8
SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
_Masu buk'atar cigaban littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_
8️⃣
Cikin tashin hankali Aliyu ya taka burgi k'uuuuuu wanda ya jawo hankalin Basmah dake kokowar kwace jikinta, a matuk'ar razane tayi baya zata kifa saboda tsantsar kid'ima da tashin hankali,
cike da bak'in ciki Ya Mu'allim ya runtse idonshi hawayen takaici suka shiga gangarowa daga idonshi,
jikin Usman na rawa ya bud'e motar ya fita ya finciko Basmah kamar zai karya mata hannu, cikin tashin hankali Zaman yabi bayan Usman yana cewa " kuyi hak'uri dan Allah,
wallahi ba laifinta bane, kuma ba abinda kuke tunani bane, tsakani da Allah nake san Basmah bazan tab'a lalata mata rayuwa ba,
dan Allah kada ku dake ta, kamar yadda kuka dake ta jiya, a hasle Umar ya bud'e motar ya fito ya hankad'a Zaman baya yana cewa " idan an dake ta ina ruwanka?
"Koda abinda zakayi?
"Kome zakuyi min kuyi min amma dan Allah karku tab'a ta, cikin matsanancin kuka tace " wallahi Yaya ba laifinshi bane laifi na ne dan Allah karka yi mishi komai,
ganin ana neman yin aika-aika yasa Ya Mu'allim dakatar da Umar, "dakata Umar ba laifinshi bane laifin 'yarmu ne, ko ince laifinmu ne,
Umar na huci ya dannata cikin mota, ya gaya ya shiga motar yaja zuwa gida,
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa'aklifni khairan min ha,
Ya Mu'allim ya fad'a while hawaye na zubo mishi, jikin Zaman a sanyaye yabi bayansu da kallo cikin ranshi yana addu'ar Allah yasa kada su daki Basman,
Umma na zaune a tsakar gida suka shigo Umar yayi jifa da Basmah ta fad'i k'asa kanta ya bugu da bango, take ya fashe jini ya soma zuba,
" mu zaki wulak'anta Basmah?
"Mu zaki nemi zubarwa da mutunci a idon duniya, ki tona mana asiri Basmah?
Abubakar yayi maganar yana kallanta, jikin Usman a sanyaye cike da tausayinta yace " sister meyasa baki dubi k'ima da mutuncin gidan nan ba?
"Meyasa bazaki dubi girman mahaifinmu da ake gani a garin nan ba?
"Meyasa bazaki sai mana mutunci ki saiwa kanki ba?
"Meyasa baki tayamu kare mutunciki da darajarki ba?
"Basmah ki tuna irin soyayyar da muka nuna miki dan Allah kada ki watsa mana k'asa a ido, ki tuna Abba shi ake kawowa matsalar wasu gidajen ya gyarata,
ki tuna Abba ake kawowa 'ya'yan wasu idan sun kauce hanya ko suna abinda bai dace ba ya basu shawara yayi musu nasiha ya d'orasu a hanyar dai-dai,
ki tuna Abba ya kasance babban Malami a jahar nan, kuma yana cikin manyan malaman k'asarnan,
ba k'aramin abun kunya bane ace 'yarshi ta lalace kota bujewa umarninshi duk da irin tarbiyyar da aka baki,
idan kikayi haka kin wulak'anta mu kin tona mana asiri dan Allah Basmah kada kiyi mana haka, kodan darajar Abba data gidan nan,
cikin rashin fahimta Umma tace " kai Aliyu meke faruwa ne?
Sai da ya had'iye k'ululun bak'in ciki kafin yace " Umma ganinta mukayi a titin Allah rungume jikin wani k'ato, " la'ilaha illallahu Muhammadurrasulillahi ni Saratu na shiga uku meke shirin faruwa da mu?
