1
*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
_Masu buk'atar complete littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_
Free page
1️⃣
Fuskar nurse d'auke da yalwataccen murmushi ta fito daga lobour room hannunta d'auke da Baby,
cikin matsanancin farin ciki wani mutum me cikekkiyar nutsuwa da kamala, wanda da gani bazai wuce shekaru 45 ba,
cike da murna ya tari nurse d'in had'i da mik'a hannu zai karb'i Babyn dake hannunta,
yana cewa " me muka samu?
K'in mik'a mishi Babyn tayi, " irin wannan zumud'i haka Ya mu'allim! kamar yau aka fara yi maka haihuwa?
" Duk d'a d'a ne, dole na nuna farin ciki abisa ni'imar da Allah yayi min, wacce ba kowa Allah yake yiwa ita ba, akwai wad'anda suke nema da kud'insu, da ransu da lafiyarsu amma Allah baiba su ba,
" to naji yanzu dai aban goron albirin kafin na bada, cikin murmushi ya sanya hannu a aljihu ya zaro 3k ya mik'a mata,
" hmmm Ya Mu'allim kenan, ni ba kud'i nake san a bani ba, addu'a nake san ayi min nima Allah ya bani haihuwar,
cikin jimami Ya Mu'allim yace " ikon Allah! badai kema Allah baibaki ba?
"Eh muna ta addu'a dai Allah bayar shekarata goma sha biyu da aure amma ban tab'a ko b'atan wata ba,
" ashsha! Allah ya bada nagari, in sha Allah zan sakaki cikin addu'a ta, " amin ya Allah Ya Mu'allim nagode kwarai,
ta fad'a tana mik'a mishi jaririyar had'i da cewa " 'ya mace muka samu, fara'ar fuskarshi taga ta yalwata,
" Alhamdulillah! Alhamdulillah Allah nagode maka, yau na samu abinda na dad'e ina nema, abinda nayi shekara da shekaru ina addu'ar samu,
d'an kallanshi nurse d'in tayi, kamar zatayi magana sai kuma ta fasa, " ya mahaifiyarta ta?
"Tana lafiya, zaka iya ganinta, tana can d'akin ta fad'a tana nuna mishi k'ofar d'akin, yana rungume da jaririyar ya shiga d'akin,
zaune ya iske ta, a bakin gado, ya k'arasa kusa da ita yana murmushi, " sannu Saratu ya jikin?
"Alhamdulillah ta fad'a idonta kanshi, ganin yadda farin ciki da annurin fuskarshi ya fad'ad'a yasata gane abinda suka samu,
duk da kasancewar duk haihuwar datake haka yake nuna farin cikinshi a fili,
tana cikin zancin zuci taji yace " Alhamdulillah Mama na tazo, d'an guntun murmushi tayi tana kallanshi,
tace " dama nasan tunda na ganka haka mace aka haifa, zayyi magana wayarshi ta soma ringing,
cikin nutsuwa ya zaro wayar, jikinshi na rawa saboda tsananin farin cikin ganin sunan amininshi Yaseer, ya d'aga wayar had'i dayin sallama,
murmushi Ya Mu'allim yayi tare da cewa " ai tama sauka an samu Hajiya,
banji me akace daga d'aya b'angaren ba, naji yace " ah haba dai yau d'in nan?
