Chapter 7
WANNE HALI HAFSY KE CIKI?
Hafsat bayan ta kammala karatun Alkur’ani ne, sai ta ji ta samu natsuwa duk damuwa ya gushe ta ce, “Tabbas Allah ya yi gaskiya da ya ce da ambatonsa ne zuciya ke samun natsuwa ya Allah ka sanya mu cikin masu ambatonka dare da rana.”
WANNE HALI MUS'AB KE CIKI?
Mus'ab yana ƙoƙarin koma wa gidansa ne Abbansa ya yi masa ƙiran gaggawa da ya je ya same shi, bisa dalilin haka ya nufi wurin Abbansa.
WACCE WAINAR SAFINAT KE TOYAWA A GIDAN MAHAIFIYARTA.
Safinat, sallama ta yi aka amsa mata, Hajiya Laure mahaifiyar Finat ta fito daga cikin ɗaki, tana cewa, "To su Safinat yaushe a gari in ji maki baƙo? Zuwa ba sanarwa."
Ta ce, "Ke dai bari Umma, haka kawai na ji ina marmarin ganin uwar asali.”
Safinat ta ajeye ledojin da ke maƙare da kaya ta yi miƙa tana cewa, “Wash Allah!” Ta nemi waje ta zauna.
Hajiya Laure ta jawo leda ta fara buɗewa tana cewa, "Wannan duk tsaraba ce, yayan naki ya ce ki kawo mini?”
Safinat ta turo baki ta ce, "Lallai Umma Yaya ne zai yi wa mutum irin wannan shopping (sayayyar) ya ce na kawo miki, idan gidan su matarsa ce ko kantin Kwari ne zan yarda zai iya kai mu su amma ban da ke da iyayensa."
Hajiya Laure ta ce, "Tabbas haka ne mantawa na yi ashe mu sai a ƙarshen wata muke ga abun hannunsa yanzu kuma tsakiyar wata ake, to wa ya yi miki wannan shopping ɗin?"
"Wani saurayi na ne wallahi. Umma kin gan shi kuwa young ga shi baya kyashi wajen kashe mini Naira."
Hajiya Laure ta gyara zama, “Allah 'ya ta. Amma dai kin san duk samartakarsa ba shi muke muradi a aure ba. Don na ji kina yaba shi.”
Murmushi ta yi, “Dama mana Umma, su na riƙe su ne a matsayin masu biya mini buƙatu, kin san yaya ba a iya ɓanɓaransa a irin haka.”
“Wannan gaskiya ne 'yata. Mus’ab ki riƙe shi a matsayin mijin aure, duk mazan duniya kuma da za su yi miki kawanya su ce suna son ki, idan har za ki riba ce su ban yi miki katanga da su ba, duk ki so su, don mace allurar cikin ruwa ne, amma Mus’ab ya riga ya ɗauka ta ɓangaren aure.”
Ta buɗe leda tana kallon abubuwan da ke cikin, tana cewa, "Masha'a Allah, ina ma a ce wannan kuɗi ne aka maƙara ba kayan tanɗe-tanɗe ba."
Safinat ta kyalkyale da dariya. "Ke dai Umma da kuɗi."
"Safinat kenan ba za ki gane ba, ai kuɗi shi ne rayuwa, in kana da shi kai ne mutum. Me ya sa muka ɗora ɗamarar ki mallaki Mus’ab?”
Ta kyalkyale da dariya ta ce, "Saboda kuɗi Ummata. Dole na aure shi in darje in kwana a kan daloli na farka a kai."
"Kwantar da hankalinki gidan hutu kin samu, saboda jininki ya nuna ke matar manya ce. Kin san Allah gidan Mus’ab fa da irin ki ya dace ba waccan ballagazar ba..”
Safinat ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "Ummana sai isa nake yin ki over. Idan na auri Yaya na miki alkawarin Hajji duk shekara umura duk wata."
"Ke kuma a Saudiyya zan gama rayuwar, idan na sauke faralli ya wadatar sai zagaye Europe and Asia zan dinga yi."
