20
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
2️⃣0️⃣
Gira d'aya ya d'age mata had'i da sakar mata shu'umin murmushi yana cije lips d'inshi yace " ya dai 'yan mata ko kin kyasa ne?
Fuskarta dake tsuk'e ta k'ara turb'unewa tace " naga d'aki d'aya ne a gidan ya za'ayi ya ishemu dani dakai da wannan daka kawo?
Kafin Zaman yayi magana Shakira ta zaro ido tana fad'in " nice wannan?
"Karki kuma, karki sake koda wasa, dan na wuce wannan a wajen Zaman, har ke da kike 'yar karere dake a wajenshi zaki ce man wannan dan rainin hankali?
A hasale Basmah tace " kar'in kuma ko kuma karmu kuma?
"Dashi nake magana badake ba dan haka kema karki kuma ina magana dashi ki saka min bak......!, bata k'arasa ba taji saukar mari a kuncinta,
zafin mari ne yasa Basmah rud'ewa ta kid'ime ta dafe kuncinta, ganin bashi da niyyar yin magana yasa Basmah yin kukan kura,
ta aftakawa Shakira, da sauri ya shiga tsakiyarsu ya hankad'e Basmah ta fad'a baya, ya nunata da yatsa yana fad'in " kul karki soma cewa zakiyi min iskanci da fitsara,
in ba haka ba ke zaki sha wuya, cikin kuka tace " ni Zaman ni akan karuwa Zaman, ta fad'a tana nuna kanta, " ke d'in fa, ke har wata ce ta musamman a waje na?
" Ke bazaki bani had'in kai ba kuma na kawo wacce zatabani dan mugunta shine kike neman nakasata,
da ido ta kafeshi tana jefa mishi kallan k'iyayya, batare data kuma magana ba, tsaki yaja yana barin wajen hannunshi cikin na Shakira,
Basmah tabi bayansu da kallo, cikin sanyin jiki ta d'aura alwala taja k'afarta a hankali ta shiga d'akin, yadda ta gansu ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba,
ta tsaya cak a bakin k'ofar hannunta rik'e da labule, numfashinta ya soma k'ok'arin d'aukewa,
zindir ta iske su Shakira na sucking joy stick d'inshi, " dan Allah Malama in zaki shigo ki shigo, da sauri ta juya had'i da saka hannu ta toshe bakinta,
saboda kukan dake k'ok'arin kwace mata, wani iri take gani, kunnuwanta suna mata dummmmm, ta diririce ta rasa inda zata nufa, ta d'aga k'afarta zata fita taji an fisgota da k'arfi an warb'ar da ita gefe,
" zauna nan ki kalle mu ki koya, kiga yadda akeyi tunda ke baki iya ba, babu abinda kika iya banza lusara, kuma wallahi kika sake kika kawar da kanki ko kika d'auke idonki saina lahira ya fiki jin dad'i,
da k'arfi Basmah ta saki kukan bak'in ciki me cin rai, had'i da mik'ewa tana fad'in " ko zaka kashe ni wallahi bazan zauna kuyi zina a gabana ba,
bazan kalli tsiraici ba.... tau... tau ya kifa mata mari had'i da fisgo gashin kanta da k'arfi cike da mugunta ya gwara kanta da bango,
yana cewa " ni zaki yiwa iskanci?
