SAKI RESHE..

7

by @hauwaausmanjiddarh

SAKI RESHE...!*_

*(CIGABAN GADAR ZARE)*


*HAUWA A USMAN*

_JIDDARH_


_Masu buk'atar cigaban littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number ***, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number *** banda kira please WhatsApp chart kawai_


Free Page 


7️⃣


Cike da tsantsar farin ciki Zaman ya d'ago kanshi yana kallan cikin kwayar idon Basmah yace " da gaske my life?


Cikin sanyinta ta d'aga mishi kai, ya rik'o hanunta cikin nashi, duk da tasan illar hakan amma taji ta kasa hana shi, " kin tabbatar kinyi min alk'awarin zaki kasance da ni duk wuya duk runtsi?


"Eh nayi maka, "ke Malama ce nasan kin san fahimmancin alk'awari da illar sab'a shi, "in sha Allahu zaka same ni da cika maka alk'awari,

k'asa-k'asa yayi da murya yadda Safiyyah bazata ji abinda zaice mata ba yace " yau ki fito ke kad'ai daga makaranta karki taho da Safiyyah dan muyi shawarar ta inda zamu b'ullowa Ya Mu'allim,

kamar wacce yayiwa asiri koya shanye ba musu tace " to! zan fito in sha Allah, " yauwa 'yar albarka share hawayenki, ya fad'a cikin muryar dake narkarwa da Basmah zuciya,

da aka tashi daga makaranta Basmah bata tsaya jiran Safiyyah su tafi tare ba, da sauri ta fice gudun kar Safiyyah ta ganta,

tayi sa'ar ficewa batare da Safiyyah ta ganta ba, tsaye ta iske shi a inda yasaba tsayawa, yana hango ta ya nufeta da sauri jikinshi na tsuma,

" sannu My Life nasan a gajiye kike, murmushi tayi batare datace mishi komai ba, k'asa yayi da murya cikin salon d'aukar hankali yace " ina sanki Basmah kada ki bari a raba mu please,

wallahi kece rayuwata idan kika bari aka raba mu mutuwa zanyi, " karka damu in sha Allahu babu wanda zayyi nasarar raba mu, 

a hankali ya lumshe idonshi ya bud'e, kana ya mik'a mata ledar hannunshi, idonta kanshi tace " meye wannan?


"Waya ce!, a matuk'ar tsorace ta zaro idonta had'i da dafe k'irjinta tace " waya fa kace?


Idonshi ya jefa cikin nata yana yi mata wani irin kallo mai kashe jiki da saka zuciyar ma'abocin kallo karyewa,

cikin salon d'aukar hankali ya kashe mata ido d'aya had'i da d'age gira yace " yes! My Hope waya mana, da akwai wani abu ne!?


Basmah da jikinta ya dad'e da mutuwa, tana jin wani iri a gaba d'aya sassan jikinta, tace " kasan ba'a fara bari na rik'e waya a gida ba, 

sarai ya lura da sauyawar da jikinta yayi, dan haka ya k'ara kashe murya yace " eh nasani dama ba ina nufin ki bari a gani ba,

idan kin karb'a ki b'oye ta ita zamu rink'a magana har mu san ta inda zamu shawo kan Ya Mu'allim, na saka miki sim card a ciki, 

" gaskiya ina jin tsoron kada a gani a gida, " c'mon! ya za'ayi ki bari a gani, babu yadda bayyi da Basmah ma tak'i karb'a, ganin tak'i karb'a yasa shi tsuke fuska alamar bayyi ji dad'i ba,

yace " shikenan dama nasan bazaki karb'i kyautar farko danayi miki ba, kuma wannan ce kad'ai hanyar samun maganin matsalarmu, salon yadda yayi maganar yasata taji kamar bata kyauta ba,

zuciyarta ta shiga nuna mata rashin kyautar kin karb'ar kyautar amsoyin nata, jiki a sanyaye ta amsa, had'i dayi mishi godiya,

sai da suka d'an tab'a hira kana suka rabu, gabanta na fad'uwa tayi sallama ta shiga gidan, a d'arare ta shige bedroom d'inta,

tana shiga ta sauke ajiyar zuciya, jikinta na rawa ta ciro kwalin wayar daga cikin jikar makarantarta,

