SAKI RESHE..

29

by @hauwaausmanjiddarh

29


Zaman na janye da trolling shi while yana k'arewa gidan kallo, cikin ranshi yace " wannan shi ake kira da gida bamu da muke rayuwa a kufai ba,

mai gama tsinkewa ba saida ya shiga cikin gidan yaga aljannar duniyar da aka zubawa gidan, abu na farko daya fara zuwa ranshi shine yadda zayyi ya mallaki gidan ya zama nashi,

" nan yayi maka kona canja maka wani d'akin?


Hajiya Tanya ta fad'a tana nuna mishi d'akin, kanshi ya shiga juyawa yana k'arewa d'akin kallo kana yace " yayi, murmushi tayi tare da cewa " ga bathroom nan ka watsa ruwa ka huta idan ka gama ka fito na gabatar dakai ga sauran mutanen gidan,

batare da yayi magana ba aje jakarshi yana zagaya d'akin, ganin har zuwa lokacin Hajiya Tanya na tsaye bata fita ba, yasashi kallanta had'i da cewa " yadai?


"Ko kina buk'atar wani abu ne?


Murmushi tayi mishi irin na cikakkun 'yan duniya tace " not now letter, bata jira amsarshi ba ta fice, yabi k'ofar da kallo yana san gaskata abinda ya gani,

kafad'arshi ya d'age irin bai dameni ba yace " duk ta inda kika biyo zan iya bi dake, sai da yayi wankan kana ya fito parlour,

ya iske ta zaune ita da Nayan suka shan sigari kallo d'aya yayi musu ya zauna saman sofa yana fad'in " meye abun yi?


"Nafi san muyi komai akan lokaci bana b'ata lokaci, Hajiya Tanya zatayi magana Basmah da Ammar suka shigo gaida Hajiya Tanya,

Basmah na rik'e da plate d'in abinci data karb'o daga wajen Hajara, " ina yini?


Ta fad'a cikin nutsuwa, tunda Basmah ta shigo Zaman ya tsareta da ido zuciyarshi na wani irin bugawa da k'arfi,

tayi fresh kyanta ya fito sosai farinta kuwa har d'aukar ido yakeyi, batare daya sani ba ya yunk'ura zai mik'e Hajiya Tanya tayi saurin saka hannu ta danneshi,

while tana amsa gaisuwa Basmah fuskarta d'auke da murmushi, Basmah na niyyar fita idonta ya sauka akan Zaman,

plate d'in tangaran hannunta ya sub'uce ya fad'i k'asa ya tarwatse, lokaci d'aya cikinta ya d'auki muguwar rawa da tsuma,

k'afafuwanta suka fara kerrrma suka kasa d'aukatar tayi baya zata zube Ammar yayi saurin tallafeta ta fad'a jikinshi, Shakira dake shigowa tabi inda Basmah ke kallo da kallo,

cikin tashin hankali da matsanancin tashin hankali ta sanya hannu a bakinta idonuwanta sukayo waje kamar zasu fad'i k'asa,

Shakira ta kalli Basmah ita Bamsah ta kalli Shakira, sunyi seconds goma suna kallan juna kafin cikin rawar jiki Basmah ta d'aga hannu ta nuna Zaman,

dake zaune hard'e da k'afa idonshi kanta yana sakar mata shu'umin murmushi, k'ok'arin motsa bakinta ta soyi zatayi magana amma ta kasa saboda firgici,

" lafiya?


Ammar yace yana jijjigata, ganin Basmah na san yin magana yasa Hajiya Tanya yin karaf ta tari numfashinta tace " d'an 'yar uwata ne yazo hutu bazai dad'e ba zai koma,

ido Basmah ta zuba mata tunani kala-kala na shigarta ta tabbatarwa kanta k'arya Hajiya Tanya take babu abinda ta had'a da Zaman,

murmushi Ammar yayi had'i da mik'awa Zaman hannu, hannun Ammar Zaman ya kafe da ido batare daya bashi hannu ba, d'an zungurarshi Hajiya Tanya tana murmushi,

sai lokacin ya dawo cikin hayyacinshi ya mik'e gami da mik'awa Ammar hannu suka gaisa, k'ank'ame Ammar Basmah tayi cikin kid'ima tana fad'in,

" mu tafi mubar nan wajen please, ka mayar dani part d'inmu, sakin hannun Zaman Ammar amma yaji Zaman ya rik'e hannunshi bai saki ba,

kallan hannun Ammar yayi yana murmushi yace " hannu na fa?


"Oh! I'm sorry, Zaman yace yana sakin hannun, batare daya kuma magana ba ya tallafe Basmah suka fice, Zaman yabi bayansu da kallo,

had'i dayin kwafa, " kaga kabi komai a hankali a sannu zamu cika duka muradanmu idan mukabi komai a nitse, kallanshi ya mayar ga Shakira dake tsaye kamar an dasata,

deep down tana mamakin Hajiya Tanya, tana neman dalilin dayasa ta d'auko, ita abinda ma take san sani ma shine ina Hajiya Tanya tasan Zaman?


