104-105
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
104_105
Tsananin mamaki ne ya hana omar cewa komai, kafin ya ida tunani imaan ta sake matse shi a jikin ta tana kallon sa tace uhum gsky yau ka dade dayawa duk gidan yamin girma wlhy ta karasa mgnr cikin wata irin murya wacce ita kanta batasan tana da ita ba batare da omar ya shirya ba ya saki murmushi Wanda ga dukkan alamu ma mamaki yafi bayyana kan fuskar sa. ehem..ehem...farooq yyi gyaran murya yace karku manta fa akwai baqi a gidan sai Ku bari idan munbar wajen sai kuyi soyayyar Ku, imaan tayi 'Yar dariya tace bamason sa ido ya farooq, farooq ya ya zaro ido oh Allah wai yaushe kika zama hakane imaan? Imaan tayi murmushi tana kallon omar tace lkcn Dana zama Matar ka ko sweeet tayi mgnr hade da daga gira daya tana jifan sa da wani kafirin murmushi.. Omar kamar sakarai ya sake yin murmushi har haqoran sa suka bayyana yace eh..eh..har yana rawar baki. "Imaan ta kalli farooq daya saki baki da hanci yana kallon ikon God dukda yana lura da yanayin omar da imaan Sam basa shiri har bayan auren su toh Amman meya kawo wannan shirin...tayi masa gwaloo farooq yyi murmushi a zuciyar sa kuwa fatan sa Allah yasa wannan shirin nasu ya daure na har Abada, sannan yace uhum dadinta ma dai inada tawa Matar bare amin gori. Sai alkcn imaan ta kalli anty ameera suna hada ido suka sakarwa juna murmushi anty ameera tayi mata alama da hannu ma'ana aikinta yana kyau. "Farooq yace toh mukam tafiya zamuyi mubar Ku kusha iska. "Gaban imaan yace darararamamm yanzu suna tafiya kashinta ya bushe kila omar idan ya dinga kwallo da ita saita koma mulmulallan ball. Adan rikice tace haba ya farooq Ku kwana anan mana. "Farooq yace Tabb inaa aiko qarfe 3 ne sai munbar gidan nan, kinga tashi mu tafi yyi mgnr yana kallon anty ameera, anty ameera ta kalli imaan tayi mata alama da ido karta tsorata koda sunbar gidan, imaan ta gyada kai duk abinda sukayi babu Wanda ya lura da hakan sai su biyu. "Imaan ta kalli omar da tun dazu sai bin imaan yake da kallo ta kashe masa ido daya tace sweety daukeni mu rakasu, omar ya dan zaro ido da mamaki, farooq yyi dariya yace ke dallah tashi katuwa dake sai an dauke ki Allah bro ka sangartar d yarinyar nan dayawa yyi mgnr yana kallon omar.... Kafin yyi mgn imaan ta shagwabe fuska tace ohh durlin wannan ya farooq din ya cika sa ido ai idan kana nan Kaine me daukata koh tayi mgnr hade da dage gira.. Omar yyi murmushi yace yes..yes.. Ya kalli farooq yace malam Ku tafi karka takuramin mata. Farooq yaja hannun anty ameera yace aifa kin gani harsun fara korar mu. Imaan ta kalli omar da murmushi tace muje karsuyi fushi, aikuwa kamar sakarai haka ya dauketa suka bar falon. Har gaban mota suka rakasu, suna zuwa imaan tace yauwa toh sauko ni ya omar bari muyi sallama da anty ameera omar yayi abinda tace, da sauri imaan ta isa wajen anty ameera ta mika mata hannu sukayi shaking hands atare kuma suka dage gira. Daga haka basu CE komai ba, farooq yaja mota yabar gidan, imaan da omar na tsaye har me gadi ya rufe gate din. "Imaan tayi tsaye ta kasa juyowa ta kalli omar sai yanzu wani tsoro ya shigeta tunowa da kalaman Anty ameera da tayi ne yasa mata kwarin gwiwa, dan haka cike da isa ta juyo suna hada ido da omar ta watsa masa wani mugun kallo sannan ta wuce shi a wajen tana taku.
"Tsananin mamaki ne ya sake kama omar tmbyr zuciyar sa yyi anya imaan bata da aljanu? Dan yasan ko kusa acikin hankalin ta yanda take mugun tsoron sa bazata kwatanta abinda tayi yau ba.. Lalle ma yarinyar nan ta soma raina shi, shima falon ya nufa d niyyar taka mata burki tunkafin rainin yyi nisa. "Lkcn da imaan ta shiga falo kuwa da gudu ta haura sama tana tsalle akan gado ah lalle Ashe dai zan iya acting wani murmushi ya bayyana fuskar ta da sauri ta tashi tace bari nayi sauri na cire rigannan ayi shirin next target. "Dake doguwar rigace haka ta jawota tundaga sama ta kwaye rigar ya rage daga ita sai pant da bra., daidai lkcn kuma omar ya bude kofar yana wani dan karamin huci shi a dole ransa ya baci zai takawa imaan burki, caakkkk ya tsaya yana karewa halittar imaan kallo, imaan kuwa na ganin sa dukda tadan tsorata hakan besa ta bayyana tsoron nata ba. "Asalima sai ta nufi jikin Waldrop tana tafiye me cike da daukar hankali, sannan ta ajiye rigar data cire... Shikuwa gogan naku duk inda ta wulga Binta yake da kallo kamar tsohon maye. "Imaan duk tana lura dashi, ganin yaki barin wajen ita kuwa ta shige toilet danyin wanka. "Omar kam da kyar hannun sa suka iya jawo kofar daya rike da niyyar komawa falo, haka zalika kafafun sa ba karamin kokari sukayi ba wajen daukar gangar jikin sa, yana tafiya Amman halittar imaan ke masa yawo a ido tamkar har yanzu tana gaban sa, yana wannan tunanin sai ji yyi, yyi missing step kiiiiii....saura kadan ya zame cikin taimakon ubangiji yyi saurin riko karfen dake kusa dashi ya rike, a daddafe ya karasa falon kasa sannan ya zube akan kujera, sosai ya zurawa kallo ido duk wanda ya kalleshi zai yabbatar ya bada dukkannin hankalin sa ga TV, saidai shi a wajen sa tunanin halittar imaan yake har yake ganin kamar gizo take masa a jikin kallon.
Kuyi sorry na rashin posting dina akai2 hakan ya biyo bayane na matsalar da wayata ta samu, Amman zan dinga kokartawa na dinga maku insha Allah. Wanda sukeson daga farko kuyi searching NUCEEY LUV NOVEL HOUSE a Facebook zaku samu complete. Luv u oll 😍
Nuceey luv😘