"Wallahi idan kika ce zakiyi min rashin kunya wuya zaki sha a banza, yana maganar yana take mata wuya da iya k'arfinshi,
take jikinta ya d'auki rawa yana kerrrma ta soma kakarin mutuwa tana kiciniyar kwacewa, amma ta kasa,
Shakira na gefe na dariyar mugunta ta janyo Zaman ya fad'a kanta tace " rabu da ita karta b'ata maka rai a banza,
zo muji dad'i, zamuyi lokacinta daga baya, ta k'arasa maganar tana had'e bakinsu, a gaban idon Basmah Zaman da Shakira suka nemi junansu,
suka biyawa juna buk'ata ta gaba da baya, wa'iyazubillah, dole ce tasa Basmah tsayawa a d'akin dan bazata iya mik'ewa ba, ko motsi bata iyawa,
bata gama tabbatarwa kanta waye Zaman ba sai yau daya kusanci mace karuwa ta takashi, bata gama tsinkewa da lamarinshi ba,
sai yau dataga yana zina da mace akan idonta ba kunya ba tsoran Allah, wani irin kukan mutuwa Basmah ta fasa tana buga kanta,
yadda take kukan ne zai tabbatar maka da tagaji da duniya da abinda ke cikinta, ta tsani kanta da rayuwarta, ta gwamci mutuwa sau dubu akan bak'ar rayuwar da take yi,
basu ko kalli inda take ba balle su san Allah yayi ruwanta, fuska Shakira ta yamutsa tana kallan Zaman tace " wannan shegiyar fa ta dame ni bacci nake san nayi, kana ganin har sha biyu saura na dare,
ta hana mutune bacci da ihuuu, bayyi magana ba ya mik'e ya rik'e k'afar Basmah d'aya yaja ta a k'asa yakai waje yajefar da ita,
ya dawo d'akin ya kwanta, bai damu da ruwan saman da ake shek'awa tun bayan sallar ishaa ba, itama batayi k'ok'arin mik'ewa ba,
yadda ya barta haka ta kwana a wajen bata motsa ba, ruwan saman da aka kwana anayi ya k'are akanta, tana kwance a inda yayi jefa da ita, dakyar taja jikinta zuwa ban d'aki,
ta shiga tayi wanka ta shiga d'akin ta canja kaya, tana niyyar rab'awa ta kwanta a k'asa saman yaloluwar taburmar data fatattake,
taji muryar Shakira na cewa " d'ora min ruwan wanka, ki had'a min ki kai min band'aki, ki kuma had'a min abun karyawa,
bata kalli inda suke ba sai a lokacin sunyi lumtsum saman katifa rufe da bargo da gani babu kaya a jikinsu,
suna rungume da junansu, maganar Zaman ce ta katse mata tunani " baki ji abinda tace miki bane?
"Ko saina taso kanki na had'a miki jini da majina dan na lura ke jaka ce bakiyi saida duka, tasan halinshi sarai dan haka ta mik'e ta fita,
tana jan k'afarta, da jikinta dayayi mata tsami duk inda ta juya kota tab'a a jikinta ji take kamar ranta zai fita saboda azaba.
**********************************
Nayan da Nashwan zaune a babban parlour suna facing juma da Hajiya Tanya, jin basuyi magana ba yasa Nashwan yin gyara murya had'i da cewa " kun kira ni kunce zamuyi magana kun sani gaba babu wanda yace min komai tun d'azu ina fatan lafiya?
Glass cup d'in hannunta ta aje a saman centre table d'in dake gabanta, ta fitar da numfashi a fili ta zuba mishi ido tana fad'in " na samo mana hanya mafi sauk'i ta cika burinmu,
cikin rashin fahimta Nashwan ya kalleta yana nazartarta yace " ban gane abinda kike nufi ba, murmushi tayi me sautin dariya kana ta kwashe komai ta fad'a mishi,
shiru yayi na d'an lokaci kafin yayi ajiyar zuciya a fili cikin ranshi yana jinjina shu'umancin Hajiya Tanya, ganin yayi shiru yasa Hajiya Tanya cewa " ya kayi shiru ko shawarar tawa batayi bane?
"Abinda yasa nace a aura mishi Shakira kasan mace da mijinta sai Allah, kuma kasan karuwa da iya bariki, kissa da kisisina, cikin sauk'i,
Shakira zata shawo kanshi ta karb'ar mana abinda muke so, tunda ta fishi wayo da bud'ewar ido,
harta dasa idonta yana aika mata da shu'umin kallo mai karya zuciya, saida tayi yace " to kina ganin Shakiran bazatayi mana halin d'an Adam daga baya ba?
"Kamar Yaya?
Idonshi cikin nata yana kallan idonta, bai bata amsar tambayar data yi mishi ba, ta cikin kwayar idonshi ta karanci abinda yake nufi, " wai kana nufin zata iya butulce mana a gaba?
Da idon dai ya tsareta batare da yayi magana ba, rolling idonta tayi tana cewa " ka tsare ni da ido kasa duk na duburburce,
kayi min magana yadda zan fahimta, murmushi ya d'anyi had'i da sake tsareta da idon yana cewa " tsareki da idon yana da amfani kenan tunda gashi kin fahimci abinda nake nufi ta cikinsu,
zamanta ta gyara tare da turo d'an kwallin kanta gaban goshi tace " idan haka kake nufi baza mu bata k'ofar da zata samu damar yin hakan ba,
dan zanbi duk wata kafar da zata samu dama na toshe ta, kuma ma yanayin yadda zan bi da ita, nayi mata ruk'on talala bazatayi tunanin cin amanarmu ba,
" yanzu meye next?
