114-115
by @nuceeyluv
® *OMAR* *KO* *FAROOQ* ❓
114_115
"Cikin mintuna kalilan mummy ta isa gida dake gudu takeyi sosai. "Suna zuwa falo suka zauna. "Mummy ta kalli imaan na tsawon dakika uku sannan ta numfasa tace yanzu imaan kina cikin wannan halin kika kasa sanar dani tuntuni? Imaan ta sadda kanta kasa a hankali tace kiyi hakuri mummy banason bacin ranki ne yanzun ma INA rokon ki da kiyi hakuri banso bacin ranki ba. "Mummy tace haba imaan ai wannan ba abun a kyale shi bane saikace baiwa na bashi? Mwtss, Mummy taja tsaki. "Imaan dai shiru tayi abunta karshe ma tashi tayi ta koma daki dan ta watsa ruwa.
"6angaren omar kuwa babu abunda ke nanatawa sai innalillahi wa'inna ilaihin raji'un shin meyasa sai yanzu abun zai faru? Wannan wanne irin iftila'i ne? "Wai ma INA 'yan aikin gidan da har imaan ta samu damar fitowa tayi bayin fulawa? Nazari ya shiga yi can ya yanke hukuncin ko kusa wannan aikin imaan ne, tayi shine kuma da wani manufa to tmbyr anan shine ya akayi mummy tazo gidan a wannan lkcn? Ganin tanbayoyin da yake ma kansa bazai kaishi ko'ina ba, motar sa ya shige sannan ya kunna ta shima a guje ya fisgi motar sa yabar gidan. "Gudu yake sosai akan titi hakan ya bashi damar isowa gida da wuri. "A falo ya tarad da mummy bayan yyi sallama, mummy dake zaune daga ciki2 ta amsa salamar batare data dago kai ta kalle shi ba. "Omar ya tako wajen ta a sanyaye sannan ya zauna Gaban ta. "Mummy duk tana hankalce dashi saidai ta nuna tamkar batasan da zaman mutum a wajen ba. "Cikin dashashshiyar murya omar yace mummy.. Mummy kusan 3tyms yake kiran sunan ta Amman ko uffan beji tayi ba. "A hankali yace mummy dan Allah kiyi hakuri....mummy CE tayi saurin katse shi cikin tsawa tace omar matukar ba takardar imaan zaka bani ba banason sake jin wata kalma daga bakin ka, omar hankalin sa ya sake tashi shidai harga Allah beji zai iya sakin imaan ba. "Jiki a sabule ya tashi yabar wajen sannan ya wuce side dinsa, yazo ficewa a falon kenan cikin daga murya yaji mummy tace INA fatan kana da naka gidan koh? Daga haka bata sake cewa komai ba. "Omar yyi tsaye bakin kofa yana nanata abunda mummy tace shin me mummy take nufi bazai zauna a gidan bane kome? Kamar daga sama yaji mummy ta sake cewa abunda zuciyar ka ta fada maka shi nake nufi dan haka sai ka daina tantama kabar mana gida. "A firgice omar ya dago idanun sa da suka gama zama jaaa sbd tsananin tashin hankalin da yake ciki yana kallon mummy da mamaki yanzu har bacin ran daya sata ya zamo har gidan ma bazata barshi ya zauna ba? Shi da yazo da niyyar zama har sai an bashi Matar sa? Bashi da wani zabi dole ya canja akalar tafiyar tasa zuwa hanyar fita dan baiso ya sake janyowa kansa wani lefin.
"Koda omar ya koma gida kasa tabuka komai yyi ga wata irin yunwa dake addabar sa tunowa da kajin daya siyo dazu ne ya koma mota ya dauko saidai koda ya daukesu sai yaji kwata2 bayason cin su don wadda yasiyo dominta bata nan, haka ya juya ya mikawa me gadi kazar sannan ya koma falo. "Wayar shi ya dauko ya kunna vedion daya dauki imaan ranar da take rawa yyi sanna ya fara kallo, ganin ta tana rawa shiya gusar masa d Rabin tashin hankalin da yake ciki. "Kamar yanda yasan imaan dason shan yogurt haka ya samu kansa da zuwa fridge dan shima ya sha. "Guntun da imaan ta rage shiya dauka sannan ya dawo kan kujera ya zauna yana sha yana kallo idan kallon ya kare ya sake kunnawa karshe ya shiga cikin gallery dinsa nan ya fara duba pictures din daya yiwa imaan batare data sani ba yawanci kuma Wanda take cikin kananan kaya ne, dake dare yyi sosai haka ya kashe wutar falo ya haura sama bisa ga mamaki ya samu Kansan da shiga dakin imaan kan gadon ta ya haye sannan ya rungume pillow tsam ya matse a jikin sa yana shakar kamshin da imaan ta bari. Da tunanin imaan kala2 ya samu damar yin bcci.
********
Tun 7 omar yyi shirin sa tsaf. Sannan ya fito bayan ya rufe ko'ina a gidan kafin ya wuce wajen motar sa. "Driving yake a hankali burinsa yaje yasa imaan a idon sa dukda yasan a yanzu imaan babu Wanda ta tsana tamkar shi duba Ga irin kallon data watsa masa a karo na karshe da rabuwar su jiya. Amman hakan be hana zuciyar sa azalzala dason kasancewa da ita ba. "Shi kadai a mota yana tunanin imaan har ya isa gidan su. "Bayan yyi parking sannan yyi hanyar falo, yasan ko kusa yanzu kam mummy basu tashi ba. "Dan haka ya bude kofar a hankali. "Dakin mummy ya wuce dan yasan bazai wuce anan imaan take ba. "Nan ma a hankali ya bude dakin. "Wata irin hamdala yyi ganin imaan CE ita kadai a dakin tana bcci. "Dan haka ya samu ya lababa ya isa gaban gadon. "Saida ya ajiye jakar shi cikin sanda ya bude bargon da imaan ta lulluba a hankali cikin dabara ya fara matsawa har jikin sa ya hade Dana imaan sannan ya kwanta a hankali, bayan ya kwanta ya dan jawo hannun ta zuwa jikin sa, imaan cikin bcci tayi juyi batare data sani ba ta aza hannayen ta gaba daya kan omar a azaton ta koh pillow ne dan itama jiya da kyar tayi bcci tana ta tunanin halin da omar yake ciki ta kuma rasa dalilin damuwar da tayi a kansa. "Omar kuwa yana ganin ta aza hannayen ta kansa ya sake shigewa jikin ta, rufewa bargon yyi sannan ya sake matseta a jikin sa take ya saki wata wawiyar ajiyar zuciya cikin lkci kankaki bccin daya rasa jiya ya kwashe shi a yanzu cike da kwanciyar hankali.
Nuceey luv😘