9
SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
_Masu buk'atar cigaban littafin *SAKI RESHE...!* zasu biya 300 ta account number Hauwa Auwal Usman GT Bank 0153259310 idan aka turo kud'in sai ayi screenshot (shaidar biya alert sms) a turo ta WhatsApp number 07020489340, ko a turo katin waya na 300 ta WhatsApp number 07020489340 banda kira please WhatsApp chart kawai_
Free Page
9️⃣
" I mean ki mallaka min kanki na yau kad'ai mu kasance tare mu raya ranar yau cike da soyayya mu d'ebewa juna kewa muyi nishad'i,
mu kasance ni dake a wata duniya ta daban wacce daga ni sai ke kad'ai zamu kasance a cikinta, ya fad'a gwiwarshi na rawa,
idonshi cikin nata yana aika mata sak'o ta cikin kwayar idonta, take wani abu ya dirar mata wanda ita kanta bata gane komenene ba,
ta fi kamanta shi da tsoro gabanta na fad'uwa tace " me kake nufi Zaman?
Gutun murmushi yayi dan ya gane inda ta dosa yace " Ina nufin ki bi ni muj....!, bata bari ya k'arasa fad'ar abinda yayi niyya ba tace " ina zan bika?
Tayi maganar tana zaro ido waje daga cikin ranta tana jin tuk'uk'i na taso mata, " calm down mana dear, ki barni na k'arasa yi maki bayani,
ina nufin mu fita yawo mu zaga gari, mu dad'e, bayan sallar ishaa sai na mayar dake gida, tashin hankaline yasa Basmah fara ganin bibbiyu,
jikinta ya d'auki tsuma yana b'ari, bakinta ya shiga motsi da alama so take tayi magana amma ta kasa, ta dad'e a haka kafin ta iya had'a kalaman bakinta tace " dama haka kake Zaman?
"Haka kake kasa na fara sanka, kasa na amince dakai na d'auki dukkan yardata na damk'a maka?
"Me kike nufi Dear?
Yayi maganar yana zaro ido, " bafa wani abu nake nufi ba, ba nufi na inda kike tunani ba, ina nufin muyi pretending as kamar akwai wani tsakaninmu,
so I'm sure Ya Mu'allim zai tsorata yayi gudun abun kunya ya bani aurenki, ina nufin muje park ko wani joint wanda yake da mutane,
mu zauna in public but ba abinda nake nufi kenan ba, idan Ya Mu'allim yaga munyi haka zayyi saurin bani ke, amma ke kin kai ni wani fanni daban,
ba haka nake ba Basmah, ni ba mazinaci bane,ba kuma fasik'i bane, koda ace sun kasance halayyata bazan tab'a yi miki ba, balle bama d'abi'u na bane, tur da masu irin halin nan, ya k'arasa maganar yana zubar da yawo cikin kyama,
kana ya cigaba da magana " ashe kallan da kike yi man kenan?
"Kallan d'an iska kike man dama?
" Kin bani mamaki Basmah da har yanzu kike kokwanto a kaina, kike raba d'aya biyu kina wasi-waaasi akaina,
d'an shiru ne ya gifta kafin cikin sanyinta tace " kayi hak'uri ban k'arawa, fuskarshi d'auke da fara'a tamkar ranshi bai b'aci ba yace " babu komai ki wuce makaranta karki makara,
a dakarmin ke kin san bana san abinda zai tab'a min lafiyarki, maimakon ta bashi amsa akan abinda yace, sai tace " kana ganin idan akayi haka zamu cimma burinmu?
"Eh! to bani da tabbas 100% amma ina da 80% na hakan, dan zayyi tunanin kamar zamu jawo mishi magana sai yayi saurin d'aura mana aure,
gefe ta zubawa ido tana kallan k'asa kamar me nazarin k'asa ta jima a haka sannan ta sauke ajiyar zuciya a hankali tace " na amince....!,
idonshi kanta yana san ta bashi damar kallan cikin kwayar idonta amma ta hanashi ta hanyar k'in kallanshi,
sai da ya sassauta muryarshi yace " ki barshi kawai My Life bana san kiyi abinda hankalinki bai kwanta akai ba, mu hak'ura kawai tunda kina kokwanto,
salon yadda yayi maganar ya karya mata zuciya sosai, ta d'ago kanta ta kalleshi had'i da cewa " ba damuwa na amince,
ba musu ya zagaya ya bud'e mata mota ta shiga, shima ya zagaya ya shiga yaja motar suka bar wajen,
duk abinda ya faru akan idon Safiyyah yi tayi kamar ta koma ta sanar da iyayen Basmah halin da ake ciki, " kul karki soma, cewar wata zuciyar,
cikin nutsuwa Zaman yake jan motar dukkaninsu sunyi shiru sai sautin redio dayake tashi,
a harabar wani k'ayataccen joint yayi parking, ya kalleta fuskarshi d'auke da murmushi yace " nan yayi maki?