Nayan ya fad'a cike da k'osawa da maganar, " kiranta zamuyi muyi magana da ita mu tsara mata yadda muke so, idan ta amince muyi aiki da ita, " idan haka ne me muke jira?
"Kin san fa ance da zafi-zafi kan bugi k'arfe, ki kirata a daddale asan inda aka tsaya, dan shawo kanshi ma ya aureta kad'ai b'ata lokaci ne,
" yanzu kuwa!, Hajiya Tanya tace tana d'aukar wayarta, ta kira layin Shakira, had'i da sakawa a hand free, saida ta kusa tsinkewa sannan akayi picking,
da alama har lokacin bacci takeyi, " ke ki warware babbar harka za'a buga ta Billions of Dollars, da sauri Shakira ta ware ta mik'e zaune,
had'i da cire wayar daga kunnenta ta duba number da aka kira ta, sake mayar da wayar tayi kunnenta, tana fad'in " waye!?
"Wacce irin harka ce tazo harta Billions of Dollars?
"Idan kin shirya zaki yi, ki same mu a Central Hotal bayan sallar ishaa, muyi miki k'arin bayani, kafin tayi magana Hajiya Tanya ta kashe wayar,
kallan juna sukayi ita da Zaman dan yaji yadda sukayi, tace " su waye wad'annan?
"Kya tambaye ni, ina zan sani?
"Ke fa aka kira ba ni ba, zatayi magana yayi saurin cewa " ke ina ruwanki da ko suwaye, ke dai ba kud'i kike so ba, sai kije kiji abinda zasuce miki,
Hajiya Tanya ta kalli Nayan da Nashwan tana aje wayar tace " to ku zama cikin shiri da an sallar ishaa zamu tafi, cikinsu babu wanda ya amsa,
ta nuna Nashwan tace " idan muka gama da Shakira ni da kai zamuyi aikin shawo kan waccen d'an iskan me taurin kai kamar kafiran farko,
murmushi Nashwan yayi me sauti had'i da kashe mata ido yana lasar lips d'inshi cikin karyayyar murya datasa tsikar jikin Hajiya Tanya tashi yace " sai yanzu kika san haka?
Kasa motsi tayi illa kallanshi da take tanajin wani abu na tsarga mata, ganin irin kallan maitar da take yi mishi yasashi tuntsewa da dariya had'i mik'ewa ya fice, tabi bayanshi da kallo tana had'iyar yawu.
**********************************
Ana idar da sallar Magrib Shakira ta shirya tana shirin fita Zaman yace " zaki dawo ki kwana anan kona kira GOGA da GARBU su tayani kwana?
"Jarababbe kawai kaida baka iya hak'uri, saika kira su, dan innaga ci acan zan tsaya kasan ni idan naga malasa ba dama, bayyi mata magana ba,
ya ciro wayarshi ya latsa kiran Garbu, ta fice abinta, kalle-kalle ta tsaya tana yi kasancewar wajen akwai mutane yasa ta rasa inda zata nufa,
" kingata can, Nayan ya fad'a yana nunawa Nashwan da Hajiya Tanya Shakira, batayi magana ba ta kira layin Shakiran, bugu d'aya ta d'aya,
" juyo baya ki biyo hanyar damanki ki shigo d'akin hagu, muna kallanki ta window, batayi magana ba ta kashe wayar,
tana shiga d'akin da Nayan ta soma yin arba kafin idonta ya sauka akan matar datace zata bata kwangilar kisan Nayan d'in,
da k'arfi gabanta yayi muguwar fad'uwa, tayi saurin juyawa zata zunduma da gudu, Nashwan dake kusa yayi wuf ya rik'eta, sosai tsoro yayi mugun kamata,
amma ta dake ta hankad'e Nashwan tana fad'in " dalla Malam lafiya?
