SAKI RESHE..

2

by @hauwaausmanjiddarh

_*SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


_Masu buk'atar complete littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_


Free page


2️⃣


Tsabar tashin hankali ne yasa wayar sub'ucewa daga hannunshi, ta fad'i ta tarwatse a k'asa, 

" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha, 

Ya Mu'allim ya fad'a had'i da durk'ushewa k'asa ya dafe kanshi yana kuka marar sauti, while yana fad'ar innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, 

Yaseer ya tafi ya barni, Saratu Yaseer ya rasu, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, tashin hankali ne ya hana Saratu motsawa daga inda take, 

ta kasa koda motsa hannunta balle ta mik'e taje wajen mijinta ta rarrashe shi, sai da Ya Mu'allim yayi kuka me isarshi sannan ya mik'e ya fita,

bai dad'e ba ya dawo tare da motar asibiti da 'yan sanda, idonshi yayi jajir kamar gauta, 

baya iya yiwa kowa magana, sai gaf da magriba Tanya da Nayan da sauran jama'ar Kano suka k'araso, tun daga waje Tanya da Nayan suke kurma ihuu, 

suna gunjin kuka " wayyo Allah na shiga uku, wayyo ni Tanya, Allah ya d'auke min Yaseer da Sumayya lokaci d'aya, 

sun tafi sun barni, asiri na ya tonu, Allah ya zakayi min haka ka d'auke su duka biyu a lokaci d'aya, 

Allah ka tausaya min ka bani hak'uri da juriya, wayyo Allah nayi rashin miji na, me so na adali miji a tsakanin matanshi, 

ya rabbi ka jik'an Yaseer da Sumayya, Ya Mu'allim zaune a parlour ya sanya gawar Sumayya da Yaseer gaba yana zubar da hawaye, 

ya k'i tashi daga gaban gawar, ya jiyo ihuuun Tanya da Nayan, bayyi k'ok'arin hanata ba, danshi kanshi ihuuun zuci yake yi, 

ji yake tamkar yayi hauka, a hankali yaji andafa shi ta baya, had'i da cewa " Baba Malam ina Mamy da Daddy sun ce min wajenka zasu zo?


Ido Ya Mu'allim ya runtse da k'arfi jin muryar Ammar, tausayin yaron yayi masifar kamashi, 

lokaci d'aya ya rasa gaba d'aya iyayenshi uwa da uba, " Baba Malam basu zo nan ba ko? 


"Dama nasan wayo suka yi min, nayi fushi dasu, ka fad'a musu bazan k'ara yi musu magana ba, 

sosai zuciyar Ya Mu'allim ta karye ya fasa kuka had'i da rungume Ammar tsam a jikinshi, 

yana cewa " sai dai muyi hak'uri Ammar bazasu tab'a dawowa ba sun riga da sun tafi sun barmu har abada, 

cikin rashin fahimta Ammar ya d'ago kanshi daga jikin Ya Mu'allim yace " ina suka tafi? 


Kafin Ya Mu'allim ya bashi amsa Hajiya Tanya dake shigowa parlour tayi caraf da cewa " ya mutu, sun mutu Ammar, sun tafi sun barmu bazasu tab'a dawowa ba har abada, 

duk da kasancewar Ammar yaro d'an shekara 8 hakan baisa ya kasa gane abinda take nufi ba, yasan mutuwa sarai, 

dan haka ya kalli Ya Mu'allim yace " da gaske Momy da Daddy sun mutu? 


Ya fad'a hawaye na taruwa a idonshi, batare da yayi magana ba ya kwantar da kan Ammar a kafad'arshi, 

lamo Ammar yayi a jikin Ya Mu'allim, da gudu Tanya ta fad'a kan gawar Yaseer da Sumayya, 

had'i da bud'e fuskokinsu tana gunjin kuka, wayyo Allah na, ni Tanya naga rayuwa ganin ido na,

a hankali Ammar ya saki Ya Mu'allim ya fad'a kan Yaseer da Sumayya yana jijjiga su had'i da kiran sunansu, 

