CIWON SO

13

by @khadeejacandy


“Wannan abun ya zama hauka, tun kana yin abu da hankali har ya kai yanzu ka fara fita hayyacinka, wane irin so ne wannan? Ji yadda kake kokarin maida kanka mahaukaci saboda kawai wata can da bata san kana yi ba”


Ammy ta rufe da fada domin a ganinta abun ya wuce gona da iri, amaimakon yayi magana sai ya soke kansa kasa ya rumtse ido. Fadan da Ammy ta yi ya saka Yasmin saukowa jikinta a sanyaye domin ta tsorata sosai da yanayin Abiey. Ammy ta nuna shi da yatsa. 


“And this should be the last time da zaka kara ambatar sunan Zahra ko wani abun da ya shafe ta a gidan nan? Enough is enough na gaji, ban san abun da yake damunka ba”


Sai ya dago ya kalleta cikin wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. 


“Ciwon so ne Ammy, kaddarata ce wannan”


Ya mike tsaye wanda hakan yayi daidai da faka motar Sauban a harabar gidan, sai kawai ya nufi hanyar fita daga falon Ammy ta bishi da kallo har ya bude kofar ya fita, sannan ta maida dubanta gurin Yasmin. 


“Kina nan yayi wannan haukar? I think sai mun tashi tsaye Abiey ya fara tabuwa, wai yanzu yake fada min yau ya ga hawaye a idon Zahra bla bla.. ”


“Da gaske Ammy Zahra ta zo nan”


Ammy ta kalleta da sauri. 


“Da gaske? Kim ganta da idonki? Me ta zo yi? Ita da wa ta zo?”


Yasmin ya shimfadawa Ammy abun da ya faru, ba karamin mamaki da tausayin Zahra ne ya kamata ba.


“Subhanallahi”


Ta furta sannan ta mike tsaye da sauri ta nufi kofar falon ta bude ta fita, sai ta samu Abiey tsaye a balcony din tare da Sauban. 


“Aliyu da gaske Zahra ta zo nan ashe”


“Ni ma yanzu yake fada min abun da ya faru, and i could believe what he did to her”


Sauban ya amsa mata shi kanshi mamakin abun da Abiey yayi yake. Abiey ya kalleshi yana murmushin takaici. 


“What do you expect? Kana ganin zan iya taimakon mutumen daya raba ni da rayuwata? Mutunen da ya kashe ni da raina?”


“Ba akansa zaka yi saboda Zahra zaka yi?”


“Yeah idan har zan yi saboda ita to ita kadai zan yi ma, ko zan iya taimako kowa a duniyar nan ban da wannan mashayin Sauban i can't”


Ammy ta sake kallonsa da mamaki. 


“Wannan ba halinka ba ne”


“Duniya ce take koyawa mutum wani abu da ba halinsa ba, Ammy don't you think amana ce take bibiyarsa? Yaushe zuciyarki ta manta abun da ya faru? Duk wani hali da nake ciki da damuwa saboda shi ne, abun bakinciki har yanzu Zahra kallona take a matsayin macuci saboda ya bata komai”


Ammy ta yi kasa da kanta tana tuna lokacin da abubuwa suka rinchabe, lamarin da be yi ma kowa dadi ba. Sauban ya dafa shi. 


“Yeah kana da gaskiya Abiey, amman ina son ka sani Zahra ba ita ce autar mata ba”


“A gurin Zahra ce autar mata, and i called a nan ne saboda na san Zahra zata iya zuwa neman taimako a gurinka, ko makiyina bana son ya taimakawa Deen, balle wani na kusa da ni har ke Ammy”


Ya juyo yana kallon Ammy. 


“Daman can ko zan yi saboda Zahra zan yi, but since ka ce kar ayi i won't hurt you”


Ammy ta fada sannan ta sauke ajiyar zuciya ta juya ta koma cikin falon. Sauban ma ajiyar zuciya ya sauke ya saka hannayensa aljihu. 


