SAKI RESHE..

4

by @hauwaausmanjiddarh

SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


_Masu buk'atar complete littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_


Free page


4️⃣


Cikin sand'a ya bud'e fridge ya d'auko robar ruwan faro mai sanyi da k'ank'ara ya dawo falon inda Ammar ke takure yana bacci,

cike da tsantsar mugunta Nayan ya b'alle robar ruwan ya tuttulewa Ammar ruwan a wandanshi,

a dai-dai hantsarshi idan ka gani saika rantse da Allah fitsarin kwance yayi, firgigit Ammar ya farka a rud'e saboda sanyi,

yana sauke ajiyar zuciya, d'an basarwa Nayan yayi yadda kasan bashi ne ya zubawa Ammar ruwan ba,

" fitsarin kwance kayiwa Momy a parlour!?


Nayan ya fad'a yana zaro ido, a d'arare Ammar yace " a'a ba fitsarin kwance nayi ba kai ne ka zuba min ruwa,

tauuu! Nayan ya d'auke Ammar da mari yana huci yace " ni zakayiwa sharri dan ubanka?


Azabar marin tasa Ammar gigicewa ya fashe da kuka tare da tallafe kuncinshi da duka hannayenshi,

da k'arfi Nayan ya shiga kwallawa Hajiya Tanya kira, yana fad'in " Momy fito Ammar yayi miki fitsari a parlour,

a gigice Hajiya Tanya ta fito saboda yadda Nayan ke kwala mata kira ya rud'a ta,

" wacce jarabar ke faruwa da asubar fari?


Ta tambaya tana k'arasa zura hannun rigarta, " kinga wannan tsohon munafukin yayi miki fitsarin kwance a parlour,

shine dan rainin hankali zayyi min sharri wai ni na zuba mishi...! bata bari Nayan ya k'arasa ba ta zumduma ashar had'i da janyo Ammar a zuciye tamkar zata karya shi,

" fitsari kayi min dan kan uwarka?


Zayyi magana ta kifa mishi mari gami da hankad'a shi, tace " yau saika gane kuranka, saika gane shayi daga ruwa bai kau ba, 

cikin matsanancin kuka Ammar yace " wallahi Yaya ne ya zuba min ruwa..., a zuciye Nayan yayi ball da Ammar yana gwara kanshi da bango,

" ni zakayiwa sharri dan uwarka?


"A gidan uban wa na zuba maka ruwan?


Zayyi magana Hajiya Tanya tace " au ana fad'a kana fad'a shege d'an iska marar kunya, tanbad'ad'd'e?


Sai da Nayan ya gaji da dukan Ammar kana Hajiya Tanya ta kama hannunshi taja zuwa bathroom,

cikin bak'ar mugunta ta sakar mishi shower aka, ruwan sanyin na zuba jikinshi ya bud'e baki da niyyar kwalla k'ara,

Hajiya Tanya tayi saurin gwab'e mishi baki, tana cewa " had'iye shi, had'iye kukan dan bura ubanka, tsoro ya sanya Ammar yin shiru dole duk da bak'ar azabar dayake sha,

saboda jikinshi duk ya fashe dan ba k'aramin duka Nayan yayi mishi ba, ga muku-mukun sanyin da ake yi,

" ka tsaya a haka tsirara ruwan sanyin nan yana zuba a kanka idan ka sake ka fita koka matsa daga bakin shower nan sai na lahira ya fika jin dad'i,

azaba ce ta hana Ammar yin magana, hak'oransa nata karafniya kaf-kaf, yayinda jikinshi ke mazari kamar wanda ake kad'awa gangi,

" zo nan! Hajiya Tanya ta fad'a tana isa parlour'n, Nayan dake k'ok'arin shigewa bedroom d'inshi yana dariyar mugunta,

ya juyo yana kallanta shek'ek'e batare dayace mata komai ba,

" nace kazo ko!?


"Me ye!?