Martanin murmushinshi ta mayar mishi tana kallan wajen, jikinta a sanyaye ta soma bin wajen da kallo,
Basmah da tunda take bata tab'a keb'ewa da d'a namiji ba sai yau, balle har tazo irin wad'annan wajajen taji zuciyarta na yamutsawa,
kanta ta d'aga mishi alamar eh, cikin nutsuwa ya fita ya shiga wajen, bai jima ba ya dawo,
ya bud'e mata motar ta fito suka jera kanta k'asa dan gani take kamar ita kad'ai ake kallo,
wani irin yanayi take ji ajikinta wanda ya sata taka k'afarta dakyar,
VIP suka shiga wajen yayi kyau sosai ya k'ayatu da kayan alatu, babu kowa sai su kad'ai, " zauna, yace yana ja mata kujera, ba musu ta zauna,
" me zaki ci?
Ya tambayeta bayan sun zauna, kanta k'asa tace " babu komai, " ina san kunyar nan taki Dear, tana burgeni sosai, murmushi tayi batare datace mishi komai ba, d'an shiru ne ya tsara, kafin ya kira sunanta " Basmah!,
ji tayi muryarshi ta daki zuciyarta, kanta k'asa tana wasa da yatsun hannunta ta amsa " na'am,
k'ara lankwasa muryarshi yayi cikin salon jan hankali yace " d'ago ki kalle ni, ba musu ta d'ago kanta karaf idanuwansu suka sark'e cikin na juna,
wani abu taji yana tsarga mata a sassan jikinta, taji wani abu yana fitowa daga cikin kwayar idonshi yana shiga cikin tata kwayar idon yana ratsawa tsakiyar kanta,
yana huda kwakwalwarta yana shiga cikin jikinta, jin bazata iya jure kallan kwayar idonnashi ba yasata sunkuyar da kanta k'asa,
" me kika gani cikin kwayar ido na?
Shiru tayi dan bata jin zata iya had'a kalaman bakinta tayi magana, " nasan babu abinda kika gani sai tarin zunzurutun soyayyarki,
babu abinda yake cin zuciya da ruhi na sai sonki Basmah, dashi nake kwana dashi nake tashi, babu wani abu mafi dad'i da muhimmanci a wajena kamar soyayyarki,
dan Allah kada ki bari a raba mu kada ki bari a shiga tsakaninmu please, i love you, i really really love you more & more most kece rayuwata idan babu ke nima babu ni,
idan babu ke ni ba komai bane, yayi maganar hawaye na gangaro mishi, take Basmah ta fara jinta tana reto a sararin samaniya,
ta jita ita ba'a sama ba ita ba'a k'asa ba, sassanyar iska ta fara kad'a mata, so da k'aunarshi suka rink'a shiga cikin kwanyarta, yana ratsa b'argo da tsokar jikinta,
" in sha Allah bazan tab'a bari a raba mu ba, ina tare dakai a kowanne hali, tayi maganar cikin mayen so, " thank you, thank you so much Basmah,
ya fad'a cikin zumud'i, five alive na jarka ya bud'e ya zuba a glass cup ya mik'a mata, bata san yi mishi musu dan kota so yi mishi musun zuciyarta bazata bari ba,
ta amsa wajen amsa hannunsu suka had'u mugun shock suka ji a sassan jikinsu tamkar wutar lantarki ta ja su,
da sauri ta janye hannunta tana jin bak'on al'amari na ziyartar gab'ob'inta, Zaman kam kasa motsi yayi, sai dakyar yayi controlling kanshi ya aje cup d'in a saman table yace " kisha!,
suna hira sun luma cikin duniyar soyayya har lokaci yaja batare da sun sani ba, sai k'arfe takwas sannan suka mik'e da niyyar tafiya gida,
ta taka k'afarta ta gurd'e tayi baya zata kifa, cikin zafin nama Zaman ya tare ta, ta fad'a jikinshi, gaba d'ayansu sukayi baya ta fad'a saman k'irjinshi,
yarrrr suka ji a duk ilahirin jikinsu, suka ji shock yaja su tun daga tafin k'afarsu har zuwa tsakiyar kansu,
kansu ya shiga amsa kuwwa yayinda suka rink'a jin rugugi cikin kunnuwansu, jikinta a sanyaye ta mik'e cike da kunya tana gyara hijabinta,
dakyar zaman ya iya tashi jikinshi yayi mugun yin sanyi, bayyi mata magana ba ya zagaya ya bud'e mata mota, ta shiga ya mayar da murfin ya rufe kana ya zagaya ya shiga,
kowannensu yayi shiru yana saka abubuwa da dama cikin ranshi, " tunda nake a duniya ban tab'a jin abinda naji akan mace yau ba,
d'an satar kallanshi tayi taga kamar bashi ne yayi maganar ba, hankalinshi na kan tuk'in ya kuma cewa " ban tab'a sha'awar wata 'ya mace ba,
asalima bana sha'awar mace, ban san yadda akayi naji abinda naji akanki ba, kece ta farko kuma kece ta k'arshe, yayi maganar idonshi kan titi,
cikin rashin fahimta ta kalle shi kamar zatayi magana sai ta fasa, har suka isa gida babu wanda ya kuma cewa komai, sai dai ta lura da yadda jikinshi yayi sanyi sosai.
