OMAR KO FAROOQ?

112-113

by @nuceeyluv

® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓





112_113





"Tsabar sauri mummy ko takan driver bata bi ba dakan ta take driving sosai hankalin ta ya tashi jin imaan bata da lpy har 1month lalle omar zai fuskanci hukuncin ta wannan ai wulakanci ne yaki sanar mata.. Ita kadai a mota sai tunani take yyinda ta kara gudun motar ta.

"Cikin lkci kadan mummy ta isa unguwar su imaan. "Ta 6angaren omar kuwa wani waje inda ake saida dakwalen kaji yabi, anan ya parka motar sa, cikin lkci kadan aka hado masa kajin daya bukata Wanda sukaji gashi sosai da hadi me kamshi. "Motar sa ya koma sannan ya ci gaba da driving., da haka shima ya isa unguwar.

"Horn mummy take sosai har taso firgita me gadin gidan, a kidime ya bude ganin mummy CE da kanta. "A daidai lkcin imaan ta gama sharar gidan duk tayi butu2 sbd kura., sannan ta fara bayin fulawa. "Mummy kuwa a sukwane ta Sanyo hancin motar ta gidan ko daidaita parking motar ta batayi ba ta fito, cikin azama tayi hanyar falo burinta taga halin da imaan ke ciki. "Imaan na ganin mummy tayi hanyar falo hakan ya tabbatar mata bata ganeta ba kenan. "Cikin siririyar murya tace mummy... Ko acikin mafarki mummy bazata manta muryar imaan ba dan haka ta juyo da sauri dan tantance daga ina muryar ta fito. "Daga can nesa mummy ta hango imaan tana bayin fulawa, ai da sauri mummy ta isa wajen ta dan tabbatar da abinda take gani yanzu., "mummy ta zaro ido sosai tana kallon imaan dake bayin fulawa. Imaan ta ajiye abin bayin fulawar sannan ta tako gaban mummy tana murmushi tace mummy mu shiga daga ciki tanayin mgnr ne tana Jan numfashi irin ciwon na cinta a jiki kenan. "Cikin rawar murya mummy tace me zan gani imaan? Me kikeyi anan? Meya hadaki da bayin fulawa? Dubeki da alama ke kikayi sharar gidan ma INA ma'aikatan gidan suke? "Imaan tayi raurau da idanu cikin sarkewar murya tace mummy muje daga ciki plss, mummy tace No answer my questions first. "Imaan tayi shiru yyinda hawayen da take makalewa sukayi nasarar sauka kan kumatun ta, da sauri tasa hannu ta share sannan ta danyi murmushi tace mummy wannan ai dutyna ne ba komai...da sauri mummy tace whattttt???? Imaan ta girgiza kai alamar hakan take nufi hade da wani karamin murmushi tace laa mummy karki damu ai ba wani Abu muje daga ciki. "Mummy idan ranta yyi dubu ya baci lalle omar ya watsa mata kasa a ido ya wulakanta amanar data damka masa, kafin tayi mgn omar shima ya danno hancin motar sa gidan. "Hango mummy a gidan ba karamin mamaki yyi ba cikin sauri yyi parking motar sa sannan ya isa garesu. "Mummy yaushe kikazo? Omar ya tambayeta da alamar mamaki a fuskar sa, mummy ta kalleshi kallo na tuhuma, take cikin omar yace kulululu yau kuma wanne lefi yyiwa mummy? Kafin ya ida tunanin sa mummy cikin muryar bacin rai tace ka bani mamaki omar ban taba zaton zakamin haka ba zatona zaka rungumi maraicin imaan ka rungumi amanar Dana damka maka ka rungume shi hannu bibbiyu sai gashi ka nuna min ban isa ba koda yake ba lefinka bane omar Nina nace a aura maka imaan dan kayi abinda yafi haka bakomai bane, na gode da abinda ka saka mani karshe inason ka mikomin takar dar imaan yanzu dan zamanku da ita ya qare daga yau by god grace ta Kare mgnr cike da bacin rai cike da nadamar auren data hada.

"Cikin tsananin tashin hankali omar yake kallon mummy sannan ya juya yana kallon imaan dake gefen mummy, kallon sa ya sake dawowa ga mummy murya na rawa yace dan Allah mummy kiyi hakuri wlhy tunba yau ba na daina yiwa imaan komai kuma wlhy...mummy ta daga masa hannu cikin tsawa tace ba karin bayanin ka nake nema ba omar takardar imaan nakeson ka bani kuma ayau zata bar gidan nan., omar hankalin sa ya sake kololuwar tashi yama za'ai sama takai ace ya bawa imaan takardar ta? Saida ya fara sonta za'ace su rabu? Mummy plss ki fahimce ni.... Wani uban tsaki mummy taja sannan ta finciki hannun imaan tace zamu bar maka gidan ka idan masu aiki kkeso saika nemo bawai imaan ba and karka manta INA jiran takardar ta a gida. Tana kaiwa nan ta fara tafiya... Omar ya shiga rudu da tashin hankali muryar shi na rawa ya fara kiran mummy... Mummy... Mummy. Ina ko waiwayon sa batayi ba, take ya fara kiran sunan imaan..imaan sai a karo na biyo imaan ta waiwayo omar suna hada ido ta sakar masa harara... Take omar ya dafe kansa yana fadin inna lillahi wa'inna ilaihin raji'un.

"Mummy kuwa tsabar bacin ran da omar ya cusa mata shi ya hanata juyowa ta kalleshi dan yau omar ya kaita karshe.

"Ta bangaren imaan kuwa hamdala kurum ta a ganin ta yau dai ta yadda kwallon mangwaro ta huta da kuda.






Nuceey luv😘