Safinat sai tuntsirewa take da dariya saboda kalaman mahaifiyarta ta kishingiɗa, "Ka ji 'yar tsohuwa da son holewa."
Umma Laure ta yage leda ta taɓe baki ta ce, "Lallai tabbas shi ma wannan abokin tafiyar ne, da ganin irin wannan sayayyar za ka fahimci gogan nakin baya tausayin naira, a kayan zaƙi kawai, ai mu irin haka muke so, yarinya kin ɗauko farin jinin uwarki da alama, don lokacin da nake budurwa dandozon motoci ne kullum a kofar gidanmu, ƙaddara da rabonku ne ya hana uwarki auran attajiri na tsaya akan mahaifinku ba don rabonku ba ai ni kalar a yi min jiniya ce kuma ina tafiya da security."
Safinat ta soma hamma, "Umma, bari in ɗan runtsa ko da kaɗan ne."
MU WAIWAYI MAIMUNATU
Maimunat tana shiga gidansu ta faɗa cinyar Ummanta tana kuka.
“Maimunat lafiya kike kuka? Wani abu ne ya samu Aliyu ko Fatima?”
Ta girgiza kai alamar a’a, “To ko Mama ce wani abu ya same ta?”
“Umma Aliyu ne ya sake ni.”
Ta dafe ƙirji.“Saki! Wato kin yi sa'insa da shi ko? Rashin haƙurinku na yaran zamani a gidan aure abu ƙalilan sai ku tubure."
Cikin sheshshekar kuka “Wallahi ba haka ba ne Umma.”
“Haka ne mana, idan ba haka ba ne to mene ne, ku dai yaran yanzu ba ku da juriya da haƙuri a gidajen aurenku irin na iyayenku da kakaninku, abu ƙalilan sai ku tsinƙe igiyar aurenku. Kun fi sha'awar zawarci da zaman gidan miji, mu kuma mun fi son gidan aurenmu ko da rayuwar da muke ba maraba da gidan yari.”
Cikin dashashshiyar murya ta ce, “Umma, wallahi ni ma na fi son gidan mijina duk wuya duk daɗi, ƙaddara ce kawai ta faɗa mini.”
“Ke ki faɗa mini me kika yi wa Aliyu ya sake ki. Ni nasan Aliyu tun da ya furta saki a kanki akwai babban dalili.”
Maimunat saboda ba ta son baƙanta uwar mijinta a gaban mahaifiyarta ta ɓoye gaskiyar maganar ta ce da ita:
“Umma haka kawai ya shigo ya miƙa mini takarda yana mai ba ni haƙuri akan ya sake ni saki ɗaya.”
Ta miƙe “Ƙarya kike, ke ba ki iya shirya ƙaryar ba ma irin ta wasu, haka siddan babu gaira babu dalili Aliyu ya ba ki takardar saki akwai abu a ƙasa. Maimunatu kin kyautawa kanki sai ki zauna muna haɗa kafaɗa-kafaɗa da ke a gidan, cikin ƙannai kuma tun da hakan ya fi burge ki.”
Maimunatu ta ɗora hannu aka tana rusa ihu. Mahaifiyarta ta ja dogon tsaki, "Ba ki fara kuka ba sai gaba."
Ta yi gaba ta bar ta. Sallama ta ji sai ta tsagaita da kukan ta kai dubanta ga baƙin kofar sai ta ga Aliyu mijinta da Abbanta.
UMMA LAURE DA SAFINAT.
Umma Laure Wani biscuit ta gani ta farka tana ci ta ci take magana tana cewa, "To shi kuma wannan saurayin a ina kuka haɗu? Kuma ɗan waye ne?"
Ta ce, "Umma a Instagram ne, amma a gaskiya har yanzu ban ga ma sanin ɗan wane ne ba ne, amma da kin gan sa kin jinin da za a yi alfahari ne, saboda yana saka kaya na alfarma ga kuma hawa mota na kece raini."
