OMAR KO FAROOQ?

98-99

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓




98_99





"Bcci sukayi sosai haddai imaan da ta manta rabon data koma bccin asuba sbd aikin da takeyi kullum babu damar bcci, "sai wajajen qarfe 9, omar shiya fara tashi koda ya yaye bargon abinda ya gani shiya matukar daukar hankalin sa, rigar bccin imaan CE ta dan zame daga qirjin ta na fulanin ta suka bayyana, sosai ya kafeta da ido yana sarrafa wasu abubuwa cikin ransa, ganin tayi juyi yyi saurin tashi daga gadon sannan ya fada toilet yyi wanka, kusan 20mins ya dauka kafin ya fito daga wanka har lkcn imaan na kwance sai sheka bcci take. "Ahaka yyi shirinsa sannan ya koma falo yana kallo. "Imaan ba ita ta tashi ba sai qarfe 10. Lkcn data farka ta ganta ita kadai a dakin dan haka ta tashi, bargon ta nade, sannan ta ajeshi gefe, bedsheet ta yaye na kan gadon sannan ta kakkade ko INA, kafin ta sake sabon shimfida, sannan ta maida bargon kan gadon. "Saida ta gama gyara dakin tass sannan ta zura hijab dinta ta fito. "Kamar yanda ta saba a gida haka tazo har gaban omar ta sunkuya kafin ta gaishe shi. "Omar yana kallon ta sannan ya amsa mata kamar yanda ya saba. "Tashi tayi ta fice a falon sannan ta nufi side din mummy, "omar yana kallon ta bece mata uffan ba shi tunanin dake ransa ma ya ishesa. "A daki imaan ta tarad da mummy, har kasa ta sunkuya tana gaishe ta cike da kunya, "mummy tayi murmushi bayan ta amsa gaisuwar tace mudai munyi breakfast dinmu tun 9, saiki dauki naki kikai muku can. "Imaan tace mummy bari nayi wanka tukun, sakale baki bude take kallon imaan har zatayi magana kuma sai tayi shiru. "Haka imaan ta fada toilet din tayi wanka sannan ta fito. "Simple make-up tayi dan ta saba da rashin kwalliya a gidan omar, itadai mummy na zaune na ganin ikon God. "Saida ta gama ta dauko wata Riga da skirt sunyi mata dass a jikin ta, sannan ta dauko dan kwali ta yane kanta. "Saida ta gama sannan ta nufi wajen dining table inda aka aje musu breakfast, "zama tayi da niyyar ci daidai lkcn mummy ta fito, tace ha'a kikai muku can mana, imaan tace mummy zanci anan ma. "Mummy tace aa banson shirme fah da dakuke ci tare waya sa muku ido? Imaan ta sadda kanta qasa a zuciyar ta tace mummy bazaki gane waye ya omar ba,irin mutanen nan ne da ake kira green snake inside d grass... Mummy ta katse mata tunani da fadin tashi mana imaan haba saikace ba mace ba? Tayi mgnr cikin muryar lallashi, ba yanda imaan ta iya haka ta jera komai kan tray, sannan ta dauke shi tayi hanyar side din omar.


"A yanda ta barshi a haka ta tarad shi, a yanda ta lura kallo yake Amman ga dukkan alamu yana cikin tunani, "gyaran murya tayi sai alkcn omar ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, fuskar sa a daure yake kallon ta batare d yace mata komai ba. "Imaan kam ajiye tray din tayi, cikin sanyin murya tace ya omar ga breakfast inji mummy, omar yana jinta bece komai ba, "imaan kam wata irin yunwa takeji dan haka ta dauki cup d spoon ta hada tea me kauri, plate ta jawo sannan ta zuba yam balls, sannan taja gefe, ta dauko tea din kenan zata kai bakinta taji ance dakata... "Da sauri ta dago ido tana kallon ya omar fuskar sa na kan kallo badan tasan muryar sa ba da saika rantse da Allah bashi yyi mgnr ba yanda ya nutsu yana kallon sa hankali kwance. saidai babu ko tantama shine yyi mgnr, tsaywa tayi da shan tea din tana jiran me zai CE mata dan ta qagu taci abinci... Bata ida tunanin ba taji yace kawo min tea din dake hannun ki, da plate din dake gaban ki. "Imaan tayi zuru tana kallon ikon Allah idan bazata manta ba ya omar ko sau daya be ta6a cin abincin ta ba, dukda tasan abincin waje be cika birgeshi ba Amman ya gwammace yaci snacks da drinks idan ta kama dole ya shiga kitchen ya daura indomie da kansa, acewar sa bazaici jagwalgwalen ta ba shi Allah ma ya sauwake yaci abin daya fito a hannun ta....jiki babu kwari ta kai masa tea da yam balls din. Nanta koma gefe ta dauki wani cup din da niyyar hada wani, cikin tsawa yace bakida hankali ne? Imaan da mamaki tace menayi ya omar? Omar yace oh tmbyta ma kike koh? Toh ki jirani saina gama cin abinci sannan kici understand? Imaan ta girgiza kai alamar eh, sannan ta raku6e a gefe tana kallon yanda ya omar yakecin abinci idan ya dauko yam ball daya sai yyi kusan 3mins kafin ya cinye, gefe guda kuma cikinta ne yahau kukan yunwa yana buqatar taimakon abinci.






Nuceey luv😘