“Allah yasa kar ka zo kana nadama”


Zaunawa Abiey yayi a daya daga cikin kujerun da suke gurin. 


“Na rasa abun da zan yi, so yana da zafi Sauban, Ciwon so yafi ko wane irin ciwo cutarwa da azabatar da mai shi, you got lucky you marry your first love babu wani tashin hankali”


Ya furta yana kawarda fuskarsa hawaye na cika idonsa, sai ya saka babban yatsansa ya goge, babu abun da idonsa suke masa gizo sai hawayen da ya gani a fuskar Zahra, da kuma cikin dake jikinta. 


“Ina fatar abun nan ba zai cutar da abun da yake cikinta ba”


“Is she pregnant?”


Ya dago yana kallon Sauban 


“Yeah tana da ciki”


Sai kuma ya cige baki ya kawarda fuskarsa cike da damuwa. 


“You can go”


Abiey na rufe baki Yasmin ta bude kofar falon ta fito da shirinta kamar dazun hand bag dinta na makale a jikinta, Sauban ya kalleta sai ta gaishe shi ya amsa, sannan ta karasa sauka entrance din ta nufi gurin da dayan direban Ammy yake zama wato BQ, Abiey ya mike tsaye da zimmar shiga ciki falon sai kuma ya juyo ya kalli Sauban yana hade yawu da karfi. 


“Ka bincika ko nawa ne a biya mata, amman ka yi ta hanyar da ba zata gane mu muka biya ba”


“Amman miyasa ba zaka yi abun a bude ba, ko ba komai hakan zai kara kusanci a tsakaninku kuma zata ga cewar ta nemo taimako ka taimaka mata zata jidadi wata kila ma ya shirya tsakaninku”


“Indai taimakon Deen ne zai shirya tsakani da Zahra ko ya saka ta daina ganina da laifi, bana so har a bada!”


Yana gama fadar hakan ya juya ya taka ya karasa gurin kofar ya murda ta bude ya shiga, Sauban dai binshi yayi da kallo har ya shige sannan ya nufi motarsa. 

Yana shigowa falon kai tsaye dakinsa ya nufa, a hankali ya murda kofar ya bude ya shiga ya kwanta saman gadonsa ruf da ciki ya rumtse ido, ya bar kofar dakin a bude. Ammy dake dakinta ta fito da saurinta ta shigo dakin danta, tsaye ta yi jikin kofa tana kallonsa kamin ta karaso ta zauna saman gadon sai dai hakan be saka ya dago ba.


“Aliyu...”


Ammy ta kira shi.


“Komai na rayuwar duniya dan hakuri ne, rabuwa da abun da kake so tabbas be shi da dadi”


Sai kuma ta yi shiru, hakan ya saka shi dagowa ya bude idonsa da suka kade ya kalleta. 


“A lokacin da mahaifinsu Zainab ya rasu, na shiga damuwa da dimauta sosai a lokacin mutane suna ganin kamar ba zan damu ba, saboda ya tafi ya bar ni da rana biyu maza da mace daya kuma ya bar mana duniyar da har jikokina za su gaje ta, dan haka mutuwarsa ba komai ba ce wasu na gani kamar murna ya kamata na yi, but deep down inside my heart ina jin kewar mijina, domin miji wani jagora ne na rayuwar mace, musamman wanda yake kyautatawa iyalinsa, kuma yake da kyakkyawar mu'alama da su, na shiga damuwa sosai ba dan na rasa komai ba domin babu abun da ya canja na daga ci ko sha na mu, kamin Allah ya kawo mahaifinka ya aureni, hakuri ya kamata ka yi ka cire Zahra a ranka ba ina nufin ka cireta kwata kwata ba, no ka bawa wasu matan damar gwada sa'arsu, lokuta da dama abun da muke gani alheri a garemu sai ya zama ba alheri ba, wanda kuma muke ganin ba alheri ba ne sai ya zama alheri, abubuwa da dama da muke so ko muke ki zasu iya zama alheri ko akasin a gari ka”


Tashi yayi zaune. 


