SAKI RESHE..

27

by @hauwaausmanjiddarh

27


A kid'ime Abubakar yacewa Umar " kira likita, ba jimawa suka dawo tare da likita da sauri aka d'auke suka shiga bashi taimakon gaggauwa,

cikin sa'a ya sauke ajiyar zuciya bakinshi d'auke da salatin Annabi, ya bud'e idonshi suka sauka akan Ya Mu'allim dake tsaye a kanshi cikin tashin hankali,

Basmah kam mamaki da tsoro ne suka sandarar da ita a saman gadon, ta kasa koda kwakkwaran motsi, " wanne irin so wannan bawan Allah take min da har yake neman mutuwa akaina?


Ta tambayi kanta " ina da irin wannan masoyin na gaskiya nayiwa kaina *SAKI RESHE...!* lalle *RASHIN SANI...* yafi dare duhu, amma bakomai *K'ADDARA TA* ce tazo da hakan,

babu abinda Ammar baifi Zaman ba, k'afar Ammar tafi fuskar Zaman kyau, ina da kamar Ammar na jefa kaina a halaka?


"Masoyi na hak'ik'a me k'aunata dan Allah da zuciya d'aya, why na jefa kaina a taskon rayuwa?


" *RABO AJALI...!* ta bawa kanta amsa rabon cikin datayi da Zaman kad'ai ya isa haifar da komai, balle raban aure da raban abincin datashi, ruwan data sha, da inda ta taka,

da mutanen data gani ta kuma huld'a dasu tasan idan ba ta dalilin hakan ba ta ina zata sansu har wata mu'amula ta shiga tsakaninsu, *GADAR ZARE...!* yayi man na rufta, amma bakomai shida Allah,

kanshi ya soma girgizawa Ya Mu'allim yana fad'in " Abba ba haka kukayi da Daddy ba, ba wannan alk'awarin ka d'aukar mishi,

shin ka manta da irin farin cikin dake kan fuskokin Daddy da Momy a lokacin daka furta ka bani Basmah?


"Wannan farin cikin nasu shine abu mafi mahimmaci kuma na k'arshe dana gani a rayuwata a tattare dasu, tayaya bazansu cikata musu farin cikin su Abba?


Murmushi Ya Mu'allim yayi had'i da shafa kan Ammar yace " ban manta yaro na, ni kaina shine abu na k'arshe dana gani a tattare dasu nake yake kuma sanyani murmushi a duk yayinda na tunashi,

Usman, Umar, Aliyu da Abubakar suka durk'usa gaban Ya Mu'allim suna hawaye suka ce " dan Allah Abba ka bashi aurenta, muna rok'arwa d'an uwanmu alfarma a wajenka,

bisa mamakin Abba sayyaga Umma ma ta durk'usa, da sauri ya mik'e ya d'aga ta yana fad'in " wato ware ni zakuyi ko?


"Nine bare a wajenku ku duka kun koya mishi baya, da sauri Ammar yace " a'a ni ina bayan Abba na, " kai tafi can ka bani wajen rago kawai, me kuka kan mace,

ni da Yaseer jaruman mazane sai dai ayi mana kuka badai muyi ba, Umma tayi gyaran murya had'i da cewa " un un fa kar in tona, a tsakaninku dai a samu wanda ya gado, 

gaba d'ayansu suka saka dariya, Ya Mu'allim yakai bakinshi kunnen Ammar yayi mishi rad'a, Ammar ya zaro ido yana fad'in " anya Abba zan iya kuwa?


"Oho ya rage naka nidai shawara na baka, su Usman sukace muma a bamu Abba, Abba yace " sai bari sai tayi iddako, a tare Basmah da Ammar suka baki wajen cewa " ba idda akaina, shi kuma yace " bata da idda, kallansu Ya Mu'allim yayi cikin tuhuma, kanta k'asa muryarta na sark'ewa tace " Abba ba musulmi bane Christan ne, ido suka zaro gaba d'ayansu, had'i da cewa " me!?


Tana kuka ta kwashe komai tun daga farko har k'arshe ta sanar dasu, da irin bak'ar rayuwar uk'ubar datayi a gidan Zaman har zuwa yau da suka rabu dashi,

babu wanda bayyi mata kukan tausayi ba, musamman Umma, datake kuka kamar akanta abin ya faru, Ammar kam ba'a magana danjin zuciyarshi yake kamar ta kama da wuta,

bayan an natsa Abba yace " ya saki ko?


