SAKI RESHE..

25

by @hauwaausmanjiddarh

25


" Ga 'yarka Basmah can a bolar unguwarku mijinta ya kawota ya yarda da ita da takardar saki bata san inda kanta yake ba,

wani dummmmm shuuuuu Ammar yaji cikin kanshi da kunnuwanshi, kwakwalkwarshi ta shiga san tunano mishi abinda yaji,

kanshi ya girgiza yana fad'in " Azubillah nasan ba gaskiya bane, hasashe na ne kawai ke bani, ya fad'a yana k'ok'arin barin wajen,

ganin Ya Mu'allim bai kalli inda yake ba, yasa mutum d'aga murya yace " Ibrahim nace maka 'yarka Basmah ta cikinka,

gata can yashe a wulak'ance a bola fa amma baka ko kalli inda nake ba,

kai Ya Mu'allim ya d'ago ya kalli mutum yana murmushi yace " bani da 'ya me suna haka, asalima bani da 'yaace, 

duk 'ya'yana maza ne, ban tab'a haihuwar 'ya mace ba, cikin rashin fahimtar mutumin yace " ban gane abinda kake nufi ba Ibrahim,

'yarka Basirah nake nufi ba, "eh ita dai, bani na haifeta ba, ya fad'a yana danne abinda ke taso mishi, a fusace mutumin yace " Ibrahim ni zaka kalli ido na kace min Basmah ba 'yarka bace?


"Ni Ibrahim?


Mutum ya fad'a yana nuna kanshi, Ammar daya k'ame a tsaya yana jin abu dame tab'a ji ba a rayuwarshi na ratsa shi, tunda daga tafin k'afarshi zuwa tsakiyar kanshi,

zuciyarshi ta shiga tsalle tamkar zata tsaga k'irjinshi ta fito, har wani d'aci-d'aci yake ci a mak'ogwaranshi zuwa bakinshi,

jikinshi kam ji yake tamkar an saka shi a deep freezer, jin maganar yake kamar almara, ganin mutum yayi fushi zai fita fuuu yana fad'in " laifina ne dana zo na fad'a maka,

da wani irin zafin nama Ammar ya rik'o mutum yana fad'in " ina take ina Basmah?


"Tana bolar unguwarku a yashe, a kid'ime tamkar zararre Ammar ya fisgi hannun mutum kamar zai b'allashi yace " muje ka raka ni,

" idan ka d'aga k'afarka daga inda kake ban yake maka ba Ammar, cewar Ya Mu'allim, cak Ammar ya tsaya a inda yake, had'i da sakin hannun mutum,

yana jin maganar kamar a mafarki, " Ammar, Ya Mu'allim ya kira sunanshi, bai jiyo ba bai kuma amsa ba, yana tsaye kamar wanda aka dasa,

takowa gabanshi Ya Mu'allim yayi, ya kalli Ammar da kallo d'aya zakayi mishi kasan yana cikin bala'i da tsantsar tashin hankali,

" ba 'yata bace Ammar, Basmah ba 'yata bace a halin yanzu, zab'i na bata ta zab'i abinda take ganin ya dace da rayuwarta,

a gaba na akan idona tabi namijin data zab'a akaina, ta fifita akaina, har Allah ya isa tayi min akanshi, tayi min mugun fatan dako mak'iyinka bazakayiwa ba,

ta dasa min mugun ciwo a zuciyata, ta fad'a min kalaman da ban tab'a zata ba, wad'anda ko a gigin mutuwa aka ce Basmah zata iya furtawa wani ma ba ni ba,

bazan yarda ba, dan haka gaba d'ayanku kar wanda ya rab'e inda take koda zata mutu duk wanda ya sab'awa umarni na bazan yafe mishi ba,

a firgice cikin tashin hankali idawanshi a waje k'uru-k'uru yace " Abba Basmah ba akace ko baka ji bane?


"Basman fa, sai me?


"Amma Abba.....! dakatar dashi Ya Mu'allim yayi ta hanyar d'aga mishi hannu yana fad'in,

" umarni na baka ba rok'onka nake ba, idan kuma kaima zaka sab'a umarni na ne tum, ga hanya nan, yayi maganar cikin b'acin rai,

sakwaf jiki ba nauyi Ammar ya zube k'asa had'i da dafe kanshi da duka hunnuwanshi, zuciyarshi na bugawa da k'arfi kamar zata tsaga k'irjinshi ta fito,

mak'ogwaranshi nayi mishi mak'ak'i while gumi ya gama jik'ashi sharkaf, fuskarshi ya sanya tafukan hannayenshi ya rufe,

had'i kura ihuuuu da iya k'arfinshi, " innalillahi wa'inna ilaihirraji'un raji'un, ya fad'a yana fashewa da matsanancin kuka,

nufarshi Ya Mu'allim yayi da nufin d'aga shi sai kuma ya fasa ya nufi k'ofar fita, " Abba kana tunanin Basmah ce kad'ai me laifi, me karya alk'awari?