“Ammy da ace Zahra mutuwa ta yi, zan fi samun kwanciyar hankali sama da ace tana raye, and the most painful part is Zahra ta tsane ni, Deen ya riga ya bata komai”


“Ka dauka haka Allah ya kaddara tun farko, kuma kar hakan yayi tasiri a zuciyarka, shi wanda aka zalunta kullum a sama yake ko da kuwa mutane suna ganinsa a kasa ne, ina son ka cire komai a ranka ka taimaka masa saboda Allah, na san da ace Zahra tana da inda zata kai hawayenta a share mata su da bata zo nan ba, ta zo nan ne saboda tana jin tana da gata a nan”


Ya saka yatsunsa na dama cikin na hagu. 


“Na riga na fadawa Sauban ayi mata duk abun da ya kamata, you know ba zan iya barin hawayenta su yi ta zuba ba”


Ammy ta yi murmushi. 


“Allah ya maka albarka ya baka mata ta gari kuma ya yaye maka wannan damuwar Allah ya maka albarka”


“Ameen”


Ya amsa yana tuna lokacin da Zahra ta shigo rayuwarsa yana jin kamar dukanin damuwarsa ta yaye ashe mafarin budewar wata damuwar ne. 




ZAHRA POV.


Kaje neman abu ace maka babu yana da ciwo sosai, sai dai abun da Abiey yayi min a yau ya fi ko komai ciwo, na san yana da halin taimaka amman yaki ya taimaka min, bayan rashin taimakon ma sai ya biyo har da wulakanci a ciki. Ko da yake ba laifinsa ba ne laifi na mi zai saka na je neman taimako a gurin? Bayan duk abun da yayi min? Wani sabon kuka na ji ya zo min, ga zafin wulakanta ni da yayi ga kuma rashin samun taimako da ban yi ba. Na yi tafiya mai nisa kamin na iso inda babban titi yake gurin da motoci suke hada hada, domin titi area su Abiey irin titi nan ne na manya masu kudi da ba kasafai kake ganin Napep ba ma. Ga ciki ga bacin rai ga damuwa ga kuka haka na iso titi na tsaya ina tunanin yadda zan koma na fadawa Hajiya cewar ban samu abun da nake so, ga kuma wulakancin da ya biyo baya. Ina tsaye a gurin wani tsoho rike da sandarsa ya zo ya tsaya kusa da ni, sai dai shi da alama tsallaka babban titi zan yi ba kamar ni da zan hau abun hawa ba, da dukan alamu tsoro yake ji domin sai yayi kamar zai tsallaka sai kuma ya dawo. Ganin hakan ya saka na share hawayena na kara matsa kusa da shi. 


“Baba tsallakawa zaka yi?”


“Eh so nake na tsallaka na tafi gida”


Ya amsa min cikin maganarsa ta tsofi marasa hakora, hannu na mika na kama hannunsa. 


“Bari na tsallaka da kai Baba”


“Tohm”


Sai na duba titi na ga babu motoci sosai sannan na tsallaka da shi ni da shi muka tsaya a tsakiyar titin kasancewar express ne, sai motoci suka rage sannan na tsallaka dayan titi da shi.


“Baba ina zaka bi”


Na tambaya. 


“Nan ma ya isa, zan iya gane hanyar gida ai”


“Tohm”


Na juya da zimmar tsallaka na koma hannun da na fito, sai ya kira ni. 


“Yata”


Na juyo da sauri. 


“Na'am”


“Kina da wani abu nan ki bani? Tun yamma nake gidan wani mai hali kuma ban samu komai ba, iyali kuma suna can gida na baro ban basu komai ba”


Ba tare da tunanin komai ba na saka hannuna a jaka na ciro dubu biyu a cikin kudin da na samu na mika masa. 


“Gashi”


A take ya saki sandar hannunsa ya duka kamar zai kama kafata ya karba. 