Ya Mu'allim kasa yiwa Yaseer wanka yayi, sai wasu daga cikin d'alibanshi ne suka yi mishi, yana d'auke da Ammar a kafad'arshi, 

aka kaisu makwancinsu na gaskiya suka dawo, Ammar nata shashshekar kuka, dakyar Ummi ta lallab'a shi, 

tun da aka dawo daga kai Yaseer Ya Mu'allim ya shige d'akinshi ya kulle kanshi ciki, 

sai da lokacin sallar asuba yayi ya fito yaja jam'i ya kuma komawa ya rufe kanshi, 

dan kwata-kwata bai san yiwa kowa magana, ko abinci bai ci, Ammar kwana yayi da zazzab'i me zafi a jikinshi, 

ko bacci bayyi ba, haka bai ci komai ba, Ya Mu'allim bai fito daga d'aki ba sai da yaji ance Ammar bashi da lafiya, 

kana ya fito ya kira likita ya duba shi, aka bashi magani, bayan kwana bakwai da rasuwar Yaseer Tanya tace zata koma Kano, 

Ya Mu'allim yaso rik'e Ammar Tanya tace dashi zata tafi idan zasu dawo sadakar arba'in sai su taho masa da kayanshi gaba d'aya, 

badan Ya Mu'allim so ba, ya hak'ura dole, suka tafi, cike da zumud'i Tanya ta koma Kano, 

in banda da dare suka isa Kano da tun a ranar taso kiran Lawyer kan batun dunkiyar Sumayya da Yaseer, 

washe gari tun da sassafe ko breakfast bata yi ba, ta kira Lawyer a waya, ya sanar mata yana gida bai fito ba, 

idan ya fito zai biyo, kafin Lawyer ya fito daga gida Tanya ta kira shi a waya yafi a irga, tun yana picking wayar harya daina picking, 

yana harabar gidan ya ciro wayarshi a aljihu ya kira ta, jikinta na rawa ta d'aga wayar " ina waje!, Lawyer ya fad'a a tak'aice, 

bakin Tanya a washe tace " to shigo mana, bayyi magana ba yayi dropping call d'in, 

a parlour ya iske ta zaune, tana ganinshi ta washe baki had'i da cewa " zauna mana, ta fad'a tana nuna mishi d'aya daga cikin kujerun parlour'n, 

" meye na tsayawa ka kira waya kamar wani bak'o? 


"Daga yau idan kazo gidan nan ka daina tsayawa ka rink'a shigowa kanka tsaye kawai, kanshi ya shafa yana murmushi yace " ina kwana Hajiya? 


"Lafiya lau Alhamdulillah, bari a kawo maka breakfast, da sauri yace " a'a a k'oshe nake, ya fad'a kanshi k'asa, 

d'an shiru yayi yana sauraren abinda zata ce danya tabbatar akwai wani abu, " am dama kan maganar dunkiyar Alhaji ne da Sumayya yasa na kira ka, 

mamaki ne ya hana Lawyer yin magana, illa ido daya zuba mata, " tunda Allah yayi musu rasuwa shine nake san na had'a kan yaran da gaba d'aya dukiyar, 

Lawyer kasa b'oye mamakinshi yayi, ya kafe da ido deep down yana mamakin ace yau kwana takwas da mutuwar mutum, 

amma har an fara maganar abinda ya bari, take abubuwa da dama suka d'arsu a zuciyar Lawyer, 

" kina nufin rabon gado za'ayi tun yanzu? 


Yayi maganar yana karantar yanayinta, shiru Hajiya Tanya tayi dan kwata-kwata ita ta manta da maganar rabon gado, 

bama ta tab'a kawo shi cikin ranta ba, murmushin yak'e tayi had'i da cewa " a'a ai ba sai an raba gado ba, 

tun da gaba d'aya yaran nawa ne, nice mahaifiyarsu, " Ammar fa? 


Ya fad'a idonshi kanta, " am dama danaga bashi da kowa sai ni a fad'in duniya shiyasa nace haka, 

" to amma kin san baku da gadon Sumayya ko? 


"Duk duniya Ammar ne kad'ai me gadonta, tun da bincike ya nuna Yaseer ya rigata mutuwa da wajen awa d'aya, 

kinga tana da gado a cikin dukiyar Yaseer, haka gaba d'aya danginta babu me gadonta saboda kafiri baya gadon mumini, 

haka mumini baya gadon kafiri, cikin alamun rashin gaskiya Tanya tace " eh! na sani, dan haka nace ai a had'a gaba d'aya a bani na rik'e mishi a hannu na, 

d'an guntun murmushi Lawyer yayi yace " ke kin san yawan abinda Sumayya ta bari kuwa? 