Ta fad'a tana rushewa kuka tamkar ranta zai fita tace " kayi hak'uri Yaya wallahi ina sanshi bazan iya rabuwa dashi ba, dan Allah ku aura min shi,
shine rayuwata duk wanda ya aure ni gangar jikina ya aura, kuma ba lalle ne ya samu yadda yake so daga gare ni ba tunda bana sanshi,
da ayi abinda za'a dawo ana danasani ko yakawo lalacewar zumunci kwara a hak'ura, a hankali ta rarrafa ta rik'e k'afafuwan Ya Mu'allim tana gunjin kuka tace,
" dan Allah Abba ka taimake mu kada ka raba mu, muna matuk'ar so da k'aunar junanmu, idan ka raba mu komai yana iya rafuwa,
muna iya mutuwa kaga hakk'in ranmu ya hau kanka kenan Abba dan All......! gigitattun marikan da Abubakar ya zuba mata ne suka sakata yin shirun dole,
ya nuna ta da d'an yatsa yana cewa " wallahi ko zaki mutu bazaki auri wannan d'an iskan ba, fasik'i, mazinaci, wanda ya rungume ki a titin Allah,
tana dafe da kuncinta tace " Allah ba d'an iska bane ba kuma rungume ni yayi ba, na diro daga katanga zan fad'i shine ya tare ni amma ba abinda kuke tsammani bane,
k'ululun bak'in ciki ne ya hana dukkansu magana,
a hankali Ya Mu'allim ya fitar da numfashi yace " kin bani mamaki Basmah, ban san yadda akayi halaye da d'abi'unki suka canja ba,
ban san yadda akayi wannan yaron yayi min shigar sauri ba, ya shammace ni yayi min illa ba, amma ki sani koda bazaki auri Ammar ba,
bazan tab'a bashi aurenki ba, ki kawo duk wanda kike so zan aura miki shi amma banda wannan yaron, fashewa tayi da rikitaccen kuka tana cewa,
" shi nake so Abba, wallahi shi kad'ai nake so, bana san wani d'a miji inba shi ba, " wallahi koda zaki mutu bazan tab'a aura miki mishi ba, yayi maganar yana juyawa zai shige bedroom,
kai tsaye Basmah tace " wallahi sai dai na mutu banyi aure ba, amma matuk'ar zanyi aure a duniyar nan bani da wani miji sai Zaman,
shi kad'ai nake so kuma shi zan aura inba haka ba sai dai na mutu banyi aure ba, cak Ya Mu'allim ya tsaya yana jin kalaman Basmah na sauka a kunenshi tamkar saukar aradu,
a zuciye Umar, Aliyu da Abubakar sukayi kanta, tayi saurin mik'ewa da gudu ta shige bedroom d'inta ta rufe k'ofa,
sai da ta tabbatar sun fita tayi dailing number Zaman, yana tsaye a tsakiyar d'akinshi ya kasa zaune ko tsaye yana tunanin halin da Basmah ke ciki ya ji wayarshi ta soma ruri,
jikinshi na rawa yakaiwa wayar raruma dan ringing d'inta dabanne, kashewa yayi ya kira ta, bugu d'aya ta d'aga,
" Abba yace bazai tab'a baka aure na ba Zaman, ban san yadda zamuyi ba, tayi maganar cikin lalataccen kuka, mai soya zuciya, tashin hankali ne ya sanya wayar sab'ucewa daga hannunshi,
wani abu ya tsarga mishi tun daga tafin k'afarshi zuwa tsakiyar kanshi, a hankali ya dafe kanshi dake barazanar tarwatsewa,
bazaice ga abinda yake ji cikin ranshi da zuciyarshi ba, jin tana cewa " hello hello, ya sashi tattara d'an sauran k'arfin daya rage mishi ya d'auki wayar dake yade a gefe,
muryarshi na sark'ewa yace " ina jinki Basmah, yanayin maganarshi ya bayyanar da halin dayake ciki, " Abba yace zai aura min duk wanda nake so amma banda kai,
ta fad'a tana fashewa da kukan dayafi kama dana mutuwa, tana jin zuciyarta tamkar zata tsage, jin kukanta yake yana huda k'ohon zuciyarshi yana ratsa b'argon jikinshi, sai da ya cije lips kafin yace " ki daina kukan please,
" bazan iya ba, kabarni nayi kuka kona samu sassaucin abinda nake ji a zuciyata, " kin san bana san kukanki, idan bakiyi shiru ba nima zanyi kukan,
yadda yayi maganar ya tabbatar mata da kuka na gaf da kwace mishi, " karkayi please, ta fad'a tana danne abinda yake taso mata a k'irji,
" yauwa kiyi shiru, kije ki kwanta gobe mayi magana,
zatayi magana yace " no argument please, just do as i said, & promise me zakiyi bacci, kamar yana ganinta ta d'aga mishi kanta, "good girls i love you bye,
ya fad'a had'i da saurin kashe wayar, kanshi ya kifa akan table d'in dake gabanshi, tuk'uk'in dake taso mishi ya shak'e mishi k'ofofin shak'ar iska,
zuciyarshi ta shiga bugawa da sauri da sauri, yana jin wani abu dabe san komenene ba yana fasa zuciyarshi, while yana jin k'irjinshi tamkar zai tsage,
a hankali ya mik'e yana tangad'i had'i da had'a hanya kamar wanda yasha wani abu ya shige bedroom d'inshi, washe gari matan da take koyarwa agida suka taro suna jiranta,
ganin lokaci yaja sosai Basmah bata fito ba yasa Umma cewa Aliyu " shiga ka kira ta kace mata tabar mutane na jiranta,
tana kwance saman bed Aliyu ya shigo, " ke! baki san mutane na jiranki bane?