“Allah ya miki albarka, Allah ya saka miki da alheri, Allah ya biya miki bukatunki na alheri, Allah ya yaye miki damuwarki cikin dake jikinki Allah ya raba ki da shi lafiya ya baki da mai tausayinki”


“Amin”


Na amsa hawaye na cika idona domin addu'ar ce abar da nake da bukata a yanzu. Sannan na sake juyawa a karo na biyu da niyar tsallaka titi, sai kuma wata zuciyar tace ba sai na tsallaka ba, sai kawai na juya na cigaba da tafiya zuciyata na min wani irin zafi marar misaltuwa. Da gangan na ki na hau abun hawa na yi ta tafiya a hanya hawaye na sauko min har na isa roundabout na titi sannan na tari abun hawa na hau na fada masa inda zai kai ni. Wallahi har muka isa asibiti kuka kawai nake domin na san bayan gurin Abiey babu wani gurin da zan iya samun taimako kudi mai hawa haka, yanzu kam na sadakar zan rasa mijina. Bayan na fita na bashi kudinshi na shiga cikin asibitin cikin rashin dadin rai, ina shiga dakin na samu Hajiya zaune ta saka danta a gaba taba ta kallonsa kamar mai masa kallon karshe, yanayin yadda fuskata da yanayina yake kadai ya isa ya karantar da ita cewar ban yi nasara samun abun da nake so, bata ce min uffan ba ni ma ban ce mata ba, domin bayyana yadda Abiey ya wulakanta ni zai kara saka min damuwa ne kawai. Na karasa na zauna saman gado kusa da shi. 


“Likitoci sun ce ni daina kusantarsa”


Kallonta kawai na yi na dauke kai ba tare da na matsa din ba, kuma ban ce mata komai ba. A dakin muka kwana ni da Hajiya ni na hau dayan gadon ma karar lafiya na kwanta ita kuma ta kwanta a saman tabarma, misalin bakwai na safe mijin Yaya Maryam ya kawo mana abun karyawa, daman yar'uwata ba daga baya na inda gurin nuna kula sa kauna ne, sai dai a yanzu kamar yafi na da, mijinta ma na lura yama tausayina sosai, kamin ya fice sai da na yi masa maganar zuwa gurin dan siyasar da yace yana taimaka sai ya fada min cewar mutumen da zai mana hanya yace dam siyarsa baya garin. Hajiya ta hada tea ta sha sannan ta hada min ta miko min, na karba na sha rabi na aje kofin sai ya dauko plate ta zuba taliyar da Yaya Maryam ta aiko mana da ita, kai na girgiza mata domin har ga Allah ba zan iya ci ba. Sai ta maida taliyar gabanta ta dan ci kadan ta tashi ta dauki Hijab dinta ta saka. 


“Bari na tafi gida na yi wanka jiya ma haka na wuni ban yi wanka ba, ai kina nan ko?”


Na daga mata kai, sai ta dauki purse dinta ta fice tana gargadi na kiyaye ban da matsawa kusa da shi, ni kam har yanzu mamaki abun da zai hana ni matsawa kusa da mijina nake. Ina nan zaune a dakin har takwas da rabi na safe ina ta tunani kala kala har ta kai yanzu bana hawaye sai dai na ji zuciyata ta bace babu dadi. Sai ga likita ya shigo tare da nurse biyu kamar yadda ya saba wani lokacin kuma nurse daya yake shigowa da ita. Mikewa na yi tsaye ina gaishe shi sai ya amsa yana kallon fuskata. 


“Ya mai jiki?”


“Gashi nan”


Na amsa masa murya kasa kasa irin ta wanda ya rasa makama.


“Na fada muku ku yi kokari ku hada kudin maganin nan saboda Wallahi akwai matsala”


A take na ji hankalina ya kara tashi, sai ya karasa kusa da Deen da tun jiya be farka ba, ni na rasa gane wane irin bachi ne yake ma. 