"Ai da ka bari sai gobe sai kazo Yaseer, d'an shiru yayi yana sauraran maganar Yaseer kafin yace " to shikenan Allah ya kawo ku lafiya,
bayan ya kashe wayar ya mayar da kallanshi ga matarshi Saratu yace " Yaseer ne zai zo, "ayya dakace mishi ya bari yazo daga baya,
" na fad'a mishi yace sai yazo, " to shikenan Allah ya kawo su lafiya, Ya Mu'allim ya amsa da " Amin ya Allah, kasancewar Saratu ta haihuwa lafiya yasa aka sallame ta,
yana rungume da jaririyar ya bud'e mata mota ta shiga, ya zagaya ya shiga yaja suka fita daga harabar asibitin,
koda suka isa gida iskewa sukayi har Hadiza mak'ociyar Saratu ta d'ora ruwan wanka, cike da fara'a Hadiza ta karb'i jaririyar ta goya ta,
kana ta kwashe ruwan wankan ta kaiwa Saratu ban d'aki, kafin Saratu ta fito daga wanka tuni Hadiza tayiwa jaririyar wanka ta shiryata tsaf,
sai da Saratu ta gama shiryawa sannan Hadiza ta kawo mata abinci, ta aje gaban Saratu had'i da cewa " Bismillah ga abinci nan ki ci nasan cikin jego,
" har da su girki kikayi Hadiza?
Saratu ta fad'a cikin mamaki, " eh! ai su Umar na fad'a min kun tafi asibiti da Ya Mu'allim na shigo,
"nagode sosai Hadiza Allah ya saka da alkhairi Ubangiji yabar zumunci, " Amin ya Allah, d'an jim sukayi na wani lokaci,
kafin Hadiza tace " idan baki buk'atar komai bari na shiga gida, a nutse Saratu tace " bana buk'atar komai, nagode sosai,
tana shirin fita daga d'akin Ya Mu'allim ya shigo, fuskarshi a sake yayiwa Hadiza godiya, ta amsa da bakomai ai duk yiwa kai ne, kana ta fice,
daga tsakar gida suka jiyo muryar Sumayya matar Yaseer tana sallama,
bakin Ya Mu'allim a washe ya fita,
ya tare ta, cikin zumud'i yace " ina Yaseer?
"Yana waje! kafin ta gama rufe bakinta Ya Mu'allim yayi wajen da sauri, Sumayya tabi bayanshi da kallo tana murmushi,
cike tsantsar farin Ya Mu'allim ya tari Amininshi suka rungume juna, kallo d'aya zakayi musu kasan suna cikin matsanancin farin ciki,
" muje naga Mamana, cewar Yaseer yana shigewa gaba dan bashi da iyaka da gidan Ya Mu'allim,
bayanshi Ya Mu'allim yabi yana dariya yace " kaga uban 'ya ko bari mu gama gaisawa ma bakayi?
Kafin Yaseer yayi magana AMMAR yace " baka ganni bane Baba Malam?
Sai lokacin hankalin Ya Mu'allim yakai kan Ammar, da sauri ya d'auke shi yana dariya, Ammar ya turo baki irin na shagwab'abbun yaran nan 'yan gata yace " nayi fushi,
" yi hak'uri kaji yaron Baba Malam, Yaseer na dariya yace " har yanzu baka bar d'aukar Ammar ba, dube shi gud'ai-gud'ai dan Allah,
cikin shagwab'a Ammar yace " kaji ko?
"Rabu dashi yaron kirki, duk girman mutum yaro ne a wajen iyayenshi, balle kai da duka-duka shekararka takwas,
cikin murna Ammar yace " Baba Malam zaka rink'a d'auka ta ko na zama babba kamar ka?
Yaseer da Ya Mu'allim suka runtse da dariya, Ammar ya shagwab'e fuska zayyi kuka, Ya Mu'allim yayi saurin cewa " yi shiru kaji,
idan shekarunka sun kai 40 ina iya d'aukarka balle shekara 8 kawai, duk sanda kake san na d'auke ka, ka gudo Zamfara zan d'auke ka,
Ammar ya saka dariya had'i da sumbatar Ya Mu'allim, yace " shukran, Ya Mu'allim yace " afuwan,
" dan Allah idan kun gama azo a sadani ga 'ya ta, Yaseer ya fad'a yana k'arasa shigewa cikin gidan,
Ya Mu'allim yabi bayanshi yana dariya d'auke da Ammar a kafad'arshi, a falo suka iske Sumayya da Saratu suna hira,
Babyn nakan cinyar Sumayya, Ya Mu'allim ya zauna saman kujera tare da zaunar da Ammar akan cinyarshi,
Yaseer kuma ya nufi Sumayya yana murmushi yace " uhnn kaga Maman Ammar an kama Baby an rik'e,
abinka dama dame neman 'ya mace, Saratu tace " idan tana so ta d'auka an bata, a hankali Ammar ya zame daga jikin Ya Mu'allim,
ya nufi Abbanshi dake rik'e da Babyn, ya k'ura mata ido had'i da cewa " Abba wannan new teddy ce?