"Kanta k'asa tace " eh! ya sake ni, yana duka na yana furta min saki a club, kuma daya kawo ni bola ya yar harda takardar ya jefa min, "ina takardar?


Cewar " Aliyu, " bana cikin hayyacina acan aka barta a bolar, kallan Ammar Ya Mu'allim yace " idan ka warke muje sai muje ko?


Ya mik'e da sauri yana fad'in " na warke sumul muje, masallacin Ya Mu'allim suka wuce bayan an idar da sallah Magrib aka d'aura auran AMMAR YASEER DA BASMAH IBRAHIM akan sadaki naira dubu d'ari, Ya Mu'allim yayiwa Ammar waliyyanci,

Madu yayiwa Basmah, Ammar najin an shafa fatiha ya saki kukan dayakasa rik'eshi yana fad'in " Alhamdulillah Alhamdulillah ya Allah nagode maka,

Allah kaine sarkin sarakuna me zartar da komai akan wanda yaso a inda yaso, Allah nagode maka daka cika min burina ka mallakamin farin ciki na, yayi maganar kamar zautacce yana kuka wiwi,

kusa dashi Ya Mu'allim ya zauna shima yana kukan dukkaninsu an rasa me rarrashin wani, shima Ya Mu'allim hamdala yake yana godewa Allah,

daya nuna mishi wannan rana daya cika burinshi ya sauke alk'awarin dayake kanshi, saida sukayi me isarsu kana suka jera zuwa asibitin,

Basmah na kwance bata wainar da ake toyawa ba, idanuwanta lumshe amma ba bacci take ba, ta rasa dalilin dayasa kalmar Abba ta cewa yau aka d'aurawa Ammar aure ta tsaya mata a rai,

tayi-tayi ta manta da maganar amma ta kasa, haka nan taji tana jin haushin Ammar d'in, da gudu Safiyyah ta shigo d'akin ta fad'a kan Basmah,

tana fad'in " i missed you k'awata, jin muryar Safiyyah yasata saurin bud'e, a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da rungume Safiyyah,

" kiyi hak'uri Safiyyah nasan na b'ata miki, na ci miki mutunci na wulak'anta akanshi, ina jin kunyarki, ina jin kunyar baki hak'uri,

tayi maganar hawaye na gangarowa kan fuskarta itama Safiyyah hawayenne suka shiga zubo mata, tasa hannu tana gogewa Basmah hawaye,

tace " bakiyi min komai 'yar uwata, in baki manta ba tun a lokacin na fad'a miki na yafe miki na kuma yi miki uzuri saboda kin had'o da munafukin namiji,

nace miki k'ofa a bud'e take a duk lokaci da zaki zo wajena ina maraba dake zan karb'e ki hannu bibbiyu, kuma kinanan a matsayinki har abada babu abinda zai canja,

hawayen saman fuskar Safiyyah Basmah ta goge mata had'i da rungume tana fad'in " nagode sosai Safiyyah, samun k'awa irinki zayyi wuya a wannan zamanin,

" nima har abada bazan tab'a samun kamarki ba, babu wacce zatakai matsayinki a wajena, ganin har lokacin Basmah kunyarta take ji, yasa Safiyyah cewa " wai kin yadda akayi abun ya faru kuwa?


"A'a Basmah tace tana tattara gaba d'aya nutsuwarta ga Safiyyah, saida ta sauke ajiyar zuciya kana tace " tana zaune akayi min text ta wayar Ummanmu,

wai inzo waje kaza Basmah ba lafiya, ko Ummanmu ban tsaya fad'awa ba na figi hijabi na fita, bayan naje wajen ne aka kuma turo min text ta wayar Umma dan da ita na tafi,

wai in shigo gida me bak'in get wanda yake kallo na, abinka da k'uruciya batare da tsoran komai ba na danna kaina cikin gidan,

a parlour na iske Zaman zindir ina shiga ya finciko ni, ya soma shafani yana yin wasu irin abubuwa, nan fa muka shuga dambe dashi, yace wallahi idan ban tsaya ba, 

zai tattaro k'atti su bank'are mishi ni yayi yadda yake so dani idan ya gama ya kashe ni ya jefar da gawata, wai dama ya dad'e yana sha'awata, damata ce bai samu ba, 

in banda Allah ya rufa min asiri bani da rabon wahala kin dawo da ban san abinda zai faru ba, ajiyar zuciya Basmah ta sauke kana ta fad'awa Safiyyah duk abinda ya faru tsakaninta da Zaman,

da mugayen halayenshi, sosai Safiyyah tayi kuka saida Basmah ta rarrasheta kana tayi shiru, Umma dasu Ya Mu'allim suka shigo, d'auke da abinci da bargo da pillows,

Safiyyah ta zubawa Basmah abinci ta d'iba a cokali takai bakinta hannunta har rawa yake, Umma tace " umm ba zama fa Safiyyah an had'u da Basmah,

Ya Mu'allim yace " bakiga yadda jikinta yake rawa ba?