Nayan ya fad'a batare daya kalleta ba, fashewa Hajiya Tanya tayi da shu'umar dariya tana cewa " shege bak'in mugu, 

ai dama barewa batayi gudu d'anta yayi rarrafe ba, 

ko ba'a fad'a ba nasan kai jini na ne, kuma muddin jinina yana yawo a jikinka ba mamaki dan kayi abinda yafi haka,

cikin rashin fahimta Nayan yace " dalla kiyi maganarki kai tsaye , " dan ubanka nasan ruwa ka zubawa yaron nan nasan bayyi fitsarin kwance ba,

guntuwar dariya Nayan yayi yana shafa hab'arshi batare da yayi magana ba, 

Hajiya Tanya ta shafa kanshi tana murmushi tace " good boy, jeka kwanta Allah ya tashe mu lafiya,

bayyi magana ba yayi shigewarshi bedroom, itama ta d'auki Leenah ta shige bedroom, while Ammar nacan bathroom ruwan sanyi na sauka kanshi.


Hajiya Tanya da Nayan basu futo parlour ba sai k'arfe d'aya na rana, suna zaune saman dinning table,

Hajara ta fito daga kitchen ta tsaya gefensu kad'an kanta k'asa, d'an kallan juna Hajiya Tanya da Nayan sukayi kafin Hajiya tace " ke! lafiyarki?


Cikin fad'uwar gaba da rawar murya Hajara tace " am....! am... da...ma Ammar ....! ne ban gani ba,

tayi maganar a rarrabe, sai lokacin Hajiya Tanya da Nayan suka tuna da Ammar, 

kauda kai gefe Hajiya Tanya tayi ta cigaba da cin abincinta, kamar bazatayi magana ba, kafin tace " ki duba bathroom....!,

jikin Hajara na b'ari ta nufi bathroom, salatin Hajara da suka jiyo ne ya tabbatar musu da wani abu ya faru,

amma basuyi ko gezau ba, Hajara na d'auke da Ammar ta fito parlour'n tana cewa " ya mutu!, babu wanda ya d'ago kai ya kalle ta a cikinsu balle tasa ran samun taimako daga gare su,

" Hajiya Ammar fa ya mutu! Hajara ta kuma fad'a cikin kuka,

cikin masifa Hajiya Tanya tace " to sai me idan ya mutu?


"Kwananshi ne suka k'are, kuje kuyi mishi sutura, ta fad'a batare data kallin inda Hajara ke tsaye ba,

da sauri Hajara ta nufi k'ofar fita, " idan kin fita kija mana k'ofar, Nayan ya fad'a a tak'aice, 

tun daga harabar gidan Hajara ta soma kwalawa Madu kira cikin tashin hankali, 

a matuk'ar kid'ime Madu ya tare ta jikinshi na rawa, yana tafiyarta lafiya, " Malam Ammar ya mutu! ,

Hajara ta fad'a cikin matsanancin kuka, ba Madu kad'ai ba, hatta drivers, me wanki da guga da sauran ma'aikatan gidan sun kad'u,

lokaci d'aya suka yi kan Hajara, jiki na rawa suka k'arb'i Ammar,

a hankali Madu ya kara kunnenshi a k'irjin Ammar, jin zuciyarshi na bugawa yasa shi saurin d'agowa, yace " bai mutu ba, idan muka gaggauta kaishi asibiti za'a iya ceton rayuwarshi,

ai bai k'arasa ba, Hajara ta zari Ammar ta sab'ashi a baya tayi waje, Madu na kwala mata kira bata ko juyo ba,

jikin Madu na tsuma ya ciro waya ya sanar da Ya Mu'allim abinda ke faruwa saboda tsoran abinda ka iya zuwa ya komo,

sosai hankalin ya Mu'allim ya tashi ya kasa zaune ko tsaye, a ranar suka taho Kano shida Saratu,

a asubiti kuwa ba k'aramin fad'a likita yayiwa Hajara ba, ganin yadda Ammar yayi masifar jigata, ga sanyi ya kamashi sosai, 

dole aka kwantar dasu, da magariba Ya Mu'allim suka k'araso garin Kano, direct gidan ya nufa,

yayi parking a d'an nesa, kana ya kira Madu a waya ya sanar dashi sun k'araso, " dan Allah Malam Audu ka kular min da k'ofa,

zan raka Ya Mu'allim asibiti, Madu ya fad'a cikin rok'o, " to! to! ba damuwa kaje zan kular maka da ita in sha Allah, ka duba shi, 

