24
Guntun tsoki Shakira taja cikin ranta tana fad'in " ba fus tsuliyar me k'osai, sai cika baki, bari na samu na aure shi, korarki daga gidan shine farkon abinda zan farayi,
kamar yadda suka tsara hakan ce ta faru, Ya Mu'allim yazo kano suka had'u da Madu Nashwan yayi musu jagora wajen iyayen Shakira na bogi,
bayan sunyi bincike da duk abinda ya kamata aka saka ranar aure wata d'aya, wanda sukaje wajenshi a matsayin mahaifin Shakira,
ya sanar dasu babu abinda yake buk'ata bayan sadaki, sauran al'adu kamarsu lefe idan taje gidanshi yayi mata duk abinda yaga dama,
tana a matsayin matarshi, haka bayasan bidi'a d'aurin aure kawai yake buk'ata, sosai Ya Mu'allim yaji dad'in maganar,
ya tabbatarwa kanshi mahaifin Shakira mutum kirki ne me dattako, yasawa ranshi Ammar yayi dacen mata sai dai fatan Allah ya basu zaman lafiya.
******************************
A b'angaren Basmah babu abinda ya ragu saima abinda ya k'aru, dan Zaman da abokanan sharholiyarshi sun mayar da ita kamar 'yar aikinsu,
ita keyi musu har wanki da guga, dai-dai da pant da bra saita wankewa karuwanshi, ta wankewa abokanan luwad'inshi gajerun wandunansu,
Shakira ma na gidan bayan an gama komai na saka ranar aurenta da Ammar gidan ta dawo ta tare suka cigaba daga inda suka tsaya da Zaman,
a gaban idon Basmah suke neman juna idan sun kai su goma ko fiye da haka ba ruwansu kamar dabbobi,
idan bazata iya jure ganinsu ba ta fito, ruwan sama yayi mata dukan tsiya, haka duk sanyin da akeyi zai k'are a kanta, ta rame ta lalace,
ta k'ek'ashe gaba d'aya kammaninta sun canja, ta zama kama tsohuwa 'yar shekara 80 a duniya, abin tausayi, tun tana kuka da tausayawa kanta,
harta gaji ta daina, kuka ya k'aurace mata, ta mik'a lamuranta ga Allah, ta dage da Istigfari da addu'a, suna zaune tsakar gida shida abokananshi, Basmah na tsugunne tana alwala,
Garbu yace " mik'o min giyar can, ya fad'a batare daya kalli inda Basmah take ba, itama bata kallenshi ba ta cigaba da alwalarta,
dan duk abinda zasuyi yanzu iyakacinta dasu ido, mik'ewa tayi bayan ta gama alwalar ta shiga d'aki ta yafa kod'add'an zanin atamfarta,
daya gaji da duniya, wanda idan tayi kwakkwaran motsi zai iya darewa,
kun san ta siyar da kayanta kaf sai kala biyu ta rage, wanka saka takeyi, idan ta cire d'aya ta wanke sai ta saka d'ayan,
ko hijabin sallah bata dashi sai dai ta yafa zani tayi sallar, tana k'ok'arin tada sallah Garbu yace " ke dan kan tsohuwarki bakiji abinda nace miki bane?
Bata tanka mishi ba ta fara tada kabbara, Garbu ya kalli Zaman cike da mamaki yana fad'in " a gidanka ake sallah Michael?
Da sauri Zaman ya d'ago kanshi ya kalli Basmah dake tada Sallah, ido ya zaro kamar wanda yaga mutuwarshi,
ya lailayo ashar irin ta 'yan jagaliya ya maka mata yana cigaba da cewa " dama sallah kike yi min a gidana ban sani ba Basmah?
