22
_*SAKI RESHE...!*_
*(CIGABAN GADAR ZARE)*
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
2️⃣2️⃣
Danne abinda zuciyarshi ke san bijiro mishi dashi yayi, ya k'ak'aro murmushi ya sanyawa fuskarshi yace " amma fa konayi aure bazan dena hawa cinyarki ba,
bazan dena zuwa cin abincinki ba, ba zan dena zuwa nayi miki kuka da shagwab'a ba, yadda yayi maganar ya basu dariya,
Hajara ta d'ago kanta daga jikinshi tana fad'in " a'a ai ni kuma na huta, idan surukata tazo saina bar mata kai,
taje tayi ta fama itama kafin jika na yazo ta yayeka, cikin shagwab'a yana san wankewa Hajara zuciyarta yace " Allah ban yarda ba,
ni anan ma zan rink'a kwana abuna, Hajara tayi dariya sosai, tana cewa " rufa min asiri ina zan ganka, kana can kana rawar kai akan amarya,
sai da ya tabbatar zuciyar Madu data Hajara ta wanke kana ya fita, suka bi bayanshi da kallan tausayi,
d'akinsu ya shige ya rufe k'ofa haka nan yaji yana san kasancewa shi kad'ai, Nashwan part d'in Hajiya Tanya ya wuce,
ya iske su zaune sunata busa hayak'in sigarin, tsakiyar Hajiya Tanya da Shakira ya zauna, yana jefa musu shu'umin kallo me narkar da zuciyar ma'abocin kalla,
muryarshi k'asa-k'asa kamar me busa sarewa cikin salan jan hankali yayi musu bayanin yadda sukayi, ya mayar da kallanshi ga Shakira yana fad'in
" kinyi k'ok'ari sosai fa, kin cancanci jinjina, ya k'arasa maganar had'i da kashe mata ido d'aya,
had'i da hura mata sassanyar iskar bakinshi, kad'an ya rage Shakira ta saki ihuu, dan ba k'aramin sanyaya jijiyon jikinta yayi ba, in banda itama 'yar hannu ce daya zautata,
kanshi ya juyar ga Hajiya Tanya ya d'ora kanshi saman kafad'arta had'i da hura mata iska a kunne, cikin kasala yace " yunwa nake ji,
dakyar tayi k'ok'arin had'a kalaman bakinta tace " ba...baka ci abinci ba?
Tayi maganar a rarrabe, rigarshi ya d'age ya kamo hannunta ya d'ora a saman shafaffan cikinshi yana cewa " shafa ciki na kiji banci komai ba,
ya fad'a a shagwab'e, jin hannunta saman fatar jikinshi, yasa jikinta d'aukar rawa, babban burinta ta ganta dashi a saman gado suna more rayuwa,
kasa d'auke hannunta tayi daga saman cikinshi, tayi sama da hannun tana shafo k'irjinshi, tana k'ok'arin had'e bakinsu,
ta jiyo motsin Leenah, saurin sakinshi tayi had'i da ja baya had'i da jan tsoki.
*********************************
Yau kam gidan Basmah ko Club bazai fad'a mishi shaid'anci ba, an taru anyi mak'il, maza da mata tsirarar Allah ana shaye-shaye da tik'ar rawa,
wajen k'arfe sha biyu da dare ya kalleta k'iri-k'iri ba kunya ba tsoran Allah,
yace " zamu fita fashi da makami yanzu, ki tabbata kafin mu dawo kin gyara d'akin nan, ki kwashe kalaban giya, da ragowar tabar wiwi, da condoms d'in nan,
ki dafa mana ruwan wanka ki aje mana, jikinta a sanyaye tace " yunwa nake ji, rabo na da abinci yau kusan kwana uku kenan,
" ni kinga naci abincin ne?
