21
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
2️⃣1️⃣
Basmah na kwance a k'asa kanta yayi mata nauyi kamar an d'ora dutse, dakyar take fitar da numfashi k'irjinta na sama da k'asa,
a buge ya shigo yana had'a hanya yana marisa, bata d'aga kai ta kalleshi ba saida taji alamar bashi kad'ai ya shigo ba,
idonta ta ware tana bin 'yan Daudun daya shigo dasu da wani irin kallo, had'i da k'ok'arin mik'ewa,
" karki damu 'yar uwa yi zamanki, d'aya daga cikinsu ya fad'a yana kallanta, bata kula shi ba ta dafa bango ta mik'e, had'i da kafe Zaman da ido,
yana layi ya taka ya had'e tazarar dake tsakaninsu, ya rik'e hab'arta da k'arfi, yana kallan lips d'inta yace " ki tsaya ki kalli yadda maza suka fiki iya bada had'in kai,
ya k'arasa maganar yana tsotsar lips d'inta cike da mugunta, batayi k'ok'arin kwace kanta ba dan bata da cikekken k'arfin da zata iya kokawa dashi,
sai da ya gaji dan kanshi kana ya saketa had'i da tura ta baya, d'aya daga cikin mazan ya k'arasa gaban Zaman yana rangwad'a da karairaya,
ya sanya hannu yana shafa k'irjinshi gami da cije lips irin na cikakkun 'yan bariki yace " muna kusa fa,
ya fad'a cikin salan d'aukar hankali idonshi kan lips d'in Zaman, murmushi Zaman yayi ya tallafo Goga sosai ya tsotsi lips d'inshi,
sororo Basmah tayi a tsaye kamar wacce aka dasa, ta kasa motsa koda d'an yatsanta, zuciyarta na wata irin muguwa da mugun k'arfi,
k'irjinta nayi mata zafi da rad'ad'i, mak'ogwaronta yayi mata d'aci-d'aci, mak'ak'i ya shiga taso mata, dakyar take iya shak'ar numfashi,
ta hancin, dole tasata bud'e bakinta ko ta samu isar ta isa ga hunhunta, tsikar jikinta ta tashi, k'ofofin gashin jikinta suka bud'e,
wanda yasa gashin jikinta mik'ewa, da mugun tashin hankali take kallansu Zaman dake neman junansu a gabanta.
Idonta taji yana yaji tamkar an watsa mata barkono, tashin hankali, tsoro da firgici suka sakata sakin bangon data dafa ta zube k'asa,
tunda take a duniya bata tab'a ganin tashin hankali irin na wannan ba, ko'a mafarki bata tab'a zatan iskancin Zaman ya wuce duk inda take tunani ba sai yau,
koda take ji ana fad'ar maza na neman maza, mata na neman mata bata tab'a gaskatawa ba, sai yanzu da ake yi akan idonta, da ta d'auka duk zance ne da shati fad'in mutane,
duk da ta ta karanta a karance, bata tab'a zatan hakan mai yiyuwa bane sai yau, akan idonta ake *D'UWAD'I*, amma babu yadda zatayi,
a gabanta k'attin maza ke neman junansu, su uku sun zage suna fasik'anci, suna aikata abinda Allah ya la'anci masu aikata su,
mala'iku suke tsinewa masu yi, Allah bai tab'a kifar da duniya saboda zina, sata, shan giya ba amma ya halakar da Al'ummar Annabi Lud'u saboda suna neman junansu,
abinda ko sunanshi aka kira sai al'arshen Allah ta girgiza, Ubangiji yayi fushi, sama ta fara tangal-tangal sai Mala'iku sun karanta Suratul Iklas,
kafin Allah ya huce saboda bala'inshi amma yau a gabanta, akan idonta, a gidan aureta, a d'akinta akan shinfid'arta ta aure aka aikata shi,
bata tab'a tsinkewa da al'amarinshi ba sai yau, bata gama sarewa ba kamar yau, yau kam ta tsorata matuk'a, taga bala'in dayafi k'arfinta,
lalle Zaman ya wuce duk inda take tunani, ya wucewa saninta, ta sara mishi, " group gay, anus sex, Zaman a gaba na, akan idona kake d'uwad'i da maza har biyu Zaman?