Hajara na zaune Madu da Ya Mu'allim suka shigo, Saratu na biye dasu a baya, cike da tausayawa Saratu da Ya Mu'allim suka k'arasa bakin gadon da Ammar ke kwance,

Ya Mu'allim ya shafa kanshi cike da tausayin yaron, yana k'ok'arin mayar da kwallar dake k'ok'arin zubo mishi,

Saratu tace " meya faru Hajara?


Saida Hajara ta sauke ajiyar zuciya kafin ta basu labarin abinda ta sani, Ya Mu'allim ya girgiza kanshi had'i da cewa " bakomai akwai Allah, 

yana ji yana kuma gani!, yana rufe bakinshi Doctor ya shigo, yadda yayiwa Hajara fad'a haka yayiwa Ya Mu'allim dan a zatonshi shine mahaifin Ammar,

shiko Ya Mu'allim hak'uri kawai yake bawa likitan, kana yace " ina so nayi transferring d'inshi zuwa Hilal Hosptal,

Likitan ya d'anyi jim kana yace " ok ba damuwa, a ranar aka mayar da Ammar Hilal Hospital one the best hospital in Zamfara state,

dakyar Hajara ta koma gidan dan cewa tayi wllh daga ita har Madu sun bar aiki a gidan, sai dakyar Ya Mu'allim ya rarrasheta,

" kada kice haka Malama Hajara, ki tuna Ammar, ki tuna halin da zai shiga idan akace baku nan, yau inda ace baku nan ke kanki kin san komai yana iya faruwa,

ku kwatanta rayuwar Ammar ace baku gidan nan, Hajara kuna nan d'in ma ya aka k'are bare baku nan, wajenku kad'ai yaron nan ke samun salama a rayuwarshi,

dan Allah kuyi hak'uri ku zauna kodan shi, a hankali Hajara ta sauke ajiyar zuciya kana tace " ai dama koda zamu bar gidan niyyata mu tafi shi, 

Ya Mu'allim yace " hmmmm kina ganin Hajiya Tanya zata barku ku tafi dashi ne?


" Kina gani ni kai na ta hana ni koda rab'arshi dan kar yaji dad'i, akan idonki fa komai ya faru, " shikenan bakomai Malam in sha Allah zamu zauna dan Ammar kawai,

Ya Mu'allim yayi murmushin jin dad'i, zayyi magana Ammar ya farka, idonshi ya sauka akan Ya Mu'allim,

murmushi ya saki yana k'ok'arin mik'ewa yace " Baba Malam kai ne kazo waje na!?


Fuskar Ya Mu'allim d'auke da murmushi ya tallafe Ammar yana cewa " eh! nine Ammar, " ina Basmah ta!?


Ammar ya fad'a idonshi kan Ya Mu'allim,

" ka ganta nan! sarkin kuka da k'iriniya bata ji, bata da aiki sai b'arna, baki ya turo yana cewa " amma dai baki dukar min ita ko Umma?


"Duka kai! ta fad'a cikin wasa, cikin shagwab'a ya kwab'e fuska zayyi kuka yana cewa " ni dai kar'a k'ara dukarmin ita,

a rink'a lissafa duk abinda ta lalata idan na girma na fara aiki zan biya duka amma kar'a k'ara tab'a ta,

a barta ta fasa koma meye ni zan biya, " Allah yabar soyayyar nan har girmanku, Ubangiji yasa itama ta so ka kamar yadda kake santa,

Allah yasa kada ka canja ra'ayi idan ka girma, Ya Mu'allim yayi maganar yana murmushi had'i da shafa kan Ammar,

