OMAR KO FAROOQ?

110-111

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓





110_111





"Haka yayi ta tunani barkatai har lkcin tashin sa yyi.

"Imaan ce ta sauko kasa shigar da tayi na wata arniyar riga d wandon ta ¾ sai gashin ta data kama da ribon Wanda ya sha gyara sosai. "Cikin takun data saba ta iso falon sannan ta nemi waje ta zauna, kallon data gaji dayi ta kashe sannan ta kunna wakar India take falon yahau kara dumdumdum kamar zai tsage dan kara, saikace mazari tuni imaan ta mike tana rawa hankalin ta a kwance. "Omar ne ya dawo daga office tun daga bakin kofa ya fara jin karar wakar da sauri ya bude, yana budewa baki wangalgal ya saki yana kallon imaan data koma masa 'Yar India sakkk sosai ya baza ido yana kallon yanda take juyi kamar dan ita akayi wakar, hakanan ya samu kansa da dauko wayar sa sannan ya fara daukar ta vedio yana murmushi. "Imaan kuwa ko kadan batasan da shigowar omar ba dan haka ta zage sosai tana rawar ta. "Saida ta fara gajia sannan ta fara sassauta rawar, juyowar da zatayi taga omar a tsaye rike da waya suna hada ido sai yyi saurin danna stop sannan ya kara a kunnen sa da sauri yana fadin hello na tsaya duba number ne olryt, duk wannan abun da yake yana tafiya ne dan haurawa sama. "Imaan ta bishi da kallo a zuciyar tace kaddai ya omar tun dazu ya shigo? Wata zuciyar tace mwtsss da tun dazune ai zaki sani haka dai tayi ta tunani batare da ta kawo cewar omar ya dauke ta ba.

"Omar kuwa yana shiga daki ya daina wayar karyar da yake, toilet ya fada yyi wanka sannan ya shirya cikin irin shigar da imaan tayi karamar Riga da ¾, shima falon ya sauka saidai koda yaje be sameta a falon ba harta bar wajen, ba yanda yaso ba kenan., yaso ace ya ganta koda iya kallon ta zai debe masa kewa., haka dai ya kunna kallon daya dauki imaan a wayar sa yana gani.

"Sai bayan magrib sannan imaan ta sauko kasa alkcn shima omar din ya sauko. "Shigar data saba irin wannan lkcn shi tayi wani dan guntun wando ta sanya Wanda d kadan ya sauko Rabin cinyar ta. Sai wata Riga dudu iya na fulanin ta suka rufe, daga nan bata qara komai ba. Sai wani karairaya take. "Omar kamar kullum sai kallon ta yake yana lashe baki kamar tshohon maye, yanason zama kusa da imaan Amman yana tsoron karta raina shi, shiyasa yake mazewa. "Imaan na kan kujera ta fara wata irin mika tana jujjuya manyan idon masu kama da tana jin bcci saboda gajiar rawar da tayi duk jikinta yyi tsami. Habawa wannan mikar a wajen omar tuni ta sake birkita masa tunani duk yabi ya rikice da kallon ta, kasa zama yyi dan wani irin yanayi data jefashi, ba zato ba tsammani imaan sai ji tayi an rungumo ta. "Cike da tsoro ta kalli omar daya fara shinshina ta saikace tsohon maye, cike da tashin hankali ta saki wata irin rikitacciyar kara tana kokarin ture omar, omar ya dago rinannun idanun sa yana kallon imaan cikin dashashshiyar murya besan lkcn da yace imaan plss, imaan ta zaro balabalan idanun ta tana kallon sa atake itama tace plss for wat? Omar ya sake yin kasa da murya yace ki zauna a haka kinji, imaan tsananin mamaki ne ya kama ta anya yau omar lpyr sa? Ta tmbyi kanta,... kinji ya katse mata tunanin da take, imaan batasan lkcn data saki wani dogon tsaki ba tana jifan sa da wani mugun kallo, da iya qarfin da Allah ya bata Tayi azamar ture shi sannan ta haura sama a guje. "Omar yana nan a zaune sai yanzu hankalin sa ya dan dawo jikinsa, ya kasa tantance abinda ya faru shida imaan, hannun sa ya cusa cikin gashin sa yana murza su, wata zuciyar tasa tace wai meke damunka omar? Kasan abinda ka aikata yanzu? Wannan ai saita rainaka kana wani rokon ta. "A wani bangaren zuciyar sa kuwa tace masa toh ba Matar ka bace? Mwtsss a fili ya furta wai yaushe ma na fara ajiyeta a matsayin mata? Shikadai a falon sai surutan sa yake.