Tunda akayi la'asar Basmah bata dawo gida ba hankalin gaba d'aya 'yan gidansu yayi mugun tashi musamman Ya Mu'allim da Umma,
hankali a tashe suka je makarantar suka tambaya ko lafiya, shugaban makarantar ya bincika aka sanar dashi bata zo makaranta ba,
ya sanar dasu bata zo makaranta ba yau, ba k'aramar kunya Ya Mu'allim yaji ba, daga makarantar gidansu Safiyyah suka nufa direct anan tayi musu bayanin duk abinda ke faruwa,
tun daga ranar da suka fara had'uwa da Zaman har yau, jiki a sanyaye suka koma gida, ranar kam sun shiga mummunan tashin hankali,
dan azatansu guduwa Basmah tayi, Ya Mu'allim dasu Umar suna tsaye a k'ofar gidq suna shawarar abinda ya kamata suyi motar Zaman ta faka a k'ofar gidan,
ganinsu a k'ofar gida gaba d'ayansu ba k'aramin tsorata ta yayi ba,gabanta ya shiga fad'uwa yana dukan uku-uku, " ki daure ki tattaro gaba d'aya k'arfin gwiwarki ki saka a jikinki dan ta wannan hanyar ne kad'ai zamu samu damar mallakar juna,
ya fad'a cikin karyayyar murya, cikin sanyi jiki ta fito kanta a sunkuye ta kasa d'ago kanta, gwiwarta tayi sanyi ji take tamkar tana taka k'ank'ara, tazo gaf dasu zata wuce Abubakar ya yunk'ura da niyyar cafkarta,
Ya Mu'allim yayi saurin girgiza mishi kai, bayan ta shige gidan suka mayar da kallansu ga Zaman dake tsaye yana kallansu, a hankali ya saki ajiyar zuciya a fili ganin ta shige gida lafiya,
bayyi magana ba ya shige motarshi yaja yabar wajen, Umma na tsaye tsakar gida ta kasa zaune da tsaye Basmah ta shigo kanta k'asa yayinda take jinta wani iri kamar wacce aka kama tana zina,
" Assalamu Alaikum..!, Umma na watsa mata kallan tuhuma tace " daga ina kike?
Shigowar su Ya Mu'allim ta hana Basmah magana, " meyasa Basm....!, " bana ce kada wanda yayi magana ba?
Cewar Ya Mu'allim yana katse Aliyu, sunkuyar da kai Aliyu yayi yace " kayi hak'uri, cikin bada umarni Ya Mu'allim yace " na riga na gama yanke hukunci, dan haka kada wanda yace mata komai,
bai jira abinda zasu ce ba ya shige ya barsu anan, " kiji tsoran Allah Basmah, ki guji sakamakon abinda kike shirin aikatawa,
Umma ta fad'a tana share hawaye, zata kuma yin magama Abubakar da Umar suka rik'eta suka shigar da ita ciki, Aliyu ya bi bayansu,
a sanyaye Usman ya rik'e hannunta yaja zuwa bedroom, " ki canja kaya, bai jira tayi magana ba ya fice, ya shiga kitchen ya zubo abinci a plate da ruwa ya kawo mata,
yadda ya barta haka ya dawo ya sameta, " ki ci abinci ki kwanta kinga dare yayi, jiki a sanyaye ta bud'e baki zatayi magana, Usman yayi saurin ficewa bai jira jin abinda zata ce ba,
bayan tayi wanka ta ci abinci ta kira Zaman ta bashi labarin duk abinda ya faru, cikin zumud'i Zaman yace " kin gani ko?
