SALMA

Part 2

by @meenatyandoma

👽 *SALMA* 👽

    (HORROR STORY)

  

   _NA MEEN@RT A YANDOMA_



*🌍MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION 📚🖊️*

       *M. W. A*


```Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. ```🤙🏻

***

________________________

*NOTE* Labarin Salma nina kirƙiri abuna, aguji juya mani labari ta kowa ce Siga sai da izinina.



*NA KUƊI NE, KI TURO 300 TA WANNAN ACCOUNT ƊIN AISHA ABUBAKAR 2151366600 UBA BANK, KO KATIN MTN TA WANNAN NUMBER ****



*BANYI ALƘAWARIN YIN FREE PAGE DA YAWA BA, SABODA LABARIN NADA YAWA, HAJIYA KI BIYA KUƊI KISHA LABARI* 🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️🤷🏼‍♀️


*FREE PAGE 3️⃣__4️⃣*

...........Wasa yake mata tana sheƙa dariya tamkar ba jaririya ba.



Duk wannan bidiri da ake su Sahabi basusan mike faruwa ba suna nan han6are suna kwasar bacci.



Wasa yake mata irin na yara duk da kasancewarshi shima yarone, harda ƙyalƙyatawa take, daga ƙarshe ya ɗauke suka tashi saman iska tamkar tsuntsaye.


Falon gidan ya bayyana tare da kwantar da ita saman kujera.


A hankali kayan jikin ta suka canza daga farare zuwa shuɗi, wata fida ta jarirai ta bayyana a hannunshi nan ya shiga feeding ɗin Salma harta ƙoshi.


Aje ta yayi nan fa ta 6ata fuska idonta ya fara ja, hannu yasa ya shafi fuskarta a take wani nannauyan bacci yayi gaba da ita.



Yaye gashin daya rufe mashi fuska yayi, ya salam kyakykyawan yaro wanda ya zarta Salma kyau.


A hankali ya buɗe bakinshi ya fara magana.

"Bazan ta6a bari kiyi kuka ba Salma, ƙaddara ita ta haɗamu, ke tawa ce, gurina na ɗaukar fansa kece zaki tabbatar mani dashi, zani kula dake ta yadda babu wani abu da zani bari ya cutar dake."


Kafin ya rufe baki wata iska ta sureshi tayi sama dashi.


Hasken ranar daya hasko fuskokinsu shiya haddasa masu tashi a tare.



Wayam Sahabi yaga babu Salma, cike da mamaki ya fara tambayar Subi.

"A'ah Subi ina jaririyar nan."?



"Niko ina zani san inda take, bari in duba ƙarƙashin gado koda ace ta faɗo ne."


Cike da mafisa Sahabi ya fara magana

"Yanzu dan baki san zafin yara ba ace ɗiyar mutane harta faɗo baki sani ba."


Wasa_wasa sai da suka bincike ɗakin tas babu Salma babu dalilin ta.



Nan fa hankalin Sahabi ya tashi, falo suka fito nan fa suka sha mamaki domin ganin Salma sukayi kwance tana wasa da hannuwanta.



"Ni fa Sahabi yarinyar nan tana bani tsoro, yarinya kamar aljana."


Bai bi ta kanta ba zuwa yayi ya ɗauki Salma ya rungume yana jin ƙaunar yarinyar na ƙara shiga cikin zuciuarshi tamkar shiya haifeta.



In Uwani mai aikin gidan Sahabi ya kira ya bata Salma domin ta gyara ta.


Ƴar Caras ƙanwar Subi da tun bayan auren Subi da Sahabi ita da yayanta ɗan Alaji suka tare gidan Sahabi.


"Aunty Subi baƙi mukayi naga wata kyakyktawar jaririya hannun Yaya Sahabi."?

Ƴar caras ta ƙarasa maganar tana ƙara sa saukowa daga matattakalar benen.



"Kedai bari ƴar caras, Sahabi ya tsintota jita."


"Tsinto ta kuma."?

Ƴar caras ta faɗa tare da ɗora hannu saman ƙirji.



Ɗan alaji ne ya fito shima daga ɗakin shi yana ƙare masu kallo.


