OMAR KO FAROOQ?

102-103

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓





102_103





"Cikin 5mins imaan ta shirya sannan ta sauko qasa, anty ameera tace taho mu tafi, imaan tace a wacce motar zamu tafi? Anty ameera tace a tawa mana. Imaan tace Amman turo maki akayi, tace eh, suna wannan mgnr suka isa wajen motar, a sannu a hankali suke tafiya har sukaje wani waje, daidai wani qaton boutique sukayi parking, bayan ta daidaita parking din suka fito, nan suka shiga ciki imaan ta baza ido tana kallon qananan kaya kala2, "bayan sun shiga Anty ameera tace toh _MRS_ _OMAR_ bismillah. Imaan tayi murmushi tace lallema anty ameera, ameera tayi driya tace toh ba Matar sa bace? Imaan zatayi mgn anty ameera tace kinga yi sauri ba iya nan zamu tsaya ba. Imaan ta kalli kayan taga dukkansu shegu ne, ta dawo d kallon ta ga ameera tace gsky wannan kayan sunyi tsaraici da yawa inani INA sasu? Anty ameera taja tsaki batare da tacewa imaan komai ba ta fara kwasar kayan da tasan xasu dace da jikin imaan, mahaukatan kaya anty ameera ta zabawa imaan, itadai imaan sai Binta da kallo take. "Saida anty ameera ta gama kwasa sannan taje akayi total ta biya kudi, daga nan sukabar wajen. "Wajen inda ake saida turaruka masu rikita me house nan anty ameera t tafi da imaan, anan ma saida ta siya mata kala2 sannan suka wuce wajen saloon, daga nan suka dawo gida d kaya niqi2, har daki anty ameera takai wa imaan, bayan ta ajiye sukayi alwala sannan sukayi sallar magrib, bayan sun idar, anty ameera ta kalli imaan tace toh imaan ga kayan yaki nan, inaso a matsayin ki na mace wacce ta amsa sunan ta, ki tattare duk wata kunya dake jikin ki lungu d saqo ki sata a side. "Sannan ki tallafi rayuwar aurenki, ki zamo mace me 'yanci, wannan kayan da kike gani sune abin sawar ki, duk yanda kikaga Riga dukmai qanqantar ta kisa ta, basai na maki bayanin yanayin kayan ba nasan kingan su, inaso imaan da nasani a da me kwalliya da kamshi t kasance a yanzu sannan ki cire wannan tsoron da kikewa omar, bawai nace ki rainasa ba a'a kindai gane abunda nake nufi koh? Imaan ta gyada kai, anty ameera tace Abu na qarshe dazan fada maki kuma kawo kunnen kiji dan wannan Nuceeyn kartaji sirrin ma'aurata ta wani baza mana kunne da ido tana daukar rahoto...lol., kuskus sukayi duk yanda nakai ga kwakwata banji komai ba. "Ita kanta imaan sunkuyar da kanta tayi dan kunyar abinda ta fada mata. "Anty ameera tace ai kin ganki ba, nidai karki bani kunya dan Allah. "Imaan tayi murmushi tace toh insha Allah zan kokarta. "Anty ameera tace gud gal haka nakeson ji. "Dabaru kala2 na zamantakewar aure anty ameera ta fadawa imaan da yanda zata jawo hankalin omar. "Saida ta gama sanna tace tashi kiyi wanka ni bari na shiga kitchen tun kafin su dawo, imaan tace toh. "Shaf2 imaan tayi wanka bayan tayi sallar isha ta tsaya gaban mirror, sadai ta kasa ta6uka komai, anty ameera ce ta shigo da sauri tace maza yi sauri gasunan dawowa... Turus tayi ganin imaan zaune ko shiryawa batayi ba, anty ameera tace ha'a me kike jira imaan? Imaan ta rausaya kai tace anty ameera anya zan iya? Anty ameera taja tsaki sannan tazo gaban madubin, cikin sauri2 ta yiwa imaan simple make-up, daga nan ta zabo mata doguwar Riga me saukin nauyi, tace ungo wannan saka, idan munbar gidan saiki saka nighty kinji? Imaan tace toh daga nan ta feshe jikinta da turaruka masu dadin kamshi., ahaka sukaji horn. "Anty ameera tasake Jan kunne imaan tace yanzu kuma aiki ya rage naki dan gasunan shigowa, imaan tayi 'Yar qara ahh kunnena anty ameera tayi dariya tace ai gwara naja dakyau dan na lura kina Neman jawo mana cikas, imaan tayi murmushi tace don't worry anty I will try insha Allah, anty ameera tace toh gud taho mu tafi, "tun daga stairs qirjin imaan ya bada darararammmm... Anya zata iya? Sunzo step na karshe anty ameera ta matsa jikin kunne imaan tace karki bani kunya fahhh tayi mgr qasa2 imaan ta daga kai as answer.


"Suna qarasawa falo, anty ameera tayi wajen farooq ta zauna, imaan gabanta na faduwa taje wajen Omar kamar bazata qarasa wajensa ba, suna hada ido da anty ameera ta wurga mata hara, aikuwa ba shiri ta matsa kusa dashi tana fadin oyoyo sweet durlin tayi mgnr daidai lkcin data zauna kan cinyar omar ta sakale hannayen ta ta bayansa sannan ta dago fuskar ta tana kallon sa da wani irin shu'umin murmushi.





Nuceey luv😘