Jin abinda Ammar yace yasa su dariya gaba d'ayansu, kana Abbanshi yace " a'a wannan k'anwarka ce Ammar,
" Abba zata rink'a ce min Yaya ni ma?
"Sosai ma, ai daga yau ka zama Yaya Ammar ma, cikin murna Ammar yace " to Abba ka bani ita ina santa,
da sauri Ya Mu'allim yace " kana santa Ammar?
Cike da k'uruciya Ammar yace " eh! Baba Malam ina santa, zaka bani ita muyi aure mu zama mata da miji irin na Uncle da Aunty?
Cike da tsantsar mamaki suka zaro ido suna kallan Ammar, wanda idan da sabo sun saba da zaro zance da manyan maganganu daga bakinshi,
yaro kamar ba d'an 8yrs ba, idan ya fad'i wata maganar sai ka rantse fad'a mishi akayi, irin sune ake cewa kunne ya girmi kaka,
Yaseer yace " ikon Allah Ammar ina kasan mata da miji da aure?
" A films da makaranta nake ji ana fad'a, kuma ai naji Aunty na yiwa Nani fad'a tana cewa idan ana san mutum aurenshi ake yi,
Saratu tayi murmushi gami da cewa " hmmm shiyasa bakowacce magana ake yi gaban yaran yanzu ba,
saboda suna da yawon tsiya sosai, Allah ya kawo mu wani irin zamani da ake haihuwar yara da wani irin wayo me ban tsoro,
idan kaji yaro ya zaro wata maganar ko kai babba albarka, wasu lukutan ma kunya suke bawa mutum,
haka yawan kallace-kallacen films, finafinan k'etare yana taimakawa sosai wajen gurb'ata tarbiyyar yaran mu,
dan mafi yawancin mugayen d'abi'u a films ake koyarsu, saboda akwai abubuwa da bamu sansu ba a arewa, akwai al'adu da d'abi'un da bana mu ba ne, aro su mukayi daga wasu k'asashen,
kamarsu, kidnapping, soyayyar shan minti, kiss, hug, fashi da makami, lesbian, gay, homo sexual, shaye-shaye, kid'a da wak'a, raye-raye, nuna tsuraici da wasu dressing d'in da sauransu,
idan kallo yaro yake san yi akwai cartoons, akwai kaset d'in addini na yara, akwai na koyar da bak'ak'an addini da addu'o'i, akwai na koyar da ABCD, akwai masu amfani sosai,
ajiyar zuciya Sumayya ta sauke a hankali had'i da cewa " kayya Umman Umar bari kede kawai, muyi addu'a ita kad'aice mafita, dan yanzu ko cartoons d'in ma akwai sex cartoons dole sai iyaye sun kula sun saka ido sosai, al'amarin yanzu sai dai addu'a, Allah ya kyauta Ubangiji ya shirya mana zuri'a,
gaba d'ayansu suka amsa da amin, Ammar ya kuma cewa " Baba Malam ka bani ita na tafi da ita idan ta girma sai muyi aure ko?
Fuskar Ya Mu'allim d'auke da murmushi ya shafa kan Ammar yace " kana santa Ammar?
A hankali ya d'aga kanshi alamar eh, Ya Mu'allim yana murmushi yace " in sha Allah, da yardar Ubangiji bata da wani miji idan ba kai ba,
bijahi Rasulillahi In Allah yaso ya yarda kai ne mijinta, kaji?