" Allah bazan tab'a canja ra'ayi ba, kuma nayi maka alk'awarin zan so Basmah har k'arshen rayuwata,

bazan tab'a k'inta ba a kowanne irin hali, zan sota da gaba d'aya zuciya ta, zan sota da rai da rayuwata, 

zan mallaka mata ruhi da gangar jiki na, da duk abinda na mallaka, kuma zan aure ta, gaba d'aya wajen kowa yayi shiru saboda mamakin kalaman Ammar,

ya cigaba da cewa " to kai ma kayi min alk'awarin zaka bani ita, bazaka tab'a raba mu ba, " in sha Allah, Ya Mu'allim yace yana shafa kan Ammar, " a'a nidai ba in sha Allah ba, kace kayi min alk'awari, gaba d'ayansu suka saka dariya,

Ya Mu'allim yace " to inbanda abinka Ammar in sha Allahu ai itace dai-dai, cikin shagwab'a Ammar ya sanya kuka yana cewa " a'a ni dai kace min ka bani ita,

" na nawa kuma Ammar?


"Halan ka manta na fad'a a gabanka Yasir da Sumayya, " eh to naji yanzu ma ka k'ara fad'a naji,

Ya Mu'allim na murmushi ya kama hannun Ammar ya d'ora mishi Basmah yace " gata nan na baka ita duniya da lahira,

ga Saratu nan ta zama sheda kona mutu Basmah bata da mijin daya wuce Ammar,

Ammar ya k'ank'ame Basmah yana yi mata wasa cike da kuruciya yace " zaki zaure ni?


Kamar tasan abinda yace ta saka mishi dariya, yace " ta yarda Baba Malam, " ba dole ta yarda ba wacece zataga santalelen farin d'ana tace bata sanshi, duk suka saka dariya,

sai da Ammar yayi kwana biyar a asibi kana aka sallame su, tuni Hajara ta koma gida bakin aikinta, Saratu ta cigaba da jinyarshi, 

ko bacci Ammar zayyi yana rungume da Basmah, idan za'ayi mishi allura ya fara kuka sai Saratu tace " idan kayi kuka Basmah ma zatayi,

dole zai shanye kukan, duk wannan tsayin kwanakin Hajiya Tanya bata tambayi Haraja Ammar ba, bama tasan yana raye koya mutu ba,

tunda suka fito daga asibitin Ammar ya fara kuka yana k'ank'ame Basmah da Ya Mu'allim yana cewa " dan Allah karka mayar dani gida wajen Momy,

sosai Ya Mu'allim ya rarrasheshi, ya lallab'a shi kana ya mayar dashi gidan bayan ya biya dashi shopping yayi mishi siyayya,

jiki a sanyaye Ammar yace " idan munyi hutu zaka zo ka kaini wajen Basmah?


"In sha Allah, kai dai ka dage da karatu kaji, kada ka bari wahala ko bak'in ciki da damuwa su hanaka karatu, 

idan kana karatu zan baka duk abinda kake so, kaga idan bakayi karatu ba Basmah ma cewa zatayi a'a bata sanka,

da sauri ya zaro ido yace " aiko zan dage nayi karatu sosai saboda Basmah ta so ni,

Ya Mu'allim yace " yauwa good boy, kwab'e fuska Ammar yayi yace " na manta ban fad'a maka ba, an kore ni daga makaranta amma Baba ya saka ni a wata,

cikin rashin fahimta Ya Mu'allim yace " ban gane an kore ka daga makaranta ba?


"Eh! wai bana biyan school fees shine suka ce karna k'ara zuwa, kallan tuhuma Ya Mu'allim yayiwa Madu yace " amma saboda Allah shine baka fad'a min ba Madu?