Kanta ta girgiza alamar a'a, yace " to!, bani da kud'i yanzu ma sata zamu, hanya zamu tare, ko muje gidajen manyan masu kud'i,
ga me k'arar kwana mu fasa kanshi da bindiga, idan kina buk'atar na abinci kina iya biyo mu, muje ayi fashin dake, yayi magana yana d'age labulen d'akin,
har ya sa kai zai wuce ya dawo da baya yace " ki wanke min kwalaben shishar can, bai jira amsarta ba ya fice, jikinta a sanyaye ta mik'e ta soma gyaran d'akin,
akan dole ta kwashe condoms d'in kace-kace da sperm, ta kwashe kwalaben giyar ta gyara komai, k'arfe uku na dare suka dawo,
kasancewar ana shek'a ruwan sama yasa bata ji motsin su ba sai ganinsu tayi a kanta, da sauri ta mik'e tsaye, dan ba bacci take ba,
k'arfin ruwan da akeyi bazai bar mutum yayi bacci ba, ruwa ake makawa sosai kamar da bakin kwarya harda k'ank'ara ga iska kamar zaata yaye rufin d'akin,
su shida suka dawo maza hud'u mata biyu, babu wanda ya kalli inda take balle yayi mata magana,
suka tub'e zindin gaba d'aya saboda kayan jikinshi a jik'e yake, d'aya daga cikinsu yace " ana cewa neman halak da wuya,
haram d'in ma ba baya ba, sauran suka saka dariya, suna shan giya da wiwi suna lissafa abinda suka samo, Zaman yace " banyi niyyar kashe wannan shegen ba, taurin kanshi ne yaja mishi,
Goga na dariya yace " ja'iri kaga yadda yake fuffukar mutuwa daka fasa mishi kai da bindiga, a buge suka fara neman junansu kamar dabbobi,
mazan na neman junansu haka ma matan na neman junansu, suna yiwa juna kiss, kafin daga baya suka cakub'e kowannensu na neman duk wanda hannunshi ya fad'a kanshi,
maza biyu na neman junansu, mata biyu na neman junansu, while maza biyu suna nemansu ta dubura,
babu abinda ke tashi a d'akin sai gurnaninsu, in banda kuka ya k'auracewa Basmah, zuciyarta ta dad'e da bushewa, da yau ihuu zatayi ba kuka ba,
a halin datake ciki gani take yi babu abinda zai tsorata ta koya bata mamaki, a fili take karanta duk addu'ar datazo bakinta,
a k'ufule Zaman ya danna mata ashar had'i da cewa " fitar min daga d'aki dan kan uwarki, batayi mamaki ba danya ce ta fita daga d'akin duk da ruwan da ake shek'awa dan ba wanne karo na farko da yake rokarata waje ana ruwa ba,
duk da haka tace " baka ji ruwan da ake ba zakace na fita?
"Kai sanin kanka ne in banda ana ruwa da bazan zauna ina kallan wannan k'azatar da rayuwar dabbobin da kuke yi ba,
kafin ta rufe baki Zaman ya fincikota da k'arfi, yana fad'in " k'azanta da rayuwar dabbobi ko?
"Kema shigo ciki ayi dake, ya fad'a yana jefata tsakiyarsu, kamar jira sukeyi gaba d'ayansu mazan da mata suka rufar mata,
kamar an jefa tsokar nama a garken kuraye, ihuuu take sosai da iya k'arfinta, tana kare jikinta, yana tsaye yana kallansu,
haka nan yaji bazai iya bari su keta mata haddi ba, " ita d'in tawace ni kad'ai, nine na fara sanin 'ya mace, kuma daga ni babu wanda zai kuma saninta 'ya mace,
duk wanda yayi gangancin yin hakan sai dai uwarshi ta haifi wani, dan sai na datse mishi mazakuntarshi, na dandak'e shi,
yadda bazai k'ara sha'awar mace ba har abada, ya tuno alwashin da yayiwa kanshi, da sauri ya fisgota ya warb'ar gefe yana nunata da yatsa yace
" ki shiga hankali daga yau kika kuma ina fad'a kina fad'a, ya cije lips d'inshi had'i da lumshe ido,
" saina lahira ya fiki jin dad'i, " Allah ya isa, Allah isar min a kanka Zaman, ina rok'on Ubangiji ya wahalar dakai a rayuwa,
ya d'aid'aita rayuwarka, ya tarwatsa farkin cikin duniyarka, ta yadda ko ruwa sai an tauna maka, mak'iyin Allah kawai, shaid'ani,
duk abinda Allah ya hana, ya la'anci masu aikatashi kana yi, wulak'antacce tab'abb'e....!, giyar kanshi ta fad'a mishi ya kashe ta,
ya jawota ya rufe ta da duka da iya k'arfinshi, da duka k'afuwanshi da hannayenshi ya shiga naushinta tako'ina,
batare da tunnin karya illatata ba, Goga da Garbu, da sauran mutum hud'u suka rufa akanta da duka,
basu daina dukanta ba saida sukaga bata motsi, sannan suka kyaleta, Zaman ya d'auke ta ya cilla ta waje, kasancewar iskar da akeyi me k'arfi ce,
ta wafci Basmah ta bugata da bango, ta zube yaraf, ruwa da k'ank'arar da aka kwana anayi ya ya k'are a kanta.
