MIJIN DARE

10

by @zinariya0102

__________Tunda Umma da Nazifa su ka shiga ɗaki su ke hira, tsarabar da ta tawo musu da shi ta bata, girki ta yo musu har da naman kaji sosai Umma ta yi ta sa mata albarka, Nazifa ta ce"dan Allah Umma ki lallaɓa aunty Inteesar ta zo muje koyan sana'o'in nan ko ɗinki ne ta koya ya fi zaman haka,idan kuma ba za ta yi ɗinki ba, ga airfreshner, car wash, Vaseline, su shampoo, hair condition da sauransu Wallahi Umma ana samu sosai a sana'ar hannu" Umma ta ce "ihum kinga dai yanda muke da ita, yanzu wanke-wanken can tun safe nake fama da ita akan ta wanke amma abu ya gagara ina tabbatar miki ƙarshe dai ni zan wanke kayana" Nazifa ta ce "a'a bari in wanke Allah ya kyauta" Umma ta ce "ki bari na yi, daga zuwanki sai aiki, ku kenan kullum aiki, haka ma da Firdausi ta zo ko zama ba ta yi ba ta hau yi mana wanki ni da Babanku daman Irfan da Imran ke yi, ni kuma in yi na su Salma to makaranta kullum a tafe su ke" Nazifa ta miƙe ta ce "ba ri dai in wanke muku kwanukan, fita ta yi, ta na janyo ruwa a rijiya ta ɗauki omo ta zauna ta fara wanke kwanukan ta na son su yi hira da Inteesar amma ta kasa magana sai dai tayi da Ummi,Umma ce ta fito daga ɗakin ta zauna suka ci gaba da hira, Nazifa ta ce" aunty Inteesar fito ki ji wani labari" shiru ba amsa, ta ƙara maimaitawa Umma ta ce" ki rabu da ƴar banzar Yarinya wa za ta yi wa zuciya kar Allah ya sa ta fito ai ta saba" Nazifa ta yi shiru ta na tsoron kar Inteesar ta ƙara hawa dan ɗazun nan ta gama zaginta,sai da ta wanke kwanukan ta share gidan tas, ta wanke musu bokitai da robobi da butocin gidan sosai ta zage ta gyara musu gidan har yana ta cire musu, daman ta kawo musu abinci ga Masara da Umma ta dafa, Nazifa ta ɗebi masarar dan tanaso ita da ƴaƴanta, duk abin nan da su ke za ton su Inteesar na ɗaki ta na jinsu, sai da azahar ta yi sannan Nazifa ta da hankalinta ya ƙi kwanciya ta koma ɗakin aunty'n nasu dan lallaɓata ta yi haƙuri, ta na buɗe labulan ta ga babu kowa a ɗakin, gabanta ne ya faɗi ta ce" ina kuma ta tafi, Umma ba ta nan ko kin aiketa?" ba tare da damuwa ba Umma ta ce" yo daman ni na isa ta sanar da ni inda za ta je, ai ta saba" cikin tashin hankali Nazifa ta ce" ni wallahi hankalina bai kwanta ba, bari na duba ko gidan Hajiya ta shiga" 

Umma ta ce"kar ki wahalar da kanki ki je ki yi sallar ki, ta dawo dan kanta" har su ka yi sallah su Na'ima da Salma da Imran su ka dawo daga makaranta babu Inteesar nan hankalin Umma ma ya fara tashi,Salma da Na'ima ganin Yaya Nazifa a gidan sai murna su ke suna ganin abinci da nama sun san ita ta kawo musu tare suka ci, da su Muhammad sai da su ka yi sallah sannan suka sa kayan islamiyya su ka tafi, Nazifa ta ɗauki gyale ta ce" Umma ba ri in dubo Aunty daɗewar ta isa haka" Umma ta ce "to nima hankalina bai kwanta ba wallahi" Ummi ta yi bacci su Muhammad na wasa Nazifa ta fita nema.



Inteesar kuwa tunda ta baro gida ta miƙi hanya ta na ta jin haushin su Umma, wajen wata bishiyar tsamiya ta je ta zauna ta haɗa kai da guiwa ga ta ba tada tsarki tana al'ada MIJIN DARE da shi ne ya tun zura zuciyarta sai dariya ya ke ya sata a ƙunci da damuwa, bacci ne ya fara ɗaukar ta a wajen babu wanda hankalinsa ya kai kanta, ta ke ta fara mafarki da wasu halittu su na ce wa, idan su ba sa sonki ai mu muna sonki, idan su ba za su iya zama da ke ba daman mu muna tare da ke, za mu iya ɗauke ki mu mai da ki duniyarmu, Ummanku ba sonki ta ke ba, tafison su Nazifa zamu tafi da ke inda za'a baki kulawa za ki zama sarauniya a duniyar aljanu, sai dai muna tsoron ƙaninki Irfan Yaron ba zai bar mu ba" a baccin Inteesar ta ce" kar ku kaini dan Allah ku yi haƙuri ku barni cikin ƴan'uwana, zan zauna da su a hakan kar ku cutar da ni" cikin kuka ta ke faɗa wa halittun haka,haɗi da tsananin tsoronsu. 