Ganin bata da niyyar ko kallan inda yake yasa shi mik'ewa yana fad'in " karki sake ki tada sallar nan, ke daga yau ma karki k'ara yi min sallah a gidana,
ko kallan inda yake batayi ba ta tada sallarta, a hasale ya nufota had'i da cewa " sallameta dan kan uwarki,
kanta k'asa ta cigaba da sallarta hankalinta kwance, batare dataji ko d'ar a zuciyarta ba,
mari ya kifa mata yana fad'in " ki sallame sallar nan in ba haka ba yanzu na sab'a miki kammani, bak'in cikin tak'i tanka mishi ne yasashi rufeta da duka,
yana zaginta ta uwa ta uba had'i da zazzaga mata ruwan bala'i, bata sallame sallar ba saida ta idar,
" daga yau na sake ganinki kinyi sallah a gida na, wallahi saina gana miki azabar da tunda uwarki ta haifeki baki tab'a ganin anyiwa wani irinta ba,
guntun murmushi tayi wanda iyakacinshi saman leb'enta tace " me yayi saura kuma Zaman?
"Wanne tsoro zaka bani?
"Ko kana tunanin akwai sauran azabarka da zanji tsoranta?
"Duk abinda zakayi ka riga kayi Zaman, babu abinda yayi saura kuma, duk wani abu da zaizo daga baya ne, satar kallan su Goga yayi yaga gaba d'aya hankalinsu na kanshi,
sun saki baki suna binshi da kallo, hakan ba k'aramin sake tunzurashi yayi ba, bakinshi na kumfa ya fincikota yana fad'in,
" baki isa ba Basmah, wallahi baki isa kiyi min taurin kai ba, ke har kin isa in fad'i abu kiyi min musu,
in kafa doka ki karya a gidana, ke ko a bariki ban tab'a fad'ar abu an karya ba balle ke k'aramar kwaruwa,
zanin datayi sallah ta soma ninkewa tana cewa " duk abinda zakayi sai dai kayi amma baka isa ka hanani nayi sallah ba,
baka isa ka hanani bautawa Ubangiji na daya halicce ni ba, baka isa ka hanani neman lahirata a wajen mak'agin kowa ba,
bayan ka hanani jin dad'in duniya ka hana ni yiwa iyaye na biyayya, baka isa ba Zaman, kazo inda baka da iko, kazo inda ko zaka saka gabana gabas ka yanka bazanyi maka biyayya ba,
kazo inda ba huruminka bane, ka wuce gona da iri.... mari ya d'auketa dashi had'i da mak'ureta a jikin bango, yana fad'in " wallahi zan iya kasheki akan sallah Basmah,
" ko rayuwata zaka bani a hannu na bazan daina sallah ba, kana mashiriki, kafiri, tab'abb'e, shagalalle baka isa ka hanani bautawa Allah ba,
babu wata azaba da wahalar duniya da zata sakani bijirewa mahalicci na, iyaye na, na sab'awa na shiga cikin bala'i da masifu a rayuwata naga kuma ga me me duka,
shak'eta yayi sosai, har numfashinta na neman d'aukewa, idanuwanta sukayi k'uru-k'uru suka firfito waje saboda azaba,
muryarta a shak'e bata fita sosai tace " wallahi sai dai ka kashe ni, kai koda zaka gididdiba nama na bazan dena bautar Allah ba,
ganin idan ya biyeta yana iya kashe ta, yasashi yin wurgi da ita gefe, yana fad'in " zaki gane shayi ruwa ne Basmah, saikin gane kuskurenki,
durk'ushewa tayi a k'asa ta rik'e wuyanta tana tarin sosai, ta had'a gumi sharkaf saboda azaba amma duk da haka bakinta bayyi shiru ba,
" har kana da wata azabar da zaka ganawa d'an Adam idan bayyi maka biyayya ba?