"Imaan kuwa tana shiga daki ta fada kan gado ta kasa tantance gskyr abinda kunnen ta ya jiye mata game da abinda omar yace "imaan plss" mgnr ya sake dawo mata a kai wata irin dariyar mugunta ta saki a fili ta furta yanzu ne ya kamata ace kasan naji zafin wulakancin da kamin lkcn dana nemi taimako a hospital dinku., sorry anty ameera har yau banji zan iya yafewa omar wulakanta min mahaifya da yyi a raina ba dauriya ma nake inayin wasu abubuwan dole ne omar ya gane kuskuren sa tayi mgnr kamar tana gaban ta.


'Omar yana nan shiru2 shi kadai a falo a zaton sa ko imaan zata dawo, Amman ko alamunta beji ba, wata zuciyar tace kaje ka duba ta mana, omar ya jijjiga kai a fili yace No kamar yana mgn da wani.



******

"Duk yanda omar yaso ya cire tunanin imaan a ransa abin ya faskara karshe ma wani irin azababben sonta yakeji kamar yyi hauka, kullum yaje office baida abin kallo sai vedion daya dauki imaan ranar shine kurum yake debe masa kewa. " duk iya tunanin sa ya tabbatar wa kansa soyayyar imaan ta gama yawo a cikin jinin jikin sa, ba abinda yafi daga masa hankali irin yanda yake tsoron tunkarar imaan dan ya sanar mata sakon zuciyar sa. Wani tunanin yyi akan gwara ya sanar mata ko zai ragewa kansa sassaucin da zuciyar sa take ciki, tunda ya lura kamar imaan din zatayi saukin kai harta yadda da kudirin sa.




******

"Imaan na zaune a kan gado kamar an mintsine ta, ta mike da sauri dakin omar ta duba anan taga dayar wayar shi daman abinda take tsammani kenan. "Da sauri tayi dialling number mummy bada jimawa ba mummy ta dauka. "Imaan ta canja murya zuwa muryar tausayi tace mummy INA wuni, mummy najin muryar imaan tace a'a dota shikenan sai najiki shiru bakya nema na? Imaan ta sake yin kasa da murya tace ayya mummy kusan 1 month kenan fa INA ciwo. Cike da tashin hankali mummy dake zaune ta mike hade da dafe qirji sai yanzu ma ta fuskanci yanayin mgnr imaan din, baki na bari tace 1 month? Shine omar din Be fadamin ba? Imaan tace mummy nidai kizo dan Allah. "Mummy da sauri tace aiko bakice ba imaan nikuma tamuce dashi saina sa6a masa., gani nan ma yanzu zan taho. "Imaan tayi murmushi sannan tasake kasa da murya tace yauwa saikin zo mummy, anan sukayi sallama. "Imaan tayi saurin ajiye wayar ta koma dakinta zuciyar ta fari kall dan tayi alkawarin yanda omar yyi sanadin cusa mata bakin ciki shima saita cusa masa, kayan data saba sawa lkcn da take aiki shi ta dauko sannan ta canja shigar ta. Da sauri ta sauko daga sama sannan ta fita zuwa waje masu Aikin gidan taje tayi saurin sallamar su sannan tace kada su dawo saita neme su. Da mamaki suka nemi Karin bayani a gunta Amman imaan tayi masu Jan ido tace idan bazasu tafi ba zata koresu daga aikin gaba1, aiko jiki na rawa suka bar gidan. "Dayake yamma ce duk ganyen flowers sun bata gidan haka imaan ta dauki tsintsiya ta fara shara dan tanada tabbacin mummy na hanyar zuwa gidan.


**""

Omar kuwa driving yake hankali kwance dan yau ya yanke shawarar gwara kawai ya sanarwa imaan abinda ke ransa su gyara zaman auren su, sai murmushi yake abinsa.






Nuceey luv😘