Ya fad'a fuskarshi a had'e, banza tayi dashi tayi kamar bata san Allah yayi ruwanshi ba, " Basmah dake nake fa, "au ashe kasan sunana kake ce min ke?
Tayi maganar batare data kalli inda yake ba, sosai mamakinta yayi masifar kama Aliyu dan duk da yasan Basmah da tsiwa yasan bata da rashin kunya balle rashin tarbiyya,
batare da ya kuma yi mata magana ba ya juya, yana cikin yiwa Umma bayani Ya Mu'allim da Abubakar, Usman da Umar suka shigo, "lafiya?
Ya Mu'allim ya fad'a yana binsu da kallo, "o'o Basmah na tura shi ya kira ganin tabar mutane a waje suna jiranta, " wai me yarinyar take san zama ne?
"Meya canja Basmah cikin k'ank'anin lokaci?
"Yarinya me kunya, tarbiyya, kara da kawaici da ganin girman na gaba da ita, balle iyayenta, Ya Mu'allim ya fad'a cikin ranshi, a zahiri kuma batare da yayi magana ba ya nufi d'akin gaba d'ayansu suka take mishi baya,
kamar yadda Aliyu ya iske ta haka suka tarar da ita, d'an gyaran murya Ya Mu'allim yayi kafin ya kira sunanta a hankali " Basmah,
jin muryar mahaifinta yasata mik'ewa zaune tana amsawa da " na'am, " baki san kin bar mutane a waje suna jiranki bane?
"Kanta k'asa tace " bazan iya koyarwa ba, bani da lafiya kaina da jikina ke ciwo saboda dukan da akayi min jiya,
dukkansu sun san magana tayi me harshen damo dan babu alamar rashin lafiya a tattare da ita, ido Ya Mu'allim ya zuba mata mamakinta na neman d'imautashi,
Abubukar daya kafe ta da ido shima yana mamakin yadda halayyarta ta canja yace " to yanzu me kike san a fad'a musu?
" Suma sun san yau da gobe sai Allah, sun san akwai cuta, akwai mutuwa da rashin lafiya idan mutuwa nayi ya zasuyi ba dole su hak'ura ba?
Dan haka yanzun ma hak'urin zasuyi har na samu lafiya tunda sun san rai da lafiya a hannun Allah suke kuma babu mai shiga hurumin Allah sai....!,
hannu Ya Mu'allim ya d'aga mata dan bazai iya jure kalaman Basmah dake barazana da lafiyarshi ba,
yace " shikenan!, Umar yace " amma Abb....!, hannu Ya Mu'allim ya d'aga mishi yana murmushin k'arfin hali yace " gaskiya ta fad'a yau da gobe sai Allah,
ya fad'a yana danne damuwarshi, yayinda daga k'ark'ashi yake ji tamkar ana cinnawa zuciyarshi wuta, " kai Aliyu kaje ka koya musu, " to Abba!, Aliyu ya fad'a cikin girmamawa,
kana ya fice, idon Ya Mu'allim kanta yace " sannu Allah sauwak'e zan sa Usman ya siyo miki magani kisha ki kwanta, bai bari ta amsa ba ya fice Umma tabi bayanshi,
Umar ya kalle ta had'i da cewa " yanzu abinda kikayi kin kyauta Basmah?