Bayan an d'an tab'a hira Umma tace " Safiyyah tashi Usman yakaiki gida, k'afad'a ta mak'ale tana fad'in " a'a Umma anan zan kwana,

Usman da Ammar suka kalli juna, Umma tace " a'a ayi haka fa amarya dake ki kwana asibiti kibi mijinki gobe saiku dawo tare, bakin Basmah bud'e cike da tsantsar mamaki tace " wace amaryar Umma?


"Au baki sani bako?


"Ai yau aka d'aura auren Usman da Safiyyah, Umar da Aisha wata k'ila kin santa 'yar makarantar ku ce, Abubakar da Fatima, ai a wajen d'aurin auren aka sanar dasu halin da kike ciki,

hannu ta sanya ta rufe bakinta idanuwanta waje ta kasa magana saboda murna, yadda tayi ya basu dariya, d'an duka takaiwa Safiyyah tana fad'in " shine baki fad'a min ba ko?


Fuskarta ta b'oye a bayan Basmah ta rad'a mata " ke fa suruka ce, tayi maganar k'asa-k'asa yadda ba mai jin abinda tace, " haba shiyasa naga kunata kyalli ashe angoye ne,

amma shine kuka bar amaranku kukazo kukata tare a asibiti wajena, zama sukayi kusa da ita Usman ya kwantar da kanta a kafad'arshi, yana fad'in " ba dole our lil sis is back ai dole suma suyi hak'urin yau,

siraran hawayenta ta fakaicin idonsu ta goge cikin ranta tana jinjina irin soyayar da iyayenta da yayyanta suke mata,

amma duk da haka ta santa k'afa ta shure ta tsallake tabi namiji, hancinta yaja yana cewa " karkiyi yau, dan daga yau har abada bazaki k'arayin kukan bak'in ciki ba,

murmushi tayi me kamar dariya had'i da ture hannunshi tace " tom ni dai yaya ga amanar k'awata nan, ka rik'eta hannu d'ari-d'ari ba bibbiyu ba,

lanshi ya langwab'ar yace " to nima ki bata amana ta, " bana jin k'awata nasan halin abuna, cikin shagwab'a yace " to ni baki san hali na?


Dariya ta sanya sosai had'i da cewa " i missed your rigima Yayana, Umma tace " ku tashi ku tafi, zan kwana da Basmah, Safiyyah tayi saurin cewa " dan Allah Umma kibarmu muyi hirar yaushe gamu,

" a'a baza'ayi wannan wautar dani ba, kuje kwa dawo gobe in Allah ya kaimu, batasan yiwa Umma musu tun asali bare yanzu data kasance surukarta,

dole ta mik'e ta kalli Basmah tace " karki bacci ki jirani da nayi sallar asuba zan dawo,

yadda tayi maganar tsakaninta da Allah yayi masifar basu dariya gaba d'ayansu, ta fice tana sunne kai, Usman da jira yake yabi bayanta,

Umar da Abubakar suka fice, Ammar ya shafa kanshi yace " Umma kije gida zan zauna da ita, da sauri Basmah ta kalleshi cike da mamakinshi,

dan bata san an d'aura musu aure ba, bisa mamakinta taga Umma ta mik'e tana fad'in " muje Malam, yaran yanzu basu da kunya kwata-kwata, korata ma yake, " a'a Umma korarki nake yi, 

naga kin gaji ne shine nace kije gida ki huta, Ya Mu'allim yana murmushi yace " yi shiru abinka , 

kasancewar kowannensu yana da motar kanshi kuma masu ra'ayin addini ne yasa babu kai amarya da kowanne da kanshi yaje ya d'auki amaryarshi,

Usman yaja kunnen Safiyyah yana fad'in " da bari na zakiyi na kwana ni kad'ai?


Baki ta turo tace " da dawa kake kwana?