Meye alak'arsu.....! " bakiyi farin cikin gani na bane Dear?


Zaman ya katse mata tunaninta zagayawa yayi ya rungumeta ta bayanta ya d'ora hab'arshi saman kafad'arta yace " gaskiya Ammar bashi da adalci,

ya had'e min duka matan nawa ya aure ko d'aya bai bar min ba, anya ya kyauta min kuwa?


A zuciye Nayan ya yunk'ura ya mik'e zai nufi Zaman, Nashwan yayi saurin shan gabanshi, a k'ufule Nayan ya kalli Nashwan yana shirin yin magana,

Nashwan ya girgiza mishi kai alamar a'a, duk abinda sukeyi kan idon Zaman, " daka barshi ya k'araso ai, yayi maganar yana sakin shu'umin murmushi,

idonshi rufe yayiwa Shakira rad'a yadda babu wanda zaiji abinda yace " ki faki idansu kizo ki same ni a d'aki muyi magana,

bai jira amsarta ba ya saketa ya shige bedroom yabarsu nan tsaye, " oops kana neman b'ata mana komai, in banda Nashwan ya tareka da Allah kad'ai kasan abinda ya faru zuwa yanzu,

dan Allah ka rink'a yin abu da lissafi ni kaina uwarka wannan yafini shu'umanci balle kai daka gada daga wajena,

" ina kake samo wannan Hajiya?


"Kin san waye shi kuwa?


"Kin bala'in dake cikin kawo shi gidan nan?


"To wallahi baga Ammar da Basmah ba harku dakuka kawoshi ku kuka dakanku, dan ba'a yin abun arziki dashi sayya koma na tsiya,

shaid'anine fiye da tunaninku duk mu nan yafimu masifa dan haka kowa yayi ta kanshi, kowa ya fara neman mafita da k'ofar da zata b'alle mishi idan ballin Zaman ya tashi,

Shakira ta fad'a tana binsu da kallan tsanake, kwatin sigari ta d'auka ta bud'e ta cira ta saka a bakinta ta kunna wuta ta zuk'a ta busa hayak'in sama,

tana kallan hayak'in tace " taba matsala ce ga rayuwa dan tana kashe mutum da wuri to amma meyasa muke shanta?


Baki ta tab'e ta mayar da kallanta ga Shakira tace " saboda ran mu naso, matsoraci baya tab'a zama gwani, da ganganci ake cimma buri,

sanin halinshi da shaid'ancinshi danayi yasa na d'auko shi na kawoshi, daya gama mana aiki zan san yadda zanyi dashi, inyasan wata ai bai san wata ba,

gaba da gabanta, shi yanzu ya fara bariki, ina yaje ina aka sanshi a iskanci?


" Shida har yanzu yatsa ya tsoma a bariki ki bari kiga yadda zan shayar dashi gidauniyar mamaki na bud'e mishi sababbin shafuka a fannin bariki,

na d'ora mishi darisin da idan ya rik'esu zayyi a duniyar shagalallu da wad'anda aka cewa jeka ka gani, guntun murmushi Shakira tayi tana kallan Hajiya Tanya tace,

" da alama Hajiya baki san waye MUGU ba, bakisan illolin da zai iyayiwa rayuwarki ba, to idan baki sani ba ki sani mutuwarki kika d'auko kika kawo gidanki da kanki,

" Allah ko?


Hajiya Tanya ta fad'a tana d'age gira d'aya ta cigaba da cewa " lokaci ne kad'ai zai tabbatar da wanda ya d'auko mutuwarshi,

murmushi Shakira tayi batare datace komai ba, 

Basmah ta kasa zaune ko tsaye sai faman zarya take a d'akin takai ta koma, ta gama tabbatarwa kanta akwai abinda Hajiya Tanya ke shirin k'ullawa,

wato datace mata Shakira 'yar uwartace k'arya take kenan tunda gashi yanzu tace Zaman d'an uwanta ne, taya suka zama 'yan uwanta?


Tabbas akwai wani abu a binne, a ranta ta yanke shawarar taje ta samu Ammar ta sanar dashi gaskiyar abinda ke faruwa, ta fad'a mishi wacece Shakira,

ta fad'a mishi Zaman tsohon mijinta ne, tunkan wani abu ya faru ya rink'a ganin laifinta, ta juya zata fice daga d'akin tayi karo da Ammar,

daya kai wajen minti 10 tsaye yana kallanta, a tsorace ta d'ago kanta dan zatonta Zaman ne, a fili ta sauke ajiyar zuciya had'i da lumshe idonta,

ganinta a firgice duk ta fita daga hayyacinta yasashi jawota jikinshi yana kallan cikin idonta yace " lafiyarki kuwa?


Bakinta na rawa tace " magana nake san yi dakai akan Hajiya dasu Nayan, fuska ya d'an tsuke tare da cewa " wacce irin magana?