Ammar ya fad'a yana daga durk'ushen, cak Ya Mu'allim ya tsaya, " kaima me laifi ne Abba, ko'a wajen Allah, haka ka karya alk'awari,

cike da mamakin Ammar Ya Mu'allim ya jiyo ya kalleshi, bai d'ago kanshi ba ya cigaba da magana " Abba kana da laifi sosai akan abinda ya faru,

ka karyawa Abba na alk'awari dan ba haka kukayi dashi ba tun farko, kuma inda tabbacin inda Abba na yana raye bazai tab'a yafe maka ba akan abinda kayi da wanda kake k'ok'arin aikaw.........,

tsawa Ya Mu'allim ya dakawa Ammar idanuwanshi sunyi jajir suna fitowa waje saboda b'acin rai, a hasale cikin hargowa Ya Mu'allim yace,

" ya isa! ya isa haka Ammar, cikin nutsuwa Ammar ya d'ago kanshi ya kalli cikin idon Ya Mu'allim, abinda ya gani ne yasashi sunkuyar da kanshi,

dan yaci alwashin kome zai faru yau sayya fad'awa Ya Mu'allim gaskiyar daya kasa fahimta da kanshi, gaskiyar da kowa har makusantanshi suka kasa fad'a mishi,

" bai isa ba Abba, kayi hak'uri Abba yau zan fad'a maka gaskiyar da kowa ya kasa fad'a maka, yau ina san nayi magana dakai ne a matsayin d'an uwanka, amininka YASEER ba d'anshi Ammar ba,

daga ni har kai masu laifi ne shiyasa Allah ya barmu da iyawarmu Abba, muna ganin kamar babu wani dalili da zai hana aure na da Basmah,

shiyasa bamu nasar da Basmah waye ni da managar auren ba, bamu tab'a fad'a mata abinda ya dangance ni ba, asalima bata sanni ba,

ina da tabbacin ko yanzu zamu had'u da Basmah saita wuce na wuce bata gane ni ba, kamata yayi Basmah ta girma da abu biyu,

ta girma da sani na da shak'uwata a ranta, ta kuma san da maganar aurenmu, nasan da anyi haka da Basmah bata soma biyewa tsayawa da wani ba,

balle harta bijirewa umarninka, da yawan mutane suna d'auka tarbiyya da ilimi kad'ai sun ishe mutum sanin rayuwa da mu'ala da mutane,

hakan ne yasa kayi watsi da fad'awa Basmah waye Ammar, meye alak'arsu, waye shi a gareta, dan a ganinka babu yadda za'ayi ta bijire maka,

kana ganin ka isa da ita, ka isa ka fad'a mata taji, ka kafa mata doka tabi, saboda ka bata tarbiyya da ilimi, ka manta hukuncin Allah,

ka manta Allah shike da iko akan komai da kowa, ka manta Ubangiji ke da ikon zartar da kome a kan kowa, ka manta zamani da rayuwa sun canja,

ka kasa cika umarnin Allah a matsayinka na uba, ka kasa sauke nauyi da amanar Ubangiji Abba,

daga ni har kai masu laifi ne, dan Basmah bata sanni ba, bata tab'a gani ba, bata tab'a jin labari na, babu zata aura?


"Duk Soyayyar da ake fad'a ina yi mata gaibu ce a wajenta tunda ban nuna mata ba, ban rab'eta na shak'u da ita ba, ban kusanci zuciyarta na koyar da ita yadda zata so ni ba,

duk abinda za'a fad'a mata bazata yarba tunda bataga tabbaci ba, ranta yana iya bata ban damu da ita ba, tana iya ganin bana santa,

ina da wacce nake so, tunda bataga zahiri ba, da zahiri zatayi aiki, zuciyar Basmah ba dutse bace, dole za'a sota zata so, ita ba katako bace dole zataji emotions da feelings,

shaid'an yana iya k'issima mata abubuwa da dama, sai bayan ta gama kamuwa da son wani rana tsaka azo mata da maganar auren wani,

wani dabata tab'a gani ba, bata tab'a jin sunanshi da labarinshi ba, tun farko da anbi abun bisa tsari da koyarwar musulci da hakan bata faru ba,

baka bata hujjar da zatak'i wanda take so ba, illar k'ok'arin cusa mata wanda kaine kake sanshi ba ita, idan cusa wani a zuciyar sauk'i gareshi meyasa kai ka kasa cusa san wanda take so?