Aljani MIJIN DARE wanda shi ne shugaban tawagar aljanun ya daka mata tsawa ya ce" kin manta akwai ƴaƴanki a duniyarmu muna da yara har huɗu da ke kuma ba zan rabu da ke ba, ƴaƴanki duk aljanu ne dan haka dole ki bi mu" 





Nazifa sai maƙota ta ke bi neman Inteesar har ta haƙura ta dawo, Umma ta ce ƙila gidan wata ƙawar ta tafi, kinsan daman ta ce ba za ta ci masara ba, ni nafi tunanin hakan" Nazifa ta ce"kai amma aunty ba ta kyautawa gaskiya ta ɗau alhakina, haka ta ƙara ci wuninta ta biya wajen Baba ta gaishe shi, nan ya dinga karanto mata uzurinsa, na babu,babu har bashin da ya ci jiya na Haidar wai ya ari dubu ɗaya ankai Inteesar asibiti, ya ce" kinga yanzu ba dan yayarku ba ai ba na dinga cin bashi ba, ga ta har yau babu Saurayin da ya taɓa zuwa da sunan zance wajenta" Nazifa ta ce" Baba aure lokaci ne ina ji a jikina Aunty za ta yi aure muddun lokacin ta ya yi,addu'a za ku dinga yi mata na Allah ya bata Miji nagari, wanda zai kula da ita Allah ya na sane da ita" Baba ya ce " addu'a ta nawa kuma tun kuna ƙanana nake muku har ita, ku ba ga shi kunyi auren ba, amma ita inda kikasan na shuka dusa har yau shiru, mtsww abun nan na ƙona min rai, Allah duk wanda ya zo ko waye ba shi ita zanyi na huta" 

Nazifa ta ce "da sanin Allah Baba komai mai wuce wa ne, fatan mu dai Allah ya nuna mana auren aunty da rai da lafiya" kuɗi ta ɗauko dubu uku ta ba shi, ya karɓa ya na washe baki sai ya hau shi mata albarka, ta yi masa sallama ta ja ƴaƴanta su ka tafi.


Wani shamshaƙin Alhaji ne ya yi parking a daidai runfar Baba, jiki na rawa Baba Ayuba ya je wajen ya tsaya sai da mutumin ya ɓata mintina uku sannan ya sauke glass ɗin motar,Alhaji Yakubu ne Yayan Baba Ayuba da fara'a Baba ya ce" Alhaji kaine ke tafe sannu da zuwa" Alhaji Yakubu ya ce" yauwa ya kasuwa?" Baba ya ce"Alhamdulillah    " sannan Alhaji Yakubu ya ce"daman akan maganar da ka zo min da ita ne rannan game da aikin company ni dai a nawa ganin ka je kaga ni,idan kaga ya fi wannan kayan gwarin da kake siyarwa samu shikenan, idan kaga bai fi ba kawai sai ka daina yi ka dawo sana'arka" sosai Baba ya ji daɗin wannan shawarar ta yayansa godiya ya yi masa ya ce "bari in zubo kayan miya akaiwa mutan gidan"dakatar da shi Alhajin ya yi "a'a basshi kawai, naga ai duk kuraye ne ba ci za suyi ba, kar ayi maka asara mun gode, ya ja motarsa ya juya ya nufi gidansa, ya na fatan Allah ya sa ba'a ganshi tare da Ayuba ba, kamar shi ace wai Ayuba ƙaninsa ne talaka faƙiri,wannan abun kunya ne.



Wasa-wasa har Irfan ya dawo ba'a ga Inteesar ba, ko zama baiyi ba ya fita nema shi da Imran, duk hankalinsu a tashe, su na fatan ba mugun hannu ta faɗa ba, dan sun santa da shisshigi ga son gwaninta, rasa inda za su nufa su ka yi, haka su ka dinga yawo a unguwar


Inteesar kuwa har magriba ta na ƙarƙashin bishiyar tsamiya ta na bacci mai cike da abin tsoro, kuka ta ke ta na magiyar kar a rabata da iyayenta,aljanun sun dage da cewar dan ginta ba ƙaunarta su ka ba,sunfi iyayenta buƙatarta a halin yanzu, ji ta yi an.............