“Kudin ne muka kan hadawa, ban san ko kuna karbar rabi ba, ko kuma kuna yin aikin bashi in yaso daga baya sai mu biya, dan Allah a tainaka mana”


“Aa ina... Ai ba a haka”


“Dan Allah a taimaka mana likita, mijina shi ne rayuwata idan na rasa shi zan shiga wani hali”


Ya kalleni kamar mai nazari sai kuma ya cigaba da duba Deen da yake ya sake yin rubutu a jikin takardar magani ya miko min. 


“Ku nemo wadannan alluran ya farka yau da safen nan?”


“Tun jiya be farka ba har yanzu” 


“Idan ya farka ku kira likita, kuma a tabbatar a nemo wannan allurar dana rubuta miki”


“Tohm, likita dan Allah a taimaka mana a karbi rabin daga baya zamu ciko, Wallahi zamu cika maka kudinka casss”


“Dokar asibiti ce, ba a karba rabi ba mu ake ba kudin ba, a account din asibiti ake sakawa, so kin ga kenan ba hurumi na ba ne”


Ya amsa min sai na kara cire hope a lokacin na kalli mijina na sake kallon likita dake daf da fice. 


“Likita to zai yi a cire hantata mai lafiya a saka masa?”


Ya juyo ba shi na jar nurse din suke tare da shi sai da suka kalleni da mamaki dayar har da zare ido. 


“Lallai kina son mijinki sosai, yanzu dai yadda za'ayi ki same ni office anjima kadan zan miki bayanin yadda komai yake”


“Toh na gode”


Na fada sannan na zauna saman kujerar ina kallon Deen, rayuwarmu ta baya nake tunawa yadda yake kula da ni yake nuna kauna da soyayya, yau kuma gashi kwance be ma san ina tsaye kansa ba. 


“Allah ya baka lafiya”


Na fada ina jin hawayen da suka min nisan zango sun durfafo idanuwa da gudunsu. Ban iya jira har sai anjima da ya ce min ba, domin kuwa ba zan iya jiran ba, mafita nake nema ko ta halin yaya. Dan haka na fita daga dakin kuwa da kasancewar na san Deen kadai zan bari a dakin domin Mama ta yi latti zuwa Hajiya kuma ta tafi yin wanka ta canza tufafi, dan haka ni kadai aka bari. Office din likitan na tafi na tsaya daga bakin kofar har ya gama abun da zai yi ya shigo corridor da be da tsayi sosai sai ya same ni a tsaye ina jiransa. 


“Yanzu kika zo?”


“Tun dazu”


Murmushi yayi ya tura kofar office din ya shiga.


“Bismillah”


Ya fada sai na bi bayansa, da kansa ya nuna min inda zan zauna, ina zama aka kwankwaso kofar aka turo wani mutum ne mai kayan likitoci ya shigo suka yi magana ya fita, sannan ya likitan da har yanzu be san sunansa ya kalleni ya ce. 


“Ya sunanki ma?”


“Zahra”


Na amsa da sauri abun ka da mai nema, domin gani nake kamar taimaka mana zai yi yayi mana aikin bashi. 


“Zahra”


Ya kira sunana sai kuma yayi shiru ya dauko wayarsa ya tana sannan ya fara magana 


“Zahra wannan cikin na ki na nawa ne? Shekarar nawa da aure? Kuma watan cikin nan nawa?”


Ba tare da tunanin komai ba na amsa masa. 


“Shekarar mu daya da wata hudu, cikina kuma yana cikin wata na takwas yanzu”


“Kina zuwa awo? Abun da ke cikinki lafiyarsa kalau?”


“Eh ina zuwa, kuma sun ce babu wata matsala”


“Sun fada miki abun da zaki haifa?”


“Aa ba mu yi wannan hoto ba, tun hoton da muka yi lokacin da cikin yana karami ba mu sake yin wani ba”


“A rayuwata ban taba ganin mace mai tausayi da kaunarsa kamar ke ba, ban tana gani ba, da dai labarai ne sai na ce na tana ji shi ma ba kasafai ba”


Na sauke kaina kasa. 