Ya fad'a yana karantarta, cikin zak'uwa Tanya ta gyara zama had'i da cewa " bari kai dai, naji labari, 

jin abinda ta fad'a ya tabbatarwa Lawyer akwai wani abu a k'asa, dan haka ya shiryawa maganinta, 

yace " wallahi idan za'a had'a bajet d'in Nigeria na shekara 50 bazai kai rabin abinda Sumayya ta bari ba, 

rud'ewa ce ta sanya Tanya mik'ewa tsaye tayi duru-duru kana ta koma ta zauna, tace " to yanzu ya za'ayi? 


D'an jimm! Lawyer yayi kafin yace " gaskiya akwai matsala?


A d'an tsorace tace " wacce irin matsala kuma? 


"Kin san k'asar waje ba kamar nan bane, suna da dokoki hakan yasa baza'a tab'a bawa Ammar gadon Sumayya ba har sayya kai 25yrs, 

idan kuma ya mutu ko wani abun ya same shi sun san babu me gadonshi sai su zuba duniyar a baiyul mali, 

take gumi ya soma ketowa Tanya ta ko'ina, tayi sharkaf cikin k'ank'anin lokaci, tsantsar tashin hankali ya fito ya nuna k'arara akan fuskarta, 

" yanzu Lawyer babu wata mafita? 


"Gaskiya babu mafita, saboda Sumayya ta riga ta saka hannu a takardun komai nata akan sai Ammar yakai 25yrs zai mallaki komai nata, 

ko tana raye ko bata raye, haka shima Yaseer yasa hannu akan gadon Ammar akan a bar gadonshi a hannun hukuma, 

sayya kai 25yrs kafin a bashi, so yanzu koda an raba muku gado baza'a baki gadon Ammar ba, 

illa kawai za'a rink'a bada kud'in komai nashi duk wata, sakaka Tanya tayi tana kallan Lawyer har ya dasa aya, kana ta daki centre table d'in gabanta, 

tana huci ta mik'e tsaye tace " wallahi k'arya ne, kome za'ayi saina mallaki dunkiyar nan, 

duk shekarun dana d'auka ina....!, " ya isa haka Mama! Nayan yayi saurin katse ta yana shigowa parlour'n, 

" to meye a ciki Mama dan ance haka? 


Ya fad'a yana k'ifta mata ido, an karewa tayi da tana neman sakin layi dan haka ta k'ak'aro murmushin yak'e, 

tace " bakomai Allah ya raya mana su, Lawyer yayi shu'umin murmushi mai nuna cewa kar nake kallanki, 

yace " Hajiya su uku ne yaran Alhaji ko? 


"Nayan, Ammar sai Leenah ko? 


"Uhnn tace batare data kalleshi ba, zai kuma magana tace " kaje please zan kuma nemanka letter, 

dan Allah Allah Tanya take yi Lawyer ya fita, saboda ji take yi kamar tayi hauka, cikin nutsuwa ya mik'e fuskarshi d'auke murmushin gefen baki yace " sai anjima, ya fad'a yana ficewa daga parlour'n, 

" ina! wallahi ba'a isa ba, lalle ma ashe na kashe maciji ne ban sare kanshi ba, har yanzu da sauran aiki a gaba na, 

" dan Allah ki nutsu Mama yanzu fa in banda nazo da tuni kin saki layi gaban Lawyer nan, 

a zuciye Tanye ta d'auke Nayan da mari tana huci kamar kububuwa, idanuwanta sunyi jajir kamar gauta, 

tace " rufe min baki dan ubanka, kasan shekara nawa na d'auka ina tsara komai? 


"Kasan tsayin lokacin dana d'auka bana bacci ina neman mafita? 


"Idan baka sani ba ka sani shekaru tara 9 na b'ata ina jiran wannan lokacin, akan wannan damar na b'ata rayuwa ta, 

ta fad'a tana zaro ido kamar zasu fad'o k'asa, "amma Mama ai sai abi komai a hankali ko tunda anyi me wuyar, 

" inji ubanka yace anyi me wuyar? 