Sai da yayi dariyar turo bakinta kana yace " dasu Aliyu mana, da zuciya d'aya tace " tokaje yauma ku kwana tare ni kuma na koma na kwana da aminiyata, " a'a da yayan aminiyarki zaki kwana yau, ya fad'a yanayin parking a harabar gidansu,

a jere gidajensu yake iri d'aya sak guda hud'u, gidajen masu kyau sosai, sun tsaru ba laifi ga kayan more rayuwa, babu abinda babu, kazar amarci Aliyu ne yasai musu gaba d'ayansu, dayake shi bayyi auren ba, 

a daren babu wanda ya d'agawa amaryarshi k'afa kowannensu ya amshe budurcin matarshi, Safiyyah kam an gurzu a hannun Usman, matar datake cewa k'arfe biyar zata dawo saigashi har sha d'aya tana baccin wuya.


Bayan fitar Umma da Abba Ammar ya had'e ranshi danya lura duk inda yayi tana biye dashi da ido, yadda bakinta ke motsi ya tabbatar mishi magana take sanyi,

amma yak'i bata dama, dayake d'akin bakomai bakowa saisu, da ban d'aki a ciki, ga fridge da TV, daga gefe set d'in sofa ne a zagaye, dayake tangamemen d'aki ne me girma sosai,

batare daya kalli inda take ba yace " tashi muje inyi miki wanka, ita mamaki ma yake bata, wanne irin abu ne haka, wai ace namiji daba muharraminta ba shine zayyi jinyarta kamar bata da kowa,

basarwa tayi kamar bata ji abinda yace ba, " bakiji abinda nace bane?


Ya fad'a yana tsare gida, " naji sai dai ban fahimci kalmomin naka bane, "oh! inaga kamar ba hausa nayi miki ko?


"Ko kuwa kece baki jin hausar oho, banza tayi dayi dashi danta lura yana bala'in jida kanshi, hannun rigarshi ya shiga tattarewa batare daya kuma yi mata magana ba, idonta ta kawar gefe tana kallan tv,

amma a zahiri hankalinta na kanshi tana san ganin abinda zayyi, ba dato taji ya d'agata sama, ido ta zaro had'i da bud'e baki zatayi tsiwa,

amma kwarjini da haibarshi suka hanata furta koda kalma d'aya saima shagala datayi da kallan kyakkyawar fuskarshi, " idan baki gane magana ai kina zahiri ko?


Yayi maganar yana direta cikin kwamin wanka daya cika da ruwan me d'an zafi, ido ta runtse had'i da sakin 'yar siririyar k'ara tana k'ank'ame shi,

tace " Allah da zafi, ta fad'a tana k'ok'arin mik'ewa, mayar da ita yayi cikin ruwan yana fad'in " zakiji dad'in jikinshi sosai idan ruwan ya ratsaki,

tana rik'e da hannunshi gam while idonta a rufe ta zauna cikin kwamin wankan, ajiyar zuciya ta sauke a fili, wacce ta saukarwa da Ammar nutsuwa,

danya tabbatar taji dad'i, batare dayayi mata magana ba ya soma k'ok'arin cire mata kayan jikinta,

da sauri ta rik'e hannunshi had'i da cewa " ka fita zanyi sauran da kaina, ido ya tsura mata alamar kin tabbatar, kanta ta d'ata mishi, ya mik'e ya fice,

kanta a k'asa ta fito d'aure da towel iya cinya tana rarrab'ewa kallo d'aya yayi mata ya kauda kanshi gefe, ya mik'a mata jallabiyarshi batare dayace komai ba,

" wannan zan saka?


Hankalinshi nakan Tv yace " idan kina da wani abun sakawa kina ina k'in saka wannan d'in, " idan su Abba suka ganni da kayanka a jikina fa?


Banza yayi da ita yana cigaba da kallan labaranshi, " uban girman kai, ta fad'a cikin ranta tana saka rigar, batare daya kalli inda take ba yace " ko?


Ido ta zaro danta fahimci yaji abinda tace, batayi magana ba ta haye gado tana k'ok'arin kwanciya, " sallah fa?