Koda gari ya waye bata da niyyar motsawa daga inda take, sai da rana ta take, ta tabbatarwa kanta bayan wuya, rana harda yunwa ke wahalar da ita,
da dafa bango ta tashi ta rarrafa ta wanke jikinta, ta shiga d'akin ta canja kaya, har lokacin bacci sukayi, babu ko pant a jikinshi,
daga kallo d'aya ta kawar da kanta, kud'in da sukayo fashi daren jiya zube a d'akin, babu yadda zata iya dole tasa ta d'auki uku acikin kud'in,
ta zumbula hijab ta rufe fuskarta da nik'af, ta bar gidan, saida taci tafiyar k'afa me nisa sannan ta samu adai-daita sahu,
a k'ofar restaurant ta tsaya ta biya me adai-daita sahun ta shiga, ta bada oder abinda zata ci, yadda take cin abincin hannu baka hannu kwarya yadda kasan ta shekara bata ci ba,
zai baka tausayi, sosai taci abincin ta k'oshi, dan saida ta cinye plate biyu, tayi hamdala, tayi take away da ragowar canjin, tayi sa'a har ta koma gida basu tashi daga baccin ba,
da sand'a ta lallab'a ta b'uye abincin ta aje hijab d'inta, bata dad'e da dawowa ba suka farka, yana daga d'akin ya kwala bata kira ya bata umarnin dafa musu ruwan wanka,
ba musu ta had'a k'irare ta dafa musu ruwan wankan takai musu bayi, tare su biyar d'in suka shiga bayin, tana zaune suka wuce ta suka shiga d'aki,
babu wanda ya kalle ta, jikinta duk a kumbure, ashar Zaman ya danna da k'arfi dasa gaban Basmah fad'uwa,
yana fad'in " sata!, ni za'ayiwa sata a gidana a d'akina, Basmah ni zakiyiwa sata?
Kafin tayi aune ta kanshi akanta yana huci kamar maciji yace " uban ya saki d'aukar min bada izinina ba?
Bakinta na rawa cike da tsoro tace " wallahi ba satar maka nayi ba, yunwa nake ji shine na d'auka naci abinci, ashar ya kuma yi had'i da cewa " da zamu tafi fashin ba saida nace miki kizo muje ba kika k'i?
"Wato mu gamu asararru wad'anda ba iyaye na suka haife mu ba, wanda bamusan ciwon jikinmu ba, munje munyo miki fashi da makami kin rigamu cin kud'in,
zatayi magana ya d'auketa da mari yana fad'in " uban yace miki ki d'aukar kud'i?
"Dama b'arauniya ce ke bani da masaniya?
Tana dafe da kuncinta tace " ina ciki dan haka bazan iya jure yunwa ba, " au musu ma kike min?
"Wato dan kin rainani ina fad'a kina fad'a ko?