" A iya sani na Ubangijin komai da kowa shi kad'ai keda ikon azabtar da bayinshi a bisa k'inyi mishi biyayya, shi kad'ai keda wannan ikon Zaman,
ba mutum kamarka da kake kamar kowa ba, me ido biyu, hanci d'aya da baki d'aya ba, dan haka kama sani baka da azabar da zata tsoratar dani da zan bar bautar Allah,
Idan ma kana da ita na shirya jure mata, azabar Allah itace abar tsoro da gudu Zaman amma ba taka ba, manyan kafiran farko da suka kafa tarihi a duniya,
sunyi sun gaji sun shud'e babu su sai labarinsu, wasu ko labarin nasu ma babu balle kai da ko yatsa baka tsuma a iskanci da kafurci ba,
tunda bazaka iya k'ona koda farcanka akan kafurci ba, kuma banga shaidar bariki a tattare dakai har yanzu ba,
ya yunk'ura a zuciye zai cafki wuyanta Shakira tai saurin rik'eshi tana shafa k'irjinshi cike da bariki, ta rad'a mishi magana a kunne wanda koni Jiddarh,
ban san me tace mishi ba, kallanta yayi kafin suka fashe da dariya, ya mayar da kallanshi ga Basmah ya nuna mata yatsa alamar gargad'i,
while yana cigaba da dariyarshi ya cije lips yana fad'in " you made a mistake but zaki gane baki da wayo,
bakin juna suka tsotsa shi da Shakira hannunta zaman join stick d'inshi tana murna ta, idonshi lumshe yana mayar da numfashi,
kwata-kwata abinda sukeyi baya bawa Basmah haushi, ko kad'an bata jin kishi ko wani abu cikin ranta, saima tausayi da suke bata,
dan babu d'igon son Zaman a zuciyarta, asalima babu wanda ta tsana a duniya sama dashi, idan tana k'aunar mutuwarta,
tana k'aunar ta bud'e idonta taga Zaman, da za'a bata free life da babu wanda zata kashe sai shi,
kwata-kwata bata jinshi cikin ranta, tsoki taja a zahiri had'i da k'ok'arin barin wajen, Shakira ta fisgota ta watsa mata marin dayasa Basmah ganin taurari,
" ni kikeyiwa tsaki dan kan uwarki?
"Shegiya wacce bata san arziki ba, yanzu na kwace ki, amma kike yi min tsaki, ni ba kanwar lasa bace, idan shi kinyi mishi ya shanye,
ni bazan shanye ba dan bani da matacciyar zuciya, wuya zakisha a hannu na, " da kin bari ya kashe ni ai tunda rai da rayuwa a hannunku suke,
Basmah ta fad'a tana dafe da kuncinta, a hasale Shakira tabar jikin Zaman ta rufe Basmah da duka tana surfa mata ashar,
Zaman na tsaye yana kallo hannunshi hard'e a k'irjinshi, da gudu Garbu da Goga suka shigo d'akin, ganin Basmah ake duka yasa babu tambayar ba'asi suma suka rufar mata,
muddin za'a dageta a gabansu sai sun taya, sai da suka gaji dan kansu suka kyaleta, Shakira ta fita waje tana hakki kamar wacce tayi gasar tsiran gudu,
jibgin kayansu da Basmah ta wanke ta shanya, Shakira ta watsar a k'asa, ta saka k'afa ta damasu cikin cab'i, sukayi futu-futu,
ta koma d'akin ta jawo Basmah ta jefa kan kayan tana fad'in " na baki awa d'aya ki sake wankesu, kallan kayan data kwana tana wanke su tayi saboda yawansu,
ta kalli Shakira, kamar zatayi magana sai kuma tayi shiru, tsayuwarta ta gyara tana hard'e hannuwanta tace " ko bazaki wanke ba?
Jikinta ba kwari ta fara tattare kayan, Shakira taja tsaki tare da cewa " k'aramar mara kunya aina d'auka bazaki wanke ba, abincin da Basmah ta dafa Shakira ta d'auka duka ta juye musu suka cinye tas basu bata ba,
duk da ita ta dafa, bata damu ba ko'a jikinta dan inda sabo ta saba dafa abinci su cinye tas su hanata ko d'and'ano, shiyasa data gama take d'ibar nata ta b'oye,
in ba haka ba, haka zata kwana bata ci ba, duk ranar da suke gida da yunwa take kwana dan bata samun damar d'iba, kafin su d'auka,
ta dafa abincin, tayi wanke-wanke wani lokacinma ita zatayi cefanen da kud'inta amma su hanata ko d'and'ano,
" wayar da saida naji ciyo, aka kusa harbina lokacin danaje fashin kud'inta kika siyar?