IPhone XS Max ta gani, gudun kar a kira tayi k'ara yasata saurin sakata a vibration, tana sakawa kiranshi ya shigo, sai da ta kulle k'ofar kana ta zauna bakin bed had'i da amsa wayar,

" sannu My Life, ya fad'a cikin sanyin murya yana sauke ajiyar zuciya, ajiyar zuciyar itama ta sauke had'i da lumshe ido tana jin mugun dad'i yana ziyartar sassan jikinta,

" My Love! ya fad'a cikin shagwab'a, "na'am ta amsa a sanyaye, "kin isa gida lafiya?


"Alhamdulillah, kai fa?


"Nima haka, cikin kulawa yace " kin ci abinci?


"A'a yanzu nake san nayi sallah naci abincin, da sauri yace " ki daina zama da yunwa please kar ulcer ta kama min ke, ki taimake ni ki rink'a kular min da kanki,

kafin muyi aure na cigaba da kula dake, murmushi tayi mai sauti saboda yadda yayi maganar ya burgeta, tace " in sha Allah zan kular maka da kai na, 

kai ma ka kular min da kanka, ta fad'a tana rufe fuska tamkar yana ganinta, " to Ustaziya ta zan kular miki da kaina, but ki tashi kiyi sallah kici abincin, "to tace, ta cikin wayar yayi mata kiss had'i da kashe wayar, 

ta dad'e a zaune tana bin wayar da kallo tana murmushi kafin ta mik'e ta fita, da daddare ma sun sha love ta waya inda Zaman yayi tayiwa Basmah kukan shagwaba,

yana rikitata da zazzak'ar soyayyarshi, ya haukata ta, ya zauta ta, ya mantar da ita kowa da komai sai shi, tun daga wannan rana kullum Basmah da Zaman suna manne da juna ta waya, wani lokacin ma har a makaranta waya suke, Malami nacan na b'ab'atun lesson itako ta manne earpiece a kunne tana hira da Zaman, 

yayinda ta dad'e da daina tafiya da Safiyyah da an tashi take yin wuf ta fice haka ma a zuwa bata tsayata, yauma da sauri ta fice daga get d'in makarantarsu tana sauri,

suna had'a ido ya sakar mata shu'umin murmushin shi me narkar mata da zuciya, cikin shauk'i ta lumshe ido ta bud'e ta mayar mishi da matartanin murmushin shi, "wow! ina san dimples d'in nan naki suna bala'in k'arawa murmushinki kyau, ta kuma yin murmushin a karo na biyu,

yayi saurin dafe k'irjinshi yana cewa " am dead, "kai My ba wani nan, " tom naji muje ki shiga mota na kaiki gida, " gida fa kace!


Tayi maganar tana zaro dararan fararen idanuwanta waje kamar zasu fad'o k'asa, yace " yes! yana kashe mata ido d'aya, "a'a ni dai karsu Yaya su ganni,

" bazan kaiki har k'ofar gida ba, daga nesa zan aje ki, kamar karta yarda sai kuma ta amince mishi, da kanshi ya bud'e mata k'ofar motar ta shiga,

kana ya zagaya ya shiga yayiwa motar key, suna tafe suna hirarsu ta masoya, daga d'an nesa da gidansu yayi parking zata bud'e motar ya dakatar da ita,

ya fito ya zagaya ya bud'e mata, fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi tace " kai! My daka barni na bud'e ai, "wane ni nabar my Love ta wahala?