Abinda take san fad'a kenan a zahiri amma bazata iya ba, saboda harshenta dayayi mata nauyi, ya sark'e, d'if taji komai ya d'auke mata,
bata dawo cikin hayyacinta ba saida taji saukar marin daya sakata sakin fitsari dan ji tayi kamar an kwad'a mata rodi,
" bakiji abinda nake ce miki ba?
Goga ya fad'a yana girgiza k'ugu kamar mace, idanuwanta da suka gama bushewa saboda masifa ta d'ago, ganin garadan maza,
tub'e tsirara a gabanta babu ko kunya ya sata saurin kunyar da kanta k'asa tana fad'in " a'uzubillah, " wani abu ne haka?
Cewar Garbu yana jingina jikinshi dana Zaman, bata yi magana ba, sai idonta data runtse da k'arfi, tana jin k'iyayyar Zaman na huda zuciyarta,
yana bin magudanar jini da jijiyarta, yana gangarawa cikin b'argo da tsokarta, a halin yanzu duk duniya babu wanda Basmah ta tsana sama da Zaman,
da gaske ta tsane shi, tana jin k'iyayyarshi cikin komai nata, ta yadda ko ganinshi bata sanyi, sai yanzu ta gane dalilin dayasa shaid'an keyin tasiri a zuciyoyin wasu matan,
suna huda k'irjin mazajensu da wuk'a, sai yanzu ta gane dalilin dake saka wasu kashe kansu, sai yanzu ta gane dalilin dake saka wasu fara shaye-shaye,
sai yanzu ta gane illar biyewa san zuciya da rud'inta, sai yanzu ta gane illar sab'awa iyaye da bujirewa umarninsu,
sai yanzu ta gane dalilin dayasa Allah yace iyaye su zab'awa 'yarsu miji, sai yanzu ta gane dalilin dayasa Allah yace mu zab'awa 'ya'yanmu iyaye nagari,
sai yanzu ta gane illar biyewa gurb'atattun maza, ta yadda zasu samu damar yi maka illa su ruguza maka komai, su wargaza maka farin cikinka,
sai a yanzu ta gane ta tabka babban kuskuren da idan batayi da gaske ba zaita bibiyar rayuwarta harta koma ga Allah,
sai yanzu taga amfanin zuwa gaban iyaye a nemi auren mace, su bada aurenta da kansu, wato anfi darajata, da ganin k'imarta,
sai a yanzu ta gane komai, ta fahimci babbar illar da tayiwa kanta da rayuwarta, ta wargaza komai nata, ta lalata duniyarta, tasan bazata k'ara jin dad'in duniya da rayuwarta ba,
matsanancin kuka ta fashe dashe me ban tausayi tana fad'in " ka rabu dani da rayuwata Zaman,
ka fita daga duniyata, ka kauracewa ji da gani na, kabarni na rayuwa kamar kowa, please na rok'e ka, ka barni ta k'arshe maganar tana k'ara sautin kukanta.
" In barki fa kika ce?
"Kije ina da ciki na Basmah?
Murmushi yayi me kamar dariya yana rik'e da joy stick d'in Goga yace " ni dake mutu ka raba, mutuwa kad'ai zata raba mu,
matuk'ar kina raye ina raye a duniya banga abinda zai raba mu ba, cikin kuka tace " me nayi maka?
"Me nayi maka Zaman?
"Wanne irin girman laifi nayi maka dana cancanci wannan izaya da uk'ubar?