"Kin san gudun kilometres nawa nayi da 'yan sanda lokacin danaje fashin kud'in dazan siya miki wayar?
"Ba damuwa tunda abinci kika siyo, but ki sani ke zakiyi girkin, kiyi wanke-wanken, amma d'igon abincin bazai shiga bakinki ba,
duk ranar dana kanki ko tukunyar kin lasa wallahi saina shak'eki kinyi amanshi, Basmah ta tuno kashedin da Zaman yayi mata,
ajiyar zuciya ta sauke data tuno yau kwanan yunwa zatayi dan bata d'iba ba, tana kallansu tana had'iyar wayo, har jiri ke d'ibarta saboda yunwa.
Bayan kwanaki abincin da Basmah ta siyo da kud'in wayar Zaman ya k'are tas, ta koma 'yar gidan jiya, ganin yunwa zata kashe ta yasata yanke shawarar neman abinyi,
tun kafin yunwa ta k'arasata, dan haka su Zaman na fita ta yafa zanin atamfarta ta fice, dakyar ta k'arasa cikin gari, a galabaice sosai take jefa k'afarta saboda yunwa da gajiyar tafiyar k'afa,
Basmah tasha wuya sosai dan duk gidan data shiga neman aikatau korarta suke yi, wasu ma ko shiga me gidan baya barinta tayi,
idan ta kafe tana rok'onsu su hankad'ota waje su rufe gidansu, wani gida da aka koreta tak'i tafiya karnuka suka sakar mara dakyar tasha,
ta sadak'ar ta koma gida kawai dan bazata samu aiki ba, ta juya tana jan k'afarta ta nufi gida, wani gida ta gani bud'e kamar zata wuce,
sai kuma ta danna kai ta shiga, tayi sa'a mutanen gidan masu mutunci ne, suka tareta hannu biyu,
dakyar tace " abinci, batare da b'ata lokaci ba aka kawo mata, bayan taci ta lafa ta dawo nutsuwarta,
tace " neman aiki nazo, ban sani ba ko kuna buk'atar 'yar aiki, d'an shiru matar tayi kafin tace " a gaskiya ina buk'atar me aiki, sai dai dakyar idan me gidan zai yarda,
duba da yadda zamani ya lalace duniya ba gaskiya, saika jawo mutum jikinka ya cutar dakai, marairaicewa Basmah tayi had'i da durk'usawa gaban matar,
" ki taimake ni dan Allah, wallahi zan rik'e amanarku, nayi miki alk'awarin bazan tab'a cutar dake ba, gyaran murya me gidan dake tsaye yayi,
" tashi!, ya fad'a tak'aice, " dan Allah ku taimake ni, zan zauna daku lafiya da yardar Allah,
dakyar suka yarda suka d'auketa aiki, zata rink'a yi musu wanke-wanke, shara da sauran gyaran gida,
sukayi zasu rink'a biyanta 5000 a wata, tayi farin ciki sosai tayi musu godiya, ta fara aikinta daga ranar, sai la'asar tayi musu sallama ta koma gida,
kullum take zuwa tayi musu aiki, tayi sa'a Zaman bai tab'a ganewa ba, babu abinda yayi fi mata dad'i kamar abinci data samu take ci,
har bata sukeyi idan zata tafi, ko kud'in albashin bayyi mata dad'i kamar abincin ba, satinta d'aya da fara yi musu meyi musu wanki ya tafi ganin gida,
Basmah ta had'a duka tanayi, suka k'ara mata 3k yayi making 8k a wata, gudun kar Zaman ya kamata,
yasa take fita da asubar fari, kafin su tashi taje ta dawo, dan sai su kai azahar suna baccin asara, haka kullum take yi musu wankin yaransu,
dan karya taran mata, idan ta dawo gida kuma tayi surfan mutane na masara, gero, dawo da take karb'owa daga cikin gari,
dare take bi tayi surfen idan su Zaman sun tafi fashi da makami, ko yawan iskancinsu na club,
sai tayi sauri tayi surfenta kafin su dawo, Allah yasa bai tab'a lura ba.