Yayi maganar a tak'aice ta lura yana da rainin hankali, yasan fa bata sallah tunda yasan b'ari tayi, amma shine dan neman magana yake tambayarta sallah fa,

" idan bazakiyi sallah ba kici abinci kisha magani, rolling sexy eyes d'inta had'i da cewa " ya Rabbi!, bayyi magana ba ya mik'e ya had'a mata tea me kauri ya mik'a mata,

kallanshi tayi kana ta kalli tea d'in ta girgiza kanta, kafad'a ya d'age irin i don't care d'in nan ya koma ya zauna yana shan tea d'in,

sosai Basmah ke jin yunwa tace bata sha ne dan a zatonta zaice mata tasha, ta k'ulu sosai da yadda yayi mata amma ta kanne tayi kwanciyarta,

shima a nashi b'angaren yasan tana jin kunyar yayi mata haka ne danta gane kuranta, cikin bacci taji ba kanta yunwa ta hanata sakat, sai faman juyi take,

dariya ya saka had'i da cewa " ki magantu a taimaka miki, bak'in ciki yasata fashewa da kuka abinda dame jira, yana dariyar ya mik'e ya had'a tea ya d'umamata farfesun cow tail a microwave,

ya mik'a mata, kaita kawar tana cigaba da kukanta, yadda yayi mata d'azu haka ya kuma yi, ya d'age kafad'a zai juya, tayi saurin rik'o shi tace " bani, dariya ce ta kwace mishi yayi me isarshi kana ya zauna ya bata abaki harta k'oshi, ta turo baki tana fad'in " kuma saina fad'awa Abba da Umma gobe ince kar'a sake bari na dakai baka iya jinya ba,

bayyi mata magana ba, ya mayar da kwanikan ya aje ya koma saman sofa me zaman mutum uku ya kwanta ya rufa da bargo, da safe bayan yayi sallar asuba yana zaune saman sallaya yana addu'o'i,

jikinshi ne ya bashi ana kallanshi dan haka ya juya duk da sun had'a ido hakan baisa ta d'auke idonta ba, ta shagala sosai da kallanshi, " kallan ya isa haka ki tashi na kaiki ban d'aki, 

a dururuce ta d'auke idonta cike da kunya, cikin nutsuwa ya mik'e ya had'a mata tea ya mik'a mata yana fad'in " nasan yunwa kike ji shine kika tsare ni da ido.


K'arfe takwas na safe ta bud'e idonta a hankali suka sauka akan Ammar dake bacci saman kujera, haka nan taji tana san kallanshi,

ta ku'ura kishi ido deep down tana jin wani abu na tsara ta, ta d'auki tsayin lokacin da bata san iyakarshi ba tana kallanshi, kamar daga sama taji yace " bana san yawan kallo, ya fad'a batare daya bud'e idonshi ba, saurin rufe idonta tayi kamar me bacci,

yayi murmushi had'i da mik'ewa ya shiga bathroom, yayi wanka, ya had'a mata ruwan wanka, batare dayayi mata magana ba ya d'auke ta, idonta ta bud'e da sauri had'i k'ok'arin kwace jikinta, tana cewa " ni ka sauke ni, ban san irin haka,

bayyi mata magana ba sai da ya direta a kwamin wanka, yana juyawa yace " kiyi sauri su Umma sun kusa zuwa, baki ta turo mishi batare da tayi magana ba,

ya fice yana murmushi, da kanshi ya shafa mata mai ya saka mata, yana gama shiryata su Umma na k'arasowa, bayan sun gaisa Basmah tace " wai Umma bani da kowa ne da za'a bar namiji yana jinyata?


Umma tayi murmushi tana mamakin yadda har yanzu halin Basmah bai canja ba, a shagwab'e tace " Umma kinyi shiru, 

" a'a bani zaki tambaya ba, bari Malam ya shigo saiki tambaye shi, shi yafi dacewa ya amsa miki, Ammar na gefe baice komai ba, Umma ta mayar da kallanta gareshi tana fad'in kaje gida ka huta,

inyaso ka dawo, kanshi ya durk'usa k'asa had'i da cewa " a'a ma koma gidan gaba d'aya idan an sallamemu, Safiyyah bata dawo asibitin ba sai bayan kwana biyu,

wai tafiyarta ba dai-dai take ba idan tazo Umma zata gane, fuskarta d'auke da murmushi ta shigo tana fad'in " Aminci na, ko kallan inda take Basmah batayi ba,

" kai Aminci na kiyi hak'uri, " badai kin manta dani ba, kina can wajen Yaya kuna shan soyayya ko?