Ta fad'a kamar zata rufe shi da duka, " kana jin abinda wannan shegen Lawyer me kama da gwaggon biri ya fad'a, " ki bi komai a hankali Mama, 

kunnenshi ta rik'e kamar zata tsinke mishi kunnen tace " maganar trillions ake dan ubanka, ta fad'a da k'arfi cikin kunnenshi tamkar zata tarwatsa mishi dodon kunne, 

ta cigaba da cewa " ba k'ananan kud'i bane, mazajen kud'ad'e ne dole sai anyi amfani da nan ta fad'a tana nuna mishi kanta, 

" bada ka za'ayi komai ba, dole sai mun saka kwakwalwa da tunani, mun kuma lura da takun kowa, 

saboda a irin wannan harkar babu yadda dan ko kai kanka ban yarda dakai ba, " har ni fa kika ce Mama? 


"Eh! har kai, kai ba mutum bane, ni na haifeka idan kasha a nono na fa, nasan muddin jini na yana yawa a jikinka zaka iyayin komai dan biyan buk'atar ranka, 

kasan hausawa sunce makoyi yafi ma'iyi dole na kula dakai da duk wani takunka,

zayyi magana kukan Leenah ya katse shi, 

ta kalli inda jaririyar 'yarta 'yar wata uku take, da k'arfi ta runtse idonta tana jin tamkar ta shak'e Leenah ta huta,

tana dafe da kanta ta juyawa Leenah da Nayan baya tace " d'auke ta ku fita, " Mama baki ji kuka take yi ba? 


Jajayen idanuwanta kawai ta zuba mishi batare datayi magana ba, jikinshi na tsuma ya d'auki Leenah yayi waje, 

safa da marwa ta shigayi tana zagaye parlour'n, ganin kanta ya d'auki zafi da yawa ta rasa mafita yasa ta, 

kunna karan sigarinta ta zuk'a da k'arfi ta d'aga kanta sama ta furzar da hayak'in tana hura hanci, 

jin kukan Leenah yana neman k'ara mata zafi yasa ta kwalawa Nayan kira ta amshe ta bata nono, 

k'arfe sha biyu na rana Hajiya Tanya ta karkata d'aurin d'ankwallinta ta hau mota ta fice, 

duk wata kotu, da babban Lawyer dake garin Kano babu wanda Hajiya Tanya bata kaiwa ziyara ba a ranar, 

amma a banza amsar da Barrister Mukhtar ya bata haka kowanne Barrister yake bata, abinda Hajiya Tanya bata sani ba shine, 

tuni Barrister Mukhtar ya turawa America sak'o ta Gmail, ya tura musu diary da documents d'in Sumayya, 

wanda ta tabbatar da kada a bawa kowa dukiyarta sai Ammar shima sai ya kai 25yrs, 

haka duk kotun dataje yana biye da ita a baya, data fito Barrister Mukhtar yake zuwa yayi musu bayanin komai, 

ya shaida musu shine Lawyer mamacin ga kuma abinda mamacin yace, sai da Hajiya Tanya tayi kwana uku tana bin kotuna da Lawyers office amma a banza, 

dan duk inda taje maganar dai d'aya ce, shine bazayyiyu ba, dole ayi hak'uri sai yakai 25yrs, 

tana kishingid'e saman sofa ta tallafe kanta da duka hannayenta, 

idonnuwanta rufe, sai dai ba bacci take yi ba, bakinta d'auke da karan sigari, Nayan ya shigo, 

idonshi kanta yace " yadai Mama? 


Bata motsa ba, balle ta amsa mishi, ya kuma cewa " Mama ban karan sigarin nima na d'an busa, 

still banza tayi dashi, " Mama wai ya kuka yi da Lawyers da kike zuwa wajensu? 


Banza ta kuma yi mishi, " Mama kina ji ina yi miki magana amma ki....!, a k'ufule Tanya ta mik'e ta shak'i wuyan Nayan tana huci, 

" dan ubanka bana hana ka yi min magana idan ina cikin zafin kai ba? 


"Ko so kake tsohuwar kwayar data sha ta motsa a kanka?


"Ni sake ni! ya fad'a yana hankad'a ta baya, " Mama yunwa nake ji, Ammar yayi maganar cikin sanyi, 

a zafafe tace " nemo wuk'a ka yanki naman jiki na kaci dan uwarka, ta fad'a kamar zata yagi naman jikinshi, 

" Mama zanci abinci, Ammar ya kuma fad'a dan bai gane abinda take nufi ba, a zuciye ta sanya k'afa ta hank'a shi ya kif'a, 

kanshi ya fashe, 

kukan daya saka ne ya sanya Leenah tsindara kuka itama, gashin kanta ta shiga yamutsawa tamkar mahaukaciya, 

ta kalli Leenah dake kwance cikin gadonta, tace " Nayan mik'o min ita, " idan bazaki d'auke ta ba ki barta ta mutu, 

tsoki taja had'i da mik'ewa ta d'auki Leenah ta saka mata nono a baki, 

ganin irin kallan da Ammar keyi mata yasa ta kallan Nayan tace " dan Allah d'auke min wancan tsohon mayen karya cinye mu, 

da k'afa Nayan ya rink'a haurin Ammar, ya tura shi d'aki ya rufe.