"Ku abinda kukayi kun kyauta ko dai-dai kukayi?
Karaf maganarta ta sauka kunnen Ya Mu'allim, murmushin takaici yayi yana cewa " Allah ka sani ban yiwa iyaye na ba,
" kin kyauta, Abubukar yace had'e da ficewa Umar yabi bayanshi fuuu, jikin Usman a sanyaye ya zauna a bakin gadon kusa da ita,
had'i da zuba mata ido na tsawun lokaci batare daya furta koda kalma d'aya ba, turo baki tayi tana cewa " ni ka daina kallo na haka,
" hmmm Basmah dole na kalle ki dan gaba d'aya kin canja mana ganinki muke yi tamkar wata bak'uwa, meyasa bazaki hak'ura da zab'in da Abba yayi miki ba?
"Kin san dalilin da yasa Allah yasa akayi haka Basmah?
"Baki san me Allah ya b'oye tsakaninki da Ammar ba dan ina da tabbacin akwai alkhairi a ciki, nasan Abba bazai tab'a yi miki zab'in banza ba,
bazayyi miki zab'in da zai wahalar dake da rayuwarki ba, bazai kaiki inda zaki wahala ba, dan Allah kada ki bashi kunya kada ki watsa mishi k'asa a ido please Sister ki taimaka ki bawa Abba had'in kai ya cika alk'awarin daya d'auka tun ranar da aka haifeki,
ki tuna iyaye na gaba da komai, tun kafin kisan kanki, kisan wacece ke, kisan komai da kowa a duniya su kika fara sani,
suka ciyar dake, suka shayar dake, suka tufatar dake, tun baki da k'arfi har kika samu k'arfi, sukayi d'awainiya dake tun daga zanin goyo har yau basu daina na, su suka koya miki komai a rayuwa, sune jinki alokacin da bakya ji,
sune ganinki a lokacin da bakya gani, sune maganarki a lokacin da bakya magana, iyaye suna gaba da kowa da komai a duniya idan kika d'auke Allah da Ma'aiki,
shi kanshi wanda kike son in banda iyayen naki sun gyara ki da bazai so ki ba, inda a wulak'ance ya ganki ba zai rab'i ko inda kike ba balle yace yana sanki,
kada ki yarda ki bijirewa iyayenki akan d'a namiji, kada ki biyewa zuciyarki da zab'in ranki kiyiwa kanki *SAKI RESHE...!*,
ki hak'ura da zab'in Allah wato Ammar dan ina da tabbacin Ammar shine mahad'in rayuwarki kada ki dawo kina danasani Basmah,
namiji ba abin yarda bane, mad'aci ne, d'an kunama ne, kyan d'an miciji ne dashi, d'acin namiji yafi d'ata da mad'aci, dafinshi yafi na bak'in kumurcin maciji,
illarshi tafi kowacce irin illa a duniya, zai iya saka miki dabon da har ki mutu bazaki manta ba, idan kikaje asibitoci layin 'yan hawan jini da ciwon zuciya zakiga yawancinsu duk mata ne,
mazan k'alilanne, kuma idan kika bincika su zakiga yawanci ciwon nasu yana da nasaba da illar d'a namiji, shiyasa nake miki gudun abinda zai iya zuwa ya dawo,
ina fad'a miki ne saboda gaba kada kice ba'a fad'a miki ba, kina cewa ba'asan meye rayuwar aure ba, to kece baki san meye aure ba,
yanzu kanki rawa yake yi kina d'oki, soyayyarshi na fisgarki, idan akayi so da soyayya tafiya suke yi, sai dai zaman hak'uri,
duk matar datace miki batada matsala a gidan mijinta k'arya take yi, ke hatta wad'annan celebrities da kike gani hak'uri suke yi a gidajen mazajensu,
auren celebrities nawa kikaji ya mutu?