Ta kula da yadda yanayinshi ya canja amma bazata iya yin shiru ba, " wannan data kawo tace d'an uwanta ne wallahi ba d'an uwanta tsoh.....!,

dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu yace " enough Basmah bana san maganar, ya fad'a yana k'ok'arin ficewa daga d'akin,

saurin shan gabanshi tayi tace " ka tsaya ka saurari wallahi da akwai babbar matsala..... tsawar daya daka mata ne yasata yin shiru dole,

ya nunata da yatsa yana fad'in " nace miki bana san maganar ko?


Ido ta zuba mishi cike da tsoro, ganin zata karya mishi zuciya yasashi saurin ficewa daga d'akin, jiki a sanyaye ta zauna jiki ba kwari had'i da fashewa da kuka,

sai taci kuka mai isarta kana ta mik'e ta fita takai bakin k'ofar shiga part d'in Hajiya Tanya tajiyo magana k'asa-k'asa,

batayi niyyar yi musu lab'e ba jin an kira sunan Ammar yasata d'an dakatawa, muryar Hajiya Tanya ta jiyo tana cewa " kaga Zaman kayi duk abinda zakayi bani da matsala,

inda zan mallaki dukiyar Ammar koda kasheshi ne kayi bani da matsa muddin hak'onmu zai cimma ruwa, naga kamar kai zakayi abin arziki,

ba kamar waccan lusarar danayi hayarta na aurawa mishi dan ta san yadda zatayi ta mallakar mana dukiyar ba, amma ta kasa aiwatar dakomai ,

illar hudd'a da karuwai kenan ta fad'a tana zubawa Shakira harara, a zafafe Shakira tace " oho dai kwari ni watanni kad'ai nayi na kasa, wanda yayi shekara talatin ya kasa komai fa?


"Wallahi hannunki bai cud'i bayanki ba, duk cika bakinki da kurin da kike yi ke uwar sharri da tuggu amma kika kasa kawar da k'aramin alhaki kamar Ammar,

saida kikayi hayar ta hakan ma be isheki ba saida kika nemo Zaman, ga Nashwan, hannu Basmah ta sanya ta rufe bakinta had'i da zaro idanuwa waje cikin tashin hankali,

" karki damu Hajiya ina da mafita, abu na farko daya kamata mu farayi shine kashe Ya Mu'allim,

mahaifin Basmah tunda shiya tsayawa Ammar idan muka kawar dashi jikin Ammar zayyi sanyi, fargaba da tsoro zasu shige shi,

kafin ya farga zamu cimma masa mu samu damar kashe shi, kai Hajiya Tanya ta jijjina cike da gamsuwa da maganganun Zaman,

tace " kamar kasan na tsani wannan shegen munafukin, yadda na tsani Ibrahim ko mutuwata ban tsana haka ba,

bani da burin dayafi naga yayi mushe, shine yake taja min asara da fad'uwa, ta k'arasa maganar cikin matsanancin b'acin rai,

" karki damu yau za'a aiwatar da komai, Zaman ya fad'a yana mayar da kallanshi ga Nashwan yace " kai na baka kwangilar kashe Ammar,

a zabure Nashwan yace " wa ni?


" Eh!, kai nake san ka kashe Ammar da kanka da hannunka, kanshi ya shiga girgizawa yana fad'in " bazan iya ba, bazan iya kashe Ammar da hannuna ba, a k'ufule Zaman yace " kaji k'aramin shege da baka shiryawa abin ba?


"Ko ba kud'i kake so ba?


"Tunda har ka iya cin amanarshi akan abin duniya meye bazaka iya yi ba?


" A dai canja shawara amma banda wannan dan bazan iya kashe Ammar ba, Zaman zayyi magana Nayan yace " shikenan ka kashe Ya Mu'allim,

ni da Zaman zamu gama da Ammar, " to wannan da sauk'i shi zan iya, Nashwan ya fad'a yana juya kai, Zaman ya kalli Nayan yace " ni bana had'a aiki na da kowa,

saboda gudun matsala ka barni zan kawar dashi daga doran k'asa dama ni yafi dacewa na tsinke mishi numfashi, dan nayi alk'awarin duk wanda ya rab'i koda inuwar Basmah ne sai dai uwarshi ta haifi wani,

yanzu zan fita na cire mishi birkin mota, ke kuma saiki kira shi ki aike shi, a kid'ime Basmah tayi baya ta bar wajen, jikinta na rawa ta fad'a d'akin Ammar,

bata ganshi a d'akin ba dan haka nufi bathroom inda tajiyo k'arar ruwa, kai tsaye ta fad'a ciki ta iske shi yana wanka, kallo d'aya yayi mata yasan ba lafiya ba,

bata damu da yadda yake ba ta nufe shi a haukace cikin matsanancin kuka tana fad'in " zasu kashe min kai, naji su suna shirya yadda zasu kashe ka kaida Abba,

wallahi naji su da kunne ta fad'e cikin rashin nutsuwa, a hankali ya kama kafad'arta yad'an girgiza, idanshi kanta yace " ki nutsu kinji?