“Mijina shi ne rayuwata, ya nuna kauna da gata a lokacin da nake tsananin bukatarsu, duk yadda zan fada maka mijina yake na maka karya, Wallahi ya wuce duk yadda kake tunani”


“Allah sarki Allah ya bashi lafiya”


“Amin”


“Maganar gaskiya ba a karbar kudin aiki rabi, ko naira biyar ce babu ba za a karba ba sai kin cika”


“Yanzu babu wata mafita kenan likita? Babu wani taimako da zaka iya mana? Ko rance dan Allah Wallahi zamu biya”


Na fada da dukan gaskiyata ina magiya, sai yayi murmushi. 


“Abun da yasa na same ni a officeafita zan fada miki, sai dai be zama lallai ki aminta ba, amman ni na aminta da ke, ina da yakin zaki rike min sirrina ko da abun da nake kudiri be karbu a gurinki ba”


“Doctor ni fa mafita nake nema, ko ma minene ka fada min Wallahi zan aikata indai zan samu kudin”


Yayi jimmm kamar ba zai ce komai ba, sai kuma ya sake kallona ya ce. 


“Ina son ki min rantsuwa”


Na kalleshi da mamaki. 


“Rantsuwa kuma na me?”


“Saboda abun da zan fada miki be zama lallai ki aminta ba, sai dai abu ne da zamu taimaki juna ni da ke, ni ma wata zan taimaka domin tana cikin tsananin damuwa da bakinciki”


“Doc ban gane ba, i thought magana kake yi sai kuma na ji kana zancen wata”


Yaja dogon numfashi ya sauke, sannan ya bude laptop din dake gabansa yayi dan dane danen da zai yi ya juyo min da laptop din ya dawo gafe na yana nuna min hoton da aka dauka na ciwon Deen. 


“Kin ga yanayin yadda hantarsa take, daga nan zuwa nan kin ga har na fara baki, so dole sai mun bude gurin mun wanke mun saka magani sannan a dora shi akan wasu magunguna dazai wata 8 zuwa 12 yana sha, da kuma ba shi kula ta musamman, sannan akwai tests din da zamu masa before then like chest X-ray, electrocardiogram, urinalysis, white blood count da sauran, kuma zan fada miki tsakani da Allah idan ciwon ya kara wasu kwanaki zaki iya rasa mijinki”


Na kalleshi hawaye na sauko min. 


“Na zo nan ne saboda neman mafita, ba dan ka kara daga min hankali ba”


“Na sani, ina son na fada miki komai ne, domin bana son ki ga kamar zan yi hakan ne saboda kawai ina neman wata mafita”


“Dan Allah ka taimaka ka fada min”


Na koma gurinsa ya zauna yayi shiru na dan mintuna, sannan ya ce. 


“Akwai wata mata mai suna Jamila sherarta tara da aure, tana zaune da mijin lafiya kamin abubuwa su fara canjawa, saboda Allah be bata haihuwa ba tun da ta yi aure har zuwa yanzu da nake maganar nan da ke, sanadin hakan yan'uwan mijinta da shi kanshi mijinta sai suke fara canjawa mata har ya fara neman aure zai kara mata saboda likitoci ciki har da ni sun fada masa ba shi matsala ita kuma ba ta da matsalar komai lokaci ne kawai be yi ba”


“Ban ga ta inda labarin wannan matar ya shafe ni”


Na fada domin har ga Allah ban ga alakar labarinta da matsalata ba. 


“Na sani, ina shimfida miki abun ne ta yadda zaki fahimta da kyau, tana tsoron kar mijinta yayi aure ya rabu da ita, ko kuma yan'uwan mijin da mijin su juya mata baya kamar yadda suka fara yi mata yanzu, sanadin hakan ya saka ta same ni tana kuka tana neman taimako...”


Ban bari ya karasa ba, na tari numfashinsa. 


“Da ka takaita labarin wata kila zan fi fahimta, domin ba labarin mijin Jamila ko yan'uwanta ko ita kanta ne yake gabana ba”


Ya sauke ajiyar zuciya ya gyara zamansa. 