Bayan anyi sadakar arba'in da kwana uku Ya Mu'allim da Saratu suka tafi Kano ganin tunda su Tanya suka tafi basu k'ara ji daga gare su ba, ko waya babu, 

sai da suka biya Singa suka siyi kayan abinci me yawa, har da kayan shayi, kwai, dankalin turawa da indomie, 

sannan suka nufi gidan, kasancewar Madu me gadi gidan yasan Ya Mu'allim farin sani, 

yasa ya bud'e mishi get suka shiga, tun daga harabar gidan suka fara jiyo kukan Ammar, 

da sauri Saratu ta shiga parlour'n, ta iske Hajiya Tanya zaune saman kujera tana rungume da Leenah, 

yayinda Nayan ke zaune yana shan fruits salad, ya d'ora k'afarshi gadan bayan Ammar, 

jikin Saratu a sanyaye tayi sallama, fuska Hajiya Tanya ta yamutsa had'i da amsawa a dak'ile, 

d'an d'osanawa Saratu tayi ta zauna saman kujera, tana bin k'afar Nayan daya d'orawa Ammar da kallo, 

cikin kuka Ammar yace " Ummi ki bani abinci yunwa nake ji, da k'arfi Tanya ta zuba masa uban rankwashi a aka, 

tana cewa " kaji bak'in munafuki, wai kai ma harka iya kitumurmura, 

k'ok'arin mayar da hawayen dake san zubo mata Saratu tayi, cikin sanyin jiki tasa hannu ta d'ago Ammar, ta zaunar dashi kusa da ita, 

" tare muke da Ya Mu'allim, Saratu ta fad'a tana gogewa Ammar jiki, baki Tanya ta tab'e kana tace ya shigo mana, 

Saratu na d'auke da Ammar ta fita tayiwa Ya Mu'allim iso suka shigo tare, 

" ina yini? 


Ya Mu'allim ya fad'a bayan ya zauna yana binta da kallo, " lafiya! tace tana jefa mishi walak'antaccen kallo, 

" na ganku shiru shine nazo naga lafiya, " to! aika zo ka gani kana iya tafiya, tayi maganar tana tab'a baki kamar taga kashi,

murmushi Ya Mu'allim yayi dan bayyi mamakin abinda Tanya tayi ba, zayyi magana Ammar yace " dan Allah Baba Malam ka bani abinci inci yunwa nake ji, 

jiki a sanyaye yace muje na siya maka abinci kaji, ya fad'a yana mik'ewa, saurin mik'ewa Tanya tayi ta sha gabanshi, 

tare da cewa " wallahi ko k'ofar parlour'n nan bazaka fita dashi ba, tsohon munafuki kawai, ko an fad'a maka ban san abinda kake nufi ba? 


"Nasan gado kake yiwa, kuma wallahi kwandala bazaka ganta ba balle ka ci, cike da mamaki Saratu tace " Hajiya Tanya ke....! 

saurin d'aga mata hannu Ya Mu'allim yayi wanda yasa ta kame bakinta, 

tsoro yasa Ammar ya damk'e Ya Mu'allim k'em had'i da basa kuka yana cewa " dan Allah Baba Malam ka tafi da ni Zamfara karka barni anan, 

" oh! kaji min da munafurci shege annamimi, ta fad'a tana finciko shi,

kamar Ya Mu'allim zayyi magana sai kuma ya fasa, ya fice daga parlour'n Saratu ta bishi tana cewa " Malam yanzu haka zaka bar yaron nan? 


Bayyi mata magana ba ya isa gaban Madu me gadi, ya mik'a mishi hannu sukayi musabaha, Ya Mu'allim yace " anan BQ kake da zama kai da matarka Hajara ko? 