Bai gama wankan ba ya d'aura towel a k'ugunshi ya fito yana rik'e da ita yace " meya rud'aki haka?


" Hajiya Tanya zasu kashe ka kaida Abba da kunne na jisu......, " stop it please Basmah, karki kuma kawo min maganarsu dan Allah,

baki ta bud'e zatayi magana yayi saurin cewa " please! bana san maganar, koma ma zasuyi suje suyi, meye bata yi ba, babu abinda yarage wanda batayi ba,

duk abinda zatayi daga baya, bani da kowa sai ita da yaranta, matar mahaifina ce, matsayin uwa take a gari ni, Nayan da Leenah ne kad'ai 'yan uwana na jini ya kike san nayi?


" jikinta na rawa while muryarta na creaking tace " Abba na , shima zasu kashe min, please kayi wani dan Allah karsu..... a tsawace yace " Please kibar maganar nace miki bana so, 

itama cikin tsawa da hargowa tace " ba sanka suke yi ba, dukiyarka suke su, ka basu dukiyar da duk abinda suke so much tafi, 

muje inda zamuyi rayuwa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, b'acin rai ne yasashi d'aga hannu zai kira mata mari, hannun ya tsayar cak a dai-dai fuskarta,

Basmah tabi hannun da kallo, bata kuma yi mishi magana ba ta zame k'asa ta fashe da matsanancin kuka tana fad'in " Abba na,

ido ya runtse had'i da naushin iska, yana fad'in " oh God, ido ya zuba mata na tsayin lokacin yana mamakin yadda kuka baya yiwa wasu wuya,

dama shine yake samun damar kuka haka daya samu sauk'in azalzalar da zuciyarshi keyi mishi, daya huta da k'unar da k'irjinshi keyi mishi,

bayyi mata magana ba ya sanya hannunshi ya d'aga ta tsaye yakaita bakin gado ya zaunar da ita, ya juya ya fita, bai dad'e ba ya dawo rik'e da glass cup cike da ruwan sanyi,

ya mik'a mata ba musu ta amsa ta shanye tas ta sauke kofin daga bakinta tana fitar da numfashi a fili, a hankali ya zauna kusa da ita, 

ya rungume ta tsam a jikinshi yana shafa bayanta tare da bubbuga bayanta cikin sigar rarrashi, " kina san kisan rayuwar danayi?


Ya fad'a cikin karyewar murya, a hankali ta d'aga mishi kanta alamar eh, bai b'oye mata komai ba ya sanar da ita tun daga ranar da aka haifeta,

har zuwa yau dayake bata labarinshi ya k'arasa maganar hawaye na zubowa saman fuskarshi, bata san sanda ta fad'a jikinshi ta fashe da matsanancin kuka ba,

hannunshi yasa yana danna kanta a saitin zuciyarshi dan nemarwa kanshi sauk'i, saida ya had'iye wani k'ululu daya tokare mishi wuya,

kana yace " a lokacin duk danake shan wannan bak'ar azaba ban damu ba saboda bani da wani buri daya wuce na girma na aure ki,

ban taso da san kowa a zuciyata ba saike, ban sabarwa zuciyata da soyayyar kowa ba sai taki, tun kan nasan kaina nasan soyayyarki,

tun kan nasan ciwan kaina sana ciwon sanki Basmah amma sai kika...... kasa k'asara fad'ar abinda yayi niyya yayi, ya had'iye yawo kwata,

cikin kuka tace " kayi hak'uri kowanne mutum daka gani a rayuwa yana da k'addararshi babu wanda ya isa ya kaucewa k'addararshi,

Allah yayi saina auri Zaman da farko kafin na aure ka, Allah k'addara akwai rayuwar zama waje d'aya katsani na, ga raban cikin danayi shi,

muyiwa Allah godiya da bai sa an sami raban a titi ba, duk abinda kaga Allah yayi akwai dalilin yinshi Allah baya tab'a yin abu babu dalilin,

bayanta ya shiga shafawa yana sauke ajiyar zuciya gami da cewa " duk lalacewarsu nawa ne su, jini na ne, dole nane su, babu yadda zanyi dasu,

dan Allah kada ki shiga tsakanina dasu Basmah kada ki raba zumuncin Allah please, ina rok'onki kada ki k'ara yi min maganarsu, duk abinda zasuyi Allah yana ganinsu shi zai tsare mu daga sharrinsu,

kai ta d'aga mishi alamar to, wayarshi datayi k'ara ya kalla sunan Hajiya Tanya ya gani yana wayo a saman wayar, kallan juna sukayi ya sakar mata murmushi yana d'aga wayar,

" to gani nan zuwa in sha Allah, sosai tsoro yayi masifar kama Basmah k'irjinta ya shiga buga da k'arfi, a hankali ya zameta daga jikinshi,

ya mik'e ya sanya kaya ya fesa turare yace " ina zuwa, bata iya bashi amsa ba illa ido data zuba mishi, kamar yadda suka shirya Zaman ya cirewa Ammar burki,

bakinshi d'auke da sallama ya shigo, ta amsa fuskarta cike da fara'a, d'an shiru ne ya biyo baya kafin Hajiya Tanya tace " dan Allah idan ba dawo aikinka nake sanyi,

yana murmushi yace " ba damuwa, " kaina ke ciwo nake san ka siyo min paracetamol, ta fad'a tana yamutsa fuska, " Ok bari na siyo miki,

harya kai bakin k'ofa tace " baka karb'i kud'in ba?