“Ina son na kai ki a gabar da zan taimake ki ne. Na kawo mata shawarwari daban daban sai dai ta nuna min mijinta irin mazan nan masu akida ba lallai ne ya yarda da abun da zata gabatar masa ba, ko kuma ni na gabatar masa, daga karshe sai muka cin ma wata matsaya ko kuma na ce mafita ni da ita, sai ta fara yin laulauyi na karya da aka je asibiti sai na auna cikin na yi ma mijinta bushara cewar tana dauke da juna biyu, sanadin hakan ya fasa nenan auren da yake, yan'uwan mijin kuma suka dawo suna kaunarta, aka yi ya tafiya a haka, na yi mata allurar da zata hana period dinta zuwa, lokacin da cikin ya kai matakin girma kuma sai na bata magunguna da allurar da duk ya kamata ayi mata cikin ya kumbura yanzu idan kika ganta zaki dauka cikin na gaske ne, alhalin babu komai a ciki sai iska, amman har hoto na yi mata na bata ta nuna ma mijinta cewar mace zata haifa, sai dai banbancinki da ita tana wata na tara ne, ke kuma kina wata na takwas”


“Ni ban gane wannan labarin ba”


Na fada ina masa kallon rashin fahimta da kuma mamaki a lokaci daya. 


“Gabar ce zan kaiki a yanzu, mun shirya ni da ita cewar idan zata haihu zamu samu wanda ta haihu a lokacin sai ta bata danta a matsayin danta”


“Me kake kokarin fada min?”


Sai ya jingina da kujerar da yake zaune. 


“Idan kin shirya cigaba da rayuwa da mijinki, kin shirya ceton rayuwarsa, zamu biya kudin aiki zamu dauki nauyin duk wata dawainiya tasa har sai ya warke bisa yarjeje ni da sa hannu cewar abun da zaki haifa na Jamila ne, zamu yi hakan a gaban sheidu kamar lauyanta ni ke kuma zamu baki copy yarjejeniyar mu dauki dayan copy kuma bisa sharadin cewar ba zaki taba karya alkawarinmu ba”


Na mike tsaye da sauri tsoro ya kamani, a take jikina ya fara rawa. 


“Ni kuma na yi yaya?”


“Zamu baki matacce wanda zaki shaidawa duniya da yan'uwanki cewar abun da kika haifa be zo da rai ba”


“Anya kasan darajar ďa? Ka taba haihu? Miyasa ba zaka ce matarka ta bata nata ba? Ka san wahalar daukar ciki tun yana wata daya har a haife? Kazan wahala da zafin da mace take ji idan ta haihu ďanta be zo da rai ba balle kuma ace ta siyar da shi? Jahilcina da talaucina be kai can ba”


Ya mike tsaye shi ma yana kallona irin kallonta na babu wasa a maganarsa ko fuskarsa. 


“Wannan maganar tsakanin ni da ke, domin Wallahi bayan ke da na fada miki maganar nan a yanzu da ita Jamila babu wanda ya san da ita, ciki kuwa har da matata, saboda ki iya bakinki idan ba haka ba rayuwarki zata shiga tsari, mafita nake nema miki shiyasa na fada miki idan ba zaki iya ba ba zai kowa ya sani ba”


“Amman dai baka da imani”


“Da bani da imani da ban zauna na fada miki haka ba, domin ba cilasta miki na yi ba, mafita kike nema kuma na fada miki”


Na girgiza kai ina mamakin yadda zuciyar mutane ta lalace suke son cutar da mutane a take, domin wannan cutarwa ce. 


“Ba zan yi ba”


“Toh ko ki iya bakinki”


Ya sake gargadina, ban saurareshi ba na juya na fice rai na bace, a yanzu na tabbatar neman taimako yana saka mutane fadawa hali kala kala, tun da gashi har ya samu damar da zai zaunar da ni ya fada min wannan maganar.