Bayan ta cinye biscuit da ke hannunta ta ce, "To lalle abu ya yi kyau, irin mazan da nake buƙata dama kina abota da su, akhir naki da abota da irin jinin su Kamaye (ɗan Azumi Baba."
Dariya ta yi, “Ai ko akan hanya na yi gamo da irin su, ni da kuma bin hanyar har abada.”
“ Ba za ki ma yi gamo da su ba, duk wanda ya gan ki ya san ke ɗiyar manya ce ba ta matsiyata ba.”
Safinat murmushi ta yi kafin ta ba ta amsa sai ta ga wayarta na ringing tana ɗagawa sai ta ga Bros nata wato Mus'ab, tsaki ta yi ta ɗaga ya ce, "Ya minutes da na ba ki ya yi ban ganki ba?"
Ta ce, "Go slow ne amma ina kan hanya."
Mus'ab ya katse wayar ya dubi matarsa ya ce, "Kin ban mamaki dear, ƙarya baya daga cikin halayyarki, me ya sa za ki yi mini ƙarya? Kin ha'ince ni da safe yanzu kuma kin mini ƙarya, hakan ba girmanki ba ne.”
Ta dafa forehead nata, "Ka yi haƙuri dear wallahi...."
Cikin fushi da harzuƙa ya ce, "Ban son jin komai daga gare ki, abin da kike yi wa Safinat shi ne so? Kina dai gurɓata rayuwarta, kin ban mamaki ban taɓa tunanin za ki ci amana haka ba.Jiya mun yi magana da ke daban, da kika je gare ta sai kika juyar da magana, anya ikirarin da kike na cewa kina son ta gaskiya ne?"
Ta cija laɓɓanta tare da girgiza kai, ta ce, "Na shiga uku ya Allah ka ban mafita bisa lamarin nan, Allah kai ka san komai, kuma kai kaɗai ka san me na ce, kuma kai ka san sirrin zuciya, ya Allah ka dube ni don buwayarka da ɗaukakarka ka bayyanar da gaskiya gaskiya ce ka wanke ni bisa laifin da ake tuhumata da shi alhali ban yi ba.”
Mus'ab wani irin kallo ya yi mata ya ce, "Idan an taɓo ki komai ki ce Allah saboda kin iya yaudara ko? To shi Allah baya goyon bayan azzalumai kuma baya tare da munafukai, da maha'inta da maƙaryata kuma masu wannan halayyar komai daren daɗewa za su ga maƙomarsu.”
Ƙwalla ne suka cika idanuwanta ta ce, "Haba my one ya kamata ka tausasa harshenka a kaina ban san ka da yi min muggan kalamai ba. Ni ce na zama munafuka, maha'inciya maƙaryaciya duk tsawon rayuwar da muka yi da kai ba ka fahimci hakan nake ba sai yau, ka dinga nazari kafin ka furta magana.”
“Yanzu ne ai Allah ya bayyana su a zahiri.”
Cikin kuka ta ce, “Tun da har ka ce haka to ka zauna mu fahimci juna. Don Allah ka saurare in faɗa maka komai game da lamarin."
Mus'ab tsaki ya ja mata ya yi gaba, tana bin shi a baya, yana shiga bedroom ya sa sakata kafin ta ƙaraso.
UMMA LAURE DA SAFINAT
Hajiya Laure ta dubi ɗiyarta ta ce, "Ke da wa kuke waya?"
Safinat ta fara sosa keya ta ce, "Wani sugar daddy ne shi ma ya dame ni."
Umma Laure ta ƙyalƙyale da dariya ta ce, "Yarinya mai farin jini gaskiya hatimin Yusufa da na yi miki yana aiki, shi kuma wannan sugar Daddy a ina a ka samo shi? Ina dai fata shi ma zurriyar ƙaruna ne”
Safinat dariya ta yi tana cewa, "Ummata! Ummata! gaskiya ba ki fa da dama, sai nanata batu ɗaya."
Hajiya Laure ta ce, "Magana ce ta gaskiya ke ba matar talakawa ba ce, dole na nanata ƙirarki da Allah ya ba ki na jinin su Ɗangote da billgate ne, ba jinin kamaye ba ne na daɗin kowa."
