OMAR KO FAROOQ?

108-109

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓





108_109





"Sai bayan imaan ta fice a dakin kuma sai yaji kwata2 bai kyauta mata ba dan yasani sarai shine da lefi, tashi yyi sannan ya wuce toilet danyin alwala bayan ya fito yazo ya wuce masallaci. "Imaan ma na shiga daki toilet ta wuce tayi alwala bayan ta idar da sallar a zuciyar take tunanin anya zataci gaba da aikin da anty ameera tasa ta? Dan gsky rainin hankalin omar ya fara isarta wlhy, wata zuciyar tace toh idan banda abinki ai aikin kwato 'yan kike yi daman ai sai ansha wuya akan sha dadi, tabe baki tayi sannan ta haye gado dan komawa da bcci kamar yanda anty ameera tace mata. "Omar kuwa koda ya dawo masallaci ya saba ya hadu da imaan ta fito shara ko kuma ta fara sharar ga mamakinsa yaga wayam. "Haka ya wuce sama shi abinda yafi damunsa be wuce yaga yanayin imaan ba dan yasan ya 6ata mata rai. "Tsaye yyi yanason budewa kofar saidai wannan girman kan nasa ya kasa barinsa toh idan ya shiga ya CE mata me? Da yasaba kare kansa a yanzu kuwa baida abin cewa ma. "Har zai juya yaji bazai iya tafiya ba kawai yanason sanin halin da take ciki yanzu. "Ta maza yyi sannan ya bude kofar a hankali. "Yana shiga ya hango imaan kan gado sai bccinta take hankali kwance, karasawa yyi ya zuba mata manyan idanun sa yana kare mata kallo. "Saida yyi kusan 5mins yana kallon ta sannan yabar dakin nata, dakinsa ya koma shima ya haye gado saidai duk yanda yaso dayin bccin ya gagara bargon sa ya tattaro gefen inda imaan ta rufu jiya ya lullube fuskar sa yana shakar kamshin da imaan tabar shi.

"Karfe 9 imaan ta tashi sannan ta sauko kasa, kitchen ta wuce ta hadawa omar breakfast dukda tana tunanin ba lallene yaci ba. Haka ta gama hada komai sannan ta jera akan dining table. "Bayan ta gama ta wuce dakinta ta fada wanka. "Bayan tayi wanka tazo gaban mirror ta tsara kwalliya me kyau, sannan tasa wata atamfa skirt din ya matseta sosai yyinda rigar ta fito Dana fulanin ta kamar zasu yaga rigar, cikinta a shafe sannan ta zauna zaman daurin dankwali. "Masha Allah daurin da tayi ba karamin karbata yyi ba tayi kyau sosai kamar a sace ta. "Yanzun ma kallon kanta ta shiga yi ita kanta tasan ta hadu iya haduwa, fesa turaruka tayi masu matukar kamshi da dadin shaqa. "Saida ta gama sannan ta bude dakinta, kamar hadin baki daidai lkcin omar ya bude tasa kofar shima cikin shirin sa na kananan kaya Wanda suke matukar yi masa kyau tamkar dan India, Baki ya saki yana kallon kyakkyawar hallitar dake gabansa anya wannan imaan ce?, gefe guda hankalin sa yafi tafiya Ga na fulanin ta yanda suka firfito suna CE masa morning kamar yaje yyi hugging dinta. Imaan kuwa tana lura da irin kallon da omar yake jifanta dashi kamar ya hadiyeta batasan lkcn da wani murmushin mugunta ya kubce mata ba, cikin kissa ta isa gaban shi tana murmushi tace morning ya omar, omar shima besan lkcn da nasa murmushin ya kubce ba dan duk yando yaso daya daure fuska abun ya gagara, saidai ga dukkan alamu NASA na farinciki ne a ganin sa imaan ta huce da fushin da take dashi, morning ya bata amsa, imaan ta karbi jakar daya rataya a kafadar sa sannnan tace muje kayi breakfast, omar ya mika mata jakar kamar wani wawa sannan ya bita a baya kamar jela, imaan data lura ya biyota saita canja takun tafiyar ta zuwa wani irin salo me rikita Wanda yake kallo. "Omar dake bayanta kuwa sai ganin duwaiwai yake a zuciyar sa yace Allah yyi hallita anan. "Da haka suka isa dining area. "Jawo plate tayi ta zuba masa farfesun da tayi Wanda yaji hadi sosai, tun kafin ta gama zubawa omar ya fara hadiyar yawu dan kamshin ya gama cika masa ciki. "Imaan ta matso da komai gabansa sannan tace bismilla, omar ya daga ido yana kallon ta yaso ya maze yace bazai ci abincin ba, saidai kashh ya kasa cewa uffan kamshin abincin ya damesa. Dole yasa spoon ya fara kwasar girki, spoon na farko ya dago ido yana kallon imaan suna hada ido sai ya tabe baki yana yatsina, can kuma ya ware sai kwasa yake. Imaan dai kallon shi take tana ganin ikon Allah mutumin daya yatsina fuska a farko shine kuma ya ware kamar bashi ba yana cin abinci. Saida omar yajishi damm sannan ya ture plate din, nan kuma yaji kunya dan bayason ta zata ko abincin nata ne ya masa ddi har yaci dayawa. Dan haka ya samawa kansa lpy ma'ana ya daure fuska kamar bashi ba. "Jakar sa ya dauka ya fice abinsa batare da yyi mata mgn ba. Imaan dai ta tabe baki kawai sannan itama tayi nata breakfast din.


"Haka ya kasance kullum shigar imaan ta safe daban ta rana daban ta darema daban, duk tabi ta rikita omar a yanxu bashida wani abun tunani sai imaan baida abin zance sai imaan, duk ya shiga tunani ya rasa ma me yakeji game da imaan a yanzu dukta birkita masa tunani da salon ta. "Ba abunda yafi bawa imaan mamaki kamar yanda cikin dan kankanin lkci omar ya Sanya masu aiki a gidan sa aikinta yanzu girkine kawai dake sun dade da gama exam sai kuma bcci ko tayi kallo, wani kuma ta karanta littafi a karance karancen NATA ne ta samo wani littafi me suna RAYUWAR NUSAIBA gsky littafin ya tafi da imanin ta bata gajiya da karanta shi domin cike yake da tausayi, jarabta,hakuri, da kuma Uwa uba soyayya me tsayawa a rai. Hakan yasa imaan ta sake murmurewa ta sake wani haske na ban mamaki ga wani iron cika da qirjin ta ya sake yi kamar su fasa riga hips dinta kuwa ba ace komai dan ya dace da jikinta komai daidai.






****

Omar zaune a office ya kasa tabuka komai daya kalli wani wajen sai yaga kamar gixo imaan take masa duk tunanin ta ya damesa a yanzu ya fison kasancewa a gida dan yasan zaije yaga kwalliyar imaan koda baza suyi mgn ba, shi yama rasa meke damunsa cikin kwanakin nan, shin wai me hakan ke nufi? Na fara damuwa da lamarin yarinyar nan ne kome? Ko kuma na fara Sonta??? Mwtssss yaja wani uban tsaki Wannan yarinyar ai saita rainani mwtsss ya sake jan tsaki a karo na biyu Amman dukda haka ya kasa banbance me yakeji game da wannan yarinyar wadda yake mata kallon jaririya ada. "Ba abinda yafi daukar hankalin sa da ita sai arsenal da Manchester'n ta. ( na Fulani da duwaiwaiii..lol)






Nuceey luv 😘