Murmushi yayi yana cewa " Haba Momy ko wanda ban sani ba ai zan sai mishi magani bare ke, martanin murmushinshi ta mayar mishi ta d'ora da cewa " nagode, 

ya juya zai fita ta kuma cewa " af gaba d'aya motocin gidan basa nan sai dai kayi amfani da tawa, ta fad'a tana mik'a mishi key, 

amsa yayi ya fice batare dayace komai ba, gaba d'ayansu suka lek'a ta window suna ganinshi ya shiga motar ya fice, Hajiya Tanya ta dake k'irji tana fitar da iska daga bakinta,

tace " Allah yasa daga can ayi can kar a dawo min har abada, dariya Zaman ya saka yana fad'in " aiko yau duniya ko gidan tsoronshi ce sayya barta,

shigowar Shakira yasasu yin shiru, bata dad'e da zama ba suka ji shigowar Ammar har rige-rigen lek'awa sukeyi ta window,

lafiya sukaga ya fito ko kwarzabe babu a jikinshi, Hajiya Tanya ta kalli Zaman, shima ya kalleta, Nayan ya kalli Nashwan, nan fa aka shiga kallan kallo,

k'ofa ta k'urawa ido cikin tashin hankali, fuskarshi d'auke da murmushi ya shigo ya mik'a mata maganin, bata amsa ba ta cigaba da kallanshi,

d'an zungurinta Nayan yayi tayi firgigit tare da had'iye yawo, hannunta na rawa kamar mazari ta amshi maganin, rawar da hannunta yake yi ne yasa maganin sub'ucewa daga hannunta,

ya sunkuya ya d'auka ya mik'a mata yana fad'in " ki kula da lafiyarki Momy rai da rayuwa a hannun Allah suke babu wanda ya isa ya tsinke numfashin wani,

face lokacinshi yayi ki kula da kanki bana san wani abu ya sameki, ya fad'a yana murmushi, bakinta na rawa tace " ka......ka... kadawo?


Hannayenshi ya hard'e a k'irji yana binta da kallo yace " gani tsaye a gabanki kuwa, a dururuce tace " ina nufin babu abinda ya same ka?


Ido ya tsura mata yana jefa mata kallan tuhuma, " i....i....ina...nu..fin...ba..ka...ji....ciwo..ba, ta fad'a tana runtsu idonta, saurin mangarinta Zaman yayi, " kaje nagode k'ok'arin saita kanta, had'i da goge gumin daya karyo mata,

kanshi ya girgiza ya fita yana mamakinta, " wani abu kuka shirya mishi ya tsallake ko Hajiya?


Shakira ta fad'a cike da tuhuma, a zuciye Zaman ya shak'i wuyanta ya had'ata da bango yana fad'in " idan kika k'ara cewa tak saina kashe ki yanzu a waje nan,

hannayenta ta saka ta hankad'a shi baya tana tari ta tallafe wuyanta, ta jima tana tarin sannan ta d'ago jajayen idanuwanta ta zuba mishi tana fad'in " baka da hankali ne?


Matseta yayi a jiki bango muryarshi can k'asa yadda ba maiji yace " nace kizo ina san ganinki shine kika k'i zuwa ko?


Idonta ta d'aga ta kalleshi batare datace komai ba, " idan baki zo ba yau sai kin gane kuranki, " kunga yanzu kuzo musan meye mafita,

kunga dai Ammar yasha meye abinyi yanzu?


"Guba....! cewar Nashwan yana gyara zamanshi, cikin rashin fahimta suka ce " Guba kuma?


" Eh! guba ita kad'aice sha yanzu magani yanzu, azuba mishi guba a abinci Hajiya Tanya ta tsare shi sayya ci a gabanta,

hannu Hajiya Tanya ta tafa had'i da cewa " good idea kanka yana kawo wuta matashin saurayi, kai Shakira ta shiga girgiza tana fad'in " a'a dan Allah karku kashe shi please, ko kallan inda take babu wanda yayi cikinsu, suka mayar da hankali kan shawarar abinda zai fishshesu,

daga k'arshe suka yanke shawarar zuba mishi shinkafar b'era, ganin babu wanda ya saurareta cikinsu,

balle su kulata yasata ficewa daga d'akin, Zaman yabi bayanta, direct d'akinta ta wuce ta fad'a saman bed, jin an shigo d'akin yasata d'agowa da sauri,

cikin zafin nama Zaman ya fincikota ya matsata tare da cewa " ki tsaya muyi magana dan nemarwa kanmu mafita,