Zayyi magana Garbu yace " ni fa zafi ya dame ni, wanka nake sanyi, kallanta yayi k'asa-k'asa kana yace " ki tashi ki kai mana ruwan wanka band'aki,
sannan kizo ki kwashe condoms d'in nan da mukayi amfani dasu ki zubar,
ki gyara d'akin, ki d'ora mana girki yau muna da manyan bak'i, dan yau nan ne club gwara ma ki ware, 'yan caca na nan zuwa,
idonta cikin nashi ta tsare shi da ido tace " ni zan kwashe muku condoms, na gyara muku shinfid'a?
Sakin Garbu yayi ya nufota a zuciye yana fad'in " ko bazakiyi bane?
Ganin yadda ya nufota yasata mik'ewa dakyar dan tasan matuk'ar tayi mishi musu duka zataci, cikin kyama tana kuka ta durk'usa,
ta soma tsince condoms d'in, ta gyara musu d'akin tas, kana ta fita takai musu ruwan wanka bayin, tare su ukun suka shiga wankan.
*********************************
Hajiya Tanya na bedroom d'inta tana bacci ta jiyo muryar Ammar sama-sama a parlour, firgigit ta farka, had'i da kasa kunnenta danta tabbatar,
jin shine yasata saurin mik'ewa ta fita ta iskesu zaune shida Nashwan, tana gyaran zaninta tace " a'a yaran kirki yaushe ka shigo?
Kanshi k'asa yana murmushi ya gaida ita, ta amsa fuska wasai tana washe baki, ya mik'ewa yana cewa " dama shigowa nayi na gaidaki,
ganin yana shirin fita yasata saurin yin gyaran murya had'i da cewa " am dama ina nemanka, tsayawa yayi yana kallanta batare da yace komai ba,
yana jiran abinda zatace, kallan juna sukayi ita da Nashwan kafin tace " ka zauna mana magana nake san yi dakai, bayyi magana ba ya koma ya zauna,
idonshi kanta kamar me san gano wani abu, a dake cike da duniyanci kai tsaye tace " matar aure na zab'a maka, dan naga baka da alamar fiddo da mata,
a firgice ya mik'e kamar wanda aka cakawa mashi, lokaci d'aya walwala da fara'ar fuskarshi suka d'auke,
gumi ya tsatstsafo mishi a goshi, idonshi yayi jajir, ita kanta saida ta tsorata da yanayinshi amma ta dake ta d'ora da fad'in,
" 'yar k'awata ce naga yarinya ce me hankali da nutsuwa, tana da kyawawan halaye da d'abi'u shiyasa nayi maka sha'awarta, dannaga kamar zakuzo d'aya,
harta gama maganar ya kafeta da ido yana girgiza mata kanshi, lab'anshi na rawa,
da alama magana yake sanyi ya kasa, ya d'an jima a tsaye yana san had'a kalaman bakinshi ya kasa, dan haka ya fice daga parlour'n batare dayace komai ba,
" tashi ka bishi ka zuga shi, Hajiya Tanya ta fad'a da sauri tana mangarin Nashwan, saida ya sakar mata murmushin dake shagaltar da ita kafin ya fita,
a d'aki ya same shi kwance a k'asa ya had'a uban gumi idonshi lumshi kamar me bacci,
Nashwan yasan ba baccin yake ba, dan haka ya zauna kusa dashi had'i da dafa shi, ya soma magana a sanyaye.
" Why bazaka nemarwa kanka da makusanta sauk'i ba?
"Basmah fa matar wani ce tana gidan wani, da aure akanta, ya kamata ka manta da ita, ka rayu kamar kowa, ka nemarwa kanka gobe me kyau,
kada ka bari akan mace ka lalata rayuwarka, bayan ita tana can tana rayuwar farin ciki da jin dad'i da wanda take so,
wanda shine zab'inta, shine cikar muradinta, so grow up, ko haka zaka k'are rayuwarka ba aure?