"Tom! nagode sosai da kulawa, bari na shiga sai munyi waya, "ok bye my Love, tana tsaye ya shige motar yaja yabar wajen, fuskarta d'auke da murmushi ta juyo karaf idonta ya sauka cikin na Ya Mu'allim da Abubakar dake tsaye bayanta suna binta da kallan data kasa gane ma'anarsa,

razananniyar fad'uwa gabanta yayi da mugun k'arfi, k'irjinta ya shiga bugawa yana dukan uku-uku, Abubakar ya bud'e baki zayyi magana Ya Mu'allim yayi saurin dakatar dashi,

cike da tsoro ta rab'a ta gefe ta wuce su, tana shiga gida ta shige bedroom d'inta ta kulle ta kira Zaman a waya,

kashe kiranta yayi ya kira ta, bata jira yace wani abuba tace " na shiga uku My, ta fad'a tana rushewa da kuka, cikin tashin hankali ya taka burki k'uuuuuu har saida ta jiyo ta cikin wayar, " lafiya my love meya faru?


"Abba ya ganmu!, ta fad' tana cigaba da kukan, " oh! God!, ya fad'a yana runtse idonshi, saboda yana jin kukanta har cikin ranshi, yanzu yaya kenan?


"Wallahi ban sani ba, ban san matakin da zasu d'auka ba, sai daya karyar muryarshi kana ya shiga rarrashinta " kiyi shiru please, 

kin san bana san kukanki, yana d'aga min hankali sosai, yakan gusar min da nutsuwata, kiyi hak'uri mu san abin yi, a hankali ta sassauta sautin kukanta,

" to! kinga yanzu Allah ya kawo mana hanya mafi sauk'i ta camma burinmu, dan yanzu ne kika samu damar tura sak'onki ga Ya Mu'allim,

cak ta tsaida kukanta had'i da cewa " kamar yaya ban fahimceka ba?


"Eh! nasan zasu tambaye ki waye ni, anan saiki sanar dasu, kuma ki fad'a musu kina so na ni kike so, cikin sanyinta tace " an ya kuwa zan iya?


"Zaki iya Basmah matuk'ar kina san burinmu na mallakar junanmu ya cika, dole sai kin nemo k'arfin gwiwa kin sakawa kanki,

kin cire tsoro dan inba haka ba kina ji kina gani za'a raba mu, kuma kinyi min alk'awarin zabaki tab'a bari a raba mu ba,

Basmah dan Allah karki bari a raba mu, ki jajarce ki tsaya tsayin daka please, kin san ina sanki,

ya fad'a yana neman fashe mata da kuka, " naji zanyi yadda kace amma dan Allah karka yi kuka, kamar me jira ya fashe mata da kuka,

yana cewa " dole nayi kuka Basmah dan kece rayuwata kece duniya ta, Basmah ni maraya ne bani da uwa da uba, bani da kowa a duniya sai ke,

" ban gane baka da uwa da uba ba?


K'ara fashewa yayi da matsanancin kuka tunowa da rayuwarshi ta baya yayi, yana kuka wiwi yace " ni maraya ne Basmah,

ban san mahaifina da mahaifiya ta, ban san dangina ba, ban san kowa na ba,

ni kad'ai na rayu a duniya ta, babu wanda ya tab'a kira na da nashi sai ke, babu wanda ya tab'a yi min izinin na kira shi da nawa sai ke, babu wanda ya tab'a bani damar koda tsugunnawa ne a gidanshi balle zama,

babu wanda ya tab'a kira na da d'ana, ban tab'a kiran kowa da Baba ko Mama ba, na bud'e idona ne na ganni a gidan marayun dake garin Kaduna, anan na girma,

ke kad'aice tawa Basmah bani da wani hope sai naki, ban tab'a tsara future life d'ina ba sai da na had'u dake a baya ina rayuwa ne kamar gantallale amma had'uwata dake ya tabbatar min nima mutum ne kamar kowa,

kuma ina da galihu, zan iya yin rayuwar farin ciki kamar yadda kowa keyi, please karki k'ara mayar dani maraya karki cire min hope please, ya k'arashe maganar cikin rikitaccen kuka mai tsuma zuciya,