Da sauri ya d'aga kanshi sama yana dariya, Yaseer yace " um um fa baka san me gaba zata haifar ba, kada ka shiga hurumin Ubangiji Ibrahim, " ai Allah nace, kuma cewa nayi in sha Allahu, kuma da izinin Allah shine mijin ta,
tun daga yanzu zan saka ku a addu'a kaji Ammar, Ammar yayi dariya cike da k'uciya yace " kayi alk'awari?
" In banda abinka Ammar kai ma me aurar da ita ne, ko wani ka bawa ai ta bayu bare kai da kanka namijin duniya,
" a'a ni dai kayi alk'awari, Ammar ya fad'a yana kallan Babyn, "In sha Allah, in Allah ya so ya yarda, idan Ubangiji ya nufa kai ne mijinta nayi maka alk'awarin bata da wani miji sai kai, ko bayan rai na zan bar wasiyyar a aura maka ita,
Yaseer yace " a'a bafa za'ayiwa 'ya ta auren dole ba, idan kuma bata sanshi fa ayi yaya?
"Aiko dolenta ta aure shi, dan babu macen da zataga baturen d'ana tace bayyi mata ba, Ya Mu'allim ya fad'a yana murmushi,
Yaseer yace " naji na yarda amma kayi min alk'awarin bazaka tab'a yi mata auren dole dashi ba, " naji Ya Mu'allim yace yana wagarar da maganar,
sanin halin amininshi yasa Yaseer ya kuma cewa " baka ce komai ba, cikin basarwa Ya Mu'allim yace " naji!, Yaseer da Sumayya suka saki murmushi jin dad'i,
Sumayya tace " aiko idan Allah yasa Ammar ya aure ta danafi kowa farin ciki, ta fad'a cikin yalwa,
" a'a da dai kinyi farin ciki, ke kanki kin san da sai nafi kowa jin dad'in wannan had'i, cewar Yaseer yana kallan Sumayya, Ya Mu'allim yace " kai ma fad'a kake dan kasan sai na fika murna,
kasancewar magana ba damun Saratu tayi ba, yasa batayi magana ba, illa murmushi kawai da take yi tana binsu da ido,
" anyi mata hud'uba ne?
Yaseer yayi magana yana k'ok'arin karb'ar jaririyar daga hannun Ammar, " waya isa yayi mata hud'uba ubanta bai zo ba?
" To wanne suna za'a saka mata?
"Duk sunan da yayi maka, amma idan so na ne a saka mata sunan Hajiya, sosai Yaseer yaji dad'in kalamin Amininnashi, yayi murmushi batare dayi magana ba, yana mik'a hannu a karo na biyu zai d'auki Babyn yayi mata hud'uba,
amma Ammar ya hana ta, "ikon Allah ka badata a saka mata suna, kafad'a ya mak'ale gami da cewa " a'a ayi mata a haka,
yin duniya Ammar ya bada Babyn a saka mata suna amma ya hana, daga k'arshe ma kuka ya saka,
dole sai d'aukar Ammar Yaseer yayi ya tallafe Babyn tana hannun Ammar yayi mata hud'uba da sunan mahaifiyar shi BASIRA,
bayan ya gama ya d'ago kai ya kalli Aminshi yace " yarinya taci sunan Hajiya, wanne suna za'a rink'a kiranta dashi?
Kafin kowa yayi magana Ammar yayi karaf yace " BASMAH, Ya Mu'allim yace " gashinan Yayanta ya zab'ar mata,
Yaseer yace " kai yanzu biye shi zakayi?
Maimakon ya bawa Yaseer amsa sayya mayar da kallanshi ga Ammar yace " kana san sunan, yayi maka?