"Kwanannan Abishak Bachan yayiwa Ashwariyya rai mugun wulak'anci a gaban mutane, da ana hira da Rani Mukhrajee akayi mata tambaya akan mijinta cewa tayi I know Allah has course me to married Aditya,
wallahi duk soyayyar da namiji zai nuna miki kada ki yarda ki sab'awa Allah akanshi, kada ki bijirewa iyayanki akanshi, akwai abinda Allah yake ajewa mutane Izzina da aya,
koda ace Ammar ba alheri bane zai iya zame miki alkhairi saboda biyayyar da kikayiwa iyayenki,
_(Maza kuyi hak'uri ba zaginku ko ci muku mutunci da fuska nayi ba salon rubutunne yazo a haka so I'm sorry)_
a fili Basmah ta sauke ajiyar zuciya tana jin maganganunshi tamkar tatsuniya ko kid'an ajo dan tuni shaid'an ya buga mata ganga ya fitsare mata kanta, ganin yana neman cigaba da surutun banzanshi injita,
yasata soma hamma tana k'ok'arin kwanciya tace " naji nagode, ta fad'a ataik'aice, mamaki ne ya sashi kafe ta da ido na tsayin lokaci kafin ya fita,
yana fita taja uban tsoki had'i da d'auko wayarta tayi dialing number Zaman,
washe gari da wuri Basmah ta shirya ta fice makaranta bata tsaya ta gaida Umma tayi mata sallama kamar yadda ta saba ba,
bata biyawa Safiyyah ba tayi wucewarta, tsaye ta ganshi hard'e da hannuwanshi a k'irji sanye cikin k'ananan kaya na kamfanin red tag,
kayan sun amshi jikinshi tamkar saida aka auna da jikinshi, kyanshi da k'uruciyarshi sun fito sosai,
ido ta k'ura mishi sonshi yana fisgarta yana ratsa k'irjinta had'i da huda zuciyarta yana samun matsagunni,
sosai kanshi keyi mata dad'i iska ta shiga busata ta fara mayen san kasancewa tare dashi, taji zata iya dauwama tana kallan fuskarshi,
zuciyarta ta shiga aiyano mata irin rayuwar jin dad'in da zasuyi me cike da soyayya, cikin salonshi na d'aukar hankali ya busa mata iskar bakinshi a saman fuskarta yana sakar mata k'ayataccen murmushi yace " wannan kallon fa?
Cike da jin kunya ta kawar da idonta dan bama tasan yabar inda yake tsaye yazo gabanta ba, " i love you my life, ya fad'a cikin sanyin murya,
idonta kan flowers dage gefe tace " jiya kace ka samo mana mafita ko?
"Eh! amma gaskiya nasan dakyar idan zaki bani had'in kai, kuma ta haka ne kawai zamu samu damar mallakar junanmu, ta haka ne zamu saka dole Ya Mu'allim ya barmu mu cika muradin zuciyoyinmu, ya fad'a cikin sanyin rai,
" karka damu ka fad'a indai shawarar zata kaimu ga cika burinmu nayi maka alk'awarin baka had'in kai, " kin tabbatar kinyi man alk'awarin zakiyi komeye?
"Eh! zan baka had'in kaina d'ari bisa d'ari, ka fad'a kawai, idonshi cikin nata yana kallan kwayar idonta yace kin san fa muhimmanci alk'awari, idonta ta juya alamun a matse take taji shawarar dazata kaisu ga mallakar junansu tace " humm go ahead please,
cikin mutuwar jiki ya gyara tsaiwarshi yana fargar abinda zai fad'a yayinda wata zuciyar ta shiga gargad'inshi kan abinda yake shirin fad'a,
tsoron dayake k'ark'ashin ranshi ya ratsa ta cikin k'ahon zuciyarshi ya fito saman fuskarshi ya bayyana k'uru-k'uru,
d'an k'arfin halin daya rage mishi ya tattara dakyar zuciyarshi na bugun uku-uku muryarshi na rawa yace " aron kanki zaki bani yau, "ban gane ba?
Ta fad'a tana tallan yanayinshi " i mean ki mallaka min kanki na yau kad'ai mu kasance tare mu raya ranar yau cike da soyayya mu d'ebewa juna kewa muyi nishad'i,
mu kasance ni dake a wata duniya ta daban wacce daga ni sai ke kad'ai zamu kasance a cikinta, ya fad'a gwiwarshi na rawa,
idonshi cikin nata yana aika mata sak'o ta cikin kwayar idonshi , sun d'auki lokaci a haka kafin tace " na amince.............
*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKU.........*
MOMYN ZARAH. 'YARBAIWA