"A'a ba haka bane, " shine harda wani cewa da nayi sallar asuba zan dawo, munafuka kawai, dariya Safiyyah tayi had'i da rad'a mata wani abu,

ido Basmah ta zaro cike da tsoro tana fad'in " wai sannunki kice kinji gumu?


"Bari kedai kawai in ana sallah ba'a magana amma na gurzu, suka saka dariya gaba d'ayansu, Safiyyah tace " ku naku first night d'in inaga a gadon asibiti zakuyi,

cikin rashin fahimta Basmah tace " kamar ya?


"Ina nufin keda *ANGONKI AMMAR....!* mana, " ango na kuma?


"Au wai baki san tun ranar aka d'aura muku aure da daddare ba?


Cikin kid'ima Basmah tace " what?


"Aure fa kika ce?


Basmat ta fad'a cikin tashin hankali,

"wallahi da gaske, ke wai da baki sani ba?


"Yo in banda ma abinki ya za'ayi a barshi yayi jinyarki idan ba mijinki bane?


"Kiyi tunani mana Aminci na, d'an shiru Basmah tayi kana ta sauk'e ajiyar zuciya hawaye na gangaro mata ta kalli Safiyyah tana fad'in " wacce irin soyayya Ammar yake min?


" Da yake so na har yanzu a lokacin dana sara komai, komai ya k'are min, bani da wani abu dazan bashi, na cuci kai na Safiyyah,

nayiwa kaina illar da har in mutu bazan manta ba, i hope baya tana iya dawowa dana gyara kuskuren danayi, bani da saurin abu me muhimmanci da zan bashi Safiyyah,

fashewa tayi da matsanancin kuka tana cigaba da fad'in " bani da komai Safiyyah, " bana buk'atar komai daga gareki daya wuce zuciyarki da soyayyarki,

idan kika bani so kin gama mallakamin abubuwa mafiya muhimmanci agareki Basmah, da sauri ta kalli inda take jiyo maganar,

yana tsaye hard'e da hannuwa a k'irjinshi ya sakar mata murmushi had'i da takowa inda take yana cigaba da fad'in " soyayyarki a cikin jinina take,

had'in Allah ne bawai na mutum ba, ba jikinki ko wani abu naki nake so ba, ke d'in nake so Basmah,

zan iya rayuwa dake har abada koda baki da komai, koda babu sex, tun kan ki mallaki koman nake sanki, tun kan ki isa abin sha'awa awajen namiji nake sanki,

ba jikinki nake so ba, badashi nake san kasancewa ba dake nake san kasancewa Basmah, ban damu da abin ke jikinki ba, bama na kallanki a matsayin kin tab'a aure,

ko wani ya tab'a saninki ya mace, a sabuwa fil nake kallanki, kwanaki uku da suka wuce Safiyyah budurwa ce, amma yanzu fa?


"Da wasu 'yan matan ma gwara Zawarawa so dubu wallahi dansu kasan aure sukayi ba'a titi suka bayar ba, abinda yake lalata mafi yawan auren zamanin nan kenan,

saboda ba'a gina shi saboda Allah ba, ba'a ginashi bisa soyayyar gaskiya ba, an ginashi akan sha'awa, da an kwana sai aure ya lalace, to dama can ba san juna ake ba,

sha'awar juna akeyi, kuma an gusar da ita me yayi saura?


"Idan har kana san mace tsakani da Allah ko baka kanta tayi a titi bazaka tab'a lalata ba, babban burinka ka aure ta ka kaita gidanka,

dan haka ni ke nake so, ba sex nake san yi dake ba, ba kuma sha'awarki nake yi, budurci wani abu ne d'an lokaci kad'an da zarar an kawar dashi budurwa da bazawara sun zama d'aya,

idan kana san mace ka aure ta kanka tsaye karka damu da maganganun mutane na cewar bazawara ce ko makamanta haka,

gwara ka auri wacce ka lalata ko bazawarar daka auri wacce wani ya lalata dan bazaka tab'a yiwa Allah wayo ba, bata san sanda ta fad'a jikinshi ba ta kasa kuka me cin rai,

kanta dake kan kirjinshi ya d'ago had'i da goge mata hawaye yana girgiza mata kai alamar tayi shiru, yace " nayiwa Abba alk'awari bazaki k'ara kukan bak'in ciki ba sai na farin ciki,

cikin muryar kuka tace " wannan ma na farin cikin ne, Ya Mu'allim da Umma dake tsaye suka kalli juna suna murmushi, deep down suna godewa Allah.