" A matsayinka na uba kamata yayi ka jawota jikinka ka nuna mata illar abu ta yadda da kanta zata kyamaceshi, ba dole ya kamata ayi mata ba,

tun asali saida kayiwa Yaseer alk'awarin bazaka tab'a yi mata auren dole ba, bazaka matsa mata akan abinda baby shi a ranta ba,

ka karya alk'awarin Abba, ka fad'a min meyasa Allah bazai jarrabeka ba?


"Ka nuna kana da iko akan abinda Allah ked'ai keda iko dashi wato zuciyar mutum ka fad'amin kai waye da Allah bazai barka da ikonka ba?


"Ka shiga hurumin Ubangiji, ka kafe ka dage akan aure wanda Allah kad'ai keda ikon aurawa wanda yaso, kayi yak'inin babu wanda ya isa ya juya akalar auren dake tsakanina da Basmah, ka fad'a min meyasa Allah bazai jarrabeka ba?


" Ka manta wani baya auren matar wani, haka wani baua haihuwar d'an wani, Allah ya k'addara akwai raban aure tsakanin Basmah da wani,

haka ni da Hurayya, ka fad'a min wanda ya isa ya kawar da wanzuwar haka duk duniya, babu wanda ya isa ya janwa wani k'addararshi,

babu wanda ya isa ya canja abinda Allah ya zartar akan bawanshi, babu wanda ya isa canja hukuncin Allah, ka godewa Ubangiji dayake sanka da rahama abin ya tsaya iya nan,

kallanshi ya mayar gasu Umar da jikinsu yayi sanyi sosai yace " meyasa idan shi kasa ku baku taimaka masa kun sauke nauyi a matsayinku na yayyanta ba?


"Meyasa kuka kasa fad'a mishi gaskiya?


Sunkuyar da kansu sukayi suna goge hawaye, " Abba na me fahimta, ne sauk'in kai da tausayi, na san halin Abbana kamar yadda nasan halaye na,

bazan tab'a sab'a umarninka ba Abba yanzu da har abada, ina rok'on Allah da karya bani ikon sab'a maka tsayin rayuwata,

zanyi hak'uri da duk hukuncin daka zartar a kaina har abada, kayi hak'uri idan maganganun da nayi sun b'ata maka, ya k'arasa maganar yana mik'ewa zai bar wajen,

kasancewar wajen cike yake mak'il da 'yan d'aurin yasa aka soma maganganu k'asa, jikin kowa yayi sanyi harda masu hawaye,

Ya Mu'allim dake jin kamar ana tsintsinka jijiyoyin jikinshi, nadama ta shige shi, jikinshi yayi mugun yin sanyi, ya rasa abinda yake yi mishi dad'i,

ya san maganganun Ammar duka gaskiya ba k'arya, bai kuma tab'a kula da hakan ba balle ya zauna yayi tunani akai,

dakyar yaja k'afarshi ya isa inda Ammar yake ya dafa kafad'arshi muryarshi can k'asan mak'ogwaro bata fita sosai,

yace " jeka Ammar, kaje ka na yafe maka amma...! Ammar bai jira jin k'arshen abinda Ya Mu'allim zai fad'a ba, ya rungume yayi da gudu,

baiko tsaya d'aukar takalminshi ba, Usman kam bai tsaya bi takan Ya Mu'allim ya bashi umarni ba, yabi bayan Ammar a guje,

Umar, Aliyu da Abubakar suka rufa mishi baya, Ya Mu'allim yabi bayansu da kallo hawaye na zubowa daga idonshi, cikin nutsuwa Nashwan ya taka daga inda yake,

ya tallafe Ya Mu'allim dake shirin zubewa, ya sanya shi a mota ya nufi gida, a tsakar gida suka iske Saratu zaune cikin 'yan biki,

ganin Nashwan ya shigo rik'e da Ya Mu'allim yasa ta mik'e tana fad'in " lafiya?