Bai jira amsar Ammar ba ya cigaba da magana dan yasan ba samun amsar zayyi daga gare shi ba, " ya kamata mu girma mu wuce wajen Brother,
ni fa saboda kai nak'i yin aure har yanzu, kai na tsaya jira dan kar abun yayi maka yawa,
shekarunmu nawa kullum kwanan duniya shekarunmu k'aruwa suke yi, kuma ma koba komai ita Hajiya Tanya ai kayi mata kara,
idan kayi mata haka bazata ji dad'i ba, musamman yadda ta nuna damuwa akanka da halin da kake ci, bai kamata ka watsa mata k'asa a idonta ba,
duk hak'uri da kawaicin Ya Mu'allim saida ya gaji yayi mana maganar aure, nasan ido ya zuba mana, idan mukayi mishi haka sai inga kamar bamu kyauta ba,
zaiga kamar badanshi ya haifemu ba shiyasa muka tsallake maganarshi, itama Hajiya Tanya zataga kamar badan ita ta haifeka ba,
musamman da yanzu take kula dakai, so karka tsaya b'atawa kanki lokaci akan abinda baka da tabbas akanshi,
kuma ma idar har san nata kake yi da gaske ai zaka so abinda take so, a hankali Ammar ya bud'e idonshi dake lumshe ya zubawa Nashwan,
ya dad'e yana kallanshi deep down yana mamakin yaushe Nashwan ya fara yarda da Hajiya Tanya,
da har zai goyi bayan abinda tazo dashi, yana mamakin kalmar da Nashwan ya fad'a ta shi yake jira da tuni yayi aure,
a hankali ya fitar da numfashi had'i da juyawa Nashwan baya batare daya furta koda kalma d'aya ba,
" da gaske kai nake jira dan ina da wacce nake so, ka tsaya kana b'ata mana lokaci akan wacce bata sanka ba, tana can tana rayuwa mai dad'i,
Nashwan ya fad'a cike da tsokana, a fili Ammar ya fitar da numfashi, murya a sanyaye yace " bata rayuwar farin ciki da jin dad'i Nashwan,
na tabbatar duk inda take hankalinta ba'a kwance yake ba, jiki na ya dad'e yana bani hakan ga mugayen mafarkai danake yawanyi akanta,
" to Allah ya kyauta Father of reaction, ya fad'a yana kwanciya kusa dashi.
Washe da safe suna karyawa a BQ, Nashwan ya kalli Madu da Hajara yayi gyaran murya kafin yace " Baba kuyiwa Ammar fad'a baya jin magana,
a tare harda Ammar d'in suka kalli Nashwan, Hajara na fad'in " kamar yaya baya jin magana me yayiwa wani?
D'an zakud'awa yayi ya gyara zamanshi kafin ya fara magana " kwanakin baya Ya Mu'allim ya kira mu yayi mana maganar aure, ya kwashe yadda sukayi ya fad'a musu,
Madu yace " uhunnn muna jinka, " jiya Hajiya Tanya tayiwa Ammar maganar aure, baki Madu da Hajara suka had'a wajen cewa " wa!?
Kallansu Nashwan yayi ganin yadda suka tsorata yana fad'in " Hajiya Tanya mana koda wani abun ne?
" Wacce Hajiya Tanyan?
Cewar Madu, " wacce dai kuka sani, jiya take fad'a mishi ta samo mishi mata, 'yar k'anwarta ce, jinjina maganar Madu da Hajara sukayi cikin ransu,
cikin shakku Hajara tace " kaga rabani da matar nan, danni hankali na bai kwanta da ita ba, Nashwan zayyi magana Madu ya cafe da cewa " hala ka manta halinta ne da kake wannan maganar?