Idonshi ne ya sauka kan Salma da Inna Uwani ke ƙoƙarin cirema kaya amma sunƙi fita.



"Wow! Wata zazzafar beb nike gani, ina muka sameta."

Da gudu irin na ƴan duniya ya taho zai sauko daga saman matakalar benen da zata sadaka da tsakiyar falon, sai dai kafin ya ƙarasa saukowa tamkar an kwaso ƙafafunshi haka aka wulloshi ya fara mulmulowa har ya iso tsakiyar falon.


Su duka falon fashewa da dariya sukayi.


Ɗan alaji daya bugu da ƙyar ya samu ya miƙe.


Sai da suka tsagaita da dariyar hankalinsu su yakai ga Salma dake darzar dariya itama.


A matuƙar firgice Inna Uwani ta saketa tabar falon a guje.



Wasu yawo Su Subi suka haɗiye cike da firgici da tsananin mamaki.


Su dai ko a almara basu ta6ajin jariri sabuwar haihuwa yana dariya ba.


Dariya take hada kyalkyatawa tana kallon Ɗan alaji dake faman zare namujiya tsabar firgici.



Sahabi ko a jikinshi ɗaukar Salma yayi shima yana dariya.


"Yau ni subi nashiga tara, yanzu Sahabi kana gani tana dariya tamkar ɗiyar aljanu har kayi ƙoƙarin ɗaukarta, munshiga bala'i shikenan kasamo mana ɗiyar al'janu."

Subi ta ƙarasa maganar tamkar zatayi kuka.



"Ni ba shirme na tambayeki ba Suwaiba, yanzu dai riƙe mani ita inje in samo mata kayan sawa da abincinta, yauwa subi in ba damuwa muje asibiti su baki magani kisha ki samu ruwan Mama saiki shayar da ita tunda riƙeta zamuyi tamkar ɗiyarmu."



"Ni shegiya inji ɗan daudu, wallahi bazani shayar da wannan al'janar ɗiyar ba, kai nifa in badan dole ba bazani zauna da ɗiyar nan acikin gidan nan ba."



"Ƴar caras riƙe mani ita inje in dawo."

Sahabi ya fada tare da miƙo mata.


"Dan Allah kayi haƙuri wallhi ni yau zani koma gidanmu bazan iya zama da wannan ɗiyar aljanun ba."


Tsoki yayi tare da kwantar da Salma da sai yanzu tayi shiru tana kallon kowa ɗai_ɗaya.


ATM ɗinshi ya ɗauka tare da barin gidan.

____________________________

ENUGU STATE

    Unguwa ce ta masu hannu da shuni, mafi aka sarin mazauna unguwar kiristoci ne.



Wani ƙayataccen gida daya fi ilahirin gidajen wurin ƙayatuwa na tura kai tare da shigewa.


Mata da mijine zaune sai ƙaramin yaronsu da bazai haura wata tara ba.


Daga yanayin su zaka fahince kwata_kwata basu haɗo alaƙa da musulumci ba.



Wata ƙasaitacciyar dariya ce ta su6ucema mijin.


Matar ƙare mashi kallo tayi cike da nishaɗi.




Ta fara magana, cikin hausar da bata goge ba sosai.

"Kuɗi yaro, yanzu gasu munsamu, MAKEL a baya munyi sakarci yanzu gashi muna cikin wadata kuɗi kamar mu ƙona tsabar yawa da sukayi mana."

BANESA ta ƙarasa maganar tare da rungume yaronta ɗan kimanin watanni tara.


Cike da alfahari irin na wanda yayi bankwana da talauci ya fara magana.

"BANESA abinda baki sani ba shine, bamu ba hatta yaronmu DAVID da jikokin da zai haifa nan gaba sunfi ƙarfin talauci."

MAKEL ya ƙarasa maganar cike da alfahari irin na waɗan da jahilci yayi ma katutu.


Ci haba da magana yayi tare da kurba lemun daya ɗauka.

"BUSARI bazai ta6a daina yi mana aman kuɗi ba harsai ranar da muka mutu gaba ɗaya ahalinmu."



Fuskar BANESA canzawa tayi daga yanayin farin ciki zuwa yanayin damuwa.