"Dama na fad'a miki zamuyi nasara, so karki damu, " ina jin tausayin Abba da Umma, ina jin babu dad'i a jiki na, na rasa meyasa hankali yak'i kwanciya,
sai da ya karya murya kafin yace " ni ma bana jin dad'in abinda ke faruwa Basmah,
dole ce tasa muke yin hakan bana son muyi iskanci, tunda ke a al'adarku abun kunya ne, cikin rashin fahimta tace " a al'adarmu kuma?
"Kai ba al'adarku bace?
"Kuma ai ba al'ada ce tazo da haka ba, addini ne yazo mana da hakan, a bisa fad'ar Allah da koyarwar fiyayyan halitta,
" na sani mana, ina nufin al'ada da addini, zatayi magana yayi saurin cewa " ki kwanta zuwa gobe mayi magana,
" ni fa na tsorata da hukuncin da Abba yace ya yanke, tayi maganar so calm, " no karki damu babu abinda zai faru zai alheri kinji?
A hankali ta d'aga mishi kai kamar yana gabanta, sun dad'e suna hira kafin sukayi sallama, washe gari da wuri ta shirya cikin uniform tana k'ok'arin fita ta jiyo muryar Ya Mu'allim na cewa " ina zaki?
Take duk ilahirin jikinta ya d'auki rawa, har hartar cikinta sai da ta motsa, muryarta na sark'ewa tace " ma......ma...makaranta,
fuskarshi d'auke da murmushi yace " ai kin gama zuwa makaranta Basmah, in dai a gabana ne, ban sani ba idan mijiki zai barki ki cigaba da karatu amma ba dai agabana,
wani abu taji ya tsarga mata tun daga tafin k'afarta har tsakiyar kanta,
cikin tashin hankali ta kalli Ya Mu'allim had'i da fasa kuka, " dan Allah Abba karkayi min haka, kayi hak'uri karka cire ni daga makaranta,
bai kula da abinda take cewa ba yace " na baki sati d'aya ki fito da miji kowaye zan aura miki shi amma banda Zaman, indan sati d'aya ta cika baki fito da miji ba zan aura miki duk wanda naga dama,
ya mayar da kallanshi ga Umma yace " ki kula da ita karki bari ta fita ko k'ofar gida, yana kaiwa nan ya shige bedroom,
fad'ar tashin hankalin da Zaman ya shiga bayan Basmah ta sanar dashi Ya Mu'allim ya hanata zuwa makaranta bazai fad'u ba, dakyar ya tattara nutsuwarshi ya rarrashe ta,
" kiyi hak'uri Basmah bamu da ikon yiwa kanmu komai sai abinda k'addararmu tayi,
amma ina baki tabbacin muddin aka raba mu mutuwa zanyi, Basmah kece rayuwata bani da kowa a duniya saike,
kece ahalina Basmah kece uwata kece ubana ban tab'a kiran kowa nawa ba saike babu wanda ya tab'a kira na da nashi sai ke,
karki bari a rabamu please, duk k'arfin halin da Zaman yakeyi wajen danne zuciyarshi kasawa yayi ya fashe da kuka yana fad'ar ina sanki,
shi kuka ita kuka babu mai rarrashin wani sun d'auki lokaci a haka kafin yayi k'arfin halin share hawayenshi, ya shiga rarrashinta.
Bayan kwana biyar sosai Zaman da Basmah suka shiga damuwar rashin ganin junansu, dan tunda suka had'a basu tab'a dad'ewa haka batare da sunga juna ba,
ga takunkumin tsaron da aka saka mata a gida, Umma da Yayyanta sun saka mata ido sosai suna kula da duk wani motsinta,
ko waya sai k'afa ta d'auke suke yi, ta k'ara figewa ta rame kallo d'aya zakayi mata kasan tana cikin damuwa, yayinda a cikin Yayyanta Usman kad'ai keyi mata magana,
da misalin k'arfe biyu saura na sare Basmah na manne da waya a kunne tayi kwanciyar rigingine idonta a lumshe while fuskarta d'auke da murmushi,
" nayi kewarki sosai, nayi kewar ganin kyakkyawar fuskarki da k'ayataccen murmushinki.
" Nima haka, ina kewarka sosai masoyi na, ta fad'a a hankali.
" Idan da gaske kina san gani na meyasa baki tab'a cewa nazo na ganki ba?