"Ko baka tsoran ta cutar dashi da hanyar matar da zata aura mishi, kasan halinta sarai batayin abu dan Allah, duk abinda kaga tayi akwai manufarta tayinshi,
zama ya gyara yana aje kofin hannunshi dayake shan shayi, yace " nasan yarinyar Baba, tana da hankali da nutsuwa, kuma ai tsakanin mata da miji sai Allah,
idan da wata manufar tayi sai kaga hakan ya zama alkhairi mugun abunta ya koma kanta ya kare mata can, tunda naga ana auren wacce ba musulma bama,
ana auren 'ya'yan wad'anda ba mutanen kirki ba saboda halin 'ya'yan nasu, harya dasa aya idonsu na kanshi, " ya akayi ka santa ni ban santa ba, bayan duk mutanen daka sani na sansu?
Ammar ya jefawa Nashwan tambayar, a dururuce yace " eh! amm.. ta dalilin Leenah na santa, idon Ammar kafe akanshi yana kallanshi abubuwa da dama nayi mishi yawo aka,
" idan abun arziki ne meyasa bata bawa d'anta ba, tunda naga tana da d'a miji itama?
Hajara tayi maganar tana kallan Nashwan, " amma naga.....! shigowa Shakira sanye cikin zumbulelen hijabi har k'asa ne ya hanashi k'arasa maganar,
cikin nutsuwa Shakira ta durk'usa ta gaida Madu da Hajara kanta a k'asa, tana sunne kai cikin hijabi, suka amsa fuska a sake,
tana durk'ushen ta juya ta gaida Nashwan da Ammar, Ammar bai amsa ba, sai Nashwan daya amsa, a kunyace tace " Baba d'an mukullin get za'a bani zan shigo da mota,
" muje na bud'e miki mana ai aiki na me,
" a'a ka barshi zan bud'e, mik'ewa Madu yayi yana fad'in muje na bud'e miki 'yata, cikin mutuntawa da girmamawa tana k'ara sunkuyar da kanta k'asa,
tace " dan Allah ka bari zan bud'e, ka k'arasa cin abincinka, ba kyau ana cin abinci ana tashi, ba musu Madu ya mik'a mata key d'in, yana cewa " nagode 'yata,
fuskarta cike da murmushi tace " bakomai Baba, ta fad'a had'i da ficewa, Madu ya koma ya zauna, Nashwan yayi murmushi yana fad'in " wannan ce yarinyar Baba,
da sauri Hajara da Madu suka kalle shi, Madu ya kalli k'ofa kamar zai sake ganinta yace " ikon Allah aiko mai hankali da sanin ya kamata,
Hajara tace " gaskiya kam, tana da kamala da nutsuwa indai itace nima ina goyan baya d'ari bisa d'ari, Madu ya kama hannun Ammar cikin nashi,
muryarshi a sanyaye yace " kamala da k'imar mutum bata cika ya zama cikekken mutum sai yana da aure,
Basmah matar wani ce a halin yanzu, dan Allah ka taimakemu mu k'arasa sauke sauran nauyinka daya rage mana, yayi maganar cikin karaya,
Hajara ta d'ora da cewa " nasan da mahaifinka da mahaifyarka suna raye da tuni kayi aure, dan nasan bazasu barka haka ba, zasu so ganin jikokinsu,
nima ina san naga kunyi aure tun ina raye, ina san naga yaranku nayi wasa dasu, idan kuma rowa kuke min saina mutu zakuyi to,
ta k'arasa maganar hawaye na zubo mata, jikin Ammar yayi mugun sanyi, ya rungume Hajara, yana shafa kanta yace " kiyi hak'uri Umma na, ki daina kukan, ki fad'i duk abinda kike so zanyi,
cikin muryar kuka tace " kayi aure, " shikenan abinda kike so?
"Idan nayi aure zakiyi farin ciki?
Hawaye na gangaro mata tace " eh, guntun murmushi yayi yana danne abinda ke taso mishi yace " zanyi aure matuk'ar hakan zai sakaku farin ciki, ya fad'a yana k'ok'arin mayar da kwallar dake san zubo mishi.........!