Ta ce, "Ba ruwa na Umma da alama kin fa kulla wa Baba Kamaye (ɗan azumi Baba), Idan ya jiki kwa yi shari’a.''
Ta ce, "Ya ji ni mana ai gaskiya na faɗa shi ma na san ba son talaucin yake ba, talaucin ya tsaya a iya fim. "
Finat wayarta ce ke ringing da ta ga number Mus'ab ne taki picking har 3 missed call ba ta ɗaga ba.
Mahaifiyarta ta dube ta, "Ke ana kiranki ba za ki ɗaga ba."
“ Umma irin su Baba Kamaye ne fa, in kuma kin amince sai na ɗaga."
"Ina ban amince ba, jefa number a black list."
Safinat ta ƙyalƙyale da dariya.
Umma Laure ta kuma gyara zama ta fuskanci ƴar nata ta ce, "Yanzu abar zancen Ɗan'azumi Baba (Baby Kamaye,) mu koma kan sugar Daddy da kika ce, ya fa kamata ku haɗu ki ɗan yakato mana a samu na zuwa gurin boka wannan aikin fa sai mun dage kafin a cimma buri."
Safinat ta ce, "Yauwa Umma, kin ga ƙawata Abida yadda take juya Alhajinta gaskiya bokan nata shu'umi ne ko ita za mu kama ta kai mu wurin bokanta."
"Ke Safinat ƙawa za ki ba ta yarda kuna samun saɓani fa za ta fallasa komai, ban yarda ba kin ga Rufaida dai yarki ce ta jini ko. To ko ita ban aminta ta fahimci shirin mu ba, saboda haka ki yi gaggawar yanke alaƙa da Abida idan ba zai yiwu ba ku yi sama-sama kuma ki nuna mata kin haƙura da Mus'ab mahaifiyarki ta ce ba za ta yi wannan cin amanar ba. Ni za a nuna wa Bokaye na ɗarata a wannan ilimin sha kuruminki ke dai samo kuɗi."
"To shi kenan Umma, kuɗi za a samu wannan ba matsala ba ce."
HAFSY NA CIKIN TSAKA MAI WUYA.
Hafsy hawaye na zirya saman fuskarta ta latsa number Finat ya shiga yana ringing har ya katse ba ta ɗaga ba, again ta ƙara sai ta yi picking ta ce, “ 'Yar Aunty a ina kike?”
Cikin fushi ta ba ta amsa, “Ina inda kika faɗa wa mijinki na je.”
Cizon laɓɓanta ta yi tare da girgiza kai alamar ba ta ji daɗin amsar da ta ba ta ba, ta danne damuwar ta ce da ita, “Don Allah duk inda kike ki dawo gida, na shiga tashin hankali ta dalilinki.”
Safinat ba tare da ta ba ta amsa ba ta ja mata dogon tsaki ta katse call ɗin, ta ƙara yin trying number yana shiga Safinat ta yi rejecting.
Hafsy ta takaici ya cika ta, ta kuma retrying aka ce switch off.
Hawaye ke malala a fuskarta, "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un!" shi ne kawai abin da laɓɓanta ke furtawa, shi ko Mus'ab da ma ya kulle kansa a ɗaki ya shiga sake-sake.
Finat girgiza kai ta yi, a zuciyarta ta ce, "Kaɗan kika gani Aunt ai ba ki ma fara shiga tashin hankalin ba, na yi alkawarin sai na tarwatsa miki farin cikin da kike taƙama da shi." Safinat ta sheke da dariya.
Ummanta ta dube ta ta ce, "To 'ya ta me ya faru naga ke kaɗai kin tuntsire da dariya?"
Ta ce, "Umma ina mafarki rayuwar da nake daf da tsundumawa cikinta, rayuwa mai daɗi."
Ita ma Umma Lauren tuntsirewa ta yi da dariya ta ce, "Idan da gaske mafarkin kike kuma kina fatan ya tabbata, sai ki kira wanda zamu ji alert a yanzu haka."