"Yi hak'uri Ya Mu'allim, naga kana hidima sosai damu ne shiyasa ban fad'a maka ba, gudun kar mu takukura ka,

" duk da Ya Mu'allim mutum ne mai sanyin rai dan baya fushi kwata-kwata sai da yanayin fuskarshi ya canja,

yace " wallahi koda zan k'arar da gaba d'aya abinda na mallaka akan Ammar zan k'arar dashi batare da nayi danasani ba,

zan iya bada raina da rayuwa ta fansa akan jinin aminina kuma d'an uwana Yasir, ko a wuta ake nemowa zan nemo nayiwa Ammar,

ido Ammar ya kafe Ya Mu'allim dashi yana kallanshi deep down yana jin wani irin abu daya kasa fahimtar komenene, 

haka duk da kasancewar Ammar yaro ya k'ara ganin girma da martabar Ya Mu'allim, " ku koma cikin motar muje makarantar tunda naga da sauran lokaci,

ya fad'a yana kallan agogon hannunshi while yana shiga motar,

school fees d'in 5yrs Ya Mu'allim ya biyawa Ammar da Nashwan, ya bada number wayarshi akan kome ya taso kar'a nemi kowa a nemeshi, 

sosai Madu ya rink'a zubawa Ya Mu'allim godiya, yana kwarara masa addu'a, 

sai da suka gama duk abinda ya kamata kana ya mayar dasu gida,

bayan kwana biyu da sallamo Ammar daga asibiti suka cigaba da zuwa makaranta shida Nashwan,

bak'aramin mamakin Nayan yayi ba ganin Nashwan a makarantarsu, ana tasowa da saurinshi ya shiga gida ya iske Hajiya Tanya a parlour,

" ubanwa ya saka Nashwan a makarantar mu?


Nayan ya fad'a yana tsaye kan Hajiya Tanya k'erere, " Nashwan kuma?


"Eh! yace yana huci, " a makarantarta ku?


Hajiya Tanya ta fad'a cike da mamaki, "eh! naga Ammar ma ya koma karantar, ko ubanwa ya biya musu?


Hajiya Tanta tace " oho ni ina zan sani sai dai ka kira shi ka tambaye shi, fita Nayan yayi kiran Ammar yana cewa " wallahi bazata sab'uba ace makarantar danake yi ita d'an me gadinmu da me aikinmu ke yi,

sai dai na dena zuwa makarantar, kusa da Madu ya iske Ammar da Nashwan suna hira ,

ya kwala musu kira " kai! kuzo nan, ya fad'a yana juyawa, jiki na kerrma suka bi bayanshi zuwa parlour, a tare suka zube gabansu,

sun dad'e kafin Hajiya Tanya tace " kai ubanwa ya biya muku kud'in makaranta?


Bakin Ammar na rawa ya fad'a mata duk abinda ya faru, "tsinanne tsohon najadu dama nasan babu meyin wannan mak'ark'ashiyar sai wannan tsohon munafukin,

wai gashi na Allah, wallahi idan be kiyaye ni ba, saina k'ulla mishi k'ulalliya, na saka shi a tsakiyar ruwan da bazai iya fitowa ba,

" na rasa meyasa wannan mutumin baya k'aunarmu, ko ince baya k'aunarki, tun Dad yana raye yafi san me jan kunne, (sumayya babar Ammar),

shiyasa wallahi nima na tsaneshi bana ko san ganinshi shege me gemun d'an taure, ya k'arasa maganar yana furzar da iske,

kana ya mayar da kallanshi gasu Ammar dake durk'ushe gabansu yace " ku kum......! dakatar dashi Hajiya Tanya tayi tana murmushi tace,

" kai in banda abinka meye abin damuwa Allah ya kai maka nama, Ubangiji yana nufinka da hutu kana tada jijiyoyin wuya,

kallanta yayi ido cikin ido na d'an tsayin lokaci kafin ya gane abinda take nufi, tana nufin ya musguna musu a makarantar ya hana su sakewa, yayi murmushin mugunta,

had'i da cewa " an gama ma, suka saki murmushi a tare, wayarta dake ringing ta d'auka had'i da cewa " to jarababbiya yanzu zan shirya,

ta fad'a tana dariya, d'an shiru tayi kafin tace " yanzu fa zan shirya, "to to!, ta fad'a tana kashe wayar, ta kalli Nayan tace " ka kaiwa me guga rigar anko na ya goge min?