"Eh! Madu yace cikin girmamawa, hannu Ya Mu'allim ya saka cikin aljihu ya ciro rafar 'yan d'ari biyar-biyar ta dubu hamsim ya mik'a mishi, 

yace " ga wannan ka rik'e a hannunka, duk abinda Ammar yake so ka rink'a siya mishi komai tsadar shi, 

ga kayan abinci nan zan aje muku babu abinda babu dan Allah ka rink'a fakar idon Tanya kana bawa Ammar abinci dan girman Allah ka dubi maraicinshi, 

murmushi Madu yayi had'i da maidawa da Ya Mu'allim kud'in daya bashi yace " wallahi koda zan k'arar da rayuwa ta wajen kula da Ammar zanyi hakan, 

kuma koda gaba d'aya abinda na mallaka zai k'are zanyi, idan dan kula da Ammar ne karka damu in sha Allah zan rad'a mishi duk sanda yake jin yunwa yazo zan bashi abinci, 

ya k'arasa maganar hawaye na gangaro mishi, murmushin jin dad'i Ya Mu'allim yayi yana goge hawayen kan fuskarshi, 

yace " nagode nagode sosai Madu Allah ya saka maka da alkhairi, Madu ya amsa da "Amin, ai Alhaji yayi mana komai, ya bamu ci ya bamu sha ya bamu wajen zama, 

babu abinda zanyi na mayar mishi da abinda yayi min, 

_(take note amfanin kyautatawa mutane kenan dan baka san me gobe zata haifar ba, baka san waye me jin k'anka ba, shi alkhairi dank'o ne bashi fad'uwa k'asa banza, haka sharri d'an aike ne, duk nisan da yayi sayya dawowa me shi, dan haka mu rink'a kyautatawa na k'asa damu, muna tausaya musu dan Allah ya tausaya mana muma)_

k'ara mik'awa Madu kud'in Ya Mu'allim yayi yana murmushi while hawaye na zubo masa, 

yace " bakomai ka karb'a kuma duk abinda kuke so kayi min magana, Madu bayyi musu ya sanya hannu biyu ya amsa had'i dayi mishi godiya, 

tare suka sauke kayan abinci suka kaisu BQ, kana Ya Mu'allim yayi mishi sallama ya tafi. 


Tun da Ya Mu'allim ya koma Zamfara hankalinshi yak'i kwanciya kwata-kwata, ya kasa zaune ko tsaye, 

abun duniya ya taru yayi mishi yawa, ga rashin d'an uwanshi kuma amininshi na rai da rai, ga halin da marayan Allah Ammar yake ciki, 

duk yabi ya rame ya lalace kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana cikin mawuyacin hali, ya zabge gaba d'aya kamar wanda ya shekara yana rashin lafiya, 

ajiyar zuciya ya sauke a hankali had'i da gyara kwanciyarshi, "meya hanaka bacci? 


Ya Mu'allim yaji muryar Saratu ta katse mishi tunani, bayyi niyyar b'oye mata komai ba dan yasan tasan halin dayake ciki, 

sai da ya furzar da iska daga bakinshi kana yace " halin da Ammar yake ciki, 

cike da tausayawa tace " kayi hak'uri Malam komai yana da iyaka a rayuwa, in sha Allah wata rana sai labari, 

" haka ne Saratu amma yanzu ina ji ina gani haka zan bar Ammar a wahala bayan ina da halin taimakonshi? 


Yayi maganar hawayen bak'in ciki na zubowa daga idonshi, " kayi hak'uri Malam, Allah ya sani bamu da yadda zamu yi,

iyakaci muyi tayi mishi addu'a, bai kuma magana ba ya juya mata baya, cikin ranshi ya k'udurce gobe sammakon tafiya Kano zayyi ya gano Ammar, 

k'arfe biyu na rana Ya Mu'allim ya isa gidan, ana shek'a ruwan sama, kamar da bakin kwarya, 

yana danna kan motarshi harabar gidan ya hangi Ammar rakub'e jikin bango ruwan sama yana dukanshi, 

a kid'ime yayi parking ya fito bai ko tsaya rufe motar ba, cikin tashin hankali ya tallafe shi a jikinshi, 

a galabaice Ammar ya kalli Ya Mu'allim, 

had'i da yin murmushi yace " Baba Malam mutuwa........! bai k'arasa ba idonuwanshi suka kakkafe, 

numfashinshi ya d'auke jikinshi ya saki.........!


KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE IYA KUD'INKI IYA SHAGALINKI...! 


MOMYN ZARAH