"MAKEL ina matuƙar kewar BUSARI shikenan yanzu bazani sake ganinshi ba, yanzu shine arziƙinmu shine sanadin yaron da muka samu, abin tsafinmu yayi mani gargaɗi, MAKEL mi ya faɗa gameda BUSARI da muka tsafa yana mana aman kuɗi"?

Ta ƙarasa maganar cike dason jin amsar tambayar da tayima Mijin nata MAKEL.



Cike da son 6oye mata gaskiyar abinda ke faruwa ya fara magana.

"BANESA! Ki cire komi a ranki, bazamu ta6a talaucewa ba, kuma babu abinda zai samu yaronmu."

Ya ƙarasa maganar zuciyarshi na ƙara yi mashi tuni da maganar shugaban matsafa Oduduwa.


"MAKEL ku daina ganin mun tsafa maku wannan yaron Taurarinshi nada ƙarfi, kasan cewarshi yaron maƙiyanmu wato musulmai, kasani akoda yaushe ruhin yaron nan zai iya dawowa jikinshi, wanda hakan zai iya jawo maku tonen asirinku ga kuma babban bala'i wanda yafi komi shine koda wasa kada ku bari ɗanku DAVID yayi gangancin shiga garin garin IBADAN, domin alamu sun nuna mani tabbas ruhin busari yana ya cikin garin, radda duk kuka bari BUSARI yayi ganganci haɗuwa da DAVID tabbas ranar DAVID zai mutu."

Maganar BANESA ce ta dawo da MAKEL daga duniyar tunanin daya lula.


"MAKEL! Ya muna magana ka tafi wata duniyar tunanin."

Ta ƙarasa maganar ta cike da damuwa.


"Bakomi BANESA ina tunanin inda zamuje mu gabatar da BIRTHDAY ɗin DAVID kinsan yakusa cika shekara ɗaya."


Cike da farin ciki naga sun ɗunguma su duka sun nufi bayan gidan tare da shigewa wani sirrataccen ɗaki.



Tsabar Duhu baka ganin ko tafin hannunka, makunnin wuta MAKEL ya latsa.



Take haske ya gauraye ɗakin.


Innalillahi wa'innah ilaihi raji'un.


Yarone karami ɗan kimanin shekaru biyar, gabarshi uwayen kuɗine daya amayo marasa adadi.....

______________________

 Sahabi yana gama sayayyah kai tsaye gidan Mahaifanshi ya nufa ya sanar dasu halin da ake ciki.



Kasan cewar mahaifanshi mutanen kirkine yasa suka goya mashi baya akan ya riƙe yarinyar Ubangiji kadai yasa fasahar yin haka.



Gidanshi ya wuce kai tsaye.


Tun daga bakin Get yake jiyo ihun ƙato, ba shiri ya fito mota a guje.


Ƴar caras ce tsaye kan yayanta ɗan alaji dake baje ƙasa yana numfashi da ƙyar tsabar azabar dayaji.


"Miya faru dashi haka."?

Sahabi ya tambaya.


Cikin in ina Ƴar caras ta fara magana cike da mugun nufi akan jaririyar nan.


"Yaya ne ya ce yanason waccen mayyar yarinyar daka kawo, shine yaje ɗaukarta sai dai muks jiyo ihunshi.


Shine fitowarmu muka ga jaririyar na kyalkyata dariya shikuma Ɗan alaji kwance ƙasa ya suma ga zawo daya wanke mashi jiki.



"Ku mai dani gidan iyayena, na gama zaman gidan nan, abinda zani faɗa maku shine ku yi gaggawar rabuwa da yarinyar nan aljana ce."


Tsoki Sahabi yayi tare da ɗaukar Salma daketa wasa abinta.


Ko ina ya duba amma babu Subi acikin gidan.



Abinda bai sani ba shine tun bayan fitarshi ƙungiya ta kira taron gaggawa Subi ta fice.



Tura ɗakin Subi tayi tare da shigowa cike da tsoron abinda zai biyo baya.


"Uhm' uhm, yaushe kadawo."

Subi ta faɗa cike da rashin gaskiya.



"Daga ina kike."

Sahabi ya Fada yana kare mata kallo.