tunda Zaman ya fara magana har yayi shiru Basmah kuka take saboda tausayinshi, take taji tausayinshi, so da k'aunarshi sun mamaye duk ilahirin jikinta,

ya zamana babu wani gurbi da soyayyarshi bata ratsa ba, taji idan za'ayi yak'i babu wanda zai rabata dashi, ta sawa ranta koda za'ayi ruwan wuta bazata tab'a juya mishi baya ba,

koda hakan yana nufin rabuwa da kowa nata a duniya ciki kuwa harda ranta, ta saka a ranta zata jure duk wata wuya da barazanar Ya Mu'allim data Yayyanta,

koda zasu rabata da numfashinta, koda zasu tsaga k'irjinta su ciro zuciyarta su yar,cikin kuka tace " wallahil azim nayi maka alk'awarin kasancewa dakai koda hakan yana nufin mutuwata,

nayi maka alk'awarin bazan tab'a barinka ba komai za'ayi min, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana cewa " thank you, thank you, 

ki daina kuka karkiyi ciwon kai please, idan wani abu ya sameki bazan tab'a yafewa kai na ba, kiyi shiru kije kiyi wanka kici abinci,

maimakon tayi abinda ya sata saita k'ara fashewa da kuka tace " meyasa baka tab'a gaya min kai maraya bane?


"Meyasa baka tab'a fad'a min baka da kowa ba?


"Meyasa baka tab'a bani labarinka ba?


"Saboda karki shiga damuwa, ina gudun karki shiga halin da kika shiga yanzu, dakyar ya lallab'ata tayi shiru kana sukayi hira, ta kashe wayar,

da daddare sun had'u gaba d'ayansu a parlour suna cin abinci, Ya Mu'allim ya kalli Aliyu yace " kira min Basmah, cikin nutsuwa ya mik'e, tana kwance saman bed ya shigo, " ki zo inji Abba, 

duk da ta samu kwarin gwiwa a wajen Zaman hakan bai hana gabanta fad'uwa ba, cike da tsoro ta mik'e tabi bayan Aliyu gabanta na dukan uku-uku,

ta rab'a ta zauna kusa da Usman, batare da Ya Mu'allim ya kalli inda take ba, ya zuba abinci a plate ya mik'a mata, "karb'i kici, 

jikinta na rawa ta amsa, tunda Umma taga haka tasan akwai wani abu, dan tasan waye Ibrahim wato Ya Mu'allim,

kanta k'asa tana kallan abincin ta kasa kai koda loma d'aya bakinta, " ki ci mana!, still bata iya ci ba, batare daya kalleta ba yace " waye shi?


Umma tace " wa!?


"Ita wacce nake tambaya ta sani, kanta k'asa taba ce komai, "na ce waye shi?


Yayi maganar hankalinshi kwance, muryata na sark'ewa tace " shine wanda yazo neman izini wajenka, "kin sanshi ne dama?


A hankali ta k'ara sunkuyar da kanta k'asa, " amsa zaki bani nace dama can kin sanshi ne?


"Eh!, nasanshi, "da saninki kenan yazo waje na?


Sai da tayi d'an jim kana tace " eh!, " a ina kika sanshi?


"A hanyar makaranta, duk maganar da akeyi Ya Mu'allim bai kalli inda Basmah take ba sai yanzu, ya tsame hannunshi daga kwanan dayake cin abinci yace " bai fad'a miki abinda na fad'a mishi ba?