Yayi maganar had'i da fisgota ya rufeta da duka, Goga yace " kuzo muje mu lodi kud'in mu, kun san Mugu bazai d'auki asara shi kad'ai ba,
ato! dan haka ni bari naje na doki kud'i tunda ita jaka ce batayi dai da duka, Garbu da sauran suka rufa mishi baya, tare suka nad'a mata duka iya san ransu,
suka fice suka barta nan kwance, bayan kwana biyu Basmah taji yunwa na neman kashe ta, jikinta har rawa yake saboda azababbiyar yunwar dake azalzalarta,
d'aki ta shiga ta ninki kayanta kala biyu ta fita dasu, takai kasuwa ta siyar ta siyo abinci, taci k'oshi, haka Basmah ta rink'a idan taji yunwa,
saita kwashi kayanta takai kasuwa takai siyar, idan yau taci abinci gobe bazata ci ba, tsallaken kwana d'aya take a cin abinci,
har kayan sawarta suka k'are suka rage kala biyu kawai, tana zaune ta saka sauran kayanta kala biyu da suka rage mata a gaba,
tana neman mafita, idan ta siyar da kayan bata da kayan sawa tasan idan zatayi yawo tsirara babu abinda ya damu Zaman,
haka idan bata ci abinci ba yunwa ta illata ta ta illata abinda ke cikinta, hawayen fuskarta ta goge tana shafa cikin,
" kayi hak'uri zaka zo duniya ka iske abinda yafi k'arfinka, banyi maka adalci ba daban zab'ar maka mahaifin kwarai ba, mahaifinka bai kasance mutumin kirki abinda alfahari ba,
ya kasance fasik'e, mazinaci, mashayi, d'an fashi, babban abun Allah wadaran shine shirka had'a Allah da wani,
ya kasance ba musulmi ba, kayi hak'uri ya yafe min kada ka hukunta akan abinda bani da masaniya akai,
ta k'arasa maganar tana tallafe cikinta da duka hannayenta, Astagfirullah! Astagfirullah! Allah na tuba, ka yafe min, ka kawo min d'auki da sassauci ya mak'agin sammai da k'assai,
kukan da take dannewa ya kufce mata, saida tayi me isarta kana ta mik'e tana mayar da kayanta,
wayarta k'irar Iphone XS Max ta fad'o daga cikin akwatin wacce Zaman ya sai mata, kasak'e tayi tana kallan wayar a d'an tsorace,
a sanyaye ta d'auki had'i da juyata tana kallanta a fili Hamdala ta godewa Allah, batare da b'ata lokaci ba ta zumbula hijab da nik'ab ta fita kamar yadda ta saba,
bata zame ko'ina ba sai wajen mai sai da waya a kes, ta mik'a mishi wayar tana fad'in " siyarwa zanyi idan zaka siya,
juya wayar yayi a hannunshi yace " nawa?
" Ka fad'i yadda zaka siya, k'ara juya wayar yayi sannan yace " kin siyar dubu hamsin?
D'an jim tayi gabanta na fad'uwa kafin tace " gaskiya ka k'ara, " idan kin siyar 70k ga kud'in idan baki siyar ba shikenan,
ya fad'a idonshi kanta, shiru tayi tana nazari zuwa can tace " kawo kud'in, baki washe dan jin banza ta fad'i, yace " zauna nan Hajiya bari na kawo miki lemo,
a tak'aice tace " ka bani kud'in saurin nakeyi, jikinshi na rawa na 'yarga 70k ya mik'e mata, ta karb'a hannunta na rawa,
kasuwa ta wuce ta yiyo siyayyar kayan abinci komai da komai, harda kayan shayi, mai da magi, tayi cefanan kayan miya,
tasan yadda take shan wuya wajen hura wutar ruwan wankansu Zaman, dan haka ta siyi kalanzir, dai-daita sahunta na tsayawa a k'ofar gidan su Zaman na k'arasowa,
da sauri ta sallami me adai-daitan ta soma k'ok'arin shigar da kayan, tunda daga nesa ya kafeta da ido har ya k'araso inda take,
yana kallanshi ya mayar kan kayan abincin data siyo kana ya mayar da kallanshi gare ta yana fad'i daga ina kike?
Baya taja tsoro fal fuskarta tace " daga kasuwa, " kasuwa?
Ya maimata, tsayuwarshi ya gyara yana fad'in " uban wa ya baki izinin fita?
Ido ta zuba mishi tana kallan kwayar idonshi tace " why! meyasa Zaman?
A tsawace yace " uban wa ya baki damar fita?
Ba k'aramin razana tayi ba, bakinta na rawa tace " ba...ba...babu, " sai kin jawo mana bala'i, kin saka 'yan sanda sun biyo bayanki, ko baki san nemana ake wanted ba?
"Idan baki sani ba ki sani hukuma nemana take yi WANTED a raye ko'a mace har mak'udan gwamnati ta saka akan duk wanda ya kawo ni,
bakinta dake rawa tana san tambayarshi dalili ta saka ya kalla,
ya fahimci abinda take san fad'a yace " saboda nine na saka boom d'in da aka saka a kasuwa, yayi sanadiyar mutuwar mutane 300,
duk da bata fita bata huld'a da kowa ta samu labarin mummunan boom d'in daya tashi a kasuwa yayi sanadiyar rayuwakan mutane da yawa,
ya illata wasu, " karki sake fita inba haka ba kiyi ta ranki, idan kuma kikayi k'ok'arin sanar da hukuma,
nace musu bakinmu d'aya tare muke aiki dake, ya fad'a yana nuna mata yatsa alamar kashedi, batayi magana ba saboda tsoro,
ya fisge zai shiga gida da ita, abokan tafiyarshi suka rufa musu baya, cak ya tsaya had'i da sakinta ya karkata kanshi gefe alamar tunani,
yace " ina kika samu kud'in da kikayi siyayyar nan?