"Mama ce ba lafiya, gida naje."


Bai kara bi takantaba domin yana kara hada ido da ita yaji yadaina jin haushinta ga kuma shakkarta da yaji ta saukar mashi.



Sahabi lura yayi hannun Salma kamar alamu jini, wani siririn yankane kuma da alamu sabon yankane.



Kenan ba ai mata wanka ba tunda ga kayan jikinta nan.



Subi ya ba tare da umartar tayi mata wanka.



Bata wani damuba face tsabar farin ciki, domin ƴar ƙungiya sun bata abinda zata aiwatar akan Salmar.



Shugabansu duk wani bincike da yayi kanta ya kasa ganin komi, abu ɗaya ya gani shine in dai Salma ta girma to ita ce zata zama sanadin tonuwar asirinsu.


Garin maganin da shugaba ya bata ta wanda zata aiwatar da aiki a daren yau akan Salma.



Iya ƙoƙarin fidda kayan jikinta tayi, amma ta kasa.

"Yau ni suwaiba minike gani, wannan jinjira kodai Aljana ce, tun ɗazu nike ƙoƙarin cire kayan jikinta amma sun kasa fita."

Maganar ta taƙarshe ce ta tokare jiyo Salma ta tu tsure da dariya.



Ba shiri Subi ta ajeta gefe tare da kwalama Sahabi kira.



A guje ya karaso jin wannan kiran mafarauta da take mashi.


"Lafiya."?

Ya tambaya jikinshi na ciri kamar zai duƙa mata.


"Aljana ce, Sahabi bala'i ka kwaso mana."

Nan ta kwashe kaf abinda ya faru ta faɗa mashi.



Juyawa yayi, abin mamaki Salma bacci ma take abinta.


Ƙara tsorata Subi tayi ganin wannan al'amari.


Duk da haka a yau ta ƙuɗurci gamawa da wannan jaririyar da hasashe ke nuna ita ce sanadin tonuwar asirinta.



Anyi juyin duniya Salma taƙi buɗe baki bare kuma tasha madarar jariran da ake bata.


Daga ƙarshema duk wanda suka hada ido da shi saiya tsorata ganin yadda idanunta suka koma.



Hatta Sahabi izuwa yanzu ya fara tsorata da lamarin Salma.



Kashedi yayima su Ƴar caras aka su daina kiranta jaririya, sunanta Salma.



Duhun dare gamida kukan karunuka daya gauraye ilahirin garin ne ya haddasama ɗakin duhunda ko tafin hannunka baka gani.



A iya sanin subi Sahabi ya ɗauko Salma a kirjinshi yana rainonta bacci ya ɗauketa.


Amma abin mamaki ta duba ko ina amma babu Salma.


Kullin magani ta ɗauko tare da nufo falo dan zuciyarta ta ƙago da ta cika aiki.


Dube_dube tahauyi tun kafin ta ƙarasa saukowa daga matakalar benen.


Kamar an dafa ta tabayanta haka tajiyo.


A firgice ta juyo amma wayam babu kowa.


Ida takowa rayi zuwa tsakiyar falon nan ma wayam babu Salma.



Juyowa tayi da nufi komawa ɗakin, sai dai mi wata iska mai ƙarfi ta fizgota ta zaunar da ita irin zaman ƴan bori.


Fankokin falon dake kashe lokaci ɗaya suka kunna kansu suka cigaba da wani mugun gudu suna kaɗa labulayen ɗakin.


Wutar falon tariƙa kunna kanta tana mutuwa.


Fafarniya wutar falon taci gaba dayi ba ƙaƙƙautawa.



Iyakar kiɗimewa Subi ta ruɗe, hankalinta bai ƙara ƙololuwar tashi ba sai da idanunta suka sauka kan ƙaramin yaro ɗan kimanin shekaru biyar Salma riƙe a hannunshi tana sharar bacci, gashin kanshi ya rufe fuskarshi bata ganin komi.


Dariya irinta ƙananun yara mai firgitar da ruhin bil'adam ta gauraye falon, take falon ya fara wata irin girgiza..........











*MEEN@RT...✍🏼*

***