Kanta ta k'ara sunkuyarwa k'asa batare da tayi magana ba, Ya Mu'allim ya sauke ajiyar zuciya kana ya tattara gaba d'aya hankali da nutsuwarshi gareta,

yace " na riga nayi miki miji Basmah, kuma ina tunanin na isa na zab'awa 'yata miji kamar yadda Annabi yayi mana umarni, 

tun a ranar da aka haifeki na dake Basmah, na riga na bawa Ammar ke, daga nan Ya Mu'allim ya kwashe labarin komai ya bawa Basmah, 

tun daga alak'arshi da Yaseer da matsayin Yaseer a wajenshi da yadda suka taso sukayi rayuwa, har zuwa ranar da yayiwa Ammar alk'awarin aurenta, ya d'ora da cewa " dai-dai da sunan da ake kiranki dashi wato *BASMAH* Ammar ne ya zab'ar miki,

mahaifinshi ne yayi miki hud'uba shine ya yanka miki ragon suna, ke idan baki sani ba ki sani,

ba sunan mahaifiyata ne dake ba, sunan mahaifiyar Yaseer ne wato kakar Ammar, dan Allah ki taimakeni na cika alk'awarin dana d'aukarwa d'an uwana tun yana raye,

ki taimake ni, ki barni na cikawa Ammar alk'awarina akanki dan Allah Basmah, ina rok'on wannan alfarmar, sosai jikinta yayi mugun yin sanyi,

amma bazata iya hak'ura ta auri wanin Zaman ba, bayan dukkan alk'awarin datayi mishi, kanta k'asa tace " kayi hak'uri Abba Zaman nake so,

sai da numfashin Ya Mu'allim ya kusa d'aukewa saboda mamaki, yace " me kikace Basmah?


Kuka ta fashe dashi tana cewa " kayi hak'uri Abba amma Zaman nake so, bazan iya auren kowa ba idan bashi b.....!, tassss! tassss!,

Abubakar ya kifa mata gigitattun marika, ya mik'e yana huci ya nunata da yatsa yace " ke kin isa ace ga abinda zakiyi kice a'a?


"Ke kika haifeshi ko shi ya haife ki?


"Kece babba ko mune manya?


"Wallahi dole kibi abinda Abba yace, matuk'ar kina neman zaman lafiya dolenki kiyiwa Abba biyayya,

itama mik'ewa tayi tsaye tana girgiza kanta tace " baka san so ba Yaya, baka san me ake kira da wutar soyayya ba,

inda kasan meye so dabaka ce na sadaukar da soyayyata ga wani da ban san kowaye ba, bazan iya auren wanin Zaman ba,

bazan iya cin amanarshi ba, bazan iya butulce mishi ba, bazan iya karya mishi alk'awari ba, shi nake so Yaya, shi kad'ai zan iya aura,

dashi kad'ai zan iyayin rayuwar aure dan Allah ka fahimce ni Yaya, ta fad'a cikin matsanancin kuka, k'ara d'auke ta yayi da mari yace " lalle Basmah kin girma,

kin cika tunda kike kallan tsabar ido na kike cewa ban san meye so ba, ban san meye soyayya ba, amm.....! dakatar dashi Ya Mu'allim yayi ta hanyar d'aga mishi hannu,

kana ya kira sunan Basmah, "Baseerah, karo na farko a iya tsayin rayuwarta taji Abbanta ya kira real name d'inta,

" na'am Abba, alama yayi mata da tazo ta zauna, ba musu ta zauna a inda ya nuna mata, kiyiwa Allah Basmah ki rufa min asiri, ba umarni nake baki ba,

rok'onki alfarma nake yi, ki taimake ni ki cika min babban buri na dan Allah Basmah, idan ban aurawa Ammar ke ba, ban san da wanne ido zan sake kallan yaran nan ba,

kuma bana san nayi miki dole dan nayiwa Yaseer alk'awarin bazan tab'a yi miki auren dole ba, nayi miki alk'awarin muddin kika ce baki san Ammar bazanyi miki dole ba,

zan aura miki wanda kike so, dan haka nake neman alfarma a wajenki, cikin matsanancin kuka tace " kayi hak'uri Abba ina iya baka rai da rayuwata amma bazan iya auren wanin Zaman ba,