*******************************
Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, sannu-sannu bata hana zuwa, sai dai a dad'e ba'aje ba, cikin nufin Allah lokacin bikinsu Ammar ya rage saura kwana biyar,
duk yadda Hajiya Tanya da Shakira suka so cusa kai wajen Ammar yak'i, ko magana bata tab'a had'asu ba, iyacinshi da ita amsa gaisuwarta,
shima idan acikin mutane ne dole babu yadda zayyi, idan ba kowa kota gaidashi baya amsawa, hakan bai damu Shakira ba,
burinta kawai a d'aura aure tasan idan aka d'aura tana da hanyoyin shawo kanshi da yawa, ya zama bawanta koba dan Allah ba,
shawara akayi a d'aura auren gaba d'aya a babban masallacin Zamfara wanda ya kasance k'ark'ashin jagorancin Ya Mu'allim,
da wannan shawara suka d'unguma gaba d'ayansu zuwa Zamfara, Usman, Umar, Abubakar sai zumud'in auren sukeyi,
amma Ammar ko'a jikinshi yadda kasan ma ba ango ba, babu abinda ya shafeshi da harkar bikin, su kad'ai suke kid'ansu suke rawarsu,
iyacinshi dasu ido, ranar juma'a itace ta kasance ranar d'aurin aure, dakyar su Umar suka matsa masa ya shirya, suka tisashi a gaba har masallacin da za'a d'aura auren,
dan cewa yayi babu inda zaije saida Umma ta saka baki, bayan an idar da sallar juma'a Ya Mu'allim ya jagorancin d'aurin auren Ammar da Hurayya (Shakira),
Usman da Safiyyah, Umar da Aisha, Abubakar da Fatima, ana shafa d'aurin auren ya lumshe idonshi hawaye na gangarowa saman fuskarshi,
hukuncin Allah yafi gaban wasa, yau shine aka d'aurawa aure bada Basmahnshi ba, shine angon wata ba Basmah ba,
shikenan duk dakon soyayarta da yayi ya tashi a banza, yayi rashinta har abada, hawayen dake zubo mishi yaji an sa hannu an goge mishi,
ya d'ago kanshi Nashwan tsaye yana girgiza mishi kai, while yana goge mishi hawayen, shi kanshi Ya Mu'allim kanshi ya duk'ar,
yana tuna ranar da aka haifi Basmah ya kyautarwa da Ammar ita, ko kusa bai tab'a tunanin zai d'aurawa Ammar da Basmah aure bada junansu ba,
ko a mafarki bayyi zaton haka zata faru ba, duk da yasan hakan kad'anne daga cikin kud'urorin Ubangiji,
hawayen daya rasa na menene farin ciki ko bak'in ciki ya goge yana mik'ewa, me shela da marok'a suka kwala shailar,
" mun shaida munji mun gani an d'aura auren Ammar da Hurayyatu, ido ya runtse had'i da mik'ewa ya nufi k'ofar fita,
karo mukayi da wani mutum da jikinshi keta rawa yana b'ari, kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin tashin hankali,
Ammar na saka k'afarshi zai fita yaji cikin rawar murya mutumin na cewa " *GA 'YARKA BASMAH CAN A BOLAR UNGUWAKU A YASHE MIJINTA YA KAWO TA YA YAR DA TAKARDAR SAKI BATA SAN INDA KANTA YAKE BA.....!*