Ammar yayi saurin cewa " eh!,
" Aiko tunda ka zab'ar mata sunan nan, sunan yabi ta kenan har abada Basmah, tunda suna ne me ma'ana,
har dare Ammar rungume da Basmah, anyi juyin duniya yak'i bada ita, da aka karb'eta za'a bata nono kuka ya saka harda birgima,
sai dakyar Ya Mu'allim ya lallab'ashi yayi shiru, bayan kwana biyu da suka tashi tafiya,
anan akaga daru dan k'in tafiya yayi, ya kafe sai da Basmah zai tafi, cikin kuka Ammar ya kalli Ya Mu'allim yace " kayi min alk'awarin zaka bani fa,
Ya Mu'allim ya sunkuya dai-dai tsayin Ammar yana goge mishi hawaye yace " kayi hak'uri kaji, kaga yanzu bata girma ba, tana shan mama,
ka bari idan aka yaye ta, sai kazo ka d'auke ta ku tafi kanon tare ko?
"To yaushe za'a yaye ta?
"Kwanan nan baza'a dad'e ba, da an yaye ta kazo ka d'auki abarka ka ku tafi Kano tare,
" ka tabbata zaka bani ita?
"In sha Allah, " kayi alk'awarin zamu yi aure ko?
Murmushi Ya Mu'allim yayi yace " in Allah ya yarda idan Ubangiji ya nufa kaine mijinta nayi maka alk'arin baka aurenta,
nayi maka alk'awarin Basmah bata miji da duniya sai kai Ammar Allah da mala'iku suna shaida, a hankali Ammar ya sanya hannayenshi biyu ya goge hawayenshi,
ya yiwa Basmah kiss a goshi tare da cewa " bye sai nazo tafiya dake Kano, kamar Yaseer da Ya Mu'allim bazasu rabu ba,
sukayi ta sallama da juna a k'alla takai sau 5, wannan ya raka wannan, wannan ya raka wannan haka sukayi tayi, har motar su Yaseer ta b'atace Ya Mu'allim yana d'aga musu hannu,
" kuka kake yi Malam?
Saratu ta fad'a tana kallanshi, da sauri ya goge siraran hawayen da suka zubo mishi " ikon Allah, yace yana kallan hawayen,
" ban san sun zubo ba, Saratu ta kafe shi da ido na tsayin lokaci kafin tace " anya Ya Mu'allim akwai wanda kake so a duniya kamar Yaseer?
Kanshi ya girgiza batare dayayi mata magana ba ya shige, tabi bayanshi da kallo dan ko bai fad'a ba tasan amsar tambayarta.
*ASALIN SU....!*
Ibrahim Umar shine cikekken sunan Ya Mu'allim, haifaffan garin Zamfara ne, yana da matar aure d'aya Saratu da yaransu maza hud'u,
Umar shine babba me shekaru 12, sai Usman 10, Ali 8 sai Abbakar 6, sai yanzu da aka haifi Basmah, alak'arsu da Yaseer ta samu asali ne daga Primary school,
tare suka fara tun daga Primary 1, har jami'a duk da kasancewar akwai babbanci halayya da ra'ayi a tsakanin su,
hakan bai shafi abokarsu ba, dan shi Yaseer d'an boko ne ra'ayin turawa ne dashi, ga gayu da kwanbo,
yayinda shi kuma Ibrahim sam bashi da ra'ayin turawa kwata-kwata, ra'ayinshi yafi karkafa ga addini tun suna yara,
hakan yasa ko'a jami'a Islamic ya karanta, cikin ikon Allah ya samu scholarship a Madina, wannan damar daya samu yasa ya k'ara hab'aka,
ya zama cikekken Malamin addini mai bada fatawa, ya bud'e babbar islamiyya me had'e da yara, matan aure, maza magidanta,
islamiyyar tana had'e da babban masallaci, wanda har sallar juma'a da idi ana yi cikinshi,
Ya Mu'allim shine babban Malami kuma limamin unguwar Tudun wada, dan shike jan sallolin a masallacin, shi yake yin hud'ubar juma'a,
duk Zamfara state babu islamiyya da masallaci kamar na Ya Mu'allim, ya samu sunan Ya Mu'allim ne tun yana yaro, saboda ra'ayinshi na addini, da tarin ilimin Islama da yake dashi,
kowa da Ya Mu'allim yake kiranshi, haka matarshi Saratu wacce asali d'alibarshi ce Allah yayi auren su, mace mai hak'uri da juriya, tana da kyawawan d'abi'u,
bata san hayaniya, ita ko magana ba damunta tayi ba balle kwaramniya, idan akayi abu sai dai tayi murmushi,
itama tana da tarin ilimin Islama dan tana koyarwa a cikin gida,
yaran Ya Mu'allim sun samu ingantacciyar tarbiyya me kyau, sun biyo iyayensu wajen ilimi da ra'ayin addini,
kwata-kwata kyale-kyalen duniya bai dame su ba, yara ne amma saboda kamala da nutsuwa idan ka gansu sai ka rantse manya ne,
gidan Ya Mu'allim gida ne dayake cike da farin ciki, kwanciyar hankali da nutsuwa, suna gudanar da rayuwarsu cikin sauk'in da rufin asirin Allah.