wad'annan mutanen kallan biri suke yi mana muna yi musu kallan ayaba,

suna yi mana kallan dankali muna yi musu kallan rogo idan baki zo mun had'a kai ba wallahi zakiyi kuka daga baya,

zakiyi biyu babu ba Ammar bani ba Nayan uwa uba kuma ba dukiyar, so suke yi suyi su gwara kanmu ta yadda zasuyi amfani damu,

su cimma burinsu daga baya su watsar dasu ko su kashe ki tsaya ki k'arewa takunsu kallo sosai ki kula da duk wani motsinmu zaki gane akwai abinda suke shiryawa su biyu,

bayan abinda muke shirya gaba d'ayanmu, uwa da d'an nan ba k'ananan shaid'anu bane dan haka sai mun kula sosai,

dariya Shakira ta sanya sosai harda tafa hannu hakan ya bawa Zaman mamaki da haushi ganin yana yi mata magana mai mahimmanci,

wacce zata amfane su amma ta mayar dashi sakarai, a zafafe ya nufeta tayi saurin ja baya tana tsagaita dariyarta tace " kai yanzu ka kula da takunsu?


"Ni tun ranar da suka zo min da maganar aikin nasan ba banza ba akwai abinda suka shirya, dan na dad'e ina jin labarin Hajiya Tanya a wajen Nayan,

abin lura shine meyasa suka zab'emu ni da kai muyi musu aiki?


"Wanne dalilin ne yasa basu d'auki d'aya daga cikin mu suka had'a mu duka, tsagaida maganarta tayi ta kalli Zaman dake tsaye ya zuba mata jajaye idanuwanshi, tace " kasan me nake tunani akan had'amu muyi aiki dasu?


Bayyi magana ba sai ido daya kafeta dasu, murmushi tayi had'i da juya mishi baya tayi taku biyu zuwa uku tace " saboda ni *KARUWA CE* nabar gidan mu tun ina k'aramar yarinya bayan na kashe mahaifina,

kai kuma cikekken d'an bariki daga ni har kai babu d'an asalin garin nan, bamu da kowa a garin nan, asalima babu wanda ya sammu ko muka sani,

kaga koda mun gama cika musu burinsu sun kashe mu bamu da wanda zai tambaye mu balle ayi bincike akanmu,

idan sun kashe mu san sun sun kashe banza da bamu da kowa bamu da bai bin hakkin jininmu,

musamman kai da babu wanda ma yasan asalin sunanka garinku da inda ka fito, duk inda kake zuwa,

akwai sunan da kake amfani dashi a wajen kowanne waje sunanka daban nan Mugu, can Tono, can Michael, can Arne, shiru Zaman yayi yana nazarin kalamanta harta dasa aya,

iska me zafi ya furzar had'i da sauke nannauyan numfashi yace " akwai daru, indai kuwa haka ne dole muma mu b'ullo musu ta inda basa tsammani,

dole mu sake salo mu canja taku inba haka ba wankin hula zai kaimu dare, mu taru mu had'a k'arfi mu nuna musu mun fisu sanin bariki,

mun fisu sanin iskanci da 'yan iska zan nuna musu basu san komai ba a bariki, yanzu suka tsoma yatsa, zan shayar dasu gidauniyar mamaki,

saina nunawa matar nan tsohon bariki ta sani wanda aka dena yayinshi tun 1950, yanzu sababbin biriki akeyi wad'anda ko wad'anda aka haifa a bariki basu sanshi,

bama su fara karantashi balle su haddace, mu lallab'a a fara kawar da Ammar dukiyar tazo hannu sannan ne zasu gane ba'a zuwa lahira da bante,

dariya Shirara ta sanya sosai, shima ya saka dariyar yana cewa " toke yane me zan samu, " kamar me ?


Ido d'aya ya kashe mata had'e da d'age gira ya lashe harshe yana fad'in " ki gane mana kwana biyu ba'a had'u, dariya tayi tare da dukan k'irjinshi tace " to jarabatu,

bayyi wata-wata ba ya fad'a mata kamar dabba ya soma biyan buk'atarshi ta bayanta, hannu Hajiya Tanya ta kakkab'e tana murmushi daga inda take lab'e tana sauraron hirarsu tace,

" yaro dai yaro ne, yara kuna k'ok'arin had'iyar garwashin wuta, zaka nuna min sabon bariki ni kuma zan tabbatar maka barikin 1950 har yanzu yana amfani, mu zuba mu gani tsakanin ni daku muga wanda zai kwashe lafiya.