Ta ce, "Okay Ummata."
GIDAN SU MAIMUNATU
Bayan Maimunat ta yi shiru cikin ladabi ta amsa sallamar, mahaifinta ya ce da ita, "Je ki ƙira mahaifiyarki." Ta amsa da to, sai ga ita da mahaifiyartata. Cikin rutsunawa ta yi wa maigidan nata barka da zuwa.
Aliyu ma ya durƙusa har ƙasa ya gaishe da surkuwarsa cikin fara'a ta amsa masa.
Maimunat saboda kuka da ta yi idanuwanta sun jajir kamar gonar tattasai. Cikin rutsunawa da girmamawa ta gaishe da Abbanta da Aliyu. Daga nan ta sunkuyar da kanta ƙasa don sauraran abin da za a ce.
Aliyu duk abubuwan da ya waƙana sai da ya zayyana musu, kuma ya shaida musu yadda mahaifiyarsa ke nuna tsananta da tsangwamarta ga Maimunat amma kullum tana cikin yi mata biyayya, ya ce wasu abubuwan a idon shi take yi, wanda kuma babu idon shi Allah ne kaɗai ya sani, amma Maimunat ba ta taɓa buɗe baki ta ce ita fa abubuwan da mahaifiyarsa ke ya ishe ta.
Iyayen Maimunat sun jinjina lamarin saboda 'yar su daidai da rana ɗaya ba ta taɓa kawo ƙorafi a kan uwar mijinta ko kuma saɓani na zamantakewarta.
Mahaifiyarta ce a zuciyarta ta ce, “Tabbas 'yata yau na yarda ke ɗiya ce mai son zaman aure, da kuma ɓoye matsalolin gidan aurenta. Kullum idan kika zo sai dai kina zaiyyana mini irin karamci da surkuwarki ke yi miki, har kina kawo abu da sunan ita ta aiko mini, ashe duk ba haka ba ne lulluɓe wa kike yi.”
Aliyu bayan ya sauke gauron numfashi ya ce,
“Abba kamar yadda na shaida maka a baya ina sakin matata a take a zuciyata na mayar da ita, akwai abin da na tsara, amma ba ni da damar yin sai da amincewarku da kuma amincewar Maimunat shin kun ba ni damar furta wa?”
Abban Maimunat ya ce, “Na ba ka dama.”
Aliyu ya fuskanci matarsa ya ce, “Maimunat ba na so don ina son ki na ƙuntata miki, don kin fuskanci ƙalubale a zamantakewar mu kin yi haƙuri. Shin har yanzu kina so na? Za ki jure zama da ni?”
Maimunat ba ta amsa ba, kanta a ƙasa tana murmushi.
Ummanta ce ta ce, “Ke ba da ke ake ba ki ce eh ko a’a.”
Maimunat ta ɗago kanta tana murmushi ta rufe fuskarta tare da gyaɗa kai alamar eh ta fice a kunya ce.
Abbanta murmushi ya yi ya ce, “In ban da abin ki Hajiya kin fi kowa fa sanin halin kunyar ɗiyar taki ai mace idan ba ta son abu tana faɗa kai tsaye idan kuma kuka ga ta yi shiru tana murmushi to tana so, fatan kun fahimci Maimunatu”
Dukkaninsu suka amsa da eh.
SAFINAT DA UMMA LAURE
Safinat tana kurɓar lemo tana haɗa wa da biscuit, bayan ta gama ta ɗauki cingam ta jefa a baki tana tauna wa tana kyakyas ta dubi Ummanta ta ce,
“Umma burina auran attajiri irin yaya Mus’ab kin ko san yadda arzikinsa ke haɓaka? Idan yana waya yana magana akan kasuwancinsa sai na ce a raina lallai Yaya yanzu zai iya haɗa kafaɗa da Ɗangote da su Bua. Allah dai ya cika mini wannan burin."