Yaseer shima d'an Zamfara ne gaba da baya aiki ne ya kaishi Kano State, yana da matan aure biyu, da 'ya'ya uku, NAYAN shine babba, sai Ammar da Leenah,
Hajiya Tanya itace matarshi ta farko itace me 'ya'ya biyu NAYAN shine babba sai jaririya Leenah 'yar wata uku da haihuwa,
Hajiya Tanya 'yar uwarshi ce auren zumunci akayi musu, duk da baya santa ya hak'ura ya zauna da ita lafiya,
ko a fuskarshi bata tab'a ganin rashin so ba, balle ya furta, matarshi ta biyu asalinta ba 'yar Nigeria bace,
baturiya ce dayake tare suka samu scholarship da Ya Mu'allim, sai dai shi America ya tafi, acan ya had'u da Julia,
baturiyar America me tarin dukiya, kud'i da kamfanoni, Allah ya jarrabe ta mugun sanshi,
sai da sukayi jarjejeniyar zata musulunta, zata bishi k'asarshi kafin ya aure ta, bayan ya aure ta, ta musulunta ta koma Sumayya daga Julia,
Allah yasa ta k'arbi addini da gaskiya, tayi koyi da koyarwar fiyayyan halitta, shekararsu d'aya da aure ta haifi Ammar,
ya biyo kamannin mahaifiyar shi sak, dai-dai da gashin kanshi ja ne irin na asalin turawa,
tun daga kan Ammar Allah bai k'ara bawa Sumayya haihuwa ba, gata da bala'in san yara musamman 'ya mace,
Hajiya Tanya makirar mace ce, annamimiya marar tsoran Allah, wacce zata iyayin komai dan biyan buk'atar kanta,
tunda Yaseer ya auri Sumayya ta d'auki karan tsana ta d'ora mata, kwata-kwata bata san ganinta,
amma dayake makira ce ta iya takunta sai ta b'oye duk abinda ke ranta take zaune da Sumayya faram-faram,
dan ta kwallafa ranta akan dukiyar Sumayya musamman datayi bincike taji tari abinda Allah ya mallakawa Sumayya,
aka tabbatar mata idan za'a had'a gaba d'aya manyan masu kud'in Africa a tattara abinda suke dashi waje d'aya basu kai koda rabin abinda Sumayya take dashi ba, idan za'a canja shi daga dollars zuwa Naira,
hakan yayi mugun tashin hankalin Tanya dan ita mace me mugun son abin duniya, ga kwad'aniyi,
tun daga wannan rana data samu labarin dukiyar Sumayya ta shiga k'ulle-k'ullen hanyar zata bi ta mallaki gaba d'aya dukiyar,
tare da d'anta Nayan suke k'ulla duk wani makirci dayake ya d'an girma dan zai kai 14yrs,
tsakanin Yaseer da Ya Mu'allim akwai fahimtar juna, da sabo da shak'uwa, tunda suke basu tab'a rabuwa da juna ba sai lokacin da suka samu scholarship,
amma dai-dai da d'akin kwanansu d'aya, tare suke bacci a katifa d'aya su rufa da bargo d'aya,
tare suke cin abinci a kwano d'aya, kayan sawarsu tare yake basa bambamce komai a tsakanin su,
Allah ya had'e kansu, suna matuk'ar so da k'aunar junansu, basu saba da kowa ba a duniya kamar yadda suka saba da junansu.