"Tab! wallahi na manta, a hasale ta kai mishi duka tana surfa mishi ashar, " dan bura ubanka yanzu me zan saka naje bikin ga mutane na jira na?


Ya goce yana cewa " oho ke kika sani, ki bawa Ammar ya goge miki mana, dukan ta k'ara kai mishi tana fad'in " shege d'an iska tambad'add'e tsinanne mara albarka, 

" tambad'add'u dai ya fad'a yana mik'ewa, bata kula shi ba, ta shiga bedroom d'inta ta d'auko rigar ta jefawa Ammar tana cewa " kayi sauri ka goge min, kafin na gama shiryawa,

saura kuma ka k'ona, ta fad'a tana shigewa, Ammar ya d'auki rigar yana kallan Nashwan yace " ka iya guga Brother?


Jiki a sanyaye Nashwan yace " a'a sai dai muje mu tambayo Umma ko Baba, a tare suka mik'e suka fita suka bar rigar anan,

Nayan na ganin sun fita ya fito daga bedroom d'inshi da sauri ya d'auki rigar, ya nufi inda ake guga, 

da sauri ya juna dutsen guga, ya d'ora a jikin rigar yayi saurin barin wajen, tare Hajara dasu Ammar suka shigo,

ganin ba rigar yasa Ammar kallan Nashwan yace " ina rigar?


"Nima ban ganta ba, cike da tsoro Hajara ta zaro ido tana cewa " ina kuka kai mata rigar?


"Anan muka barta!, zatayi magana ta jiyo k'auri da sauri ta nufi wajen data jiyo k'aurin, suka bi bayanta,

a zabure Hajara ta dafe k'irji had'i da cewa " mun shiga uku ni Hajara, yau ina zamu saka kan mu?


Ta fad'a tana d'ogo rigar, ganin gaba d'aya gaban rigar ya k'one ba k'aramin d'agawa Hajara hankali yayi ba,

a matuk'ar tsorace Nashwan yace " wallahi bamu muka juna ba, can muka barta, ya fad'a yana nuna parlour,

Hajara na shirin yin magana suka jiyo muryar Hajiya Tanya na cewa " kai! mik'o min rigata, ta fad'a tana k'arasawa wajen,

" baka ji me nace maka bane ko sai.......! sark'e mata maganar tayi ganin rigarta rik'e a hannun Hajara,

da sauri ta fisge rigar daga hannun Hajara tana dubawa, " kam! bura uba! rigar da zan saka na fita ka k'ona min?


Zayyi magana ta kifa mishi mari tana cewa " dan durin uwarka ni sa'arka ce da ina fad'a kana fad'a?


"Idan ka k'ara yin magana ina yin magana saina karya ka, cikin bak'in ciki ta kalli Hajara tace " waye ya k'ona min rigata a cikinku?


"Sabuwar rigar ankon bikin da zani ce fa, ga mutane har sun zo d'aukana suna waje suna jira na, inbanda rawa babu abinda jikin Hajara keyi,

tsoro ya hanata yin magana, yayinda Hajiya Tanya ta rink'a zuba ruwan bala'i tana zazzaga tujara,

" waye a cikinku ya k'ona min riga ta kuma fad'a a hasale?


still babu wanda yayi magana, " dan kutumar ubanka baka ji na ina tambayarka bane? " nace uban waye ya k'ona min kaya?


Tsoron gargad'in datayi mishi yanzu na idan tana magana karya k'ara yin magana yasa shi yin shiru, "baka ji na dan uwarka?


" wall....ahi.... ban..... san....wa...n..da...ya k'ona....ba, yayi maganar a rarrabe, " au bama kasan wanda ya k'ona ba?


"Yanzu zaka tuna wanda ya k'ona, ta fad'a tana nufar dutsen gugan da har lokacin a june yake, batare da tayi tunanin komai ba,

ta d'auki dutsan gugan ta mannawa Ammar a gadon bayanshi, tsananin tsoro ne yasa Nashwan zubewa k'asa sumamme,

yayinda Nayan yayi saurin fitowa daga inda yake lab'e dan bai tab'a tsammanin rashin imanin mahaifiyarshi yakai haka ba,

Hajara kam saboda tsabar rud'ewa bata san sanda ta d'ora hannu aka tana kurma ihuu da kururuwa ba,

" wayyo mun shiga uku, kin kasheshi kin huta, wannan wanne irin rashin imani ne?