"To ai babu dama ne, su Ya Umar sun saka min tsaro sosai, " ko yanzu ba damar?
A d'an tsorace ta zaro idonta tana cewa " yanzu fa kace?
"Eh! ki bani dama ki gani idan ban zo ba, idonta kan agogo tace " biyu na dare fa!?
"Ko ma yaushe ne kice ki gani idan ban zo ba, " a'a dear ka bari dare yayi ina tsoran karka taho wani abu ya same ka, " ko kuma kice kina tsoran fituwa ba, " ba haka bane ka bari kawai,
" karkiyi bacci ina zuwa, bai jira abinda zata ce ba, ya kashe wayar, k'arfe biyu da rabi na dare Zaman ya k'araso k'ofar gidan, ya kira wayarta,
bugu d'aya tayi picking na k'araso, " wai da gaske !?
Ta fad'a tana zaro ido cike da tsoro, " da kin zata da wasa nake?
"Kin ganni nan a k'ofar gidanku ki lek'o kota window ne naganki please, " baiyiyu Zaman, ya za'ayi na fito k'arfe uku saura na dare?
"Gaskiya ina jin tsoro, ta fad'a a d'arare, sai daya runtse idonshi ya bud'e sannan yace " ni dana biyo hanya cikin dare bance dare yayi ba saike da lek'owa kawai zakiyi?
"Dama nasan ba wani so na kike yi ba, nike ta haukana, ya fad'a kamar zayyi kuka, " ba haka bane ina gudun b'acin ran Abba da Umma ne kuma kaga su Yay.....!,
" haka ne gwara da kika tunamin bani da kowa, bani da wanda zanji tsoro, baji da wanda zayyi kuka dan wani abu ya same ni, ya k'arashe maganar kuka na kufce mishi,
cikin sanyin murya da karyewar zuciya tace " kayi hak'uri ba abinda nufi kenan ba, kayi hak'uri bari na fito.
"A'a ki barshi bari na tafi, batayi magana ba ta kashe wayar, mik'ewa tayi ta saka hijabi ta lallab'a ta bud'e k'ofar d'akinta ta fita,
cikin sand'a ta rink'a bin bango tana nufar k'ofar falo harta isa tana tab'awa taji ta a b'ud'e, bata b'ata lokaci ba ta fice daga falon ta fita tsakar gida,
jin an bud'e k'ofa yasa su Ya Mu'allim dake jam'in sallar dare kallan k'ofar, ba k'aramin mamaki ne ya kamasu ba ganin Basmah na nufar k'ofar gida cikin sand'a,
da sauri Umar da Abubakar da Aliyu suka zabura Ya Mu'allim yayi saurin dakatar dasu ta hanyar nuna musu hannu alamar suyi shiru kada suyi motsi,
" kana gani zata fita Malam?
Umma ta fad'a cikin karyayyar muryar da alama kuka na gaf da kwace mata, da sauri ya d'ora yatsa a saman labb'anshi yace " shhhhhhhh!,
cikin sand'a Basmah ke bin bango harta fice daga gidan dan kwata-kwata bata lura dasu ba, idonta ya gama rufewa ta manta ranar alhamis daren juma'a suna sallar dare, idan suka tashi tun k'arfe 3 na dare ba'a komawa sai alfijir ya keto, tana ficewa ya kalli su Aliyu yace " ku tashi mu bita,
jiki na rawa suka mik'e zambur dan Allah Allah suke su bitan in banda ya dakatar dasu tunda farko da tuni sun cimmata,
tsaye ta same shi ya kifa kanshi a jikin mota yana rusgar kuka, " nina b'ata maka rai ko?
Ta fad'a a sanyaye, cikin kuka ya fad'a jikinta ya manneta da k'irjinshi yana fad'in " bani da kowa Basmah, bani da kowa a duniya shiyasa kowa yake k'ina,
taso ta zame jikinta ta kuma hana shi rungumarta, amma ganin halin dayake ciki ya hanata, " ka......ka....kayi hak'uri, ta fad'a muryarta na sark'ewa saboda bak'on yanayin dake ziyartar jikinta,
k'ara matse ta yayi gam da jikinshi tamkar wanda yake san tsaga k'irjinshi ya saka ta ciki, turus sukayi gaba d'ayansu ganin abinda yake faruwa Umar ya kalli Usman, Aliyu ya kalli Abubakar kafin gaba d'ayansu suka mayar da kallansu ga Ya Mu'allim..............
*KADA DAI A MANTA NA KUD'I NE, IYA KUD'INKU IYA SHAGALINKU.....*
MOMYN ZARAH 'YARBAWAI