shi nake so Abba, Abba kasan rayuwar aure ba rayuwa ce ta yau da gobe ba, ba rayuwace ta k'ayyadaddan lokaci ba, rayuwa ce me tsawo, ta din-din, har rai da mutuwa,

idan na auri wani ba Zaman ba zanyi rayuwa ne cikin bak'in ciki da takaicin rayuwa, zan k'arar da rayuwata batare da farin ciki da walwala ba,

bazan iya sadaukar da komai na ba, bazan iya sadaukar da soyayyarshi ba, bazan iya sadaukar da rayuwata ba Abba, ina sanshi sosai,

ka fahimce ni nima, kamar yadda kayi alk'awari haka nima nayi mishi alk'awari, sosai mamaki ya kama Ya Mu'allim dan yasan sarai wannan ba halin 'yarshi bane,

ba kuma tunaninta bane, ya tabbatar saka mata tunanin akayi, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,

Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha, aikin gama ya gama, muna can muna bacci ana yi mana munshari,

an lalata abinda nayi shekaru inayi, an tarwatsa tarbiyyar dana dad'e ina baki, an warware miki tunaninki, an lalata min komai, komai ya dawo baya, 

duk abinda nayi ya tashi a banza, shiyasa akace sai uba yayi shekaru 20 yana bawa 'yarsa tarbiyya, cikin sakanni 20 namiji ya lalata,

yau naga tabbas, yau na tabbatar da abinda mutane ke fad'a, yau ni Basmah ta tsaya akaina tana gaya min rayuwar aure, tana fad'ar bazata iya sadaukar da soyayyarta akaina ba,

tana kallan cikin idon babban Yayanta tana cewa bai san so ba, tana cewa bazata auri zab'in danayi mata ba, yaushe kike sanshi Basmah da zaki bijerewa umarni na akanshi?


"Yaushe kika had'u dashi daya kunce miki tunaninki ya warware miki tarbiyyar da muka shekara 16 munayi miki?


"Wanne irin so ya nuna miki wanda bamu nuna miki ba?


"Wacce irin kulawa ko gata yayi miki wacce muka gaza yi miki?


"Me ya gaya miki daya ruguje k'ima da mutuncinmu a idonki?


"Basmah kada ki zab'i namiji akanmu, kada ki biyewa son ranki da zab'in zuciyarki su kaiki su baroki, kada namiji ya hure miki kunne akanmu , 

mu ne dolenki shi ba dolenki bane, ina guje miki biyewa mayaudarar samarin nan su kaiki su baro ki,

" kayi hak'uri Abba ina sanshi nasan bazai tab'a cutar dani ba, dan Allah karku raba mu plea...........! a hasale Umar ya shiga dukanta tako'ina yana yin ball da ita

sai dakyar Usman ya kwaceta, Umma da mamaki da al'ajabi suka hana ta magana ta sauke ajiyar azuciya tana bin Basmah da kallo, deep down tana jin d'aci cikin ranta,

a ranar kowa cikin bak'in ciki ya kwanta, yayinda Basmah na can na waya da Zaman tana labarta mishi abunda ya faru,

a shagwab'e yace " kiyi hak'uri dear naja miki matsala, gashi saboda ni har duka kika sha, yayi maganar kuka na neman kufce mishi,

" lah ba komai fa, karka damu ai dama a soyayya akwai sadaukarwa, " kin san dole na damu musamman ma dukan da akayi miki,

" indai har da gaske suna sanki ai dole su so abinda kike so, ban san meyesa kowa yake k'ina ba, ban san meyasa tawa duniyar ta zo min a haka ba,

ban dan meyasa bani da kowa da komai ba, ina sanki Basmah dan Allah karki barni, ya k'arasa maganar cikin rikitaccen kuka mai karya zuciya,

" kayi hak'uri ka daina kuka dan Allah in ba so kake nima nayi kukan ba, ta fad'a muryarta na rawa, da sauri yace " nayi shiru na daina, dan Allah karkiyi kuka,

washe gari asabar babu makaranta bazasu had'uba dan haka suka dad'e suna waya, ya kwantar mata da hankali sosai, washe gari da wuri ta tashi ta kammala komai kamar yadda ta saba,

bata jira suka fito ba tayi shigewarta d'aki ta rufe, har ranar Monday Basmah bata fito tsakar gida ba tana k'unshe a d'aki,

bayan ta gama shirin makaranta ta fito ta iske Umar tsaye a parlour, " ina kwana Yaya?