Hajiya Tanya bata bi takan Hajara ba, ta sanya k'afa ta tsallake Ammar da Nashwan dake zube sume a k'asa ta barsu a wajan,

Nayan yabi bayanta da kallo cikin ranshi yana jinjina rashin imaninta, dakyar Hajara ta saita kanta, ta fita ta kira Madu,

suka kwashe su zuwa asibiti,

tun a cikin adai-daita sahu Madu ya sanar Ya Mu'allim abinda ke faruwa, hankalin Ya Mu'allim a tashe suka d'au hanyar Kano, 

sai da Ammar yayi sati d'aya cif bai san inda kanshi yake ba, kafin ya farfad'o, bayanshi ya k'one sosai, yayi rami ya rure, 

k'onuwar ta tashi, kullum sai an wanke wajen, 

wuya kam ta duniya Ammar ya sha ta, in banda taimakon Allah da addu'o'in da Ya Mu'allim keyi dare da rana da wajen so yayi ya rub'e,

dan harya fara wari yana fitar da ruwan mugunya, Ammar yasha wuhala sosai, ya rame ya k'arasa figewa, sai da sukayi wata biyar kana ya warke sumul,

ko sau d'aya Hajiya Tanya bata zo asibitin ba, asalima bata san inda yake ba, Ya Mu'allim ya kalli Saratu da Madu da Hajara yace " to an bamu sallama,

kuma da Ammar nake san tafiya, dan a halin yanzu a shirye nake da duk wata tijarar Hajiya Tanya, 

a kotu zan maka ta wllh, bata ci banza ba, sai an biwa yaron nan hakk'inshi, kafin kowa yayi magana Ammar dake rik'e da hannun Basmah,

yace " a'a ka barni na koma gida, in sha Allah babu abinda zai faru, zan iya jurewa duk wata wahalar da zata bani,

wuya bata kisa sai kwana ya k'are, kuma koba komai tana horar dani sanin rayuwa ne, wallahi ko zata dafa nama na ta cinye ta shanye ruwan, ta rink'a yankan naman jiki na bazan bar gidan nan ba,

sai dai gawa ta, tabar gidan,

babu yadda Ya Mu'allim bayyi da Ammar akan su tafi Zamfara ba, amma yak'i, dole Ya Mu'allim ya hak'ura ya barshi,

to haka rayuwa taita tafiya da dad'i ba dad'i, gida ba hutu makaranta ba hutu, dan Nayan da abokanshi babu irin azabar da basa ganawa Nashwan da Ammar a makaranta,

idan sun dawo gida ma ba hutu su had'u da Hajiya Tanya suna bashi wahala, yana da shekaru goma sha uku, gaba d'aya aikin gidan ya koma kanshi, 

wanki, goga, driven, bawa fulawowi ruwa, da sharar harabar gidan, duk inda Hajiya Tanya da Nayan zasu je Ammar ko Nashwan ke kaisu, su suka koma leburorin gidan, 

sun koma musu tamkar bayi, daga b'angare d'aya kuma Ya Mu'allim ke cigaba da d'aukar d'awainiyyarsu, 

shike yi musu komai na rayuwa, ci, sha, kud'in makaranta da kayan sawa, su Ammar na SS3 Basmah na Primary 6,

kasancewar Ammar da Nashwan nada k'ok'ari sosai yasa aka zab'e su cikin wad'anda zasu zana jarabawar samun scholarship,

cikin sa'a Allah yasa suka ci, sai da aka kai ruwa rana kafin Hajiya Tanya tabarsu suka lula Turkish, Ammar na karantar Engineering, while Nashwan na karantar Business administration............!!!


*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKI IYA SHAGALINKI....!*


MOMYN ZARAH. 'YARBAWAI