Fuskarta d'auke da fara'a ta tare shi tana fad'in " shigo mana yaron kirki, yau nayi maka girki da kaina, murmushi Ammar yayi yana jan d'aya daga cikin kujerun dinning d'in ya zauna,

jikin Hajiya Tanya na rawa ta zuba mishi abincin a plate ta mik'a mishi tana fad'in yi maza ka cinye karka samma wad'annan lusaran matan naka da basa iya yi maka girki,

a gaba ta saka shi saida ya cinye abincin tass kana ta barshi ya fita bayanshi tayiwa gwala had'i da yarfe hannu tana fad'in,

" assss bak'ar daga, Allah yasa tafiyar kenan sai dai muje muga mushenka tsinanne me taurin tsiya, Nayan Nashwan da Zaman suka fito daga inda suke lab'e,

" na bashi yau dai wahalar mu zatazo k'arshe kowa ya huta da jidali, ta fad'a zama saman sofa, dukkaninsu zama sukayi suna sauran jiyo ihuun Shakira ko Basmah,

Ammar yana shiga part d'inshi d'aki ya wuce ya shiga wanka, bai dad'e da shiga ba Basmah ta shigo d'akin, bata san yana bathroom ba dan haka ta danna kai,

ido ta zaro had'i da saurin juya mishi ta rufe idonta da tafukan hannayenta tana fad'in " so...s....sorry, dariya ya sanya yana cigaba da wankan yace " yau kuma?


"Me?


Tace dashi har lokacin hannunta saman fuskarta, " naga ranar kai tsaye kika shigo, " wacce rana?


"Ranar da kikaji za'a kashe miki miji, kika shigo har ban d'aki kika tsaya kina k'are min kallo, yayi maganar yana rungumota ta baya,

ya shiga goga mata gashin fuskarshi a saman fuskarta d'an zabura tayi had'i da sauke ajiyar zuciya, cikin kunnenta ya rad'a mata " kiyi magana idan kina buk'atar wani abu,

ba ki rink'a shigowa a fakaicewa idan ina wanka kina k'are min kallo ba, bakinta na rawa tace " kasa kaya please, kafad'e ya d'age tare da cewa " da me ya kawo ki?


"Nasan abinda ya kawo ki kenan kizo ki kalle ni ko?


Yayi maganar yana zura hannunshi saman cikinta yana shafawa, cikin salo yasa yatsanshi a kwarmin cibiyarta yana zagayawa a ciki,

a hankali ta d'an gantsare ta tura k'irjinta gaba, hakan datayi bak'armin burgeshi yayi ba, sama yayi da hannunshi zuwa k'irjinta, 

saurin yin k'asa yayi da hannunki kamar ya tab'a wuta, dariya taso kufce mata amma ta kanne, hannunshi na rawa kamar mazari ya k'ara yin sama da hannun ya d'ora saman boobs d'inta,

saurin d'auke hannunshi yayi had'i da sakinta ya juya baya yana fad'in " ya Allah, dariyar datake kannewa ce ta kwace mata,

cikin dariyar tace " matsoraci kawai, hannunshi saman k'ugunshi yayinda ya cusa d'aya hannun cikin sumar kanshi ya zuba mata manyan idanuwanshi shanyayyu masu kamar yana jin bacci,

sosai take dariyar amma idanuwanta rufe bata bud'e su ba, kyakkyawan murmushin shi ya saki had'i da rik'e k'ugunshi da duka hannuwanshi yace,

" bud'e idonki na d'aura towel batayi tsammanin bada gaske yake ba, dan haka ta bud'e fararen idanuwanta dake cike da hawaye saboda dariya

cikin rashin sa'a ta saukesu saman mararshi zuwa sandar girmanshi,

cikin tashin hankali ta saki k'ara had'i saurin rufe idonta ta juya baya, dariya ya sanya tare da had'e tazarar dake tsakaninsu, 

ya mannata da jikinshi muryarshi a karye yace " tsakanin ni dake a samu matsoracin, ki shirya tarbata na kusa cire miki wannan kunyar tawa,

yayi maganar yana ja mata hanci, su Hajiya dake ta faman jiran jiyo ihuu ko kuka daga part d'in su, har sun gaji da lek'e sukayi saurin mik'ewa a karo na yafi sau a k'irga,

kallan juna sukayi cikinsu babu wanda yace kala kamar an tsikaresu sukayi waje da gudu,

Cikin dariya Basmah ta fito daga band'akin tana fad'in " ka k'arasa ka fito, tana shirin fita daga d'akin su Hajiya Tanya suka shigo,

bata kula da yanayin Basmah ba saboda a zatanta Ammar ne ya mutu, ta rungume Basmah had'i da fashewa da kuka tana cewa " munyi rashi Basmah,

Allah yajik'anshi Ubangiji yayi mishi rahama, munyi babban rashin da bazamu tab'a cike girbin shi ba har abada, ta k'arasa maganar tana fashewa da matsanancin kukan munafurci,

sororo Basmah tayi, tana sauraren kalaman Hajiya Tanya data kasa fahimtarsu, " waye ya mutu?


Basmah ta fad'a tana zame jikinta daga na Hajiya Tanya, gefen zani ta saka ta rufe fuskarta tana cigaba da rusa tace " kaiconmu! wayyo mun shiga tara ba uku ba, cikin rashin fahimta Basmah tace " wai waye ya mutu ban gane me kike nufi ba?