Fuskarshi babu yabo babu fallasa ya amsa da cewa " lafiya Alhamdulillah, wuce mu tafi daga yau ni zan rink'a kaiki makaranta ina d'auko ki,

taji ba dad'i sosai dan an rufe mata hanyar ganin Zaman, batare data ce komai ba ta wuce, sai da suka biya suka d'auki Safiyyah kana suka tafi,

har bakin get yakaisu, yayiwa me gadi bayanin ko'an tashi karya sake yabarsu su fita sayya zo d'aukarsu, kallan tuhuma Safiyyah ta jefawa Basmah had'i da cewa " kodai akwai abinda ya faru?


Babu abinda Basmah ta b'oye mata ta kwashe duk abinda ya faru ta fad'a mata, " ke! Basmah kiji tsoron Allah, kada ki biyewa rud'un duniya da san zuciyarki su jefaki a halaka,

kada soyayyar namiji ta rufe miki ido ta mantar dake komai da kowa wallahi kibi a sannu, kibi komai a hankali, harara Basmah ta jefa mata tace " ke! dakata Malama idan bazaki bani shawarar yadda zan mallaki burin raina na cika muradin zuciyata ba,

ki fita daga maganar nan ba ruwanki idan ba so kike mu daina gaisawa ba, ba k'aramin mamaki Basmah ta bawa Safiyyah ba,

ta tabbatarwa kanta Basmah tayi nisa bazata tab'a jin kira ba, " amma Bamsah ya kamata ki san....! dakatar da ita Basmah tayi ta hanyar cewa " ke! ki fita harka ta kinji ko?


Kafin Safiyyah tace wani abu Basmah tayi tafiyarta ta barta nan tsaye, tabi bayanta da kallo cikin ranta tana mamakin sauyawar Basman,

ta waya ta sanarwa Zaman hukuncin da Umar ya yanke na kaita makaranta kullum yana d'aukota, sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya soma magana cikin kasalalliyar muryarshi,

" shikenan yanzu na daina ganinki?


"Gaskiya bazan iya jure rashin ganinki ba, dan haka mu samo mafita, ido ta lumshe tana jin dad'in yadda Zaman yake nuna tsantsar soyayarta,

yake nuna damuwa akan duk wani abu da zayyi musu shamaki da cikar burinsu, " nima ban san abinyi ba, amma kai idan kana da mafita ka fad'a,

sai da ya k'ara kashe muryarshi kafin yace " idan akayi break ki rink'a haurowa please kinga kafin a gama break mun gama hirarmu kin koma,

ido ta zaro kamar yana kallanta tace " haurowa fa kace?


"Eh! mana please dan Allah, dan farin cikinmu, dan samun nutsuwar zuciyoyinmu, ya dad'e yana rarrashinta kafin ta yarda,

ana kad'a kararrawar break Basmah tayi saurin ficewa daga ajinsu, gudun kar Safiyyah ta biyo ta,

baya ta zagaya inda katangar makarantar ta d'an zube ta samo bokitin da ake zuba ruwan alwalar malamai ta taka ta hau ta dira,

tana dirawa Zaman yayi saurin tareta ta fad'a jikinshi dai-dai lokacin Umar, Abubakar, Usman, Aliyu da Ya Mu'allim sunzo wucewa ta cikin mota zasuje wajen d'aurin aure karaf idonsu ya sauka akan Basmah dake rungume jikin Zaman..........!


*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKU......!*



MOMYN ZARAH. 'YARBAIWA