"Lafiya lau, Nashwan ya fad'a yana shigewa da Ya Mu'allim, har d'akinshi ya kaishi ya zaunar, Nashwan na fita Ya Mu'allim ya rufe k'ofar had'i da fashewa da kukan dayake dannewa,

tsaye yayi daga nesa yana hangota hawaye na gangaro daga idonshi kafin in slowly ya k'arasa inda take kwance cikin bola tsakiyar rana,

bisa gwiwowinshi ya zube ya zuba mata idonshi, zuciyarshi na wata irin bugawa da k'arfi, kamar me jin tsoro yakai hannushi jikinshi,

gani yake kamar ba gaske ba, jinshi yake yi kamar a mafarki, hannunshi rawa kamar mazari ya d'agota ta, ya had'ata da k'irjinshi ya fashe da mahaukacin kuka,

dukakninsu tsayawa sukayi akanshi suna kallan ikon Allah, bai damu da cewar a bola yake ba, a hankali Usman ya k'arasa inda yake ya dafa kafad'arshi yace " mu kaita asibiti,

kamar an tsikareshi ya mik'e yana ciccib'arta Usman yayi saurin taimaka mishi suka d'agata, Umar na tsaye yana kuka wiwi, Aliyu mamakin rayuwa yake yi,

wai yau Basmah ce a kwance a bola k'udaje na binta, kasancewar ba mota yasasu shiga taxi suka nufi asibiti.


MU WAIWAYA BAYA MUJI ASALIN ABINDA YA FARU


************************************


Gudu-gudu sauri-sauri take yi ganin ta sab'a lokacin dawowarta tuni, ga hadari ya had'o garin yayi bak'i k'irin, tana shiga kangon ta sauke ajiyar zuciya had'i da dafe k'irjinta,

tana fad'in " wai Alhamdulillah nayi sa'a, kamar daga sama taji muryarshi yana cewa " ke! daga ina kike?


Cikin dabur-dabur a dururuce murya na rawa tace " amm... um... da...dama.., a tsace yace " nace naga ina kike?


Fitsarin da take ji ne ya kwace mata saboda tsoro, jikinta ya d'auri rawa da tsuma hantar cikinta ta kad'a a tsorace " daga gari,

" gari!?


Ya maimaita cikin tuhuma idonshi kanta, kafin ya d'ora sa cewa " garin wajen ubawa?


Bata bashi amma dan bata da abinda zatace mishi, " ubanki ne ya baki izinin fita?


Iskar ya furzar yana tsareta da idanu yace " bana hanaki fita ba?


" Kin raina ni ko?


"Kayi hak'uri ban rainaka ba, yunwa nake ji, shine na fita na samo abinda zanci, " kika samo abinda zaki ci?


"Bara kikayi?


Da sauri ta girgiza kanta tana cewa " a'a, siyowa nayi, kamar zayyi magana ya fasa had'i kad'a hannu " zan kama ki ne, ya juya zai shige d'aki, 

fasawa yayi ya dawo yace " ina abincin?


Jiki na rawa tace " gashi nan, hannu ya mik'a mata yace " bani, dalolo tayi batare data mishi ba, tsawa ya daka mata data firgitar da ita " nace ki bani,

jikinta na tsuma ta mik'a mishi, ya karb'a ya shiga band'aki tayi saurin binshi, yana tuntsura dariyar mugunta, ya zazzage abincin duka a masai,

ya fito ya d'age d'aki ya barta tsaye a band'akin cikin takaici da bak'ar yuwar dake azalzalarta, saboda tsoro bata tsaya taci abincin acan ba,

jiki a sanyaye ta bar ban d'akin ta shiga d'aki, da k'afa ya hankad'a ta waje, ta fad'i da baya, fad'uwarta tayi dai-dai da kecewar ruwan sama,

ruwan ya k'are kanta, tana ji tana gani bata da damar shiga d'aki, tayi tsamo-tsamo kamar kaza, da suka gama iskancinkansu suka kirata ta kwashe comdoms da kayan shaye-shayensu,

da sassafe ta shirya kamar kullum ta zata fita wajen aiki, tana gaf da fita ta jiyo muryarshi yana fad'in " dama nasan za'ayi haka shiyasa na kafa na tsare, yayi maganar yana d'aukar steps zuwa inda take,

" ina kike zuwa?


Shiru tayi tana neman amsar da zata bashi, gaf da ita ya matsa k'irjinshi yana gogar nata, numfashinta cikin nashi ya matsata a bango yace " gidan ubanwa kike zuwa?


Bai bari tayi magana ba ya cigaba " dama fita kike yi a bayan idona Basmah?


Batare data sani ba saboda tsoro tayi sub'ul da bakar cewa " aiki nake zuwa.......!