Takowa Nayan yayi gaban Basmah yana matsar hawaye yace " ba Ammar ne ya mu........ sark'e mishi maganar tayi ganin Ammar na fitowa dafa bathroom,

cikin tashin hankali yakai hannu ya tab'a Hajiya Tanya dake juya kai tana kuka, " dena rarrashi na Nayan barni nayi kuka, wannan kukan dakaga inayi na dole ne,

" kaaaa.....lli, Nayan yace muryarshi na rawa, d'ago kan da zatayi suka sauka akan Ammar, a kid'ime ta zaro ido had'i da baya ta dafe k'irjinta da hannu biyu tace " Ammar,

murmushi yayi had'i da cewa " na'am Mum, da wani abu ne?


Baki ta bud'e zatayi magana Nayan yayi saurin tallafeta yana murmushi yace " bakomai, sai da safe Allah ya tashe mu lafiya,

ya fad'a yana turata waje dan yasan muddin ya bari tayi magana a lokacin kwab'arsu tana iyayin ruwa, bayansu Ammar da Basmah suka bi da kallo,

suka kalli juna da ido tayi mishi alamar meke faruwa, kafad'a ya d'age had'i da tab'e baki, alamar bai sani ba.


Iska Hajiya Tanya ta busar ta d'auki kwalin sigari ta kunna ta shak'a da k'arfi had'i da dukanta kanta tana cewa " kai...kai...kai, 

Nayan zayyi magana Zaman yayi saurin cewa " idan muka tsaya wankin hula zai kaimu dare, zamu cigaba da b'atawa kan mu lokaci ne kawai a banza,

batare da mun kai inda muke san mukai ba, dan haka ina ganin muyi k'onar bak'in wake kawai, " kamar ya?


Cewar Hajiya Tanya tana kallanshi " naga bayan kun fito Basmah ta fita daga d'akinshi na shiga d'akinta, yanzu ne zamu damar kashe Ammar,

mu kulli k'ofar Basmah ta baya yadda kota jiyo Ammar bata iya fitowa ba, shi kuma mu cika mishi wuk'a kar mu barshi sai munga ya dena motsi,

batare datayi magana ba ta mik'e tayi kitchen fuuuu gaba d'aya wuk'ak'en kitchen d'in ta tattataro ta fito dasu yadda kasan garken rak'uma za'a yanka,

hardu adda kowa ya d'aki wuk'a d'aya suka fita d'akin Basmah suka fara rufewa kana suka shiga bedroom d'in Ammar, d'akin babu haske sosai,

sai dumb light yana kwance ya rufe har kanshi da bargo, basuyi wata-wata ba suka fara cika mishi wuk'a tako'ina saida sukaji baya motsi kana sukayi saurin ficewa daga part,

cike da d'ago Hajiya Tanya ta fad'a saman sofa tana fad'in " Alhamdulillah yau dai mun kaishi k'asa mun huta da jaraba da masifa, 

yau kowa zayyi bacci cikin kwanciyar hankali da nutsuwa harda munshari, yau zanyi baccin da rabo na danayi bacci me dad'inshi harna manta, nan suka zauna suna mayar da yadda akayi suna bushe-bushe kayan mayansu.


Washe gari da safe har k'arfe 11:00 am na safe Hajiya Tanya na jiran azo ace mata Ammar ya mutu amma shiru wai Malam yaci shirya,

tana nan zaune tana zaman jira duk bayan minti d'aya saita kalli agogon bango ga bata ga Nayan ba balle ta tambayeshi, tana nan zaune tana zaman jiran tsammani,

ya shigo fuskarshi d'auke fara'a, saurin mik'ewa Hajiya Tanya cikin matsanancin tsoro da tashin hankali, ta shiga nuna shi tana ja baya,

bakinta na rawa ta kasa furta koda kalma d'aya rawar da k'afafuwanta suke yi ne yasata yin baya zata zube, tayi sa'a bango ya tokareta,

" Am...mar....da ma....baka....mutu ba, ta fad'a a rarrabe kamar me koyan magana, kallan kanshi yayi kana ya mayar da kallanshi gareta cike da mamaki yace " mutuwa kuma Mum?


Tana nunashi cikin razani da tsoro tace " to idan bakai ne acan jiya ba waye akan gadonka?


" Ban fahimceki ba?


Baya taja jin jiri na neman watsar da ita tace " idan kai kana nan waye acan kenan?


"Nayan.....! ya fad'a yana binta da kallo, wata irin muguwar rawa k'afafuwanta suka d'auka, tayi baya ta zube a k'asa, sai lokacin ta tuna rabanta ganin Nayan tun jiya,

Hajiya Tanya bata tab'a sanin meye tashin hankali ba sai yau, tashin hankali ne ya hanata aiwatar da komai, ko kwakkwaran motsi ta kasayi,

kamar an tsigara mata allura ta mik'e zambur had'i da sakin k'ara tayi kan Ammar tana ihuuu had'i da fad'in........


*Har a kullum bazan tab'a gajiya da baku hak'uri ba, kuyi hak'uri, nagode sosai da uzurin da kike min*