*CIGABA...*
Kasancewar Ya Mu'allim malamin Sunnah yasa gidanshi ba'a bidi'a ko taran suna ba'ayi, a masallaci aka rad'awa Basmah suna,
da ranar haihuwarta ta zagayo aka yanka raguna, Ya Mu'allim da Saratu wacce yaranta ke kira da Umma,
duk yaran gidan suka d'auki so da k'aunar duniya suka d'orawa Basmah, ko k'uda basa barin ya tab'a ta,
kowa yana nan da ita, wani lokacin har fad'a Ali da Abbakar suke yi akan d'aukarta, yau ce mummunar ranar da Ya Mu'allim ba bazai tab'a mantawa da ita ba,
tun da ya tashi daga bacci yake jin kasala da matsananciyar fad'uwar gaba, ya zama wani sakaka dashi, ko abinci ya kasa ci,
" lafiya kuwa Malam?
Umma ta fad'a idanta kanshi, danta fahimci yanayinshi, guntun murmushi yayi yana k'ok'arin b'oye halin da yake ciki yace " lafiya Alhamdulillah,
" amma na ganka haka Ya Mu'allim?
Batare daya kalle ta ba yace " me kika gani?
" Gaba d'aya yanayinka ya canja ba kamar yadda kake ba, sai da ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya mayar da kallanshi gare ta,
yace " ni ma ban san takamaiman abinda yake damuna ba, haka nan nake jina babu dad'i,
ina jin wani iri a jiki na, cike da tausayawa ta kalli mijin nata tace " kayi ta addu'a koma meye sayya zo mana da sauk'i,
ya bud'e baki zayyi magana wayarshi ta soma ringing, k'arar shigowar kiran yasa gabanshi yayi muguwar fad'uwa,
cikin nutsuwa ya dafe k'irjinshi had'i da cewa " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
Umma zatayi magana kiran ya kuma shigowa a karo na biyu, kamar bazai d'auka sai kuma ya mik'a hannu cikin mutuwar jiki ya d'auki wayar,
gami da kara ta a kunne bakinshi d'auke da sallama, " kai ne Malam Ibrahim Umar Zamfara Ya Mu'allim?
Aka fad'a daga d'aya b'angaren, sai da ya runtse idonshi deep down yana maimaita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,
kana ya amsa da "eh! ni ne, d'an shiru akayi daga d'aya b'angaren na wasu 'yan dak'ik'u kafin akace " please zaka iya zuwa police station d'in dake rimi?
A nutse kamar babu wani abu Ya Mu'allim yace " lafiya dai ko?
"Eh! to, yanzu muka samu report anyi hatsari a k'ofar gari gaf da shigowa Zamfara, bayan munje,
muka ga mace da namiji ne da muka duba d'aya daga cikin wayoyinsu sai mukaga number ka shine muka nemeka koka sansu,
sosai k'irjin Ya Mu'allim ya tsananta bugawa, tsoro da fargaba suka dirar mishi lokaci d'aya, muryarshi na rawa yace " kun ga sunansu?
"Eh! mun ga sunan namijin a jikin ID card d'inshi sai dai Allah yayi musu rasuwa gaba d'ayansu,
" ya sunanshi!?
Ya Mu'allim ya fad'a kamar me koyan magana, tamkar saukar aradu Ya Mu'allim yaji d'an sandan na cewa " Yaseer Adam...........!
*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKI....!*
MOMYN ZARAH