Wani irin muguwar bugawa k'irjinta yayi, tsoro ya kamata fiye da koyaushe, ta danne fitsarin dake neman kwace mata,
da k'arfi cikin tsawa yace " ba tambayarki nake yi ba?
"W..wa..yar...daka simin ce na siyar, tayi maganar a rarrabe kamar me koyan magana, "waya! wacce waya?
Ya fad'a da sigar san tuna wani abu, maganarta na sark'ewa tace " wacce ka siyamin loka....! bata k'arasa ba ya danna ashar,
ya d'ora cewa " IPhone XS Max ko?
Kanta ta d'aga mishi alamar eh, tana jin yadda jinin jikinta ke tsare cikin jijiyoyinta saboda tashin hankalin da take ci,
ashar ya kuma a karo na biyu yana cewa " ita kika siyar?
Ya fad'a yana zaro ido kamar zasu fad'o k'asa, ya cigaba da cewa " kin san wahalar datasha kafin na sami kud'in siyan wayar nan?
"Kin san me nayi na samu kud'inta?
Inbanda lugud'en dukan uku-uku babu abinda k'irjinta keyi, " har targad'e nayi a k'afa akan kud'in wayar nan, hannayenshi ya hard'e a k'irjinta had'i da tsare ta da ido yace " nawa kika siyar?
"70k, ta fad'a kamar an fisgi maganar daga bakinta, doguwar ashar ya lailayo ya maka da k'arfi had'i da kifa mata yace " wayar 400k kika siyar min a 70k?
Azabar taji tasa abinda ke cikinta yamutsawa da k'arfi ya d'aure mata mara, " wanne tsinannan b'arawon zaunen ne ya siya?
" A kasuwa yake, " duk yadda akeyi baya san rayuwarshi ne, ya gaji da duniya, da alama yau lahira zatayi bak'o, muna nan muna fafutuka idan zamuyi bashi,
sai munbi dare da daji munyi hayar bindigogi, amma shi yana ci daga zaune, ko ubanshi keda China da America ubanwa zayyi mishi IPhone XS Max a 70k,
"Muje ki nuna min inda yake, na gama dashi, kafin na dawo nayi maganinki, ba musu ta shiga motar, ta kaishi har bakin kes d'in ta nuna mishi,
ya dawo gida ya aje ta, ko fita daga motar bayyi ba ya juya, jikinta na rawa ta shigar da kayan abincin,
Yayi musu waje, ta saka lagwani a rishon ta zuba kalanzir ta kunna, ta d'ora ruwa ta dafa tasha da biredi, abinda dame ciki taci ta k'oshi bacci ya bugeta,
bata farka ba saida safe, a wahalce ta tashi bak'inta d'auke da addu'a tana kallan inda tayi bacci, waje ferere a k'asa, ko arzikin buhu bata samu ba,
mik'a da hamma tayi a lokaci d'aya, cak ta tsayar da hammar ta sandare a yadda take ganin gaba d'aya kes d'in wanda ya siyi wayarta,
bata gama mamaki ba muryar Zaman ta katse mata tunani da fad'in " duba ki gani shine?
Batayi zatonshi ba dan haka ta d'an tsorata ta mik'e sauri, tana kallanshi,
da ido ya nuna mata jakar ledar dake tsakiyarsu yace " bud'e ki duba, batayi mummunan zato ba dan haka ta bud'e ledar,
tana bud'ewa wani abu ya mirgino kamar ball ya fito, a d'an tsorace taja baya tana kallan abun sai da numfashinta yabar jikinta saboda tashin hankalin yankakken kan me kes d'in data siyarwa da waya, baya ta kifa saman kwanika ta zube kansu a sume bata k'ara sanin inda kanta yake ba.................
*Kuyi hak'uri bani da lafiya wannan ma dakyar na daure nayi muku dan kar kuji ni shiru, kuma kar ku manta labarin, nagode sosai da addu'o'inku, Allah ya saka da alkhairi*