Umma Laure ta ce, "Safinat burinki zai cika, mafarkinki zai zama gaskiya, amma sai kin tashi tsaye za mu cimma burin mu."
"Umma na jima da miƙewa, kuma ba zan zauna ba, har sai lokacin da muka cimma buri.”
“Amma kin san da zafi-zafi a kan bugi karfe. Kuma a bari ya huce shike kawo rabon wani."
"Haka yake Umma, ba zan yi sake ba.”
"To kin san lamari irin wannan na bukatar kuɗi ni kuma a gaskiya a yanzu haka naira 5 tafi karfina in har muna son mafarkinmu ya tabbata dole sai... Kin dai gane ai ba sai na ƙarasa ba."
Ta ce, "Ba damuwa Umma ta muna zaunen nan zan kira wani Alhaji yanzu zai sauke min alert na miki transfer, kamar nawa kike buƙata?"
Hajiya Laure ta ji alert ta rikice ta taɓe baki ta ce, "Allah 'yar gari, 'yata kina fa burge ni, da gaske kina da muradin gidan hutu. 100,00 ina ga zai yi amma zuwa gaba za a kuma buƙata."
Safinat kunna wayarta ta yi saboda tun da Hafsy ta dame ta da ƙira ta kashe. Number wani Alhajinta ta yi dialin, Alhaji na ganin number ya fara dariya yana cewa, "Lallai yau na taki sa'a, ni Finat ke ƙira?"
Ya yi picking ya sanya a kunnensa, ita ko cikin kashe murya ta fara magana tana cewa, "My baby barka da wannan lokaci, ina fatan kana lafiya?"
Ya amsa mata da "Barka dai am fine, hope my baby na ma she is fine."
Ta ce, "Nope dear."
Ya ce, "To, what's wrong?"
“Mummyna ce ba lafiya har an yi admitting namu a hospital kuma an buƙaci sai mun ajiye 100, 000 kafin a fara duba ta. Ga shi mu kuma daidai da naira biyar ba mu da shi na yi fafutuƙar neman bashi amma abin ya ci tura.”
Alhaji ya yi shiru da ya ji batun kuɗi ya fara sosa keya.
"To ki zo hotel akwai farin kuɗi ki karɓa."
Mahaifiyarta ta tsura mata idanu tana jin tattaunawar, “Ba zan iya barin Ummata ita kaɗai ba, don ba kowa a kanta face ni, kai dai ka yi mini transfer kawai."
“Babyna idan da akwai damar transfer ai ba zan miki maganar zuwa ba, ATM na ya yi expire."
Ta lankwasa wuya tana lumshe ido kamar tana gabansa suke magana ta ce da shi,, "Kana nufin you have only one account?”
Ya ce, "No amma the other accounts ɗin ba na transaction sai wannan, ke kam minti nawa za ki yi ne a zuwa da karɓar."
"kana nufin na bar mara lafiya na zo gareka."
“Zuwan da ba za ki wuce 10 minute to 15 ba, ko wasu a asibitin kika ce su kula da Umman za su yarda.”
Safinat za ta kuma magana da shike a handsfree suke tattauna Umma ta yi mata nuni da ta ce ta amince da zuwa.
Safinat ta ce, "To shi ke nan my Alhaji gani nan zuwa, a wanne hotel kake?"
Ya amsa mata da, "DUJIMA hotel."
Ta ce, "Alright za ka ganni yanzu.
Alhaji murmushi ya yi sannan ya murmuza gemunsa da hannunsa ya ce, "Ko ke fa, Sweetheart haka nake son ji sai kin zo."
Yana gama faɗin haka ya katse wayar ya kwanta bisa gadon yana miƙa yana cewa:
"Na miki transfer 100k haka kawai a banza haba 'yan mata yanzu yayin ka ba ni manda na ba ka gishiri ake, idan kin zo in har kina buƙatar 100k dole mu yi haka a tsakaninmu. Ke da kike wulakantar da ni yau na yi ƙima a wurin ki har da ƙira dama ina ga ƙiran na ayyana a zuciyata wata buƙatar ki ce."