin su Wattpad,Okada, Arewabooks baki yi?_ 

  _Sake baki nayi ina kallon ta. When rabona da Hausa Novel Allah na tuba tun Iyatuh Abba tana karanta a gidan Radion B.R.C tabe baki nayi na ce mata_

   _Ke rabani da kayan wahala rabona da Hausa novel tun zamanin Iyatuh Abba_

   

_Innalillahi!, Tace tana kallona kafin ta ce. Jasmin yanzun don Allah duk cigaban da aka samu baki san da shi ba? Lallai kin wuce yadda nake tunani kin gani wuri na karanta book din da nake fama da shi_


  _Cikin mamaki na wuce na dawo na zauna kusa da ita nace mata don Allah daura ni a hanya ina ganin kowa na karance-karancen amma ban dani_


   _hmmm lallai zata fashe... Toh saurara da kyau nan da kike gani na karanta books nake na marubuta daban daban amma idan ana dara ana fidda uwa... Kin ga last na ga The Governor's Wife, one to three, after ma gama na karanta Zaytoonah.... Abun dad'i sai na cikaro da Affiyah da Unaisah_


  _Allah Aunty Rukayyah kina karanta online hausa novel ne? Lallai toh ai yanzu ina karanta Zayn Malik Jiya na gama karanta Zanen ƙaddarata,_ 

_Kanwata Amaryan da muke bikin ta ta saka mana baki a she ba banza yarinyar nan ta nace daga gama sakandare tace a direta gidan miji_


_Amarya Zahra toh kuwa nima Zayn Malik nake karantawa musamman rigimar Hajiya da Uncle Bashir, da Zayn da Abul amma kin san zata fashe on October?_


  _Don Allah fa_

  _Hmmmm gamayyar marubutan nan sun hade wuri guda za ta fashe sun fitar da sunan Team din su_


_Aunty Don Allah ya sunan Team din?_

_TOP-NOTCH.... Za ta fashe a books uku Sahla A Paris, Bani Da Laifi Abin da Ya baka Tsoro_


_Wow da gaske?_

_Zan Miki karya ne?_

_Ina da number Mai_Dambu bari na duba nasan zata daura a status...._


_juyawa tayi ta kalle ni ina bin su sa kallo ke kuma ko garzaya Wattpad ko duba Ribar Uwa, Mutum Mugu, Wadata, Uwargidan Bahaushe, Bororoji,Kallabi does story sun tab'a ni_


  _Kut nace sannan na cigaba da cewa don Allah ga Iphone dina daura Wattpad ke kome ma daura min nima ta fashe dani_


 _Tabbas za ta fashe amma fashewar alkhairi....._


_Books din da zasu zo kamar haka_

1- Sahla A Paris

2-Bani Da Laifi

3-Abin Da Ya baka tsoro.

Dukkan su Uku 1k

_Guda daya_ 350

_Guda Biyu_700

_Guda Uku_ 1k


_Zaku iya payment ta to 3091721807 A'isha kwalam Hassan first Bank of Nigeria_


_and send evidence to does number_

*****

Or

**** or ****

_Dukka zaku iya tura shaidar biya_


_Ga masu turo katin MTN zasu iya turawa Zahrahn Addah Ramlat da kuma Yan Nijar zasu turawa Nana A'ishah_


**** a tuntube Zahrah Addah Ramlat, Yan Niger su tuntubi Nana A'ichah

*+22784506476*


_Welcome ta Top-notch Team_