Idan ba mai kula ne kai ba bazaka tab'a kula da tsoron da Shakira ke cike ba, ta daure ta shanye tsoranta, abinka da 'yar bariki me rawa a club cikin 'yan giya,
" karki damu zo ki zauna muyi magana nina kira ki a waya, Hajiya Tanya ta fad'a tana murmushi, a shagub'e tana yamutsa fuska Shakira ta kalli Hajiya Tanya tana fad'in " wacece ke!?
"Mahaifiyata ce!, Nayan ya amsa mata, ido ta zaro tana cewa " itace Tanya?
Dan tana samun labarin duk wani mugun k'ullin Hajiya Tanya a wajen Nayan, tasan makirci da tuggunta, fuskar Hajiya Tanya d'auke da murmushi ,
tace " da alama labarina na iske ki har gadan baccinki, Shakira batayi magana ba, ta zauna akan d'aya daga cikin kujerun wajen,
ganin babu wanda yace komai sun kafe ta da ido, yasata cewa " da alama baku da aikinyi, idan baku dashi ni ina dashi,
kun barni a duhu, ke kinzo kin same ni da maganar kashe Nayan, shi kuma yace min ke mahaifiyarshi ce, na kasa gane komai,
" dukkanmu nan abunyi ne ya had'amu anan, dan haka babu marar aikinyi, maganar kuma kisa na gwada ki ne dan inga ko zaki iyayi mana aikinmu yadda ya kamata,
kuma kamar yadda ya gaya miki nice mahafiyarshi Hajiya Tanya Yaseer, " wanne irin aiki zanyi muku?
Shakira tayi maganar idonta kan Hajiya Tanya, " wutar ciki, gaggawa da rashin hak'uri, Hajiya Tanya ta fad'a tana kawar da kanta gefe,
kafin tace " ki ragesu dan basu da amfani, Shakira batayi magana ba, ta zuba mata ido, batare da b'oyen komai ba, Hajiya Tanya ta fad'awa Shakira komai,
da irin aikin da zatayi musu, da mak'udan kud'ad'en da zasu samu, shiru sukayi bayan Hajiya Tanya ta gama fad'awa Shakira komai,
suka zuba mata ido suna jiran amsarta da jin ta bakinta, yalolun mayafin dake kanta ta cire, ta baza tulin k'arin gashin kanta,
had'i da d'ora k'afa d'aya kan d'aya, ta zare karan sigarin bakin Hajiya Tanya ta shak'a ta busa hayak'in tana kallan tabar tace " tana da illa ga lafiya, inji masu ita,
k'ara shak'ar sigarin tayi ta busa a tsakiyarsu tana fad'in " NA AMINCE ZANYI AIKI DAKU, murmushi Hajiya Tanya tayi hana karkad'a k'afa tace " zakiyi aiki damu ko kuma zakiyi mana aiki?
"Duk yadda kika ce haka ne, Shakira ta fad'a tana murmushi karta san kar, deep down tana cewa " dole na kula nasa musu ido a duk motsinsu,
na gama sanin takunsu dan wannan uwa da d'an shegu ne musamman uwar dan bana jin d'an shi zan iya dashi, amma uwar shegiya ce, dan haka dole nayi hankali da ita,
Nashwan yace " shi Ammar mutum ne me ra'ayin addini, dole sai dai kije masa a mumina, kamila kuma nutsatstsiya,
me tarbiya da kamun kai, " wannan ba matsala karka ji komai dan mun iya kowanne irin taku,
duk garin da muka je zamu iya zamu dasu, " un'un wannan daban yake da kowa, yana da hankali, wayo, lura da zurfin tunani,
dan haka sai kin iya takunki sosai in ba haka ba lokaci d'aya zai b'aroki, daga kallo d'aya zai iya gane wacece ke, " baka ji ana cewa mage me kwanciyar d'aukar rai ba?
"Ko bakaji ana cewa karuwa me ladabin kunama ba?
"Dan haka ka saka ido kasha kallo d'an matashin saurayi, ta k'arasa maganar tana shafo fuskar Nashwan,
d'an satar kallan Hajiya Tanya yayi aiko karaf suka had'a ido, daga yanayin fuskarta ya gane taji haushin abinda Shakira tayi mishi,
ya saki shu'umin murmushi had'i da kashe mata ido d'aya, ta kawar da kanta gefe, kallanshi ya mayar ga Nayan dake faman cika yana batsewa,
idonshi yayi ja saboda kishi..............!