   *     *    *


"Girkin ma a ce wai Yara ne za su yi, wannan ai ba dai-dai ba ne, kuma tsabar rashin adalci irin na Malam yana kallo ya ƙi cewa komai" Baba ke wannan maganar ganin Ruƙayya a kitchen ta na ɗora abincin rana, Inna na ɗaki babu wacce ta tanka mata, Ɗanmalam ne ya fito daga ɗakinsa duk kamaninsa sun sauya ya ƙara rinewa ya yi baƙiƙirin idanunsa sun zama ja,Khaleed da ke zaune ya na haɗawa Abdallah gidan kwali, wanda aka ba su Assingment a makaranta, Ɗanmalam ya ce" Ya Khaleed ashe ka na gida" Khaleed ya ce "eh yau sai 2:00 zan shiga lacture kai ya na ganka a gida?" sosa kai Ɗanmalam ya yi ya ce" kagane ne Ya Khaleed wata Malama ce ta kawo min raini shi ne na gaggaya mata magana na ware, ban ƙara komawa school ɗin ba" Khaleed ya ce"what, are mad?" Ɗanmalam ya yi shiru, Baba Maimuna ta ce" ka yi dai-dai ɗanmalam duk wanda ya yi maka kan kara to kayi masa na icce faɗa na ce ni nan Uwarka" Khaleed ya yi shiru sai bai ƙara magana ba. 


Inna ta fito ta ce "ba ki isa ba wallahi ba za ki kashewa Yaro rayuwa ba,ilimi shi ne ginshiƙin rayuwar kowanne ɗan adam baki isa ki hana Yaro ya koma makaranta ba, kai Khaleed ka shirya ku je Makarantar ka mai da Umar, in banda abinki ba fita zai yi wannan shekarar ba, haka zai ci gaba yana yiwa Malamai rashin ɗa'a" Baba ta hau "eh ɗin naga dai ɗa nawa ne, ba uwar wani ce ta haifa min ba, duk da halin da aka je fa min shi, bai isa ba sai an haɗa da takura masa, gaskiya ba zai yuyu ba shi kaɗai a sashi a gaba" Ɗan malam ya ce"ni zan koma Inna dan Allah Ya Khaleed ka kai ni in ba da haƙuri, ni da nakeson na zama Police dole in koma karatu, murmushi Inna ta yi ta na ce wa "yauwa ɗan albarka Allah ya shirya mana ku ya yi wa rayuwa albarka" Baba Maimuna ta yi shiru Ɗanmalam ya amsa zai koma, wanka ya yi ya fito Khaleed ya ƙarasa haɗawa Abdallah gidan kwalinsa ya ba shi, su ka tafi makarantarsu ɗan Malam, sai da ya je ya ji, ashe wai ba karatu ya ke yi ba, shi da abokansa bayan classes su ke zuwa su yi ta shaye² sosai Khaleed ya dinga ba su haƙuri da ƙyar aka samu a ka karɓi ɗanmalam.


Asad kuwa ya na can school anyi posting ɗinsu service an kai su Lagos tare da wasu, wasu kuma other States aka watsa su, gida ya dawo, dake alhamis ce ba zaman karatu ba kowa sai tsirarun almajiran Malam wasu na wanki wasu na rubutunsu, sannu da zuwa Magajin Malam su ka ce masa "yauwa sannun ku da aiki" ya wuce cikin gida, sunan da Baba Maimuna ba ta ƙaunar ta ji an ambaci Asad da Magajin Malam, sai tayi ta maganar ai ba shi kaɗai ne ɗan Malam ɗin ba magadan da yawa.


A tsakar gida ya ga Malam da sauran ƴan gidan, zama ya yi akan tabarmar Malam ɗin ya gaishe su, sannu su ke ce masa,nan ya basu labari sosai su ka yi masa addu'ar samun nasara Baba Maimuna in banda taɓe baki babu abinda ta ke wai zai tafi bautar ƙasa har Lagos, su Ruƙayya sai murna su ke Yayansu ya kusa gama degree ɗinsa.

Kowa sai murna ake taya shi.


Duk abun Baba Maimuna ta na shakkar Asad ba ta fiya yi masa abu a gidan ba dan ko ta na yi idan ya na wajen ba ya bari a tanka mata, bare Inna ta biye mata,amma har yau ba ta fasa halinta ba.

Zulaihat da Ruƙayya kuwa tunda tare su ka taso sune gaba da ɗanmalam su na son junansu dan wani lokacin  ma har gidan Zulaihat Ruƙayya ke zuwa ta yi mata lalle su sha hira, Yunus ma can ya ke zuwa su yi zancensu da Ruƙayya.



shirye-shiryen tafiya Asad ya ke yi, ya haɗa komai na tafiya, duk da suna murna amma har sun fara kewarsa ya ce musu zai dinga zuwa ai,ba wai har shekara ba za su ganshi ba,Malam ya faɗa wa abokansa ɗansa zai tafi bautar ƙasa,nan ma aka dinga taya Malam murna kamar wani shahararriyar tafiya zai yi, aikuwa an tara wa Asad kuɗi da kayan abinci, a tasha za su haɗu da abokan tafiyarsu, addu'a aka tara almajiran Malam aka yi wa su Asad sannan ya wuce tasha shi da Khaleed da ɗanmalam sai da su ka tafi sannan su ka juyo gida cike da kewar Yaya Zaki.......